Skip to content
Part 11 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Sai daya nutsu, sannan ya duba agogon hannunshi yaga ashe lokacin Azzuhur ma yayi. Don haka ya daura alwala, ya fita yana kokarin balle maballan links din hannun rigarshi.
Ya sameta zaune akan kujera, da alama jiranshi take yi.
Tana ganin ya fita sai itama ta shiga bandakin. Bata jima ba ta fito, da alama alwalar itama tayi.

Ya kalleta kasa-kasa, “Muje ko?” ya tambaya yana yi mata nuni da inda ya shimfida abin sallah biyu. Ta bi shi ya ja su jam’i.

Daga nan suka hada kayansu suka bar ofis din.
Wata restaurant suka fara zuwa, daga nan wajen aikin nashi zuwa can babu nisa. Bayan sun shiga an kaisu wajen zama aka zaunar dasu a teburi mai cin mutum biyu, suka yi order din abinda zasu ci. Shi tuwon semovita aka kai mishi da miyar yauki, ita kuma aka kai mata chips da wainar kwai da kaza. A nutse suka dinga cin abincin, ba sa yin hira a tsakaninsu, amma kuma babu tense silence dinnan. Bayan sun gama cin abincin ya jata suka shiga gari. Shiga wancan amusement park din, shiga wannan shopping mall, zuwa bayan la’asar sai ga bayan motar shake da ledojin sayayyar da suka dinga yi wadda rabinta AbdulMalik din ne ya dinga kwasa, yawanci kuma kayan makulashe ne sai kananun abubuwan amfani.

Wajen karfe hudu da rabi ya ajiyeta a gidan Aunt Halima, ya barta anan kan cewar bayan Magriba zai je ya dauketa.
Tarba tayi mata ta mutunci sosai da sosai, kafin kace me ita da yan aiki sun cika mata gaba da kayan tande-tande har ta rasa wanne zata ci. Gashi ta kasa sakewa da matar sam, har yanzu halinta na rashin saurin sabo yana nan.

‘Ya’yan Aunt Halimar duk suna makaranta sai yar autarta kawai, Aneesah mai kimanin shekaru sha shida, ita ta zauna tana tayata hira har ta dan saki jikinta.

Basu bar gidanta ba sai bayan isha’i, a can ta ci abinci tayi nak. Aunt Halima da Aneesah suka rakata har gaban mota, suna mata godiya da ban gajiya har da alkawarin satin sama za a kai mata Aneesah ta mata yini.
Leda guda madaidaiciya ta cike mata da tsadaddun turaruka na jiki da na daki har da na tsuguno, da yake sana’ar Aunt Halima din kenan. Suna musu bye bye AbdulMalik ya ja motar suka tafi.

A hankali yake tukin, duk da cewa babu cunkuson ababen hawa sosai. Kadan-kadan yake satar kallonta ganin yadda take dan yatsina fuska tana kuma yawan motsawa, ta kasa zama waje daya. Ranshi ya damu saboda da alama jikinta ne bata jin dadinshi.
Daga karshe dai ya kasa daurewa, ya juya yana kallonta cikin nuna kulawa, “Lafiyarki lau kuwa, Kauthar? Ko wani abun ne yake damunki?”

Ta girgiza kai a hankali tana dan ciza bakinta. Ya kalli gesture din, kafin ya jinjina kai a nutse ya maida hankalinshi ga titi.

Suna shiga gida yayi parking din mota, ta fita da dan saurinta. Yayi shiru yana binta da kallo cikin nazari, kafin ya daga kafada ya kashe motar shima ya fita ya bi bayanta. Maigadi biye dashi da ledojin sayayyarsu.

Bai sameta a falo ba, don haka ya wuce dakinshi kai tsaye. Ruwa ya watsa, ya canza kaya zuwa grey sweat pant da shirt mai kananun hannu da V-neck.
Laptop dinshi ya dauka ya koma falo, ya shiga kicin da kanshi ya hada coffee, ya juye a mug ya dauki cookies saboda ba yunwa yake ji ba, shi yasa ma ya umarci da kuku akan kada yayi girki.

Karamin teburi yaja zuwa gaban kujera, ya dora tray din da mug, kafin ya juya ya nufi dakinta.
Knocking yayi, yaji shiru ba a amsa ba, ya sake yi, nan ma shiru.
A hankali ya tura kofar, ya dan zura kanshi ciki yana karade dakin da kallo. Bata nan, amma ya jiyo alamun karan ruwa a bayi, don haka ya maida kofar ya rufe, yasan kila wanka take yi.

Ya koma falo ya fara gudanar da ayyuka yana yi yana sipping coffee dinshi
Ko bayan daya gama, TV ya kunna yana kallon labaran kasa a tasoshi da dama. Bai tashi daga inda yake ba sai bayan karfe sha daya.

Ya kashe komi na falon, ya dauki laptop dinshi ya tashi. Har ya wuce ta kofar dakinta, sai kuma ya juya ya bude kofar a hankali saboda kada ya tasheta a barci.
Sai ya tsintota shame-shame a tsakiyar dakinta tana juye-juye cikin alamun ciwo dafe da cikinta.

Ya zabura ya fada dakin a rikice, ya birkitata ta juya tana kallonshi, idanunta a dan lumshe suke, bayan ciki da suka shige sunyi ja sosai.

“Subhanallah! Kauthar, me yake damunki ne? Kauthar?!” Ya watsa mata tambayar a gigice, fuska cike da damuwa.

Ta kasa magana sai kai da take girgizawa. Ya kai hannu yana dafa hannunta dake dafe da cikinta, “sweetheart, you have to tell me what’s wrong so I can help you! Cikinki ne yake ciwo?”

Murya a dakushe tace, “Cikina, don Allah ka taimaka min!”
Ya gyada kai da sauri, “ok, ina tunanin muna da kanwa, naji Annah tana cewa idan ana ciwon ciki kanwa ake jikawa a sha.”

Ya tashi da saurinshi zai tafi neman kanwa, ta kamo hannunshi, “magani zaka bani ba kanwa ba damn you! Period nake ba kartawar ciki ba!”

Sai lokacin ya hangame baki cikin alamun nuna fahimta, “oh! Ina maganin da kike sha yake, sai in dauko miki!”
Ta girgiza kai cikin alamun galabaita, hawaye na cika mata ido, “Babu! Ba a sako min ba, ni kuma banyi tunanin in nema da wuri ba.”
Yace, “Ok, bari in zo yanzun nan!”

Wayarshi ya dauka ya kira likitar daya tanada saboda matsaloli irin haka.
Bata samu ta karaso ba sai bayan mintuna kusan arba’in, kafin nan Kauthar ta gama galabaicewa, murkususu take yi sosai, kuka tun hawaye na fita har suka daina.

Da sauri Dr. Amanda ta nufi kanta, taimakon daya dace ta hau bata. Ta mata allura, ta umarci AbdulMalik daya coge a gefe ya hada mata ruwa mai dan dumi tayi wanka, yaje ya hada ya dawo falon.
Da kyar da taimakon Dr. Amanda ta tashi, jikinta yayi kaca-kaca da jini. Bayan ta shiga bandakin shi ya hau goge-goge da gyare-gyare. Yayinda Dr. Amanda ta fita amsar pad da aka aiki dan aikin gidan ya sayo.

Kafin ta fito har ya gyara dakin, ya fitar mata da kayan barci. Dr. ta mika mata pad din da kayan barci ta kimtsa kanta, ta fito a daddafe cikin rashin kwarin jiki.
Ya taimaka mata ta zauna a gefen gado. Kofi mai shake taf da shayi hadin kauri ya mika mata, ta maida mishi kofin tana girgiza kai cikin yatsina fuska, “Zuciya yake tayar min.”

Don haka ya fita ya koma kicin, custard ya dama mata, ya koma dakin ya sameta da Dr. Amanda tana yi mata tambayoyi da bata shawarwari. Ta karbi bowl din custard din daya yiwa damu mai dan ruwa saboda haka tafi son shi. Bata tsaya mamakin ta yadda aka yi yasan yadda take son custard dinta ba, ta amsa ta fara sha a hankali.

Sai data sha da yawa, ta sha magani, sannan Dr. ta musu sai da safe ta tafi. Ya rakata har kofar falo yana yi mata godiya. Bayan ta tafi ya maida kofa ya rufe bakinshi dauke da addu’a.

Kwance ya sameta rufe da bargo, ya zauna a gefenta tare da kama tattausan hannunta ya sanya a cikin tafin hannunshi. Ya dafa goshinta da yaji ya dan fara yin zafi yana tambayarta ya jikin? A sanyaye ta amsa da ‘da sauki’ idanu a lumshe tana dan yatsina fuska kadan-kadan alamun har lokacin da zafin dai.

Haka suka wanzu har zuwa lokacin da barci mai nauyi ya dauketa. Ya kurawa fuskarta idanu, cikin dan lokacin har ta dan fada. Bai bar dakin ba sai da dare ya tsala, wajen karfe biyu da rabi.
Ya ja mata bargo har zuwa saman kirjinta, ya dukufa a saitin fuskarta yana kare mata kallo. Wani irin kyawune take dashi mai sanyi, wanda zaka yi ta kallon mutum amma baka ganin muninshi sai dai ma kyawunshi. A hankali ya duka, ya sauke lebbanshi a saman goshinta yana sumbata.
Da kyar ya iya janyewa ya kashe mata fitila ya bar dakin. Wannan dalilin ne yasa ba zai iya kwana a dakin ba. Idan yace zai kwana anan sai dai ya kwana a zaune yana kallonta don ba zai iya barci ba, idan kuma ya aikata hakan, akwai yiwuwar duk wani linzami da yake yiwa zuciyarshi yana controlling kanshi, ya cisge. Akwai wani abu tare da ita dake jan shi zuwa a gareta musamman a wadannan lokuta da suka kasance a karkashin inuwa daya a koda yaushe.
Don haka ne salin-alin ya tattara ya koma dakinshi.

Alwala ya daura ya fuskanci alkibla ya fara jero tarin nafilfili, cikin natsuwa da kaskan da kai.

Da asubah ya lekata bayan ya dawo daga masallaci ya samu har lokacin tana barci. Don haka ya koma ya fara shirin fita.

Karfe bakwai da kwata ya shiga falo, waya kare a kunnenshi yana magana. Sai ya dan dakata, ganinta zaune akan dinning tana cin abinci.

Ya taka a nutse zuwa inda take, akan kujera ya ajiye jakar hannunshi da sauran tarkace, yaja kujera shima ya zauna.
Ya kalleta cike da kulawa, “how are you feeling?!”

Kai ta jinjina a hankali, “Alhamdulillah, da sauki sosai!”
Ya gyada kai shima, “Masha Allah, that’s good!”

Dukansu suka yi shiru, ta cigaba da cin abincinta shi kuma ya fara zubawa shima.
Ya rigata tashi, ya kwashi kayanshi ya mata sallama akan ya tafi wajen aiki. Itama bai jima da fita ba ta tashi ta koma daki, magungunanta ta sha ta koma ta kwanta saboda har da na barci aka hada mata.

Ranar da wuri ya koma gida saboda tunaninta da yadda ta yini ya kasa barinshi sam.
Ko dakinshi bai shiga ba ya fara biyawa ta nata dakin.

Ya sameta kwance a tsakiyar dakin akan karamin carpet. Sai da yaji wani irin yammm!! a gabadayan ilahirin jikinshi.

Wando ne a jikinta marar nauyi mai fadi ruwan kasa mai haske, sai bakar half vest a jikinta. Barci take yi a nutse, numfashinta na hawa da sauka a hankali.
Yadda ta kwanta din a rigingine, fatarta mai dan haske tana wani irin sheki da glistening under bulbs din dakin.

Ya hau watsa mata wani irin kallo wanda bai ma san yana yi ba, ranshi ya yaba sosai da sosai, wasu abubuwa suke mishi yawo a rai da jiki bakidaya.
Cikinta a shafe yake shafal kamar babu abinda ya taba shiga ciki, hakan ya ba hourglass kirarta fita sosai da sosai musamman a cikin kayan. Kirjinta a cike yake dam yayi tudu, haka kugunta a cike yake da kira ta nunawa sa’a. A fuska ko kalar fata ba zaka jera Kauthar a sahun farko ba, amma a kira kam ko’ina ne zata shiga ta fita a bi bayanta da tafi.

Sai ya maida mata kofar dakin ya rufe a hankali ya wuce zuwa dakinshi. Duk da cewa yanayin garin da dan sanyi, haka nan ya takarkare ya dinga shekawa kanshi ruwan sanyi ko ya dan samu sawabar zuciya.

Bayan mintuna kamar talatin, ya fita daga dakin nashi ya shiga falo cikin kananun kaya na shan iska. Falon babu kowa, don haka ya fita farfajiyar gidan ya zauna akan kujerun hutu yana duba mails dinshi da mayar da amsa har duhun magriba ya fara shiga.
Ya tashi ya koma ciki yayi alwala ya tafi masallaci.

Sai wajen karfe takwas da rabi ya koma gidan. Tana kan kujera a falo tana kallon Baghi a tashar Bollywood, duk da cewa rabin hankalinta yana ga wayarta inda take chatting da Abdul.
Ta daga kai tana kallonshi a nutse lokacin daya tsaya a gabanta, “ya jikin naki?”
Ya tambaya a tausashe.

Ta daga kafada kawai, “fine!”
Da alama halin nata ya fara dawowa. Don haka bai tsaya neman wata maganar ba ya juya zuwa kan dinning yana daga warmers. Abinda zai ci ya zuba ya zauna ya fara ci, idanuwanshi a kanta yana kare mata kallo. Yadda take dan murmushi lokaci zuwa lokaci, har wani lokacin ma dariya ta subuce mata.

Ranshi yaji yana motsawa. Me yasa shi ta kasa sakewa dashi kamar haka? Me yasa shi ba zata aminta dashi ba? Me yayi mata??
A haka a daddafe ya kammala cin abincin, ya tashi ya wuceta yana mai kakaro sautin “sai da safe” da kyar daga cikin makoshinsa. Saboda ranshi ya gama dagulewa. Ita kanta sai data bi shi da kallo cikin mamakin sauyin halinshi yanzu yanzu. Sai kuma ta tabe baki ta cigaba da chatting dinta.

*****

Tsayin kwanaki hudu tana jinyar jiki, har dai ta warware ta koma kamar da. Sai dai zaman kadaici da damuwa sun koma mata, tun waya da yan gidan tana mata dadi har ta daina, musamman da su Lukman suka bi Anty Aisha zuwa California yawon shakatawa, saboda haka waya dasu sai ta fara mata wahala.

Nan da nan tsamin rai ya dawo sabo fil. Ta bi ta fandarewa AbdulMalik ya rasa ta yaya zai tarota. Duk wani abu da yasan zai burgeta ya dan kwantar mata da hankali yayi, amma Kauthar ko a jikinta wai an tsikari kakkausa.

Daya gaji ranar nan dai yace mata ta shirya ta fara bin shi suna zuwa wajen aiki. Sai a lokacin yaga murmushinta for the first time in a while, sai shima ya hau murmushin kamar wani kuntacce.

Suka kuwa fara tafiya wajen aiki tare. Wannan ofishin na kusa da nashi ya bata, daga ciki kana iya ganin komi dake gudana a waje haka na waje yana ganinka tunda gilashi ne. Hakan duk bai dameta ba. Ita dai in dai zata yini tana latsa computers, to bata da matsala.

Ta fahimci yanayin kwamfutocinsu manya ne kwarai, high quality systems da zaka iya gudanar da duk wani abu da kake so dasu wanda karamar laptop dinta ba zata iya rabin abinda zasu yi ba.

Wannan dalilin yasa ta fara gudanar da nata binciken na sirri, ba tare da sanin kowa ba. She knows her way around computer, breaching, hacking, babu abinda bata iya ba, kuma dama duk don haka dinne ya koya.
Tana takatsantsan kwarai wajen kiyaye takunta saboda koda wani zai duba abubuwan, ba zai zakulo abinda take yi ba.

Da alama kuma shes getting somewhere, musamman data bada wannan sim card din aka gyaro mata shi.
Bata tashi budewa ba sai data bari AbdulMalik baya cikin office din. Lokacin ya fita wajen wani meeting shi da sauran abokan aikinshi dake kan floor din.

Ta saka card din a wayarta, duk da haka yaki budewa saboda babu PUK code. Don haka ta jona shi jikin computer din tayi running wani program wanda cikin yan mintuna kalilan ya bude sim card din.

Murmushi ta saki a hankali tana murnar nasarar da tayi.
Sai dai tuni murnar ta nemi komawa ciki saboda fara karanta sakonnin dake ciki data fara yi. Kwata-kwata bata shiryawa abinda ta gani ba. Bata shirya ba sam! Bata kuma tunanin zata iya yarda da hakan har duniya ta nade ne!

Me ke faruwa ne?

AKWAI SAURAN LAUJE A CIKIN NAD’I!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 21

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 10Kauthar 12 >>

9 thoughts on “Kauthar 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
ร—