Skip to content
Part 2 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

A sauran kwanaki ukun da suka biyo baya, Anty Ummyn da kuma AbdulMalik sun kasance suna manne da juna a koda yaushe, ko dai ta waya ko kuma shi AbdulMalik din yazo gidan. Tun wannan haduwar ta farko da suka yi basu sake haduwa dashi ba, bata ba kowa damar hakan ba duk kuwa da yadda Anty Ummy take mita da korafin taje su gaisa da shi ko kuma ta tayata kai mishi kayan motsa baki da take bata lokaci mai yawa a rana tana shirya mishi da kanta, musamman doughnuts da lemun kunun aya da yake matukar so.

Hakan ba shi yake hana a yawancin ranaku idan sun raba dare suna hirar da suka saba, -wadda take matukar kai Kauthar karshe saboda a dakinta ake yinta-, a bada sakon gaisuwarshi ba. Bata sani ko fadar Anty Ummyn bace, ko kuwa dai da gasken yana fada, tana dai cewa ta karba ta kuma cigaba da gudanar da harkokinta.

A haka har ya juya zuwa Lagos inda yake gudanar da ayyukanshi, kuma can za a kai Anty Ummyn bayan aurensu.

Ranar da zai tafi ba karamin kokari Kauthar tayi ba wajen kawar da kanta, bata yabawa Anty Ummy magana ba.

Da yake ya shiga har main falonsu ya gaida Anty Aisha da Daddy tunda yana gida a ranar lahadin, Anty Ummy ta kasance a katarinshi, kamar wadda bata so kuda ya tabashi ko yaya.

Lokacin daya je ita tana ma daki abinta, daga ita sai pajamas mai hotunan Mickie Mouse saboda tunda garin Allah Ya waye bata sauka kasa ba. Abinci ma sai waya tayi yan aiki suka kai mata. Tana zaune akan desk dinta a gefen tagar dakin, waje na musamman data tanada saboda karatu. Ta baza manyan text books da desk top dinta da lap top tana ta latse latse da bincike akan abinda Allah kadai Ya sani.

Mahmoud ya tura kofar dakinta ya shiga da sakon cewa Abbu yace taje su gaisa da AbdulMalik kafin ya tafi. Ta turo baki, idanunta masu saye da farin gilashi manne akan lap top dinta, yatsun hannu na danna keyboard din furiously. Ba tare data dakata ko da wasa ba, tace yaje yace tana mishi fatan Allah Ya tsare hanya, saboda aikin gidan da aka basu a makaranta take yi.

Bai ce komi ba ya juya abinshi bayan ya maida mata kofar dakin ya rufe, sanin halinta na kafiya da rashin tankwasuwa yasa bai ma tsaya wani bata bakinshi ba.

Ba a jima ba kuma taji an sake bude kofar dakin, kafin ma ta juya taga ko wanene kamshinta ya bayyanata, Anty Aisha ce. Don haka taki juyawa balle ma ta kalleta.

Ta coge a bakin kofa tare da harde hannu a kirji, tace, “ko jarabawa kike rubutawa ai kin dan ajiye haka nan ki sauko kiyi sallama da shi, Kauthar. Ko babu komi yaci darajar Faheema mana!”

Anty Aisha ta santa ciki da bai kamar bayan hannunta. Wasu lokutan har mamakin yadda take fahimtarta fiye ma da yadda ita kanta ta fahimci kanta take yi. Tasan yadda amfani da Anty Ummy a kodayaushe yake saurin sauko da ita ta aikata abinda bata da niyar aikatawa, amma bata tunanin yanzu hakan zai yi amfani. Koda wasa bata kaunar haduwa da AbdulMalik musamman a yadda ta wuni a ranar a waje guda, kanta da ranta a cunkushe suke gabadaya.

Ta dan yamutse fuska da hanci, “yanzu? Gaskiya yaje kawai Allah Ya tsare hanya, akwai abubuwa da yawa da nake so in karasa kafin dare yayi!”

Ta kara gyara tsayuwarta, “duk da haka, ba zaki iya sadaukar da abinda ya gaza minti biyar ba a cikin lokacin naki? Ko akwai wani abu da yake tsakaninki da AbdulMalik ne wanda bamu sani ba? Nasan jininku bai hadu dashi ba, amma hakan ba excuse bane da zai hanaki ki dinga mu’amalantarshi ba. Nan gaba ko baku so dole dai zaku dinga zama a karkashin inuwa daya, ba gwara ku fara tun yanzu ba?!”

Sanin cewa wannan yana daya daga cikin fadan da ko tace zata yi, ba zata yi nasara ba, yasa ta mike a dan zafafe ta ja zumbuleliyar hijabinta da take sallah wadda ta nadeta tsaf ko tafin kafarta baka gani, ta fita buguzum-buguzum kamar zata tashi sama, har tana hadawa da buga kafa a kasa ta sauka kasan.
Anty Aisha ta bita da kallo kawai tana gyada kai kamar wata kadangaruwa kafin tabi bayanta.

Da saukarta kasa, da gaisuwa da sallamar da tayi dash, ba a rufa cikakken minti daya da rabi ba, ta tashi ta koma sama kamar wadda aljanu suke bibiyarta.

Anty Ummy ta hau saman bayan dan lokaci tace mata zata rakashi airport tunda daga nan kai tsaye can zai wuce, ko zata rakata? Ta girgiza mata kai. To itama sai bata zurfafa ba ta juya ta tafi.

Tunda ta dawo kuwa bakinta yaki rufuwa da labarin kannen AbdulMalik din, Na’imah da Malika, da yadda suka saba dasu cikin dan kankanin lokaci. Kai kawai ta dinga gyada mata tana kuma binta da eh da a’ah har ta gaji tayi shiru kawai tana kallonta.

Bai kara waiwayarsu ba sai da aka shafe fiye da wata daya da rabi, duk da cewa koda yaushe suna manne a waya, soyayyarsu da shakuwa tana karuwa a koda yaushe.

A sati na karshe da zai cike watanshi biyu cif da komawa birnin Ikko, ya zo hutun karshen mako ranar juma’a da yamma, amma bai je gidan nasu ba sai washegari da yamma.

Ya dira cikin dakakkiyar shaddar shi wagambari baka, bai sanya hula ba sai tattausar sumarshi da sajenshi da suka kwanta mishi a fuska luf, duk karyar mai hassada bai isa ya kalleshi ya kawar da kai ba tare daya sake daga kai ya kalleshi ba.

Anty Ummy ta rasa inda zata sanyashi taji dadi a cikin ranta, ta daure dai taje sun gaisa dashi sama-sama kafin ta koma daki.

To haka al’amura suka cigaba da tafiya har zuwa wani lokaci mai tsayi. Ita a karan kanta ba tare da kowa yayi mata fada ba, ta ga cewa abinda take yi bata kyautawa. Tasan Anty Ummy ta gama dago cewa bata son AbdulMalik, amma bata taba nuna mata hakan ba ko kuma ta nemi tursasata yin abinda bata so ba. Don haka taci damarar daurewa ranta, ko ba don komi ba, don farin cikin Anty Ummyn.

Hakan kuwa ba karamin faranta ranta yayi ba, ta nuna mata jindadinta matuka.

A kokarinta na kulla zumunci da shakuwa a tsakaninsu, al’amarin da babu wanda ya shiryawa a cikinsu su dukansu ya faru.

Wani al’amari da bai kamata ya faru ba.

Wani al’amari da babu wanda yasan idan faruwarshi alkhairi ce ko akasinsa……

Anty Ummy ta fara zuwa wajen aiki a kamfanin Julius Berger, inda zata yi transfer zuwa can sashensu na Lagos din idan lokacin aurensu yayi.

Wata ranar juma’a bata dawo da wuri ba, don kusan a lokaci daya ma suka shiga gidan ita da AbdulMalik wanda ya zo duba mahaifiyarshi data kwanta jinya kwana biyu.

Ta nemi Kauthar da taje ta taya shi hira kafin ta kimtsa sai ta samesu. Babu musu ta tashi, arabian gown ce baka a jikinta mai hawa biyu da kwalliyar duwatsu purple a jiki, ta dauki dan karamin bakin gyale mahadin rigar ta yana a kanta kafin ta sauka kasa. Tasan yan aiki sun kai mishi ruwa da lemu don haka sai ta wuce inda aka saba ajiyeshi. Ta hangi Mahmoud da Lukman dan shekara biyu da rabi suna wasa a farfajiyar gidan, suka daga mata hannu ita kuma ta wuce.

Kamar koda yaushe, ta sameshi a falon yana ta latsa waya, dayar kuma manne a kunnenshi yana magana cikin tattausar muryarshi. Ta samu kujera mai kallonshi ta zauna, ta ja gwangwanin maltina ta bincire hancin ta kai baki ta kurba. Sanyi da dan daci-daci suka mata karo har sai data dan lumshe idanunta in satisfaction.

Lokacin data bude idanunta, sai ta tsincesu tsamo-tsamo cikin nashi, duk kuwa kamashi din da tayi yana kallonta bai sa ya janye ba, sai ma zama daya kara gyarawa yana kallonta kamar wata abun kawa yana kuma cigaba da amsa wayarshi.

Tayi wuri-wuri da idanu cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa, kafin ta sauke idanun nata akan wani babban frame dake bayanshi.

Abinda ta tsana kenan a tattare dashi, ta kuma kasa sabawa. Wadannan idanun nashi da idan ya kura maka su sai kaji kamar kayi me. Allah kadai yasan iyaka abubuwan da take ji a cikin jinin jikinta idan suka hada idanu dashi, bata son jin su, bata kaunar jin su koda wasa, saboda suna jefata cikin wani irin yanayi da ita kanta bata san menene ba.

Ya kashe wayar ya ajiye akan teburi yana jifanta da wani irin kallo yana wani murmushin gefen baki, “Hajiya Kauthar Nigeria, barka da yamma!”

Ta turo baki gaba tana watsa mishi harara kasa-kasa, “ni wallahi Yaya Abdul ka daina kirana Hajiya bana so!”

Ya saki wata irin sassanyar dariya, “to naji Allah Ya baki hakuri, wani irin suna kike so in kiraki da shi?”

Kafin ta daga baki ta bashi amsa, wayarshi tayi pinging alamun shigowar sako, ya sanya hannu ya dauka tare da maida hankalinshi ga wayar. Haka kawai taji ta kulu iya kuluwa. Haka hirar tasu take kasancewa a yawancin lokaci, fiye da rabin lokuta a daga waya da tura sakonni take karewa.

Ta turo baki, “wai haka kake yiwa Anty Ummy ne a ko yaushe?”

Ya dan daga kai ya kalleta a nutse, “me nake yi mata?”

Ta yatsine fuska, “ka kama waya kana latsawa mana! Hakan fa yana nuna kafi muhimmanta waya a kanta kenan!”

Ya kalleta da mamaki, sai kuma ya saki wani irin murmushi. Ya dauki kan wayoyin nashi duka biyun ya kashe ya jefa su a aljihu, “da gaskiyarki kuma! To na daina daga yau in shaa Allah!”

Sai tayi murmushi tana gyada kai, ta dauki maltina ta kai bakinta, “yauwa ko kai fa!”

Kallonta ya cigaba da yi har sai data tsargu, ta kalleshi a darare, “wai meye?”

Kai ya girgiza yana murmushi, “babu komi! Kawai dai ina mamakin yadda kike iya shan maltina hakanan ne”

Ta saki yar dariya mai burgewa, shima sai fuskarshi ta kara fadada da fara’a ya tsaya yana kallonta.
Tace, “Audu ma haka yake cewa!”

Take dan murmushin fuskarshi ya dauke, ya dan rankwafo daga kan kujerar ya harde hannuwanshi akan gwiwarshi., “waye Audu kuma?!!”

Tace, “cousin din Anty Ummy ne.”

Kafin ya kara jefa mata wata tambayar, Anty Ummy ta shigo dakin tana rangajin tafiya mai cike da daukar hankali, hakan bai sa ya dauke idanunshi daga kan Kauthar ba da ita kuma nata kallon yana ga Anty Ummy tana jefa mata murmushi.

A gefen AbdulMalik ta zauna, ta kalleshi tana jefa mishi hararar wasa da kauna, “me Anty Ummy tayi ake ambatar sunanta? Wato yanzu kun fara hadewa mutane kai ana musu wariyar launin fata, har gulmarsu ake a bayan idonsu ko?!”

Kauthar dariya ta kyalkyale da ita, shi kuwa ya juya yana jefa mata wani miskilin murmushi, ya kai hannu ya dauki kofi mai cike da lemu ya kai baki ya kurba.

Kauthar tace, “laa, Anty ba wata magana da muke yi a bayan idanunki, kawai dai ina mishi zancen Audu ne da yadda yake mun fadan shan maltina zallanta a haka. To menene a ciki wai? Ni nafi sonta a haka, sam bata yi mun dadi da madara.”

Yace, “aikuwa dai ya dace ace kin koya, don naji ance zallan maltina bai kamata mata suna ci ba musamman ma ga wadanda suke a shekaru irin naki.”

Haka kawai taji maganar tashi ta mata nauyi, sai ta basar kawai ta sunkuyar da kanta.
Ganin hankalinshi ya karkata ga Anty Ummy, yasa ta tashi sadaf-sadaf kamar barauniya ta salube daga dakin. Ranta yana mata wata irin suya, sai take ba kanta uzurin cewa haushin da taji bana komi bane face na yadda suka manta da wanzuwarta a wajen kamar bata nan, har ma basu san da lokacin data tashi ba.

Bata kula da satar kallon da AbdulMalik yake jifanta dashi ba. Bata kula da kallon daya bita dashi ba lokacin data tashi har ta fita ba. Bata kuma lura da murmushin daya saki ba yana girgiza kai.

A washegarin ranar ya koma Lagos. Wannan karon kam duk yadda ta dinga kaucewa, sai da Anty Ummy tayi nasarar janyeta suka tafi rakiyarshi airport.

A lokacin ne ta taba haduwa da kannenshi matan, suna da kani namiji Hashim, yana makaranta a lokacin.

Macece ita da bata da saurin sabo, haka kuma bata saba da mutane ba. Don ko a wancan lokacin, Kauthar bata da wata da zata nuna tace abokiyarta ce ko aminiya, sai dai Anty Ummyn. Hakane yasa duk sai abokan Anty Ummy dinne suka zama nata.

AbdulMalik suna gefe shi da Anty Ummy suna kara yin sallama, ita da su Na’imah suma suka ware gefe daya. Sai dai duk yadda suka so janta a jiki kasa sakewa tayi dasu. Tana jinsu suna hirar rashin sakin jikinta a mota bayan sun juya, ita dai bata ce musu komi ba sai murmushi data dinga yi.

Da daren ranar tana dakinta tana karatu da laptop dinta, taji wayarta tana vibrating a kan tebur din da take karatu.

Da mamaki ta cire gilashin idanunta tana kallon agogo, karfe daya ne na dare babu yan mintuna.

Mamakinta ba karamin ninkuwa yayi ba lokacin da taga sunan AbdulMalik yana tsalle ba.
Mamakin yasa ta kasa daga kiran har ya katse. Sai da aka sake kira ya kusa katsewa kafin ta iya dagawa.

Tayi sallama da murya kasa-kasa kamar mai tsoron a jiyo abinda take cewa, shima ya amsa mata da tashi muryar da tafi tata yin kasa ma, watakila cikin gajiya da barci.

Yace, “Kauthar kema baki yi barci ba kenan?”

Ta rasa abinda zata ce mishi, sai kawai ta amsa da “uhmn!”

Tana jin sautin murmushin daya saki, yace, “shine ko ki kira kiji yadda na sauka. Anya Kauthar?”

Tace, “to ai tun dazu naji kuna waya da Anty Ummy, hakan ya nuna ka na lafiya kenan. Sai nace ba sai na kira ka ba!”

Yace, “duk da haka! Idan kina min haka ai sai in ga kamar baki damu dani bane Kauthar!”

In tace maganar bata je mata a banbarakwai ba tayi karya, sai kawai ta basar ta hanyar yin dariya, “in damu da kai kamar ya Ya Abdul? Ka manta ni ba Anty Ummy bace?”

Yayi mayar mata da martani kasa-kasa muryarshi bata fita sosai.

Tace, “me kace?”

Yace, “nothing! Sai da safe!”

Sai ‘kit!’ taji karan katse waya alamun ya kashe. Ta bi wayar da kallo da mamaki zane a kan fuskarta, me hakan ke nufi ne? Sai ta daga kafada sama ta maida wayar ta ajiye ta cigaba da karatunta.

Don idan tace zata sanya mamakin abinda AbdulMalik din yayi ta tabbata haka zata kwana bata runtsa ba tana sake-sake, don ba a ranar ya fara ba, ba kuma a ranar zai gama ba da alama.

Mutum ne shi mai cike da bazata da bada mamaki. Kusan ko wasu abubuwa da zai gudanar zasu baka mamaki. Kamar na ranar dai. Ba wani cika yin waya suka yi da juna ba balle har ta kaisu ga yin kusancin da zai sanyasu yin waya a cikin dare ba, amma ga abinda ya faru.

*****

Sati biyu da haka ya sake waiwayarsu. Ta dawo daga makaranta misalin karfe biyar na yammacin ranar Alhamis, ta hangi motarshi a farfajiyar gidan.

Instinct na farko da yaje mata shine ta falfala da gudu zuwa inda yake, ta dai daure. Kafafunta har karo suke yi da tuntube lokacin da tabi ta kofar dakin bakin da suke ciki shi da Anty Ummy, so take yi ta fada dakin a sukwane tana ihun murna da farinciki. Ji take yi kamar taje ta kamashi tasa a cikin jikinta, ko ta sanyashi gaba tayi ta kallo kamar taswira.

Tana jin sautin dariyar daya saki, taji zuciyarta tana wani irin daka a cikin kirjinta, ba shiri ta jingina da bango dafe da kirjin nata saboda jin kafafunta ba zasu iya daukarta ba.

Ta lumshe idanunta tana girgiza kanta. Me yake damunta haka? Wannan AbdulMalik fa ba kowa bane face wanda Anty Ummy zata aura, wanda take matukar so da kauna, take ji kamar mahadin rayuwarta ne!. Me take shirin aikatawa ne?.

To amma abu ne wanda ita kanta ba zata iya fayyace shi ba, koda kuwa za a dora mata hancin bindiga a ka. Bata san ko menene ba, bata taba jin hakan tattare da kowace halitta ba tunda take a rayuwarta kuwa. Watakila hakan ko wani al’amurine daya saba faruwa a tsakanin mutanen da suka saba da juna.

Ta lallaba ta ja kafafunta ta wuce bangarensu tana mai kara tausasa kanta. Sai kuma taja tayi turus! A tsakiyar falonsu.

Katan-katan na gwangwanin maltina da na madarar ruwa ta peak suka yi mata maraba. Shake da tsakiyar falon wasu kan wasu, kamar a kanti.

Lukman na zaune dangargar a kasa yana diddikar madara, Mahmoud kuma ya taka hannun kujera yana kokarin zaro maltina.

Sau tari abubuwan bukata na gidan sai dai su wayi gari su gansu kawai ba tare da sun san wanda ya kaisu ba ko lokacin da aka kai.

Haka ya tabbatar mata da cewa ba daga Daddy ko Anty Aisha suke ba.

Ta gyara tsayuwa tana kallon Mahmoud, “wannan fa daga ina?”

Ya diro daga kan kujerar da gwangwani biyu a hannunshi, “Uncle AbdulMalik ne ya kawo yace na tsaraba ne, shine zan dauki rabona kafin Mommy ta dawo tace ba zan sha ba!”.

Yana gama fada mata ya juya da gudunshi ya fada dakinsu. Sai tayi sararo a tsaye a falon, hirarsu dashi a wancan zuwan da yayi tana mata yawo a ka…

Bata kara cewa komi ba itama ta taka matakalar bene zuwa dakinta ba tare data kara kallon inda kayan suke ba.

Wannan zuwa da yayi, bai koma ba sai da aka sanya ranar aurenshi da Anty Ummy. Watanni biyu kacal masu zuwa…

*****

Wani ihun kuka ya balle mata lokacin data gama tuno abubuwan da suka faru.

Ta tashi zaune dangargar a tsakiyar gadonta, hawaye na rige-rigen fita daga idanunta. Saboda tsabar kuka har idanunta sun fara tasawa, sai sakin ajiyar zuciya take yi.

Ta kara maida kallonta ga hotonsu ita da Anty Ummy a karo na barkatai.

Anty Ummyn data kasance tamkar yar uwa wadda suka fita ciki daya da ita..

Anty Ummyn data so ta, ta kaunace ta, ta kula da ita, a lokacin da duniya da mutanen cikinta suka juya mata baya…

Aurenta da AbdulMalik kamar cin amana ne ga kaunarsu da shakuwarsu da Anty Ummy.
Ba zata iya wannan abun ba! Ta ayyana a ranta tana juya kai.

Idan har Daddy ya rantse ya kuma kafe akan maganarshi, lallai ba da ita za ayi hakan ba.

Cikin sauri ta dira daga gadon, ta bude wardrobe ta ciro akwati ta fara loda kayanta a ciki.
Sai kuma ta mayar da akwatin, ta dauko wata simple doguwar riga ta sanya, ta yana mayafi a samanta. Karamar jakar purse kawai ta dauka a hannunta ta fita daga cikin dakin.

Tuni Daddy ya fita don tun dazu taji alamun fitarshi tare da escort dinshi.
Falon kuma babu kowa balle ta damu ko wani zai ganta. Babu ko waiwaye ta fita daga gidan ta mike titi sambal.

Me zata yi a gidan to dama? Cikin sati biyun dama take kokarin barinshi anyway, don haka ba matsala bace don ta rage adadin kwanakin data debarwa kanta.

Ba damuwa suka yi da ita ba, don haka ba damuwar zasu yi ba don ta kara gaba!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 12

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 1Kauthar 3 >>

3 thoughts on “Kauthar 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×