Skip to content
Part 5 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Tun bayan da suka ajiye Anty Ummy a gidan Anty Mansurah, suka dauki hanyar komawa gida, babu wanda ya kara furtawa dan’uwansa ci-kanka a cikinsu.

Tuki yake yi cikin natsuwa da kwarewa, yana wulgawa titi da titi, unguwa-unguwa, cikin nuna halin ko-in-kula da rashin damuwa.

Kauthar sai taji duk ta takura da zaman, saboda bata taba zama da shi a waje daya suka dauki fiye da mintuna biyar ba tare daya nemeta da magana ba.

Ita din sam ba ma’abociyar hira bace, shi yasa sau tari hirarrakinta da mutane ba ita take farasu ba, sai dai suyi mata jagoranci. Kuma dama can shine mai janta da hira din. Yanzu da yayi shiru yana gudanar da al’amuran rayuwarshi kamar bai san da wanzuwarta ba, sai ta nemi zaren kamawa ta rasa.

Lokuta fiye da goma tana daga baki da niyyar fara hira, sai ta rasa wacce zata kama, ta maida bakin ta dinke.

Suna gab da karasawa gida, kwatsam! wata mota ta kusa kai musu karo. Yayi kokarin kaucewa, motar ta kwace mishi. Ta tafi taga-taga kamar zata kifa, wani irin razanannen sauti mai kama da ihu ko kuka ya kwace mata, ta tura kanta tsakankanin cinyoyinta jikinta yana masifar rawa. Wani irin zafi take ji yana ratsa mata a kunnenta har cikin kwanyar kanta.

Likitarta tace a duk lokacin da hatsari irin wanda ya sameta tana karama ya kusa faruwa da ita, zata dinga tuna abubuwan da suka faru. Zata iya jin zafi da duk wasu abubuwa da taji a lokacin, _’trauma’_ da _panic attack_ ta kira hakan.

Bata san yadda aka yi ba sai jinta tayi a wani faffadan kirji mai kira da suffar girma irinta maza, wadanda Allah Yayiwa ilhama da baiwa a rayuwa. Kamshi mai sanyi na turarenshi yana ratsa mata hanci, sai taji natsuwarta data fara barinta tana dawowa da kadan-kadan.

Zuwa lokacin data dawo cikin hayyacinta, fuskarta tana cikin tattausan tafukan hannayen AbdulMalik, tayi sak! tana kallonshi cikin wani yanayi.

Tuni ya samu ya saita motar yayi parking dinta a bakin titi. Ya furzar da wani irin numfashi, gefen bakinshi yana dan motsawa cikin alamun murmushi, “there you are!”

Tayi gaggawar dauke idanunta daga kanshi tana kallon waje, amma yayi gaggawar kara sanya hannu ya dawo da kallonta gareshi, “hey! Look at me Kauthar! Only me… You are okay, kinji? You are safe!…”

Bata sani ba, ko salama ce? Ko kuwa jindadi? Ko kuwa duka ne? Ta saki wani kuka mai tsuma zuciya, ya kara janta ta koma cikin jikinshi. Kanta a dai-dai saitin zuciyarshi da take bugawa steadily, abinda ya dinga kwantar mata da kukanta kenan.

Bai furta mata komi ba, sai dan bubbuga bayanta daya dinga yi yana shushing dinta a hankali. A haka har kukan nata ya lafa.

Ya sanya hannu a cikin aljihunshi ya ciro hankici mai taushi, ya share mata hawaye da majinar da suka bata mata fuska. Yana kuma gamawa ya dora lebenshi a saman goshinta ya bata wata sumba data sanya taji jikinta ya dauka gabadaya kamar wadda aka jonawa lantarki.

Sumba ce mai nuna wasu al’amura data karyata a take. Gesture na nuna kamar yadda yace, she’s safe. Gesture dake nuna yarda da kauna da aminta. Abinda ya tsoratata kenan, ta janye daga jikinshi a sukwane tana kame-kame da karkade jikinta kamar mai kore datti.

Ya jima yana kallonta, ita kuma ta kasa hada idanu dashi, ya fitar da wani irin sauti daga can kasan makoshinshi mai kama da frustration, ya tashi motar ya ja.
Cikinsu babu wanda ya kara yin magana har suka karasa gida.

Yana yin parking din mota ta warci jikinta zata fita daga motar. Yayi caraf! ya kama hannunta.
Tayi kokarin janyewa amma abin ya faskara, saboda rikon mace da namiji ba daya ba.

Yace, “guje-gujen da kike yi na menene wai Kauthar? Tserewa da kika yi kika bar kasar bai isheki ba, sai kin sake nesanta kanki dani?”.

Ta dan tsaya da kokarin kwatar hannunta da take yi. Sai kuma ta dan hade fuska, ta juya tana kallonshi duk da cewa ta kasa hada idanu dashi,
“Ban gane abinda kake fada ba?!”

Dan murmushi ya saki, “duk wani kauce-kauce da hade fuska da kike yi Kauthar, ba shi zai sa kuma ya hana abinda kike so da gujewa ba! Gwara ma ki tsaya ki fuskanci koma menene head on, zai fi miki!”

Ta kuwa kara murtuke fuska, taga alamun abubuwan nashi ba na wasa bane. Wasa yake mata da hankali yana sanyata tana kaucewa daga kan hanyar data dauka wadda zata fissheta, “ban fahimci abinda kake fada ba, kuma bana neman karin bayanin ka fahimtar dani. Don haka ka sakar min hannu.”

Bai yi musu ba ya saki hannun, “zamu ji ai mu gani Kauthar, with time…”

Ta murguda baki, “kai dai kasan abinda zaka ji ka gani, kuma wallahi sai na hadaka da Anty Ummy! Ai wallahi banyi zaton kai dan iska bane, kana kama hannun mutane bayan kana da mata!.”

Dariya ya saki mai sauti har da dukan sitiyari. Na dan lokaci, tsayawa tayi kawai tana kallonshi saboda yadda dariyar tashi ta kayatar da fuskarshi sosai.
Yace, “ita Anty Ummy din taki idan ta isa, don Allah ta kwaceki a hannuna duk ranar dana damkeki… Maza je ki gaya mata, ga fili ga mai doki…!”

Bata kara cewa komi ba, ta bude kofar tana yan guna-guni da ita kanta bata san me take fada ba, ta fita daga motar. Ko kallonshi bata kara yi ba ta fada gida a sukwane. Bata dakata a ko’ina ba sai tsakiyar dakinta.
Ta maida kofar ta rufe, goshinta wani irin kaikayi taji yana mata inda AbdulMalik ya sumbata. Ta kai hannu tana dan sosawa, bata san murmushi take yi ba sai data tsinci fuskarta a cikin madubi. Tayi gaggawar kawar da murmushin, zuciya na duka da lagude a tsakiyar kirjinta. Watakila dai daga ita har AbdulMalik din basu da lafiyar kwakwalwa ne.

To idan ba mutane marasa saitin kai ba, wa zai iya jin abinda take ji game dashi? Wa kuma zai yi abinda shi din yake yi, duk da cewa dai bata gama fahimtar inda ya sa gaba ba?!

Takawa tayi zuwa bakin gado ta zauna bayan tayi jifa da duk kayan dake hannunta. Anan ta dauki alwashin fita daga duk wata harka tashi, tana ganin abinda zai fi fissheta kenan.

Kamar kuma yadda tayi alkawari, haka ta gudanar har zuwa lokacin da aka fara gudanar da al’amuran biki.

Sati guda cif aka dauka ana gudanar da biki. Ciki da wajen garin Abuja babu inda bai dauka ba don kuwa daga Anty Aisha har Alhaji Abdallah sanannun mutane ne a Nigeria ma baki daya.

An dauki amarya an kaita gidan aurenta dake Lagos. Su Kauthar sune gaba-gaba. Yar gaban goshin amarya.
Da kyar da jibin goshi aka rabata da Anty Ummy lokacin da suka tashi juyawa zuwa Abuja. Haka suka rabu da juna cikin matsananciyar kewa kamar kada su rabu. Duk da haka bayan komawarta gida, ta kan je mata hutun karshen mako musamman da AbdulMalik din ya tafi wani taro a kasar Australia ya barta a gida saboda laulayin ciki.

Kauthar taje ta mata sati biyu tunda suna hutun karshen semester a lokacin.
Wani irin wahalallen ciki ne ta samu mai dan banzan laulayin wahala, ruwa wannan idan ta sha sai an ci sa’a yake zama ba tare data amayar dashi ba.

Shi yasa cikin dan kankanin lokaci tabi ta rame ta fita a hayyacinta.
Kauthar ita ta zauna tayi zaman jinyarta har zuwa lokacin da AbdulMalik din ya juyo gida.

A ranar da zai dawo tayi kokarin barin garin, amma Anty Ummy ta hanata. Tausayinta da halin da take ciki yasa ta hakura zata kara mata sati daya kamar yadda ta roketa.

Ranar da zai dawo kuwa yini tayi a daki abinta. Bayan ta gama yiwa Anty Ummy din duk abubuwan data saba yi, ta tayata suka shirya abinci da lemuka na tarbarshi, sai ta ware daki abinta. Duk da rashin jin dadin jikin data keyi, hakanan Anty Ummy ta lallaba ta tafi filin jirgi ta taryoshi. Tana jin lokacin da suka dawo, amma bata yi azamar fita ta mishi sannu da zuwa ba duk kuwa da yadda zuciyarta take kada mata gangar ta aikata hakan.

Tana tunasar da ita lokuta ne masu tsayi rabon data sanyashi a kwayar idanunta. Amma ta danne, tayi ta maza. Maimakon ta tashi ta falla da gudu, sai ta janyo wayarta ta hade da headphone wanda yake hade da hearing aid dinta, ta jona a kunne tana sauraren karatun Al-Qur’ani mai Girma.

Sai da tayi sallar isha’i sannan ta fita. Shima saboda kiran wayar da Anty Ummy tayi ta loda mata ne a waya sannan.

Tuni har kukunta ya shirya musu abincin dare akan dinning table. Ta samesu su biyun akan teburin suna cin abinci.
Anty Ummy ta canza shiga zuwa wata lafiyayyar Arabian gown baka wadda ta matukar karbarta musamman saboda farin data kara a yan kwanakin. Anyi sa’a ta fara cin abinci yanzu.
Shi kuwa gogan saye yake da simple jeans da shirt na zaman gida. Sunyi kyau sosai, sun kuma dace, kana ganinsu kaga the perfect couple.

Ta ja kujera dake fuskantar Anty Ummy ta zauna tana dannawa zuciyarta zagi da kiran kanta da duk bahagon sunan daya je mata. Saboda bai kamata taji ounce of zafin zuciya ba kawai saboda ta gansu a hakan. Sam bai kamata zuciyarta ta kitsa mata wani abu ba don kawai Anty Ummy ta canza kaya ba. Ko kuwa kyawun da tayi, ko shi wanda yayi. Wannan aikine na shaidani abin jifa ba wani abu ba. Don haka ta saki zagin da take jefawa kanta, ta fara a’uziyyah.

Tunda ta shiga falon, kallonta suke yi su duka har ta samu wajen zama. Ta kalli inda yake, ba tare da tayi magagin hada idanu dashi ba, tace, “Yaya Abdul sannu da zuwa, ya hanya?”

Ya amsa mata cikin basarwa ba tare daya kalli inda take ba. Abinda taso yayi kenan, amma me yasa taji ranta yana mata kuna?

Bata kara cewa komi ba sai plate data janyo ta bude flask din abinci ta fara zuba fried rice din da aka yi.
Anty Ummy ta nuna mata wani flask din, “akwai fate idan zaki sha.”

Tayi dan murmushi a sanyaye, “ina zan iya shan wannan faten? Ai sai dai ke!”
Dariya kawai tayi.
Hakanan ake mata faten, daga manja sai taruhu da dan maggi da yakuwa, ranar farko da Kauthar ta sha sai da taji kanta yana juyawa saboda tsabar yaji da tsamin yakuwa.

Suka cigaba da cin abincin, in banda karar cokula da yar hirar da ma’auratan suke yi lokaci zuwa lokaci baka jin komi.

Ko cikakken cokali biyar bata yi ba ta ture plate din gefe ta ja gorar lemun pulp na lemu ta bude. Anty Ummy tace, “ba dai har kin koshi ba?”
Baki ta dan tabe, “ban jin yunwa ne, kinsan na ci doughnut dazu sosai.”

Bata kara cewa komi ba, sai itama bata ce komi ba. Tana gama shan lemun ta dauki gorar ruwa ta musu sai da safe ta wuce dakin da aka yi mata masauki.

Kwana biyu suna rayuwa kamar ma bata cikin gidan, ta daga sosai da fita daga dakinta, sau tari ma sai dai Anty Ummy taje dakin nata idan AbdulMalik ya tafi wajen aiki, su yini suna hira. Sai da yamma idan ya dawo sannan suke rabuwa.

Ita dashi ya zama sai kallo daga nesa, yawanci da safe kafin ta tashi daga barci ma ya fita, da dare kuwa a tsaitsaye suke gaisawa, taci abinci ta tashi ta basu waje.

Kwanakinshi hudu da dawowa, cikin dare yunwa ta hana mata sakat, ta dinga juye-juye a kan gado amma ta kasa komawa barci. Ba shiri ta tashi ta fita neman wani abu bayan ta dora doguwar riga akan vest da 3-quarter wando dake jikinta.

Ko hula bata dora akanta ba da aka yiwa kitson kalba, ta kwanta tayi luf har doron wuyanta.
Ta fita falon, gidan yayi shiru babu hayaniyar komi, falon yayi duhu saboda hasken fitilu da aka kashe, dan hasken kadan ne kila wanda yake shigowa daga waje.

Bata fahimci daga inda hasken yake ba, sai data kai tsakiyar falo sannan ta fahimci daga laptop din AbdulMalik ce dake ajiye akan coffee table, shi kuma yana zaune akan kujera da farar singileti a jikinshi da wandon 3-quarter.

Ta dan yi turus lokacin da suka hada idanu. Babu damar ta juya tayi baya kamar yadda taso tunda ya riga ya ganta. Sai kawai tayi ta maza, ta dauke kanta ta wuce kicin. Tana jin idanunshi a kanta har ta shige.

Sai taji ma gabadaya bata jin yunwar da take ji, ta bude firjin ta dauki cupcakes guda biyu ta tura hakanan ta kora da ruwa.

Har lokacin yana zaune yana aikin da yake yi, ta sake wucewa ta gabanshi ta wuce.

Har ta bashi baya, ta jiyo sautin muryarshi a bayanta, “so this is it?!”

Ta juya da sauri saboda a bazata maganar taje mata. Bata ankare ba taji ta kaiwa faffadan kirjinshi karo. Ta ja da baya da sauri tana zare idanu don bata san lokacin daya tashi daga inda yake ba har ya taka zuwa inda take.

Ya zuba mata idanunshi da suka shanye suka yi ciki, launinsu ya canza, dauke suke da alamun gajiya da barci da wani abu da bata bukatar ta ayyanashi a cikin ranta, don ma kada ya zama gaskiya.

Taku biyu ya sake yi ya matsa wajenta, kusancin yayi yawa, har tana iya jin numfashinshi dake sauka akan fuskarta mai dauke da wannan citrussy kamshin da take matukar so a tattare dashi.
Ta yi taku biyu baya, nan ma ya sake binta. Sai tayi ta maza ta tsaya, standing her ground, don kada ya gano lagonta.

Murya a shake ya kalleta, “abinda kike yi a ganinki dai-dai ne Kauthar?”

Taji wani yarr! Tun daga saman kanta har yatsun kafarta jin sunanta daya fita daga bakinshi da tayi.
Ta yatsina fuska, “ban gane ba? Me nayi kuma?”

Yayi kwafa, “kin fini sani ai! Kin fi son kullum in kasance cikin tunaninki Kauthar! Kin fi kaunar kullum barci ya dinga kaurace min saboda ke! Kin fi son… kodayaushe in kasance cikin rashin sukuni saboda ke!! Kauthar har sai zuwa yaushe ne zaki bar raina da zuciyata su huta ne?”

Kalamanshi kokarin sanya mata ciwon kai suke yi, ta kasa fahimtarshi da inda yasa gaba. To ma, me ya kawo wannan maganar a tsakaninsu?

Tace, “ni fa Yaya Abdul wasu maganganu kake yi da bana fahimta. Kuma ma ni meye hadina da barcinka da rashin sa? Tunda Allah Yaji Ya gani ni ban ce kar kayi ba? Kuma for the record, bana son irin abubuwan nan da kake yi mun da kalaman dake fita daga bakinta… Me kake so matarka ta daukeni idan taji haka? Don haka gaskiya ka daina, bana so. Zan fi son daga yanzu har in gama zamana in koma inda na fito, kawai kaci gaba da nuna kamar baka sanni ba, zai fi mana!”

Tana gama fadin haka da sauri ta juya zata wuce dakinta.
Ya sanya hannu ya fincikota ya juyar da ita tana fuskantarshi, ta juya tana watsa mishi harara, baki a dage tana shirin fara tsiwa, sai tayi sak! sakamakon jin wani abu mai kama da almara yana faruwa da ita.

Bakinta ta tsinta dumu-dumu cikin nashi!
Hasbunallahu wa ni’imal wakeel!! Tsabar gigita sai taji duk wata jijiya ta jikinta ta tsinke, kamar anyi freezing dinta a wajen, ta kasa kwatar kanta.

Bai ma san halin daya jefata a ciki ba, yaci gaba da kissing bakinta passionately, yi yake kamar addict wanda ya jima bai samu sigari ba.

Ya dauki lokaci mai tsayi, sai daya ji kamar numfashinta yana kokarin barinta kafin ya hakura, ya saki lebenta with one last kiss, idanu a lumshe, ya hade goshinta da nashi yana sakin wani wahalallen numfashi kamar wanda yayi tseren mil.

Sai da numfashinshi ya daidaita kafin ya saketa, ya dan ja da baya yana kallon tsakiyar idanunta da har lokacin suke a bude tarwai, tana zaresu cikin gigita.

Yaja numfashi ya ajiye, “ki gama duk guje-gujenki, ko kin ki, ko kin so Kauthar, I na sonki, zan kuma fada a gaban ko waye. Kici gaba da karyata kanki ke kuma if it makes you feel better, ni dai nasan alkawarin Allah sai ya tabbata a kanmu. Don haka idan ma zaki nemarwa kanki salama…,” ya kara matsawa zuwa inda take, “… ki nema!” ya furta hakan a saitin fuskarta.

Suka yi kallon-kallo ita dashi na wani dan lokaci, sai kuma ya saki wannan miskilin murmushi da a lokacin ya sanya taji da zata iya da hannu zata sanya ta makeshi saboda haushi da takaici da suka mata rubdugu, “boyewar da kike yi da fakewa da Anty Ummynki da kike yi duk ba dabara bace, kamar yadda nace, alkawarin Allah sai ya tabbata a kanmu. Zan baki zuwa gobe, zan ji daga gareki… Sai na ganki goben!”

Ba tare daya bari ta sake cewa komi ba ya tattara kayanshi ya barta anan a tsaye kamar wata sassaken bishiya.

Bata san ya aka yi kafafunta suka iya kaita daki ba, ta zube a tsakiyar dakin hannu aka. Data rasa abin yi sai kawai ta saki kuka wanda ta rasa dalilinshi.

Washegari Anty Ummy sai ganinta tayi ta gara akwatu, shi gogan ko tashi daga barci bai yi ba.
Tambayar duniya tace babu abinda aka mata, ita kawai gida zata tafi. Jirgin farko da ita ya tashi, sai Abuja.

Bata kara komawa Lagos ba har yau dake motsi.
Ba a kuma kara tado zancen so da AbdulMalik ya furta yana mata ba. Taji dadin haka iyaka jindadi kuwa, don kuwa duk rashin ta idonta da burbushin abinda take ji game dashi, ba zata iya cin amanar Anty Ummy ba duk gumu.

Sai dai idan abinda take ji a game dashi ya kasheta murus har lahira!!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.4 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 4Kauthar 6 >>

3 thoughts on “Kauthar 5”

  1. Subhanallahi! Wannan kauna ta jawoni da yawa, gaskiya Yaya Abdul baka kyauta ba ta wani bangare, amma dai ta wani baren ka burgeni sosai

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×