Skip to content

Kauthar | Babi Na Hudu

3.2
(13)

<< Previous

Bata san ko wacece mahaifiyarta ba, bata san dangin mahaifiyarta ba. Tana da dan insight na mahaifiyarta a lokacin yarintarta kafin batan mahaifiyarta. Tana tuna daren da abin ya faru daki-daki, a kowane lokaci a cikin rayuwarta. Ta yaya ma zata manta da wannan rana? Bayan koda yaushe ta kasance cikin mafarkin abinda ya faru?!

Tana tuna irin kauna da soyayya da iyayenta suka nuna mata lokacin da tana yarinya. Amma suma wadannan in pieces take ganinsu, vividly.

Abinda tafi tunawa sosai kuma da kyau, shine lokacin data farfado daga hatsarin daya rutsa musu, wanda kuma ya tarwatsa mata rayuwa. Da kuma abubuwan da suka faru bayan nan.

Ta bude idanune ta tsinceta a gadon asibiti, kunnenta na dama yana mata wani masifaffen zugi da wata irin kuwwa kamar an jona shi da amsa kuwwa. Ta yunkura zata tashi, taji kafarta ta dama ta amsa, wani azababben zafi ya ratsata har sai data saki ihun azaba.

Aka tura kofar dakin da sauri aka shiga, ta juya tana kallon matar data shiga fuska dauke da alamun rashin sanayya.

A kallon farko babu kari, zaka tabbatar da cewa matar ta hadu gaban kwatance, kuma ilimi da wayewa sun ratsata ta kowane bangare. Cikin shiga take ta mutunci irinta hausawa, abinda bata saba gani tattare da mahaifiyarta ba. Kullum cikin kananun kaya take, babu canji.

Ta nufeta da alamun damuwa da kulawa akan fuskarta, ta taimaka mata ta zauna tare da jingina mata filo a bayanta ta kuma kara mata wani a kasan kafarta inda sai a lokacin ta kula da cewa kafar sangale take a jikin wani abu.

Tace, “sannu Kauthar, ya kike jin jikinki?”

Bata iya bata amsa ba saboda bata jinta sosai, sama-sama ta dinga jinta kamar a cikin ruwa take, ga kuma rashin saninta da bata yi ba don daga ganinta dai ba nurse bace.

Matar taci gaba da watsa mata tambayoyi, amma Kauthar ta rasa bakin amsawa. Ta kuma kasa daga baki ta tambayeta ina Mamanta da Babanta kamar yadda take so tayi saboda yadda bakin nata yayi nauyi sosai.

Cikin ikon Allah sai ga Baban nata ya shiga dakin da sauri, likitoci biyu suna binshi a baya. Kamar wadda take jira, tana ganinshi sai taji ta saki kuka. Matar nan ta jata jikinta da sauri tana lallashi da bata baki, ta hau fuzge-fuzge har ta samu ta janye daga jikinta ta fada jikin Daddynta tana rizgar kuka kamar ana zare mata rai.

Likita ya matsa ya dubata tana daga jikin Daddyn kamar wadda take tsoron a rabata dashi, ya tabbatar musu da cewa lafiyarta lau, kuma za a iya bata abinci, ya tafi ya barsu a nan.

Ba ita ta samu bakinta ba sai bayan da aka yi mata allura, zogin kunnenta ya ragu, matar nan ta goge mata jiki da towel da ruwan dumi, ta taimaka mata tayi brush, ta bata abinci mai ruwa da madara, duka Daddy yana zaune a gefen gadon yana kallonsu, kafin ta iya daga baki ta tambayeshi,
“Daddy, ina Mommyna?!”

Shi da matar suka hada idanu, ya rankwafa ya dafa kanta adoringly, “baby, Mamanki tayi tafiya ne amma babu dadewa zata dawo, meanwhile, wannan ita ce new Mom dinki, understand?!”

Sai ta girgiza kai maimakon gyadawa, don kuwa bata fahimta ba. Kamar ya Mamanta ta ainihi tayi tafiya amma kuma tayi wata sabuwa cikin dan kankanin lokaci? Kwalwar Kauthar a wannan lokaci bata fahimta ba, kuma ba zata fahimta ba sam.

Ya zauna a gefen gadon tare da kara janta cikin jikinshi, “ina nufin itama wannan kamar Mommy dinki ce, yadda zaki kira Mamanki ‘Mommy’, itama haka zaki kirata. Sannan ina so ki dinga jin maganarta da kyau”.

Ta daga baki tace, “to ita din wacece ita, Daddy?!”

Suka sake yin musayar kallo, “Matata ce ita, kuma zata koma gidanmu, mu zauna tare da ita. Kina so ko?”
Nan ma ta sake girgiza kai, daga nan kuma bata sake daga baki tayi magana ba har garin Allah Ya waye.

Data tashi atafau taki Matar da sai daga baya aka ce sunanta Aisha, ta goge mata jiki ko ta wanke mata baki, ta kuma ki Nas ko wani ya tabata har sai da Daddynta yaje sannan yayi wannan aiki.

Da yammacin ranar sai ga Daddy ya koma da wata yarinya, daga gani zata girmeta. Tana kan gado a zaune, Matar Daddy kuma na kan kujera a gefen gado tana karatun jarida.
Daddy ya shiga dakin da fara’arshi yana kallonta, “ga abokiya na kawo miki Kauthar!”

Ita da yarinyar suka tsaya suna kallon-kallo, ta taka a hankali zuwa inda take, ta mika mata katon teddy bear na Mickey Mouse, bata san ko wa ya fada mata tana sonsu ba, karo na farko tunda ta farfado data saki murmushi a fuskarta, ta amsa tana furta ta gode a hankali can kasan makoshinta.
Itama tayi murmushi ta zauna a kusa da ita, tace, “sunana Fahima…. Ke fa?!”

Tace, “Kauthar,” murya a sanyaye kuma cikin jin nauyi da rashin sakewa.

Kawancene da aka kullashi tun daga wannan lokacin, ita ta rada mata Anty Ummy saboda bata iya fadin sunanta hakanan gatsar.

Satinsu biyu a asibiti, bayan ta sha aune-aune game da matsalar kunnenta, aka bata hearing aid kafin ta gama warwarewa a kaita inda za ayi mata aiki a kunnen.

Rigima bata tashi ba sai da suka koma sabon gidansu, ta kwana ta yini bata ga Anty Ummy ba. Ta tayar musu da ballin da babu shiri sai da Anty Aisha ta dauki makullin mota da gyale da kanta taje ta dauko Faheema daga makaranta ko tashinsu ba ayi ba.

Mafarin komawarta gidan kenan da zama, idan ka ganta a gidansu to yini taje musu ko weekend, shima kuma cikin rakiyar Kauthar wadda baka taba jin hirarta sai idan da Anty Ummy din ce.

Wannan dalilin ne yasa ta zama kamar yar gidansu Anty Ummy din. Idan ba sani kayi ba, tsaf zaka ce yar gidansu ce.

Ita da Anty Aisha kuwa, it’s a mutual agreement cewa basa son juna tun gani na farko, duk yadda Daddynta yaso ya hadasu abin yaci tura. Kauthar ta kasa sakin jiki da ita balle har ta dauketa a matsayin matar mahaifi ma balle Mahaifiya.

Ba karamin jan aiki aka sha bama kafin ta fara kiranta da sunanta, da sai dai tace, ‘waccan matar’ ko ‘wannan matar’

Tuni ta nemi wannan uban mai matukar sonta da nuna mata kauna a lokacin da mahaifiyarta tana nan, ta rasa. Ya daina wasa da ita, ya daina zama ya saurari matsalolinta, ya daina damuwa da al’amuranta, gabadaya ya dauki komi nata ya damka a hannun Anty Aisha. Shi yasa a kullum rashin son matar yake karuwa a cikin ranta, tunda a ganinta daga zuwanta ne mahaifiyarta ta tafi ta barsu kuma Daddynta ya tsaneta.

Ko shekara biyu da auren ba a gama rufawa ba Anty Aisha ta haifi Mahmoud. Zo kaga murna da doki wajen Kauthar. Duk zamansu da Anty Aisha a gidan sai ranar data haihu ne ta taba shiga dakinta.
Kusan ita da Anty Ummy suka yi rainon Mahmoud, wanda sai daya shekara kusan biyar kafin ta sake haihuwar Lukman, har yau kuma bata kara haihuwa ba.

Kaunar da take yiwa su Lukman wani lokacin har mamaki take bawa mutane, tunda ba kaunar mahaifiyarsu take yi ba. Ita kuwa tsakaninta da Allah sonsu take yi, gani take yi bata da kamarsu, kamar wadanda suka fita ciki daya haka take jinsu a cikin ranta.

Kafin wannan lokaci sun ziyarci kasashe sun fi a kirga a hannu daya akan matsalar kunnenta, babu wata mafita da aka samar musu. Kunnen ya riga yayi dameji, akwai kuma yiwuwar with time, ya tabo dayan. Dole sai kan magunguna aka dorata da therapy.

Rayuwarsu na gangarawa cikin godiyar Allah, girma yana kara shigarsu, dai-dai da rana daya wani sabani na azo-a-gani bai taba shiga tsakaninsu da Anty Ummy ba. Ta zama tamkar wata babbar Yayarta, ita kuma kanwarta. Kaunar da Anty Ummy ta nuna mata yasa take jin cewa babu abinda ba zata iya yi mata ba, muddin bai sabawa shari’ah ba.

Abu na farko data kasa fahimta tun bayan bayyanar AbdulMalik Kwangila cikin rayuwarsu, shine abubuwan da take ji a game dashi.

A shekarun Kauthar a wannan lokaci, bata fahimci dalilinsu ko ma’anar hakan ba. Ita dai ba ma’abociyar karance-karance bace, kuma bata kallon fina-finai barkatai, ita kuwa ba abokiya ba balle ta tambaya taji.

Koma dai menene take ji tasan ba abu bane wanda zai haifar da d’a mai ido ba, it feels unforgivable even to her.

Wani dare daya sake kiranta a karo na biyu, karfe sha biyun dare saura. Ya hargitsa mata kwalwa da wasu kalamai data rasa ma’ana da fa’idarsu. Ta kwana tana tunaninshi da kalaman daya dinga mata, wai har da mafarki.

Ba shiri ta kwashi jikinta ta falla Saudiyya inda Kakarta, Mahaifiyar Daddy take. Ita kadai ta rage musu a cikin dangi, dama kuma shine kadai dan data haifa a duniya. Shi yasa take ji da Kauthar da su Mahmoud kamar ta lashesu.

Duk da cewa due to something unknown to Kauthar, tafi son su Lukman din a kanta. Abune kuma da bata boyewa ko a gaban wanene, akwai lokuta da dama da sai Daddy ya dan bata rai ko yayi mata magana idan ta yiwa Kauthar din wani abu. Hakanne yasa itama Kauthar din tasu bata zo daya da Hajiya Hadiza ba.

Amma a wancan lokacin, sai ta gwammace zama da Kakarta sau dubu akan zama tare da AbdulMalik yana buga mata mind games dinshi dake sanyata kasa gane inda yasa gaba.

Bata koma ba sai bayan satika biyu, lokacin kuwa kwanaki goma sha shida suka rage a daura auren Anty Ummy da AbdulMalik.

Lokacin da ta koma duk wani abu daya kamata a gudanar ya gama kammala. An buga iv, an kai akwatuna goma sha biyu shake da kayayyaki, an fitar da anko, an kama halls da za ayi events na biki, abinda kawai ya rage shine a bada kudin sadaki, a shafa fatiha kawai. Sai a dauki amarya a kai gidan angonta dake birnin Ikko.

Don haka komawarta bata zauna ba. Suka sa kafar rabon invitation card da kuma kai dinkuna da amsowa. Komai iri daya ake dinka musu su biyun, babu bambanci.
Wannan zirga-zirga da suke yi tasa tuni ta mance da wani AbdulMalik da kurar data kwasoshi, sai taji an ambaci sunanshi sannan take tunawa dashi.

Saura kwanaki goma biki har an kai kayan furnitures gidan amaryar da kayan kicin. Da Kauthar aka yi tafiyar, suka je Lagos suka mata jeren kaya. Gida ya hadu iya haduwa, ko a fadar wani kasaitaccen sarki sai haka.

Kauthar ta koma da santin gidan a bakinta, wani lokacin sai Anty Ummy tayi murmushi tace mata,
“ni yadda gidannan nawa yayi miki Kauthar, ko dai irinshi za a miki ne, ko kuma kiyi kaura can?”

Sai ta girgiza kai tace, “ni kinsan ba dream house dina bane, sai dai in binki zanyi mu tare kawai a naki gidan!”.

Anan sai yanayin Anty Ummy din ya canza, tace, “wallahi da ace zasu yarda Kauthar, da wajena zaki koma da zama. Bana son abinda zai rabani dake ko yaya yake. Yanzuma ji nake kamar ince na fasa auren wallahi!”.

Kuma da gaske take. Idan aka bata dama zata iya aikata daya cikin biyun wannan.
Ranar data fadi haka sai da Kauthar ta faki ido ta je ta shaki kukanta. Wannan kauna da wannan halittar Allah take nuna mata, ita kam dame zata saka mata ne a wannan duniyar?!

Biki yana ta kara gabatowa a duk wucewar rana.
Wata rana taje makaranta, Anty Ummy ta kirata tace zata je ta dauketa a makarantar ta rakata studio zasu yi hoto. Tace mata to.

Ta fito daga department dinsu bayan ta gama laccarta ta ranar. Tun da safe ta gama laccarta ta ranar, ta tsaya daukar darasine a wani programme da aka kirkira a makatantar na koyawa dalibai sign language wanda ta shiga ba tare da sanin kowa ba.

Kafin ta fara dube-duben inda zata hango inda Anty Ummy tayi parking din motarta, taji wayarta tana vibrating daga cikin yar karamar jakar Lamis dake rataye a kafadarta.
Ta daga da “hello,” cikin sassanyar muryarta.

Anty Ummy tace, “gamu nan ina hangoki, zaki ga wata jar KIA a gefen damarki”.

Ta juya idanu na walainiya cikin nemansu, idanun nata suka yi kyakkyawan gani.
Suka fada cikin na mutumin da ba tayi zaton gani ba, bata kuma shirya haduwa dashi a daidai wannan lokaci ba.

Har sai da taji numfashinta yana kokarin 4barinta. Wani mahaukacin kyau da yayi mata a lokacin, sai taga kamar bata taba ganin kyawunshi irin na ranar ba. Taji ta kamar wadda tayi shekara da shekaru bata sanya shi a cikin kwayar idanunta ba.

Kafafunta suna hardewa kamar taliyar spaghetti data gama dafewa ta taka ta nufi motar, da ba don Allah Yasa flat din takalmine a kafarta mahadin jakar hannunta, da tuni ta kife a wajen, ko ba don komi ba sai don zazzafan kallon da taji ana jefa mata.

Ta bude gidan baya ta shiga, Anty Ummy tana yi mata magana amma ta ma kasa fahimtar abinda take cewa ma balle ta mayar mata da amsa. Wani kamshin citrus da sandalwood da hadin amber ne yayi mata sallama wanda yasa taji kanta yana juyawa saboda tsabar dadin da yayi mata.
It smelt so good. So Cool. Just like AbdulMalik!

Motar ya tayar, ya dan juya yana kallonta, “Hajiya Kauthar Hajjaju manyan kasa, yaushe kika dawo mana Najeriyar ne bamu samu labari ba? Ko kuwa duk cikin rowar tsaraba ne ake mana?!”

Anty Ummy ta dan kalleshi, “wai dama ban fada maka ta dawo ba? To kila ko mantawa ne nayi ko?,”
Ya daga kafada.
Ita kuwa Kauthar dan murmushin yake ta saki, “kai Yaya Abdul, rowa dai kuma?!”

Baki ya tabe dai-dai lokacin daya fita daga cikin gate din makarantarsu yana dagawa wani security hannu.
“Yo ehh mana, don na kula ke din sarkice a cikin marowatan ma!”

Anty Ummy yar dariya tayi, “haba Love, ai kuwa duk duniya ban ga wanda yake da kyauta kamar Kauthar ba, ta yaya ma zaka sanyata a cikin salon marowata?!”

Cikin wani halin ko-in-kula yace, “ko? Shine ni kuma ake yi mun rowar? Ko kuwa don ba ayi damu ne?”

Ganin yana neman jan maganar da tsayi yasa tace, “wai to ni Yaya Abdul, rowar me nayi maka ne?”

Kai tsaye yace, “rowar ganinki mana data waya! Kina mun rowar muryarki!!”

Ta kalli Anty Ummy a matukar birkice, tana so taga reaction dinta game da maganar, sai taga sam hankalinta ba anan yake bama.

Ta juya tana kallonshi shima taga ko a jikinshi, kamar ma ba shi ya fadi abinda ya fada ba.
Shi kam wani irin mutumi ne haka? Wanda bashi da filter sam a maganganunshi? Yadda suka je mishi haka yake fadarsu tsakaninshi da Allah?!

Maimakon ta bashi amsa, sai ta kai hannu ta balle hearing aid dinta don ma kada ta kara jin wata katobarar da zata sake jefa ranta cikin tunani da neman amsar abinda yake nufi.

Ta daga iPad dinta tana wasu abubuwan ba tare data kara daga kai ta kalli dayansu ba. Sai da suka karasa studio din sannan Anty Ummy tayi mata magana, ta maida wayar cikin jaka suka tafi.

Anyi hotuna da sauran abubuwan da suka kamata.
Suna kan hanyar komawa Anty Ummy ta kalli AbdulMalik, tace, “Love, ka ajiyeni Maitama, gidan Anty Mansurah (Babbar Yayar su Anty Aisha), zan karbi wani sako. Amma a can zaka barni saboda sai da dare zan dawo, sai ka mayar da Kauthar gida don Allah!”

A lokaci guda suka daga baki, shi yace, “alright.”

Ita kuma tace, “a’ah, zan biki muje can din sai mu dawo tare!”

Anty Ummy tace, “kin manta masu planning din dinner zasu zo su sameki ne anjima ku tsara yadda za ayi?”

Sai ta kawar da kanta gefe daya tana turo dan bakinta cikin rashin sanin abin cewa.

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

3 thoughts on “Kauthar | Babi Na Hudu”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×