Skip to content

Kauthar | Babi Na Daya

4
(2)

Babban dakine mai fadi wanda yaji duk wasu kalolin kayan alatu na adon daki har ma da wasu wadanda idanu basu taba gani ba.

Kwance akan madaidaicin wani Italian bed mai rumfa, matashiya Kauthar ce a kwance tana shakar barcinta cike da kwanciyar hankali. Ta rufe jikinta rikif da bargo mai taushi, idan mutum ba zuba idanu yayi sosai ba, ba zai taba cewa da mutum a kwance ba saboda yadda tabi ta kannande a kan gadon kamar wata mage.

Kofar dakin ta bude, wani yaro dan kimanin shekaru hudu ya shigo dakin a guje, tsalle yayi ya dira a tsakiyar gadon ya fara jan bargon data rufa dashi yana kwala mata kira, “Adda! Adda!!”

Juyi tayi ta kara kudundunewa, ya cigaba da tabata yana kara sautin kwala mata kira.

Dan tsaki taja ta bude idanunta da suka yi alamun ja saboda rashin barci da kuma gajiyar data dauki kwana da kwanaki tana tarata, “menene wai Man, ba na fada maka kada ka shigo min daki ba yau?”, ta watsa mishi tambayar tana lumshe idanu cikin muryar data sarke da barci har bata fita sosai.

Ya turo baki gaba, “to ai Daddy ne yace kije!”

A take ta bude idanunta da sauri tare da tashi zaune dangargar akan gado kamar ba ita bace take kwance shame-shame akan gado yanzu-yanzu ba, ta zaro idanu, “daddy kuma? me ya faru ne again?!”
Yayi dan murmushi yana watso mata hakoran bakinshi da babu na gaba guda biyu saboda zubewa da suka yi, “na sani? Nima kawai cewa yayi ince kizo!”

Jiki a matukar sanyaye ta zura kafafunta kasa daga kan gadon, suka sauka akan tattausan rug carpet din dake shimfide malale a gaban gadon. Ta taka cikin tafiyarta ta nutsuwa zuwa gaban wardrobe dinta da take jikin bango ta bude ta zaro doguwar hijabi pink ta dora akan riga da wandon pyjamas dake jikinta. Lukman ya sauka daga kan gadon, ta kama hannunshi suka fita daga cikin dakin Lukman yana zuba mata labarai kamar wani radio mai jini, ita kam kai kawai take gyada mishi a sanyaye. Sam ta kasa samun kuzarin biye mishi suyi wasanni da hirarrakin da suka saba. Duk da tayi kokarin boyewa, amma can kasan ranta tunanin abinda Daddy yake son tattaunawa da ita take yi. Ba abu karami bane zai sanya Daddy ya daga baki ya aika a kirata musamman ba, duk yadda aka yi dai tasan magana ce mai matukar muhimmanci.

Suka bi matakalar bene suka sauka kasan falonsu, gidan shiru kamar yadda yake a kullum, idan ka dauke karan talbijin da kuma alamun motsi da take jiyowa daga can kofar kicin dinsu.
Suka bi wani dan siririn corridor har suka dangana da wata kofa, an dan sakayata. Ta tsaya a jikin kofar tare da kai hannu ta kwankwasa. Wata kamilalliyar murya mai cike da nutsuwa da haiba ta amsa mata. Sai data sauke ajiyar numfashi sannan ta tura kofar ta shiga ciki, kamshi da sansanyan sanyi suka daketa a take, ta juya tana wa Lukman alamun ya shiga shima, suna hada ido ya mata gwalo ya juya a sukwane ya bi ta hanyar da suka fito. Kwafa tayi a ranta tana tunanin abinda zata mishi idan Allah Yasa ta fita daga dakin lami-lafiya ba tare da wani sassa na jikinta, koma ranta sun bar jikinta ba.

Akan kujerar daya saba zama ta sameshi, ya harde kafa daya kan daya saye da farin gilashi na karawa idanu karfi a idanunshi, jaridar daily trust ta safiyar ranar rike a hannunshi yana karantawa.
Ta tsuguna kadan daga gefenshi, cikin murya kasa-kasa kamar wadda take tsoron yin magana ta gaidashi duk kuwa da cewa da asubahi lokacin da suka yi sallar safe kamar yadda suka saba, ta gaidashi.

Cikin muryarshi ta halin ko-in kula ya amsa mata. Daga nan wajen ya dauki shiru kamar babu wasu halittu dake wajen. Bayan motsin karan split babu abinda kake ji a wajen, sai Kauthar dake zubda ruwan zufa da zuciyarta dake bugawa tana tsalle tana gudu kamar dokuna na sukuwa.

Mahaifinta ne shi, amma a kullum kuma a koyaushe, kamar wasu bakin juna haka suke kasancewa. Babu abinda taki jinin ya faru kamar a ce mata yau gashi za a hadasu a waje daya ita da mahaifinta na mintuna biyar kacal.

Sai daya gama busar iska son ranshi kafin ya ninke jaridar hannunshi ya dora akan center table din dake gabanshi. Ya kalleta tare da ambatar sunanta cikin wannan no-nonsense muryar tashi, wadda take sa mutum duk rashin kunyarshi ya saduda ko bai yi niyya ba, “Kauthar!!”.

A matukar tsorace ta daga idanunta ta saci kallonshi, murya na matukar rawa ta amsa, “na’am,…. Daddy?!”

Yace, “yauwa, yaushe ne kika ce za ku fara yin exams dinku?”

Wani abu mai kama da mashi ya caki tsakiyar zuciyarta, ba tare da sanarwa ba, taji hawaye sun ciko idanunta suna kokarin zubowa, don haka tayi kasa da idanunta da sauri. Tambaya take yi a cikin ranta, wani irin uba ne bai san halin da diyarshi take ciki ba, tun daga yanayin rayuwarta, halin da take ciki dama abinda ya danganci karatunta? Anya a duniya akwai uba irin mahaifinta??!. Kamar ba shine mutumin da taje ta durkusa a gabanshi ranar da zasu fara jarabawa ta sanar dashi zata fara exams ya sakata a cikin addu’a ba.

Ta dake, a ranta tana karantawa kanta na dan lokacine kawai, don haka ta jinjina kai, tana mai kara karfafawa kanta gwiwa, ta daga baki tace, “ai mun jima da farawa har ma mun kusa gamawa!”
Yace, “ok, yaushe zaku gama exams din kenan?”

Tace, “nan da kwanaki shida!”

Yayi shiru yana jinjina kai kamar mai nazari, can ya gyada kai, “ok! Good!!”
Ta kara satar kallonshi cikin alamun tsoro, mai yake nufi?

Yace, “kin gane AbdulMalik?”

Tace, “Daddy wane AbdulMalik kake magana akai?”

Yace, “AbdulMalik dai wanda kika sani, dan gidan marigayi Nuhu Kwangila, abokina!”

Taji zuciyarta ta fara wani irin luguden daka cikin wani irin yanayi data kasa tantance ko na menene.

Tace, “ehh, na ganeshi…”, ta kasa daurewa sai data kara da, “lafiya?”

Yace, “babu komi sai alkhairi Kauthar. Ki shirya, bayan sati biyu da gama exams dinki za a daura aurenki dashi in shaa Allahu!”

Bata san lokacin data wani irin zabura ba, ta dafe kirji. Tashin hankali irin wanda bata taba fuskanta ba ya ziyarceta a take, saboda tsabar kidima sai data ji numfashinta yana kokarin barin jikinta.

A rikice ta fara girgiza mishi kai kamar wadda tayi gamo, “a’ah Daddy, don Allah don Annabi, kada ka aura min AbdulMalik, wallahi bana son shi Daddy!”

Daddy ya kalleta baki a dage cike da mamaki, yace, “kina sonshi ko ba kya sonshi doesn’t matter Kauthar, mun riga mun gama yanke hukunci don haka ki shirya, na gama magana, kina iya tafiya!”

Tasan karshen maganarsu dashi kenan, amma hakan ba shi ya hanata cigaba da magiya da roko ba, tasan mawuyaci ne, amma watakila ko Allah zai sa ya canza shawararshi.

Kuka take da hawaye shabe-shabe, tace, “don Allah Daddy ka min aikin gafara, wallahi na amince ka hadani da koma waye amma ba AbdulMalik ba, don Allah Daddy!”. Amma yayi biris da ita, yadda kasan baya cikin dakin ma haka yayi. Sai da tayi kukanta don kanta ta gaji, kafin ta hakurarwa kanta, ta tashi tana layi ta fita daga dakin.

Cikin ikon Allah har ta dangana da kafar bene bata ci karo da kowa ba. Cikin sanyin jiki kamar mara laka, ta dinga taka matakalar bene, tasan instinct ne kawai ya kaita dakinta ba wai don tasan inda kanta yake ba.

Ta samu gefen gado ta zauna, waje daya ta kurawa idanu tana kallo hawaye na malala a cikin idanunta, zuciyarta da kwakwalwarta a hautsine suke, har ta rasa inda zata jefa rayuwarta taji dadi.
Wani frame ta kurawa idanu, babba ne mai dan fadi, ita da wata matashiyar budurwa ne a jiki, daga ganinta zaka fahimci ta ba Kauthar shekaru biyu ko fi, amma kai tsaye zaka fahimci shakuwar dake tsakaninsu ba kadan bace. Ba zaka taba kiransu yan uwan juna a kallon farko ba, amma kana kallon murmushin da yake kwance akan fuskokinsu, farinciki da kaunar junan dake kwance a cikin idanunsu, kauna ce wadda ta zarce ta yan’uwa, irin wadda ba lallai a sameta a wajen wasu yan’uwan da suke ciki daya ba.

Kafin ta tantance, wani irin kuka ya kufce mata, ta wawuri hoton da rawar hannu ta rungumeshi a kirjinta tana wani irin kuka, “Anty Ummy!…” kawai take fada over and over.

Duk lokacin data tuna matsayin Anty Ummy a wajenta, ta tuna ko wanene AbdulMalik a wajen Anty Ummy, sai taji wani kukan yana kara barke mata.

Anty Ummy bata cancanci wannan danyen aiki daga gareta ba, bata cancanci kalar cin amanar da ake kokarin sanyata tayi ba. Shin Daddy baya gani ne? Ko kuwa bai san halin da zata shiga bane idan yayi wannan hadin da yake ikirari ba? Ko da yake ai ba damuwa da ita yayi ba.

Ta daga hoton tana kara kallon fuskar Anty Ummy, tana tuno ranar da suka dauki hoton kamar a lokacin ne suka dauka. Wani zuwa da tayi kasar Canada inda Anty Ummy din tayi degree dinta, suka fita yawon bude idanu a ranakun karshen mako. Wadannan lokuta sune lokuta mafiya soyuwa da dadadawa a cikin ranta.

Komawa kan gadon tayi ta kwanta, zuciyarta na suya, idanunta har wani irin radadi suke yi saboda tsananin kukan data sha. Wasu tunanika suka fara mata yawo a cikin kanta…

*****

Bata taba mantawa lokacin da maganar hada auren taje garesu.

Lokacin Anty Ummy bata yi cikakkun watanni biyu da kammala karatunta akan Mechanical engineering ta dawo Nigeria da zama ba, ita kuma tana aji biyu a jami’ar dake nan Abuja.

Wata safiya tana cikin barcinta mai dadi, taji ihun Anty Ummy a kanta tana tsalle da juyi, cike da farin ciki irin wanda bata taba hangenshi akan fuskarta ba.

Ta mike zaune dafe da kai daya sara mata, ta cire hearing aid dinta daga cikin kunnenta tana dan sosawa, idanunta da har lokacin suke cike da barci suna kallon halittar dake rawa tana girgijewa a tsakiyar dakinta. Ta dan ja tsaki. Abin ji din ta ja ta kara mannawa a kunnenta, ta kalli inda Anty Ummy take tana dan jefa mata hararar wasa, “wai lafiya zaki zo ki tashi mutane da wannan asubancin ne?!”

Murmushi ta saki wanda ya fitar mata da jerin hakoranta, kanana, farare tas-tas a jere, “ke wa yake ta wani barci yanzu? Tashi zaki yi maza-maza ki tayani fitar da kayan da zan sanya anjima, daga nan kuma kizo mu fada kicin mu shirya kalar abincin da bamu taba shirya kamarsa ba!”

Ta mike zaune a tsakiyar gadon, “me ke faruwa ne kuma yau har da girki? Baki zamu yi ne?”
Ta samu gefen gadon ta zauna fuskarta har lokacin dauke da murmushi, sai Kauthar ta fara binta da kallo cikin mamaki don kuwa duk zamanta da kusancinta da Anty Ummin, bata taba ganinta cikin fara’ah irin wannan ba. “Bako na musamman! AbdulMalik Kwangila ne fa zai zo wajena anjima!”, ta karasa fada hannuwanta a dage sama cikin tsananin farinciki.

Ita kuwa sai ta kara gyara zama tana kallonta a dage, “so….? Waye shi tukun?!”

Anty Ummy ta kalleta baki a dage cike da tsananin mamaki, sai kuma ta girgiza kai, “dama nasan zaki ce haka! Ganin cewa ke din kifin rijiya ce. Yanzu dai tashi ki wanke idanunki sai muyi maganar lokacin da zaki fitar min da kayan da zan sanya anjima.”

Ta tashi zata fita daga dakin, itama sai ta dira daga kan gadon ta shiga bayi don ta wanke bakinta.

Sun shiga cikin wardrobe din Anty Ummyn, take fada mata cewa AbdulMalik Kwangila matashine dake cikin shekarunshi na ashirin da takwas a lokacin, amma ya mallaki kamfanin kanshi a birnin Lagos ba tare da hadin gwiwa da komi ba. Ga mutumin daya rasa mahaifinshi a shekarunshi na sha tara a rayuwa, wannan ba karamin babban matsayi da mataki bane.

Matashine mai jini a jika, kyakkyawa daidai misali wanda yanmata suke matukar muradin ya daga idanu ya watsa musu koda kallon banza ne amma hakan ya gagara. Aikinshi kawai ya sanya a gaba, da mahaifiyarshi da yan kannenshi guda uku, bayan wannan kam mace koda gwal aka yi kirarki baki isheshi kallo ba.

Ta juya tana kallon Anty Ummin lokacin da take sanya wata gown ta wani silk navy blue din yadi mai santsi, rigar ta zauna mata das kamar don ita aka kerata, gashi dama Anty Ummin ba daga baya ba in dai ta fannin kira ce da kyawu na jiki. Tsaf zata lashe gasar kyawu idan taga damar shiga.

Tace, “to idan hakane, ke me yasa kike tunanin zai kalleki kema?”. Ta fadi hakan curiously, ba wai don bata yarda da rashin kyawun Anty Ummin ba.

Tayi juyi a gabanta ta kara har da hadawa da taku na dai-daya kamar wadda take akan dandamalin tallar wasu lingerie set na Victoria Secret.

Tace, “kin kuwa ganni Kauthar? Like, kin kalli wannan halittar sosai kuwa? Wane namijine a cikin hankalinsa zai kalleni yace wai ban mishi ba?!”

Da haka sai Kauthar kawai ta girgiza kanta tana dan murmushi cikin amincewa da zancen Anty Ummin.
Idan ka ganta a kallo na farko, ba zaka iya kawar da kai ba sai ka sake waiwayawa. Ta ko wane fanni a hade take, Allah Ya tsarata Ya mata halittar da kowace ya mace take burin mallaka, maza suke rububin samu.

Yayin da Kauthar ta kasance baka, Anty Ummi fara ce tas kamar ka taba jini ya fita. Tana da dogon bakin gashi sassalka, fuskarta a tsare take da idanu matsakaita, hanci dogo kuma siriri da dan bakinta mai zagaye da cikakkun lebba da bature yake kira ‘kissable lips’. Da gaskiyarta kam, Anty Ummi irin matan da suka fi karfin kowane namiji ya kallesu ne yace baya so, komi kyawu da ji da kai da izzarshi kuwa. Don kuwa ta kowane fanni ta hadu, ba ga kyawun ba, ba ga suffa da sura ba, ba kuma ga dabi’unta ba.

Suka cigaba da zabar kaya suna cigaba da hirarsu akan mutum daya kwal da bakin Anty Ummi ya kasa yin shiru a kanshi. Anan take jin cewa ai ko a kwanakin ma an so hada aurenshi dana yar shugaban kasa, Haneepha Dokaji, amma bata san ya zancen ya kare ba, daga baya dai an ce an fasa. Kauthar bata ce komi ba sai kai data jinjina kawai, don ta ga abun Azimun ne, nema yake yafi karfin tunaninta.

Zuwa lokacin da suka tsaya akan kayan da Anty Ummin zata sanya, wasu riga da siket na wani lafiyayyen yadi da Anty Aisha ta kai musu tsarabarshi lokacin da yawon kasuwancinta ya kaita kasar Turkiyya, tuni ta gama cika ta gaji da sauraren hirar AbdulMalik. Anty Ummi da gaske take, son mutumin take yi da zuciya da gangar jiki, fatanta daya ita kam shine, yadda ta kamu da sonshi shima Allah Yasa ya kamu da sonta.

Da suka gama da kaya sai suka sauka kasa suka shiga kicin, kayan makulashe dana tande-tande suka yi ta zakulowa cikin jerin kayan da Anty Aisha bata rabo dasu a gidan saboda baki da kuma motsa bakin ahalin gidan. Suka hada komi, da kansu suka shiga dakin bakin Daddy suka gyarashi kafin suka koma sama suka zauna zaman jiran tsammani. Har a lokacin bakin Anty Ummi bai gaza da hirar AbdulMalik-Kwangila ba. Tun Kauthar na kwabarta da nuna mata bata son hirar, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.

*****

Misalin karfe biyar da rabi na yammacin ranar, garin ya fara yin sanyi kuma magriba ta fara alamun kawowa. Anty Ummy taci kwalliya ta cakwade kamar ranar aurenta. Suna dakin Anty Ummin da yake fitar da kamshi na turaruka kala daban-daban, lokacin da suka ji alamun budewar gate.

Su dukansu suka fita waje ta nan balcony dinsu, suka lafe daga jikin bango su duka suna leken galleliyar Grey din Jaguar convertible g-50 data ratsa tayi fakin cikin jerin motocin dake ajiye a farfajiyar gidan.

Kyakkyawan farin matashin ya fito daga mazaunin direba, fuskarshi ma’abociyar saje da gargasa da gashin baki saye da bakin gilashi wanda ya matukar kayata kyakkyawar fuskar tashi.

Sanye yake da wani farin danyen voyel mai gida-gida, daga inda take tana iya hango farar singiletin da yake saye da ita da wani tattausan farin takalmin fata budadde.

Kamar wanda aka ce ya daga kanshi, ko kuwa ya kula dasu suna lekenshi tun fitowarshi? Ya daga kai lokaci guda ya kalli inda suke, suka yi baya da sauri hannuwa dafe da kirji. Hakan ba shi ya hana Anty Ummy sake lekawa ba bayan yan sakanni, ta ganshi makale da waya a kunne yana magana.

Ta juya tana kallon Kauthar data daga mata gira daya tana murmushi cike da tsokana, ta kyalkyale da dariya a kunyace.

Sai da suka ga daya daga cikin ma’aikatan gidan taje ta mishi jagoranci zuwa ciki sannan suka koma dakin Anty Ummy suka zauna.

Ba ayi cikakken minti biyar ba Anty Aisha ta kira tace su sauka bakon ya iso.

Anty Ummy ta kama hannun Kauthar data kara shingidawa kan gado lokacin da taji abinda Anty Aisha tace, “ban gane wannan kwanciyar da kika yi ba, me kike nufi?”

Ta watsa mata kallo da idanunta da suka fara lumshewa saboda barci daya fara kai mata karo, “abinda nake nufi kenan! Idan kun gama ganawa dashi kun fahimci juna just flash me, sai in sauko mu gaisa.”

Janta Anty Ummy ta fara yi da karfi alamun sam zancen nata bai zauna mata da kyau ba, “wannan kema kinsan wasa kike yi! Ta ya kike expecting din zan iya zuwa wajen AbdulMalik ni daya kwallin kwal? Bayan haka ma da wane hannu kike so in dauki iyayen kayan da muka hada mishi ne in kai mishi?”

Tayi gefe guda da kanta, “ba ga su Blessing nan ba? Su kai mishi mana?!”

Duk dai yadda ta kai ga turjewa da ki, sai da Anty Ummyn taci galaba a kanta. Ta dauki farin gyale mai yalwar fadi ta dora akan riga fitted da siket na atamfa dake jikinta, bata damu da daura dan kwali ba saboda sam baya cikin yan kayanta.

A jere kuma a nutse suka dinga taka matakalar bene suna sauka kasa. Anty Aisha na zaune ta hakimce akan daya daga cikin kujerun falon da iPad a hannunta tana danne-danne cikin sauri, hankalinta gabadaya akan wayar don haka sau daya ta daga kai ta kallesu ta maida kanta kasa abinta.
Suka shiga kicin suka dauko baskets da suka jera kayan tande-tande da lemuka da suka hada, suka fita.

Kafin su karasa inda aka yiwa AbdulMalik masauki, Anty Ummy ta manta da ta baro wayarta a daki, don haka ta hada Kauthar da daya kwandon dake hannunta, ita kuma ta juya da sauri don zuwa ta dauko wayar.

Kauthar ta karasa zuwa falon, kai tsaye ta danna kai bayan tayi sallama ta shiga.

Zaune yake akan kujera mai cin mutum daya, waya a hannunshi yana danne-danne, yayinda daya wayar take ajiye akan center table tana ta vibrating da kawo haske, alamun ko dai ana kira, ko kuma ana turo sakonni babu kakkautawa.

Cikin sakannin da basu fi biyar ba ta kare mishi kallo, tun daga kan yanayin suturar dake jikinshi, yanayin zaman da yayi, kalar wayar dake rike a hannunshi, kalar agogon dake rataye a tsintsiyar hannunshi….

Ta daga idanu a hankali ta sauke akan wasu rikitattun idanu, kallonta yake tun daga sama har kasa babu ko kunya, wani malalacin murmushi mara sauti dauke akan fuskarshi…

Tun daga nan ta yanke shawarar babu ta yadda za ayi jininta da nashi ya taba zuwa daya. Duk wani abu da tayi detesting a wajen d’a namiji, ta kula AbdulMalik ya mallakesu har ma da alakoron wasu abubuwa.

Murya a sake, kuma dauke da wani undertone da bata dauka a komi ba face na zallar rainin hankali yace, “Faheemah?!”

Wani abu ya caketa a kahon zuci, wani irin saurayi ne zai zo zance gidansu budurwa a karo na farko ba tare daya nemi saninta ko ta hoto ko ta wata hanyar ba?

Ta danne zuciyarta bata saki tsaki ba, murya kasa-kasa da takaici tace, “ba ita bace!”

Kamar kuma wadda aka ba cue, Anty Ummy ta shigo falon cikin takunta na dai-daya mai daukar hankali. Da alama kuma hakan shi ya dauke mishi hankali ya maida gabadaya idanunshi gareta, tayi amfani da wannan damar ta dire abubuwan hannunta akan teburi, ba kuma tare data juya ta kalli daya daga cikinsu ba ta bar dakin.

Tasan cewa Anty Ummy ta sanya rai da AbdulMalik din sosai, amma can a kasan ranta sai ta samu kanta da addu’ar Allah Yasa tafiyar tasu kada tayi tsayi. Saboda tsakaninta da Allah, mutumin bai yi mata ba sam!!

Sai dai daga yanayin yadda Anty Ummyn ta shigo dakinta bayan wani lokaci mai tsayi, fuska cike da fara’a da daddadan albishir din cewa sun daidaita kansu, sun kuma aminta da juna, addu’arta bata karbu ba. Hakan kuma ba shi ya sanyata canza fuska ba, ko kuma fara’ar fuskarta ta kasa dadada ba. Ta maida martanin rungumar da Anty Ummyn ta mata cike da murna, tana mai tayata murna da farincikin haduwa da hasken ranta.

Don kuwa a kodayaushe, kuma a ko wane lokaci, su masu goyawa juna baya ne a kowane hali, duk rintsi!

Kuma har cikin ranta ta mata farincikin, tana kuma mata addu’ar Allah Ya dawwamar mata da farincikin da take hangowa zata samu a tattare da AbdulMalik Nuhu Kwangila.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “Kauthar | Babi Na Daya”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×