Ƙa’idojin Amfani

Wannan shafi zai yi bayani ne game da ka’idojin amfani da taskar Hikaya. Don haka yana da muhimmanci mutum ya karanta shi da kyau.

A duk lokacin da mutum ke amfani da taskar Hikaya, to ya nuna cewa ya amince da duk ka’idojin da taskar ta gindaya na amfani da ita kenan.

Duk ka’idojin da Hikaya ta sanya, ta yi su ne ba don komai ba, sai kawai don inganta amfani da taskar da kuma kare sirri da martabar masu amfani da ita.

Hikaya ba ta amince wani ko wata ta shigo tarkar don muzanta wani ko wata ba, ko kuwa yin amfani da labari ko basirar wani ko wata ta hanyar da bai dace ba.

Kowa ya sanya labarinsa a taskar Hikaya, to ya nuna cewa ya amince da wani ya karanta ko ma ya aikawa wani don karantawa. Duk abinda mutum ya sanya a taskar, wani na iya gani kuma ya karanta har ma ya aikawa wani.

Idan baku bukatar wani ya karanta labarinku, to kada ku sanya shi a taskar.

Don karin bayani game da tsare sirrin marubuta har ma da sauran masu amfani da taskar sai ku ziyarci shafinmu na ‘Tsare Sirri‘.

Idan kuma kuna da wasu tambayoyi na daban ko shawarwari game da amfani da taskar, sai ku tuntube mu ta hanyar latsa nan ko kuwa ku je safin ‘Tuntube Mu’ dake menu a kasa da nan.