Skip to content
Part 10 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Washegari ma kamar jiya, shi ya tayar da ita sallah da asubahi.
Sai dai wannan karon bayan ya dawo daga masallaci, sake biyawa ta dakinta yayi. Lokacin tana zaune akan abun sallah tana lazumi, ta juya tana kallonshi a nutse.
Coganewa yayi a bakin kofa bai karasa ciki ba, yace, “kin tashi lafiya Hajiya Kauthar?”

Sai ta yatsine baki, ta coge shi gefe guda, ta juya kanta daya barin. Ganin haka sai ya girgiza kai yana mai dan murmushi, “to! Itama gaisuwar ta zama fada kenan? To Allah Ya huci zuciyarki!”

Ya fita tare da maida mata kofar dakinta ya rufe.
Maimakon ta zauna rabe-raben wannan sabon al’amari da yake tsirowa dashi, sai ta kyabe baki gefe guda ta janyo Al-Qurani Mai Girma ta fara karantawa.

Zuwa wajen karfe takwas da rabi aka sanar da ita abincin kari ya kammalu.
Ta dora dan siririn gyale akan wasu jajayen Pakistan riga da wando, ta fita.

Yau already akan dinning table ta sameshi, gefenshi tarin takardu ne da folders a ajiye.
Ya kalleta a kaikaice, ya mayar da hankalinshi ga abincin da yake zubawa.

Yau ma kamar jiya, kujera daya ta bari a tsakaninsu, ta zauna. Tana kokarin jan plate itama ta zuba, ya tura mata wanda ya shake da hadin sandwich bread da soyayyiyar doya da sauce din hanta. Ya kara tura mata kofi shake da shayi, irin hadin daya mata jiya.

Kamar kuwa wadda take jira, ta kai hannu da niyar daukar flask din shayi ta zuba wani.
Kai hannunta ke da wuya, ya dora nashi a saman nata, shima kamar mai jira.

Taji wani irin yarari tun daga tsakiyar kanta har tafin kafarta, ta janye hannun da sauri tana yarfawa kamar wadda taji ciwo.

“Shan bakin shayi babu abinda zai kara miki sai rashin kiba Kauthar, kin sani. Ni kuma ba zan laminci hakan a gidana ba!”

Wannan karfin hali da rainin wayau ya fara kaita makura fa! Ta murtuke fuska, “ba zaka yi mun iyaka da abinda zan ci ba, don wai kawai kana takamar a cikin gidanka nake!”

Ya girgiza kai, “ba zan taba yi miki iyaka da duk wani abu nawa ba Kauthar! Amma idan tazo ga lafiyarki, dole inyi magana, ba zanyi shiru ba.”

“Shan shayi babu madara ai ba alamu bane na rashin cin abinci ba ko akasinsa. Komi ya danganta da yadda mutum yake son shi ai, tunda kuma bana so sai a kyaleni in ci abinda raina yake so, idan ba so ake yi in dinga amayar dashi ba!”

Tsayawa yayi yana kallonta tunda ta fara maganar har ta dire aya. Maimakon yace mata wani abu, sai taga yayi dan murmushi.
Ya janyo flask da kofi, ya hada mata shayi kamar yadda yaga tayi jiya, ya janye wancan ya mayar da wannan a madadinshi,
“Na sakar miki Kauthar, tunda haka kike so. Amma ki sani, daga lokacin da naga kin fara ramewa, dole fa sai kin daina shan bakin shayin nan!”

Baki ta tabe tana kada idanu, “Whatever! Ai sai ka ganni sannan zaka ce zaka dinga min iyaka da abinci ko?”
Dariya taji ya saki sosai, har da yin baya da kanshi, “Har yanzu dai kina nan a yadda na sanki Kauthar, da abin ban dariya da burgewa. Har na manta yaushe rabon da mu zauna dake muna hira ta fahimtar juna irin wannan!”

Sai a lokacin ta fahimci cewa dama can wayo ne yake yi mata, don yaji me zata ce, ya kuma yi nasara.
Haushi ya cikata kamar zata yi me! Daga nan bata kara ce mishi komi ba har ta gama cin abinda zata ci, ta tashi ta koma daki.
Shi ya bita har daki ya sanar da ita zai fita, har da hadawa da tambayarta me take bukata ya dawo mata dashi? Ta bude bakinnan da kyar tace, ‘Babu komi.’

Sati guda daya biyo baya, haka routine din rayuwarsu ya kasance, Kauthar har ta saba da hakan. Sai dai na dan lokaci ne.
A kwanakin babu abinda take yi, daga hutu, sai kallo data koya don dole, watarana ta yini a bayan gida tana wasanni, wasu lokutan har dan kwarinsu take shiga ta samo fruits wani lokacin ta markada su tayi lemu, har jam take yi wani lokacin. Aikin kenan dai a kullum.

Zuwa kwanaki na goma, frustration ya fara kokarin maidata wata sakara. Ta gaji da komi na gidan, ta gaji da mutanen gidan, she just wants a change of scenery.

Ranar koda yaje tayar da ita sallar asubah, zaune ya sameta akan abin sallah tana nafilah, da alama ma ta jima da tashi.
Bai ce mata komi ba ya juya zuwa masallaci.
Bayan ya dawo kamar yadda ya saba, ya dira a dakin nata. Tana tsaye tana kokarin nade abin sallar,
“Barka da safiya Hajiya Kauthar, kin tashi lafiya?”

Ya yi mamaki da yaga ta wurga mishi harara, ta juya mishi baya. A cikin kwanaki biyun da suka wuce da yana cin sa’a ta amsa da, ‘lafiya!’ ko ‘uhmn!’ cikin basarwa.

Ganin haka yasan a tsini take, don haka ya fita daga dakin kada ya sake yin wani abun da zai takalota bai sani ba.

Duk da cewa ranar Lahadi ce, amma yana bukatar ya shiga ofis saboda akwai wani abu mai muhimmanci da yake yi wanda yake bukatar a turashi a gobe Monday, kai tsaye zuwa ofishin vice governor na nan Lagos din. Wani aikin gada da za’a fara a can karshen gari suka samu kwangilar yi.

Duk da cewa zai shiga ofis, amma bai shirya da wuri ba. Sai ma ya koma barci saboda sam cikin satikan ba wani barci yake samu mai yawa ba. Raba dare yake ko dai yana gudanar da ayyukanshi, ko kuma yana tunanin little minx din dake daya dakin da yake a kusa da na shi.
Kauthar ba zata fahimci how deep in trouble she is ba, sai ranar da yayi ram da ita sannan.

Sai wajen karfe tara da kwata ya tashi, ya fada bandaki kai tsaye, ya shiga cikin shower stall. Ajiyar zuciya ya sauke a tausashe lokacin da ruwan dumi ya daki jikinshi. Yayi wankanshi a nutse, ya fita daga stall din daure da towel a kugunshi.
Gaban mirror ya tsaya yana gudanar da abubuwan daya saba, gyara sajenshi da sumar kanshi tare da shafa musu mayuka masu kyau da tsada da yake kashe musu. Ya bi duk wasu gabbai nashi ya goga turaren Oud Alif, ya dauko wani jan yadi mai kyau da aka yi mishi dinkin Senator, ya kara daukar turaren Fahrenheit na Dior ya fesa a jikinshi.
Mutum ne shi mai matukar son kamshi da gayu, shi yasa baya kyashin kashewa jikinshi dubban kudaden da suke ci mishi. Ko babu komi dai kwalliya tana biyan kudin sabulu.

Brief case mai dauke da laptop dinshi da sauran files ya dauka, ya zuba wayoyin hannunshi a cikin aljihu, hula a hannu, yana kokarin daurawa tsintsiyar hannunshi agogo mai adon zaiba ya karasa shiga cikin falo.

Hakimar tana zaune, high waist skirt ne a jikinta ruwan hoda da bakar top, ta rufe gashin kanta da hula ruwan hoda.
Wayarta take latsawa tana buga game din Candy Crush. Kamshin turaren kawai taji, tasan ya shiga falon. Ta lumshe idanu tana shakar turaren har cikin tsakiyar kanta, jinshi take yana ratsa mata duk wani sassa na jikinta saboda dadin da take ji.
Ta juya a kaikaice tana kallonshi, tsarin zubi da yanayin kwalliyar tashi ta lokacin ta matukar kwasarta, yayi mata kyau matuka gaya. Amma ba zata yaba ba.

Bata kara kallon inda yake ba, ta dauke kanta tayi wani gefen dashi tana yatsina baki da hanci.
Tsaye yayi a kanta cikin mamakin wannan sabon hali data kirkiro. Ya kada kai ya wuce kan dinning inda ya tarar da kwanukan abinci alamun ta riga ta gama cin abincinta.

Ya ja kujera shima ya zauna ya fara zubawa kanshi abincin.
Babu jimawa ya tashi tsaye yana saisaita hular daya dora a kanshi, satar kallonta yake yi wadda tunda ya zauna bata kara kallon inda yake ba. Yana so ya tambayeta koda wani abu, amma yana tunanin kada ya tsokanota ya tadawa kanshi balli. Don haka ya fara kokarin fita, “to ni zan leka wajen aiki, akwai abinda kike bukatar in taho miki dashi?” ya tambayeta kamar yadda ya saba.

Ta turo baki cike da tsiwa, “ehh, dama tunda an gama da rayuwar mutum ana take mishi hakki da takura shi, ai dole ace me za a sayo mishi! Amma babu komi, tunda Allah Yana kallon halin da nake ciki, Shi kuma zai yi mun maganin halin da nake ciki!”

Ya saki baki yana kallonta cike da mamaki, a ranshi tambaya yake, wai anya wannan Kauthar din daya sani ce? A iyaka saninshi da Kauthar, bata da tsiwa, bata da neman fitina kuma bata da riko. Amma me ya faru da wannan Kauthar din dake gabanshi a yanzu? Me ya kawo wannan canjin halin?!

Komawa baya yayi a nutse, ya ja karamar arm chair dake ajiye a falon zuwa gaban kujerar da take zaune ya ajiye tare da zama. A nutse ya sanya hannu ya karbi wayar hannunta ya kashe, ya ajiye a gefenta.

Kaifafan idanunshi ya kura mata, ta ja fuska ta sha mur, taki yarda ta rusuna duk kuwa da yadda kallon nashi yake kokarin sanyata ta rusuna din saboda yadda taji ‘ya’yan hanjinta da zuciyarta na kadawa.

Murya a sanyaye yake ce mata, “ki fada min duk wani laifi dana miki a rayuwata Kauthar, ni kuma nayi miki alkawarin zan baki hakuri a wajen da nayi kuskure, zan kuma yi miki bayani a wajen da bani da laifi.”

Tayi shiru tana hararar gefe daya, tunda a zahirin gaskiya babu wani laifi daya taba mata a wannan dan zaman da suka yi, zuciyarta ce kawai take tafasa da yi mata zafi da kuna na babu gaira babu dalili, wanda bata san musabbabinsu ba.

Ya kura mata wadannan idanun da a lokacin suke dan lumshewa suna kallonta kasa-kasa kamar zasu lasota danyarta, “ina saurarenki, ki fada min laifukana daki-daki. Me na miki? And what brought all this fushi da bacin rai da kika tashi da shi yau? Wani ya bata miki rai ne a gidan yau? Ko kuwa ni da kaina ne na aikata hakan?”

A dame yake matuka, muryarshi kuma ta kasa boye hakan.
Ta turo baki gaba, “to ni haka kawai sai a kamani a gida a garkame kamar wata fursuna, bana zuwa ko’ina kuma bana ganin kowa, sannan ace min ba zan damu ba? Idan ban bata raina ba me zanyi?!”

Sai yaji yana sakin wata irin ajiyar zuciya, yayi dan murmushi, “Matsalar kenan dama? Idan wannan ce kadai matsalarki to tazo karshe daga yau, maza kije ki dauko mayafinki!”

Ta tashi da saurinta har da hadawa da dan tsallen murna tayi dakinta da sauri. Ya bita da kallo yana sakin wani sansanyan murmushi. Har cikin zuciyarshi yana kaunar Kauthar, yana kuma fatan yaga cewa alakarsu ta koma kamar da, har ma tafi ta da din. Zai kuma yi duk wani kokari da yaga zai iya don hakanshi ya cimma ruwa.

Cikin yan mintuna ta fito, bakar blazer ta dora akan kayan jikinta, tayi rolling da mayafi dan siriri, kyakkyawan bakin flat mai taushi a kafarta da karamar jaka a hannunta.
Yana ganin fitowarta ya mike shima, bata ce mishi komi ba, shima bai tankata ba, ya dauki hanya tana binshi a baya.

A cikin motarshi KIA ruwan silver suka fita, maigadi yana daga musu hannu da fatan Allah kiyaye hanya.

Suka nausa cikin birnin Lagos, tana kalle-kalle yayinda yake ta aikin satar kallonta.
Baka jin sautin komi a motar sai karan radio. Ya danyi gyaran murya a karo na farko tunda suka fara tafiya, “Ina kike son zuwa?”

Dan bakinta ta turo, idanunta kur akan ababen hawan dake wucewa ta gefen da take, “Ni ina na sani a cikin garinnan da zan je?”

Kai ya daga, “Alright! ni nasan wajaje da dama da zaki jidadi zuwa amma kafin nan, you’ll have to excuse me, saboda zan shiga ofis in karasa wani aiki sai muje ko?”
Nan ma bakin ta kara tabewa tana daga slender kafadunta sama, “Whatever!”

Ya dan ciza leben bakinshi yana gyada kai, a ranshi yana kara tausar kanshi da ba zuciyarshi hakuri game da wadannan dabi’u da take mishi. Idan ba ita ba ko Mamanshi, a duniya akwai wata ‘ya mace data isa tayi mishi koda rabin abinda Kauthar take mishi ne ba tare daya sanyata ta dauki kashinta a hannu ba?

Daga shi har ita babu wanda ya sake yin magana, sai ita da take bin wakar ‘Bébé’ ta MHD da aka sako a cikin radio, tana yi tana dan gyada kai sometimes.

Sai da suka yi kusan mintuna arba’in da biyar kafin suka isa wajen aikin nashi. ‘Kwangila Architectural Firm’ taga an rubuta. Tsararren gini ne hawa hudu. Bayan sun gaisa da masu tsaron wajen guda biyu, suka shiga elevator inda kai tsaye ta kaisu hawa na karshe, inda nan ne ofishin AbdulMalik din.

Ta sha jin Anty Ummy tana yabon ofis din nashi, bata tabbatar da haduwar tashi ba sai a lokacin. Ya hadu, ya kuma tsaru iyaka tsaruwa.
Musamman data hangi wani ofis wanda yake kallon nashi, shake da screens na kwamfutoci.
Ofis dinshi babba ne, akwai bandaki a ciki, kujeru biyu manya na hutu da aka ajiye, akwai kuma wajen da aka ware na meeting ko presentation. Komi a tsare yake, a shirye tsaf babu hayaniya kamar shi AbdulMalik din.
Yayi mata nuni da kujera yana sanar da ita zata iya zama anan ta jirashi, idan kuma tana so ta zagaya wajen, duk zata iya.

Ta dosana ta zauna akan kujera tana karewa wajen kallo. Shi kuma ya daga firjin ya dauko mata lemun fanta na gwangwani da cupcakes ya ajiye mata.
Ya nufi desk dinshi ya zauna ya fara gudanar da aikin daya kaishi.

Ganin haka ta dan saki jiki ta bincire hancin lemun ta fara sha. Ganin hankalinshi ya tsunduma a aikin da yake yi sosai, yasa ta mike ta fara leke-leke. Ta fahimci ofisoshi hudu ne kawai anan saman, daga na shi, sai wanda yake kallonshi, sai kuma wasu biyu daga can gefe.

Har tayi zagayenta ta koma, aiki yake. Ta koma kan kujera ta zauna tana kallace-kallace, daga karshe ta dan shingida.
Shiru-shiru taga bashi da alamun tashi, daga karshe dai bata san lokacin da barci ya dauketa ba.

Aikin yake, amma rabin hankalinshi yana gareta. Dan murmushi yayi lokacin da yaga tana gyangyadi, daga karshe dai ta zame ta kwanta.

Sai wajen sha biyu ya kammala, ya turawa team dinshi da suke aikin tare, kowa ya duba bangarenshi yaga yayi, kafin daga karshe dai ya danna alamar ‘send’ ya tura.

Yayi mika daga kan kujerar yana jin kasusuwanshi na bada kara. Yana son aikinshi sosai, gajiyar dake tattare da aikin ce wani lokaci baya so.

Takawa yayi a hankali zuwa inda take kwance, ya rusuna a gabanta yana karewa fuskarta kallo.
A hankali numfashinta yake fita.
Ya kurawa zara-zaran gassun da suka yiwa idanunta rumfa, bakake sidik, da gashin girarta da suke a kwance luf, ya gangara zuwa ga madaidaicin hancinta, bashi da tsayi sosai kuma bashi da fadi, ya diresu akan kyawawan tausasan lebbanta da suka sha lip balm mai sheki… Lumshe idanu yayi yana furzar da numfashi a hankali.

Saurin tashi daga gabanta yayi yana girgiza kai kamar wanda aka tsikara, ya hau bugun hannun kujerar inda kanta yake a hankali har ta bude idanunta akan shi.
Yayi inda-inda cikin rashin sanin abin cewa, da kyar ya iya daga baki yace, “ki tashi mu tafi!”
Ya juya da sauri ya shiga bayi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 13

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 9Kauthar 11 >>

6 thoughts on “Kauthar 10”

  1. Jeeddah a taimaka a dinga mana posting da wuri, a wattpad fa cewa kika yi duk bayan kwana biyu 😔 amma sai a jima babu wani labari

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×