Skip to content

Ko Ruwa Na Gama Ba Ki | Babi Na Ashirin Da Daya

0
(0)

<< Previous


Matar na tuba bata rasa mijin aure.

Tunda motarsu Jummai ta ɗauki hanyar ƙauyensu gabanta ya soma faɗuwa, ba komai ya jawo haka ba sai tsoron  mahaifiyarta, da kuma mutanen gari da bata san da wace fuska ce zata kalle su ba.

Addu’a ta shiga yi ƙasan ranta tana faɗin “Allah ka sa mahaifiya ta yi farinciki da komawa ta”, domin gani take har yanzu Asabe na riƙe da ita.

Aisha da ke gefenta ce ta lura da shirun da ta yi, ɗan taɓo ta ta yi ta ce “Kin yi shiru Aunty,”  murmushi Jummai ta yi saboda bata son su fahimci tana cikin damuwa, cewa ta yi “Ina jin ba daɗi ne zan bar Katsina, saboda mutanen cikinta kuna da kara da karamci”.

 Ƴar dariya Aisha ta yi sannan ta ce “Kai Aunty, ai kin kusa dawowa  Katsina gaba ɗaya da zama, fatanmu dai Allah ya ida muku nufinku ke da Uncle Ameer”.

“Amiin” Jummai ta ce suka kama dariya.

Salma na seat ɗin gaba ta jiyo su suna dariya,  ɗan leƙowa ta yi ta ce “Dariyar me ake yi ne?”.

Harara Aisha ta wurga mata tare da faɗin “Toh Uwar gulma, ba zaki ji abin da ake ma dariya ba”.

“Kada Allah ya sa ki faɗa” Salmar ta faɗa tare da murguɗa baki.

A kan kunnen Aunty da suke seat ɗin dake bayansu Jummai ita Altine Salma ta yi magana, birki ta taka musu, don abu ne mai sauƙi su kaure da faɗa “Toh Sababbi, faɗan ne ko, to ku yi”, Dariya Jummai da Aisha suka kama yi, Salma kuma ta ƙara turo baki, da yake saurin fushi gare ta. Altine ma da ke gefen Aunty dariya ta kama yi.

Shiru ce ta ratsa cikin motar, kowa da abin da yake saƙawa a ransa Aunty kuma sai fama take da Ammu da Ahamad, wai fitsari zasu yi.

Ameer kuwa mota ɗaya suka hau shi da wani abokinsa, wanda zai aje a kan hanya, kusan tare motocinsu ke tafiyar, ko da ɗaya ta wuce, toh tazarar kaɗan ce.

Uwani kuwa tun saura kwana biyu su Alhaji Mainasara su taso ta koma gida domin shirya tarbar su. Asabe kuwa bata so tafiyarta ba, saboda zaman da suka yi ya mantar da ita duk wata damuwa da ke ranta.

A ranar da ta tafi ne kuma damuwar ta fara dawowa, don in dai zata zauna ita kaɗai, toh ko shakka babu sai ta faɗa duniyar tunanin mijinta, da kuma ɗiyarta.

Yanzu haka zaune take a tsakargida tana kallon dabbobinsu da ke ɗaure a garke, wanda a baɗini ba su take kallo ba, Jummai take tunawa.  

“Ko tana ina?” ta tambayi kanta.

Rashin sanin amsar ne ya sa wasu hawaye sirara gangarowa a kumcinta “Allah ina roƙonka da ka dawo mani da ƴata, domin babu ranar da zan dena ƙunci muddin ba ganin ta na yi a kusa da ni ba”.

Da dukkan yaƙini ta yi addu’ar, tana gamawa ta shafa dukkan hannayenta dake sama a fuska.

Shiru ta yi tare da cigaba da kallon dabbobin. Neman ƙuncin da ke cike ranta ta yi ta rasa, sai ma wata nutsuwa da ta ke jin ta fara mamaye mata zuciya.

Tana cikin wannan yanayi ne ta jiyo tafiya a zaure, alamun za’a shigo.

Maida dubanta ta yi ga ƙofar, aikuwa sai ga wasu kyawawan yara maza biyu sun shigo, hannunsu maƙale cikin na juna.

Zumbur ta miƙe lokaci ɗaya kuma gabanta na faɗuwa, sakamakon fuskar Ahamad da ta gani, wadda ta ke sak da ta Salim ɗin Uwani.

Shigowar Aunty da su Salma ne ya sa ta maida dubanta gare su, cikin ranta tana tunanin inda suka samu waɗannan baƙi haka.

Murmushi ta yi tare da faɗin “Maraban ku.”

Fuskar Aunty ɗauke da fara’a ta ce “Yauwa”, domin ta ga fuskar Jummai a cikin ta Asaben, wanda ko shakka babu ita ce mahaifiyarta.

Ta buɗe baki zata yi musu iso a ɗaki ne ta jiyo muryar wata mata daga waje tana faɗin “Wallahi Jummai ce ta dawo.”

Ras gabanta ya faɗi “Jummai kuma?” ta faɗa a ranta.

Kasa yin magana ta yi, kuma bata rufe bakin ba a lokacin da Jummai ta shigo, hannunta dafe da ƙirji domin duk irin sauyawar da Jummai ta yi zata iya gane ta tunda ita ta haife ta.

Bakinta na kyarma ta ce “Mafarki nake, ko da gaske ne”, lokaci ɗaya kuma gabanta na cigaba da faɗuwa.

Kallon ta su duka suka shiga yi, kowa na jin tausayinta ganin yadda lokaci ɗaya ta ruɗe.

Sake tambayar Aunty ta yi “Baiwar Allah ki bani amsa, Jummai ce nake gani a gabana?”

Kafin Aunty ta bata amsa Jummai ta rugo da gudu tare da faɗawa jikinta tana kuka.

“Ni ce Inna, ni ce Jummanki.”

Kuka Asabe ta fashe da shi tare da rungume ɗiyarta ta ce “Ina kika shige tsawon shekara uku, me yasa kika tafi kika barni” tamkar zata maida ta cikinta take faɗin haka.

Kuka sosai suka cigaba da yi, gaba ɗaya Asabe ta manta da su Aunty, godiyar Allah ta shiga yi, domin ya yaye mata baƙincikinta.

Sosai ta ba su Aunty tausayi, don alamu ya nuna ta daɗe tana fatan ganin zuwan wannan rana.

Cikin ƙanƙanin lokaci kuma gida ya cika da mutane ana ta faɗin “Ga Jummai. Ga Jummai.”

Murna wurin mutanen ƙauyen ba’a magana.

Asabe kuwa idonta ya rufe bata ganin kowa, kuka kawai ta ke tana gode ma Allah.

Ameer da ke tsaye bakin ƙofa Asabe ta hango, tsagaita kukan ta yi tare da nuna shi da yatsa ta ce “Dr. tare kuke?”.

Gaba ɗaya idanun ƴan garin ya dawo kansa lokacin da ya ƙaraso inda suke.

“Tare muke Inna.” ya faɗa, lokaci ɗaya kuma zuciyarsa cike da tausayinsu.

“Nagode Dr. Ashe sai da ka nemo mani ƴata, nagode, Allah ya bani ikon saka muku da alkhairin da kuka yi mani.”

Murmushi su duka suka yi, cikin ɗaki ta yi musu iso, ƙatuwar tabarma ta shimfiɗa musu suka zauna.

Har cikin ɗakin wasu ƴan garin suka bi su, burinsu kawai su ga Jummai, domin

suka dasa suna ta yi, kukan da za’a iya kiranshi da kukan daɗi da kuma nadama, domin su duka sun cutar da junansu.

Ɗagowa Jummai ta yi da idanunta da ke ta ambaliyar ruwa, hannayen Asabe ta riƙo ta ce “Inna ki yafe mani laifukan da na yi maki, ki yafe mani don Allah.”

“Na yafe maki duniya da lahira, nima ki yafe mani abin da na yi maki.” Asabe ta faɗa tare da sa hannu ta share mata hawayen da ke gangara a kumcinta.

“Inna ni baki yi mani komai ba, ke mahaifiyata ce, duk hukuncin da kika yi mani na cancanci fin sa.”

Sake jawota Asabe ta yi ta rungume, tabbas ta cutar da Jummai cutarwa mai yawa, kukan ta cigaba da yi itama.

Haƙuri su Aunty da mutanen garin suka yi ta basu, Salma da Aisha kuwa kukan suma suka riƙa yi.

Sun ɗauki lokaci a haka sannan suka yi shiru, ƙuri Asabe ta yi ma Ahamad, take ta tuna sadda Jummai ta kawo mata shi numfashi na sarƙewa kamar mai cutar Corona, rungume shi ta yi tsam a jikinta, tare da lumshe ido na ƴan daƙiƙu.

Buɗe idon ta yi haɗe da gaishe da Aunty cikin girmamawa.

Da girmamawa itama Aunty ta amsa. Juyawa ta yi wurin Altine, tare suka haɗa baki wurin gaishe da juna, bayan sun amsa tare ta maida kanta wurin Ameer, wanda ya yi mata abin kirkin da bata iya mantawa da shi a rayuwarta, ya yi ɗawainiya da ita fiye da tunanin mai tunani, bayan tafiyarshi ne Dr. Misau ya dasa da nashi, wanda hada sanya hannun Ameer ɗin.

“Dr.” ta faɗa, amsawa ya yi tare da gaisheta.

Amsawa ta yi itama tare da faɗin “Allah ya saka maka alkhairi, Allah ya baka abin da kake so duniya da lahira.”

Ya ji daɗin addu’ar. “Ameen.” Ya faɗa murmushi a fuskarsa.

Jummai ce ta fara magana tare da nuna su Aunty ta ce “Inna waɗannan su ne suka riƙe ni da girmamawa, kuma suka taimake ni a lokacin da bani da kowa, suka yi ɗawainiya tare da ceto rayuwata a lokacin da na kusa rasa ta, Dr. dan gidansu ne.”

Godiya sosai Asabe da mutanen garin suka yi musu, tare da yi musu fatan alkhairin Allah.

Tashi Asabe ta yi ta ɗauki kuɗi ta fito, kira ta kwaɗa ma Aminyarta da ke cikin ɗakin.

Tana fitowa ta miƙa mata dubu biyu “Don Allah lemu da ruwa zaki siyo, idan kin dawo kuma ki yi ma mutanen can magana su fito su bar baƙi su sha iska.”

Karɓar kuɗin ta yi, cikin ɗan lokaci sai gata da uban lemu mai sanyi da ruwa, tana miƙa ma Asabe, ta ɗaga murya ta ce “Toh ƴan garinmu, ku fito mu bar baƙi su sha ruwa.”

Duk fitowa suka yi, wasu na ta gunguni, don basu gaji da ganin Jummai ba.

Sosai su Aunty suka sha ruwan da lemun, Ameer kuma ya ɗauko nasu shi da Driver ya fito musu da shi waje.

Kuɗi ta aika ma Aminyarta da shi na cefane, sannan daga gidan Kabiru kuma aka yanko kaji, domin shirya ma baƙi girki mai rai da lafiya.

Matar Kabiru na zuwa suka hau aiki, cikin ƙanƙanin lokaci suka gama girkin. 

Sosai su Aunty suka ci abincin tare da yaba ma Asabe bisa ga karamcin da ta yi musu.

Bayan sun kammala ne su Jummai suka fito tsakar gida, Aunty da Asabe kaɗai aka baro cikin ɗakin.

Hira suka riƙa yi kamar sun san juna, anan Asabe ta ba Aunty labarin komai tun daga cikin da kuma tsangwamar da ta yi mata.

Aunty ta ce “Ai irin haka jawo yaro ake a jiki, domin tsangwamar sake maida shi ruwa take.”

Asabe ta ce “Ai ban gane haka ba sai da na neme ta na rasa, na shiga ƙunci ba kaɗan ba.”

“Allah ya kyauta gaba.” Aunty ta ce.

Maganar soyayyar Ameer da Jummai Aunty ta yi mata, cewar suna son a basu damar turo magabata.

Asabe ta yi murna da jin wannan magana, domin neman hanyar da zata saka ma Ameer ta ke, toh gata ta samu.

Farinciki fal da zuciyarta ta ce “Amma wallahi na ji daɗin wannan al-amari, Allah ya tabbatar musu da alkhairi amin”.

Cewa ta yi toh a bari Alhaji Mainasara ya dawo, tunda yana hanya, sai a haɗu da sauran dangi a yi magana.

“Allah ya dawo da shi lafiya.” Aunty ta faɗa.

Wayar Uwani ta kira, amma ta ƙi shiga, burinta kawai ta sanar da ita Jummai ta dawo.

A can tsakar gida kuwa Ameer ne ya shigo, inda suka taru suka yi ta hira, mai cike da farinciki.

Su Ahamad kuwa Basheer ya ja su sun fita waje, don tunda suka zo yake ta nan-nan da su shi da Ali.

Fitowa Aunty da Asabe suka yi, gidan Aunty ta shiga kallo, sai ta ji ya burge ta, dama akwaita da son zuwa ƙauye.

Ƙarasawa suka yi ƙarƙashin bishiyar da su Jummai suke, Asabe ta ce “Ameer ashe da al-amura kuke tafe.”

Murmushi ya yi tare da sosa ƙeya, ta ce “Toh Allah ya tabbatar da Alkhairi.”

“Amin.” kowa ya ce, daga bisani ta sake gode musu, domin sun yi mata halacci, duk da sanin kuskuren da Jummai ta aikata, amma suke son aurenta.

Da yamma Aunty da Ameer suka tafi, da zimmar sati mai zuwa za’a zo neman auren.

Su Aisha kuma nan zasu zauna har ranar da su Ameer zasu dawo.

Uwar tsarabar da su Jummai suka kawo ce Asabe ta shiga rabo, kusan duk gidajen da ke kusa da su sai da suka shaida dawowar Jummai, sabulai da Omo ne aka rarraba ma kowa, Maigari kuwa hada yadin shadda biyar, aikuwa kunya duk ta kama shi daya tuna tozarcin da yayi ma marigayi Malam Amadu.

A ɓangaren Uwani kuwa,  tana can tana shirin tarbar mijinta da take sa ran isowarsu bayan magarib.

Murna wurinta abin ba a magana, don ta yi kewar sa sosai, Wani irin gyara ta yi ma gidan, sannan ta sauya jeren ɗakinta, tana gamawa ta turare lungu da saƙo na ɗakin da turaren ƙamshi, wanda har a farfajiyar gidan zaka iya jin ƙamshinsa. 

Ɗakin Habeeb ma sai da ta sanya aka gyara shi tsaf, saboda ya yi ƙura sosai.

Wanka ta yi, tare da chaɓa ado ita da ɗanta, sannan ta kame falo tana jiran dawowar farincikin rayuwarta.

Ko yaya ta ji horn ɗin mota sai ta ɗauka sune, dayake a bakin titi suke.

Sai ta leƙa sai ta ga Maigadi bai buɗe gate ɗin ba, tana nan zaune har aka yi isha’i, lokacin kuma Salim ya yi bacci, ɗaukar shi ta yi suka nufi bedroom, tana kwantar da shi ta gabatar da sallar Isha’i.

Tana cikin addu’a ta ji Maigadi ya buɗe gate, da hanzari ta shafa addu’ar tare da miƙewa, lokaci ɗaya kuma ta cire Hijabi ta aza a kan gado.

Lokacin data fita har su Alhaji Mainasara sun fito daga mota, farinciki fal da zukatansu suka tarbi Juna. 

Uwani ta ce “Toh mijin ko ɗan zan fara yi ma oyoyo”, dariya su duka suka yi “Alhaji Mainasara ya ce “Wanda kika fi so a cikinmu.”

ta ce “Nafi son ɗana, don na fi kewarsa.”

Kafaɗun Habeeb da ke ta washe baki ta dafa ta ce “Oyoyo ɗana, mun yi kewarka.”

“Nima na yi kewarku Aunty.” ya faɗa, cikin ransa yana mamakin yadda Uwani ke masa.

Zuciyoyinsu cike da farinciki suka ƙarasa cikin falonta.

Sannu da gajiyar tafiya ta yi musu, sannan ta dubi Habeeb da ya koma sauran ciwo, cike da tausayinsa ta ce “Haka ka koma Habeeb?”

Murmushi ya yi, kafin Habeeb ɗin ya yi magana Alhaji Mainasara ya ce “Ai nan ya yi ƙiba ma.”

Ta ce “A hakan Alhaji?” Domin dai yayi ramar da ko mai ciwon Sida sai haka.

Alhaji Mainasara ya ce “Ai yana de da sauran shan ruwa kawai, amma ɗan nan naki ya ci kwakwa.”

 Ƴar dariya su duka suka yi, daga bisani ta ce “Toh Allah ya ƙara lafiya Habeeb.”

“Amiin” su duka suka ce,

Ido Alhaji Mainasara da Habeeb suka yi ta zubawa basu ga Salim ba “Wai ina ɗana ne?”, in ji Alhaji Mainasara da ya riga Habeeb tambaya.

“Yana bedroom” Uwani ta bashi amsa, ɗan rausaya kai ya yi.

Sannu da gajiya ta ƙara yi musu, sannan suka tashi, bedroom suka nufa ita da Alhaji Mainasara. Habeeb kuma ya fita izuwa ɗakinsa.

A hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, wani irin sanyi ne da kuma ƙamshi suka daki jikinsa da hancinsa, kallon ɗakin ya shiga yi, wanda ya sha gyara.

Ƴar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanu, haƙiƙa abubuwa sun fara chanjawa,”Ya Allah, yadda nake jin sanyi da nutsuwa a zuciyata a yanzu, ka sanya hakan ya ɗore”, cikin ɗakin ya ƙarasa, yana son zama, yana gudun faɗawa duniyar tunani, domin in dai zai zauna shi kaɗai, toh sai ya yi tunani, kuma likita ya gargaɗe shi dayin tunanin duk abin da zai sosa masa ciwon da ke cikin zuciyarsa.

Wayarsa ya aje akan gado, sannan ya faɗa banɗaki, wanda shima an wanke shi gal, sai ƙamshi ke ta shi.

Wanka ya yi ya fito, sannan ya gabatar da Sallar magrib da Isha’i.

Yana cikin azkar ne Abbanshi ya kira shi a waya cewa ya fito su ci abinci.

Shafa addu’ar da ke bakinsa ya yi, sannan ya fito ya nufi ɗakin Uwani.

Dining ya nufa tare zuba ido ga na’ukan abincin gargajiya dake zube akan dining table, domin kuwa sun daɗe basu haɗu da su ba, fankasu, albkubus, sinasir, ga kuma dafaffen naman sa da dambun naman kaji, ɓangare ɗaya kuma ga zobo, da kunun aya, da kuma lemukan kwali.

Tun kafin Habeeb ya zauna ƙamshin abincin ya cika masa hanci, ta ke yawun bakinsa ya tsinke “Duk mu kaɗai wannan girkin Aunty.” ya faɗa yana kallon Uwani dake serving ɗin Alhaji Mainasara.

Dariya ta yi ta ce, “Kwarai kuwa, akwai wani ma, idan kun cinye sai a ƙara”

“Ai kuwa mun gode Aunty” ya faɗa shima yana dariya, lokaci ɗaya kuma ya zauna.

Alhaji Mainasara yana kai Fankasu a baki ya lumshe ido tare da cigaba da taunawa saboda daɗi.

Kallon sa su duka suka yi suka kama dariya. A hankali ya buɗe idanun ya ce “Dariyar me ake ne.”

Habeeb ya ce “Mun ga kamar kana bacci ne.”

Dariya ya yi ya ce “Ba wani bacci, daɗi ne ya kai mani karo, kasan Gimbiya akwai iya girki.”

Dariya suka sake yi, Habeeb ya ce “Gaskiya ne Abba, bari dai nima in fara.”

Cin yaushe gamo suka yi ma abincin, suna ci suna santi, sai da suka cika cikinsu, sannan suka bi da kunun Aya mai sanyi.

Wayar Uwani ce dake yashe a can falo ta fara ruri, sauri ta yi ta je ta ɗauki wayar, tana dubawa ta ga number Asabe, da hanzari ta ɗaga kiran.

Cike da walwala ta ji muryar Asabe tana fadin “Don Allah ina ki kai waya, ina ta kiranki in maki albishir, amma a kasha.”

“Wallahi ban san a flight mode take ba, sai yanzu ba daɗewa ba” Uwani ta fada, ƙasan ranta tana son jin wannan albishir.

Daga can Asabe ta ce Ayya, toh yanzu goron albishir zaki bani.”

Dariya ta yi “Na baki yaya Asabe, me ya faru?”

“Ƴarki Jummai ce ta dawo.”

 “Ke Yaya Asabe, yaushe?”

Uwani ta faɗa, hannunta dafe da ƙirji, fuskarta kuma ɗauke da jin daɗin da kuma mamaki mara misaltuwa.

Habeeb da Alhaji kuwa sun zuba mata ido suna kallon ta.

Maimakon ta ji muryar Asabe, sai ta ji Jummai ta yi sallama tare da faɗin “Aunty Uwani ni ce.”

Ido Uwani ta lumshe lokacin da hawayen murna suka ɓuɓɓugo mata a idanu “Jummai da gaske ke ce.”

Tare Alhaji Mainasara da Habeeb suka miƙe.

“Wai me kike cewa ne Gimbiya.” Alhaji Mainasara ya faɗa lokacin da ya fito daga dining ɗin.

Janye wayar ta yi daga kunnenta sannan ta ce “Jummai ce ta dawo Alhaji, ga ta ma.” ta miƙa mashi wayar.

Wani irin daɗi ne da baya misaltuwa cikin zuciyar Alhaji Mainasara, ko ba lamarin Habeeb, toh yana fatan ganin wannan rana, domin ɗiya ya ɗauki Jummai, bare kuma ga ɗansa, wanda rayuwarsa ta ta’allaƙa ne da son ta.

Habeeb kuwa, ƙuri ya yi musu, faɗuwar da gabansa ke yi ce tasha gaban farincikin da ke ransa, don wani irin tsoron Jummai ne Allah ya sanya mashi a zuciya, duk sadda ya tuna ta sai gabanshi ya faɗi, ba komai ya jawo haka ba sai tabbacin da yake da shi na ba zata sake karɓarsa ba.

Sosai Alhaji Mainasara ya yi farinciki da dawowarta, bayan ya yi magana da Jummai, sai ta bashi Asabe “Wannan abin daɗi har In

na, Wallahi mun yi farinciki da dawowarta, Allah ya kiyaye ga, sai mun zo”.

Sallama suka yi, sannan aka dawo falo aka cigaba da murna, Habeeb ma ɓoye fargabarsa ya yi aka cigaba da murna tare da shi.

Tashi Habeeb ya yi ya ce “Na tafi in kwanta,” mu kwana lafiya suka yi mashi.

Yana tafiya suka rufe ɗaki, sannan suka nufi bedroom.

Habeeb kwana ya yi yana tambayar kansa “Anya Fateema zata sake karɓa ta.”

Sanin abune mai wahala ta sake yadda da shi ya haifar mashi da matsanancin tashin hankali, gaba ɗaya idonsa ya bushe, baccin da ya dawo da shi lokaci ɗaya ya neme shi ya rasa.

Ganin ciwonsa na shirin tashi ne ya yi maza ya faɗa banɗaki, alwalla ya yi, sannan ya fito ya cigaba da sallah, yana gamawa ya shiga neman agajin Allah da kuma yafiyarsa, domin ya yadda yayi kuskure mai yawa, mafi girma kuma a ciki shine na gangancin sakin Fateema da ya yi.

Washe gari wurin ƙarfe goma na safe suka shirya sai ƙauye, su duka hada Habeeb ɗin,  gabaɗaya Jummai yake son gani, don haka ne ma ya manta da jiran mahaifiyarsa da suka yi zata zo har gida ta ganshi.

Tafiyarsu kenan sai ga Hajiya Mairo ta zo ganin sa, tun kafin ta shigo Maigadi ya tabbatar mata da sun yi tafiya yanzu.

Mamakin inda suka tafi daga dawowarsu a fuskarta ta tambaye shi “Ina suka tafi?”, ya ce “Ƙauye”

“Hada habeeb ɗin” ta sake tambayarshi, ya ce “Eh, wai Jummai ce ta dawo.”

Ras gabanta ya faɗi, yanzu Jummai ta fi ta kenan a wurinsa, ya tafi wurin Jummai, amma ita bai neme ta ba, da haushin wannan abu ta juya.

Tashar mota ta nufa tare da shiga motar garinsu suka nufi ƙauye suma.

Su Uwani kuwa ƙagare suke su ga Jummai, musamman Habeeb da bugun zuciyarsa ke ta ƙaruwa, domin a yanzu ba Jummai ce kaɗai damuwarsa ba, hada mahaifiyarta da ya taɓa zagi a baya, sannan ga wannan aika-aika da ya aikata ma ƴarta, “Anya mutanen nan zasu iya yafe mani abin da na yi musu”

Yana cikin tababar yafiyar ne motarsu ta tsaya a ƙofar gidansu Jummai, jikin Uwani na ɓari ta buɗe motar ta fito,

Gaisawa ta yi da mutanen dake ƙofar gidan, don yanzu gidan ya zama wurin taruwar Jama’a, kasantuwar motocin da ke ta kai da kawowa a ƙofar gidan tun bayan rasuwar Malam Amadu.

Alhaji Mainasara na kallon yadda take ta zakwaɗin shiga, murmushi kawai ya yi, cikin ransa ya ce “Gimbiya ba dai azarɓaɓi ba.”

Habeeb kuwa jiki a mace ya fito daga motar, da kaga fuskarsa kasan babu gaskiya a ransa, zagaye shi mutane suka yi shida Alhaji ana yi mashi ya jiki, saboda duk garin an san bai da lafiya.

Tare shi da Abbanshi suka nufi cikin gidan, suna shiga zaure Alhaji Mainasara ta tsaya tare da dubansa a tsanake, magana ya yi cikin sigar kwantar da hankali ya ce “Habeeb.”

“Na’am Abba” Habeeb ɗin ya faɗa tare da ƙara saka idanunsa cikin na Abbanshi.

“Zuciyarka cike take da tsoro ko?”.

Ɗaga kai Habeeb ya yi, Abbanshi ya ce “Toh ka yi ƙoƙari ka cire shi, tabbas kai mai laifi ne, amma sai ka jajirce ta yadda wanda ka yi ma laifin ba zai raina ka ba.”

Sake ɗaga Kai Habeeb ɗin ya yi, kafaɗarshi Abbanshi ya dafa sannan ya ce “Allah yana tare da kai, kuma nima ina tare da kai.”

Hannu Habeeb ɗin ya ɗora akan na Abbanshi dake kan kafaɗarshi ya ce “Nagode Abbana.”

Murmushi su duka suka yi, sannan Habeeb ya daidaita nutsuwarshi, cikin gidan suka sanya kai, ƙasan zuciyar Habeeb kamar zai ɓalle saboda bugawa.

Jummai na jikin Uwani suna kukan yaushe gamo, kamar ance ta buɗe idanunta dake cike da hawaye, sai ta ga Habeeb da Abbansa.

Ido ta zaro, gabanta kuma ya yanke ya faɗi, a hankali ta zare jikinta daga jikin Uwani ta ɗan ja da baya.

Gaba ɗaya Asabe da su Aisha suka maida dubansu ga su ga Habeeb da Abbanshi.

Asabe tana ganin Habeeb ta ji walwalarta na neman ƙwacewa ta gudu, ba arziki ta ruƙo ta don bata son Alhaji Mainasara ya fahimci tsananin fushin da take yi da ɗansa.

Murmushi bayyaane a fuskarta ta ce “Alhaji Marabanku.”

“Yauwa” ya ce suka ƙaraso inda suke.

Gaishe shi Aisha da Salma suka yi, idanunsa cikin nasu ya amsa, cikin ransa yana jin kamar ya taɓa ganinsu ko da a hoto ne.

Jummai kuwa kasa magana ta yi, kanta na ƙasa, tana jin wata irin kunya, idanunta kuma cike da hawaye, haka shima Habeeb kasa magana ya yi sai dai ya yi ta ƙyafta idanu.

Iso aka yi musu cikin ɗakin, bayan sun zauna akan tabarma suka gaisa.

Idanun Habeeb na ƙasa ya gaida Asabe, a taƙaice ta ce “Lafiya lau, ya jikin,”  ya ce da “Sauƙi.”

Kiransu Jummai Asabe ta yi, tare suka shiga da su Aisha, da kuma Ammu da Ahamad.

Alhaji Mainasara ya jawo Ammu da Ahamad ya ɗora su a kan jikinsa, ita kuma Jummai ya ce ta zo kusa da shi ta zauna.

Gafenshi na dama ta zauna, Habeeb kuma na gefensa na hagu, kuka ta cigaba da yi.

Kanta ya dafa ya ce “Wai na miye kukan”.

Shiru ɗakin ya yi, Habeeb kuwa ji yake kamar ya nutse ƙasa, lallashinta Alhaji Mainasara ya yi, bayan ta tsagaita kukan suka fita.

Asabe kuwa Ahamad ta kalla, sannan ta kalli Habeeb, wata irin ƙuna ce ta taso mata a zuciya, wani mugun kallo ta yi ma Habeeb ɗin, wanda Uwani ta ga sadda ta yi mashi shi.

Magana Alhaji Mainasara ya fara, wadda ta sa ɗakin yin tsit,  “Toh Alhamdulillah, ina taya ki murna Asabe, akan dawowar Fateema, wadda duk mune sanadin faruwar haka.”

Ɗan rausaya kai ta yi tare da ɗan guntun murmushi don ta san abin da yake nufi.

Cigaba da magana ya yi. “Ba za’a kaita da nisa ba, bayan murna sai kuma yafiya muka zo nema ma ɗana, wanda tuni ya yadda da kuskuren da ya aikata, don Allah muna neman yafiyarku, ku yafe mashi abin da ya aikata.”

Ɗan rumtse ido Asabe ta yi, ƙasan ranta tana jin wata irin zafi, Lallai Habeeb ya cutar da su, ya zama sanadin wargajewar farincikinsu, anya zata iya yafe mashi.

Gaskiya abu ne mai wahala ta iya manta abin da Habeeb ya yi musu, musamman saboda uwarshi. Amma saboda mahaifinsa zata yi ƙoƙarinta wurin ganin ta cire abin a zuciya.

Duban Alhajin ta yi “Alhaji kuskure ne ya riga ya faru, rashin haƙuri da shi a karon farko ne ya haifar da kuskure na biyu, ni dai na yafe ma Habeeb abin da ya yi mana, sai dai ba don kowa ba sai don kai Alhaji, ka yi mana abin da bamu da ƙarfin da zamu biyaka.”

Uwani ta ji daɗin maganar Asabe, kai ta jinjina tare da dariya a fuskarta.

Alhaji Mainasara ma ya ji daɗin maganar, Habeeb da idanunsa ke ƙasa ma ya yi farinciki.

Alhaji Maisara ya ce “Mun gode sosai, wallahi muma bamu da bakin godiya, mun cutar da ku da da yawa.”

“Wallahi ya wuce Alhaji.” Asaben ta sake faɗa.

ya yi musu,  Ya ce “Nagode Inna, sannan ina mai baki haƙuri, don Allah ki yafe mani, wallahi tuni na yi nadama”, wasu hawaye ne suka zubo mashi.

Take zuciyar Asabe ta kare, wani tausayinsa ne ya kama su.

Asabe ta ce “Na yafe maka Habeeb”, Allah ya yafe mana baki ɗaya”.

Godiya sosai suka yi, Tash

Haƙuri da godiya Habeeb ɗin yayi ya fito, can ƙarƙashin bishiya ya hangi Jummai  ita da su Salma zaune a kan tabarma.

Sarƙewa idanunsu suka yi cikin na juna, ɗauke kanta ta yi, tare da duƙar da shi tana yi ma Ahamad da ke kan cinyarta magana, cikin ranta kuma tana tunanin abin da ya ramar da shi haka.

Wucewa ya yi ya fita, Salma ta ce “Amma wannan yana da alaƙa da Ahamad ko?”, don ta ga kama.

Kai ta ɗaga “Babanshi ne, kuma shine sanadin rushewar duk wani farincikina” idanunta cike da hawaye ta ƙarasa maganar.

Idanunsu na zaure suka ce “Kansa ya cutar, tunda gashi nan da gani duniya ce ke bi da shi.”

A can ɗaki kuwa Uwani ce ta samu damar nema ma Habeeb damar neman yafiya a wurin Jummai, da kuma sake neman aurenta a karo na biyu.

Tabbatar musu da Asabe ta yi ta samu miji, yanzu haka su ake jira dama su dawo a nemi auren wurinsu.

Duk inda walwalar Alhaji Mainasara ta ke sai da ta ɓace.

Jiki a mace ya fito ɗakin, cikin ransa yana jin wani irin tashin hankali, domin Mutuwa ce zata iya ɗaukar Habeeb idan wani ya auri Jummai.

Ƙofar gida ya samu Habeeb yana danna waya, bai bari Habeeb ya fahimci wani abu ba dangane da damuwar da ya fito da ita, na samun miji da Jummai ta yi.

“Mu je ka gaida kakarka ya faɗa yana kallon Habeeb.

Kai tsaye gidansu Hajiya Mairo suka dosa. Da shigarsu zaure suka jiyo muryarta tana sababi tana faɗin “Wato ko ganin shi ban yi ba, amma ya tafi wurin Jummai ƙanwar Uwarshi.”

Tare suka kalli Juna shi da Abbanshi, “Sai ka san yadda zaka kare kanka, ni dai ba ruwana,” Alhaji Mainasara ya faɗa cikin sigar tsokana, dariya Habeeb ya yi, suka shiga cikin gidan.

Zaune suka hange ta kan tabarma, tamiƙe ƙafafunta da suka fara kumburi saboda ciwo.

Tana ganinsu ta yi tsit, idanunta tar akan tilon ɗanta, wanda ta daɗe da fidda rai da sake ganinsa.

Habeeb kuwa wata irin faɗuwar gaba ce ta same shi, saboda chanjarwar da mahaifiyarsa ta yi, da tunanin halin da ya sa ta rama da ɓaki suka ƙarasa inda take.

Haƙiƙa ta yi farinciki da ganin Habeeb, amma sai haushin bai fara zuwa inda take ba ya sa ta ƙin gwada murnarta.

Gwaggo da sallamarsu tasa ta fitowa daga ɗaki ta washe baki tare da faɗin “Oyoyo, mijina ya dawo”, lokaci ɗaya kuma ta tarbi Habeeb ɗin.

“Rai kan ga rai maigida,” ta faɗa tare da riƙe haɓa tana dariya.

Dariya su duka zuka yi, sannan ta juyo wurin Alhaji Mainasara ta ce “Sannunku da zuwa Alhaji.”

“Yauwa Gwaggo.” Ya faɗa. Ita kuwa Hajiya Mairo sai ƙara ɗaure fuska take.

Ɗaki gwaggo ta shiga ta ɗauko tabarma tare da shimfiɗawa. Zama Alhaji Mainasar ya yi, shi kuma Habeeb ya je kan tabarmar da Ummanshi take ya zauna a gefenta.

Genfen Habeeb ɗin Gwaggo ta zauna suka sanya shi tsakiya, cike da farincikin samun lafiyar Habeeb ta sake dubanshi “Allah Sarki Habeebeena, ina nan na gaza ci na gaza sha saboda mijina bai da lafiya.”

Dariya su duka suka yi hada Hajiya Mairo ɗin.

Gaisawa Alhaji Mainasara ya yi da gwaggo, sannu da zuwa da kuma ya jikin Habeeb ta yi mashi, bayan ya amsa Habeeb ma ya gaishe da ita.

Ta ce “Ai ba rabon in chanja miji” suka sake yin dariya, fatan ɗorewar lafiya ta yi mashi.

Hajiya Mairo ce ta juyo wurin Alhaji Mainasara ta gaishe da shi, babu alamun fushi ko kaɗan a ransa, sai ma tausayinta da ya kama shi ya amsa.

Sannu da zuwa ta yi mashi, shima ya amsa.

Habeeb ne ya riƙo mata hannu ya ce “Umma Ina wuni.”

Janye hannunta ta yi, ta ce “A’a Habeeb, Ai Asabe ce Ummanka.”

Ido ya lumshe cikin ransa domin ya fahimci ta ji haushi.

Sassauta murya ya yi, tare da sake riƙo mata hannu ya ce “Don Allah ki yafe ni Umma, ke duk duniya ba wanda zai mani iso akan ki, amma su ba zan iya zuwa inda suke ba sai da ɗan jagora.”

Shiru wurin ya yi, Habeeb ya ce “Sune ciwo na Umma, kuma sune maganina, don haka idan kina son ɗorewar lafiyata kada ki ji haushi don na fara zuwa wurinsu kafin ke.”

Wani mugun kallo ta yi mashi, wanda ya sa shi faɗaɗa maganarsa ta yadda zata fahimta.

“Umma yafiyarsu na je nema, domin na cutar da su, kuma alhakinsu ke bibiyata, Umma Allah ya jarabce ni da son rayuwa da su, Fateema ce zaɓina, ita nake so, kuma ita ce lafiyata da rayuwata.”

Idanunsa cike da ƙwalla ya ƙarasa maganar, hannunsa ta riƙe gam tana jin kamar ta yi kuka.

Gwaggo kuwa tuni idanunta sun cika da hawaye “Allah Sarki Jikana.”

Alhaji Mainasar kuwa take ya kiɗeme a ransa, domin baya fatan rasa ɗansa, daga inda yake ne ya riƙa lallashin Habeeb ɗin.

“Habeeb, ka kwantar da hankalinka, komai ya zo ƙarshe da ikon Allah.”

Shiru Habeeb ɗin ya yi, daga bisani ya ce “Umma, mahaifiyar Fateema ta yafe mani, kema don Allah ki yafe mani.”

Hannu ta sa ta goge ma Habeeb hawayen dake gudana a idonsa.” Na yafe maka Habeeb, Allah ya yafe mana baki ɗaya.”

“Nagode Umma, sannan don Allah kada ki hana ni auren Fateema.”

Ido ta lumshe, don bazata iya bashi amsa a wannan gaɓar ba, saboda bata san da wace fuska zata kalli su Asabe ba.

Gwaggo ta ce “Insha Allah sai ka maida matarka, ka dena kuka ka ji.”

Jikan Gwaggo ne ya shigo, bayan sun gaisa Alhaji Mainasara ya ce ma Habeeb ya tashi ya bishi a waje.

Goge hawayen dake fita a idonshi ya yi, sannan suka tashi, acan jikan gwaggo ya yi ta bashi haƙuri saboda ya san komai. 

Anan kuwa Alhaji Mainasara ne ya yi gyaran murya, wanda Gwaggo da Hajiya Mairo suka maido hankulansu gare shi.

Gwaggo ya duba ya ce “Ki zama shaida anan.”

Kai gwaggon ta gyaɗa alamar “Toh,” duban Hajiya Mairo ya yi “Mairo yanzu dai rayuwa ta isa ta bayyana mana gaskiyar lamari, Ɗanki Habeeb shi ya zama silar lalacewar Fateema, wanda dalilin haka munanan abubuwa da yawa sun faru waɗanda kare ba zai ci ba. 

Kasaƙe su duka suka yi, wayarsa ya zaro daga aljihu ya nuna mata hoton yadda zuciyar Habeeb ta kumbura.

“Kin ga zuciyar ɗanki, saura ƙiris ta fashe Allah ya agaza masa”.

Karɓar wayar ta yi, aikuwa ta shiga sallami, take ta fara kukan da ya maƙale mata a zuciya.

“Kalli zuciyar Habeeb, gwaggo, na shiga uku ni Mairo.”

Gwaggo na karɓa itama ta fara sallalami.

Alhaji Mainasar ya ce “Toh an yi aiki kuma an samu nasara, sai dai me lafiyar zuciyar na tare da kwanciyar hankalinsa,  shi kuma kwanciyar hankalin yana tare da Fateema, Ita yake so ya rayu da ita.”

Charaf gwaggo ta yi ta ce “Ai abu ne mai sauƙi, tunda Asabe ta iya yafewa, toh har ƴar ba zata hana shi ba.”

Girgiza kai Alhaji Mainasara ya yi ya ce “Ba sauƙi fa gwaggo, don ta samu miji, yanzu haka rana irin ta yau zasu zo neman aurenta.”

Ido Hajiya Mairo ta zaro, don “Na shiga uku, toh yanzu Habeeb din fa.”

Ya ce “Nima shi ne damuwata, don haka aiki Ja a garemu, idan zaku yi watsi da gaba da ƙiyayya, toh zaku iya ceto rayuwar ɗanki.”

Ido Hajiya Mairo ta lumshe cikin ranta tana jin wata ƙuna, domin duk ita ce sila, da bata sanya Habeeb ya saki matarsa ba, da duk waɗannan matsalolin da suke ciki ita da shi basu faru ba.

A hankali ta buɗe idanun, sannan ta fara magana mai cike da nadama ” Wannan matsalar duk ni ce sila, da na san haka zata faru, da ban sa ya saki matarsa ba.”

“Hmm” kawai Alhaji Mainasara ya faɗa a ransa, don shi har yanzu bai yadda kukan gaske take ba.

Gwaggo ma shiru ta yi, saboda Mairo bata ga komai ba.

Tashi Alhaji Mainasara ya yi zai fita, Gwaggo ta ce “Ga fura da ruwa Alhaji “

Ƴar dariya ya yi ya ce “Ashe zaki bani, tunda muka shigo kike ta miji, shi kuma ɗa kika barshi a gefe.”

Ta ce “Toh idan ban tari miji ba, wa zan tara.” Suka kama dariya.

Komawa ya yi ya zauna, da yake gwani ne a wurin shan fura. Mairo kuwa tashi ta yi ta shige ɗaki.

Sabuwar fura Gwaggo ta dama mashi yasha, yana gamawa suka dasa hirar yaushe gamo.

Gaba ɗaya Al-amura sun cakuɗe ma kowa akan lamarin Jummai da Habeeb. Hajiya Jummai ta rasa yadda zata ɓullo ma lamarin, haka Alhaji Mainasara ma.

A wurin Asabe ma hakan take, domin ta ga matuƙar sauyi a fuskar Alhaji Mainasara lokacin da ta faɗa mashi Jummai ta samu miji, kuma hakan bai mata daɗi ba, domin bata fatan ta zama silar ɓata ransa, saboda alkhairorin da ya yi musu a rayuwa.

Abin na ta cinta a rai, ta rasa ta ina zata fara yi ma Uwani maganar, sai can bayan magarib suna zaune a ɗaki ta dubi Uwani.

“Uwani duk wani iri nake ji wallahi, gani nake kamar ban kyauta ma Alhaji Mainasar ba da na ce Jummai ta samu miji.”

Tabbas itama Uwani ta ga sauyin yanayinsa, toh amma tunda ba hana shi aka yi ba ai ba wani abun damuwa bane, cewa ta yi “A’a Yaya Asabe, sai in ga kamar ba wani abu, tunda dai da gaske ta samu mijin nan, kuma nagartacce wanda ya fi ɗansa ma.”

Ɗan shiru Asabe ta yi, daga bisani ta ce “Allah kuwa da wani abu Uwani, baki ga yadda ya fita bane?”

Uwani ta ce “Na gani, amma dole ya yi haƙuri, tunda an riga ɗansa.”

“Ni dai don Allah ki fahimtar dashi, bana son ya ji wani abu a ransa dangane da wannan lamari.”

Tabbatar mata ta yi da har idan ta ga wani abu mai kama da damuwa a tare da shi, toh zata fahimtar da shi.

Cike da rashin jin daɗi abin suka cigaba da maganar, har aka kira sallar Isha’i, tashi suka yi suka gabatar da ita.

A ɓangaren Habeeb kuwa tunanin yadda Jummai ta yi wani irin kyau yake “Wai wane irin gata ne ta samu haka” ya tambayi kansa, domin ta ninka sadda suka haɗu a UK.

“Allah ka bani Fateema, ka sa ta saurare ni a karo na biyu.”

Haka ya yi ta kwararo addu’a, domin bai san wace waina ake toyawa ba, Alhaji Mainasara bai faɗa mashi ba, itama Hajiya Mairon bai ji daga bakinta ba.

Ƙagara ya yi safiya ta yi don ya je gidan.

Gari na wayewa ya je gaida mahaifiyarsa, kallonsa ta yi, sai ta ga tsakanin jiya da yau ya ƙara ramewa.

Cikin raunin murya ta ce “Habeeb”

Saka idanunsa da suka yi zuru-zuru ya yi cikin nata.

“Ko dai baka warke bane?”

Kai ya girgiza. “A’a Umma.”

Shiru ta yi, don ta san bai warke ɗin ba, saboda Jummai ce cikakken maganinsa.

“Toh shikenan, bana son kana sanya damuwa a ranka.”

“Toh Insha Allah Umma”.

Gaishe da Gwaggo da ta shigo ɗakin ya yi, sannan ya tashi zai fita.

Tsaida shi Hajiya Mairo ta yi ta ce “Ka tsaya ga kalaci.”

 “Sai anjima zan yi.” Ya faɗa tare da fita.

A ƙofar gida ya tsaya a jikin bishiyar bedin gidan. Mutanen dake ta kai da kowawa ne yake ta kallo.

Daga nesa ne ya hango Basheer riƙe da hannun Ahamad suna tafiya, sauri ya yi ya ƙarasa wurinsu.

Gabansu ya sha, da yake Basheer ya ganshi jiya a gidansu ya gaida shi. “Ina kwana.”

“Lafiya lau” ya faɗa, lokaci ɗaya kuma idanunsa na kan Ahamad da ke ta kallon shi.

“Ina zaku je ne?”  Basheer ya ce “Aiken mu aka yi.”

 Ɗan jinjina kai ya yi sannan ya duƙa tare da dafa kafaɗun Ahamad ya tambaye shi “Ina Mama?”

Cikin rashin iya magana ya ce “Tana jida.”

Murmushi ya yi ya ce “Toh ka ce Abba na gaida ta.”

“Toh” ya ce, sannan ya shafi kansa.

Miƙewa ya yi, ya ce ma Basheer, “Ka gaida Inna”, toh ya ce ya ja hannun Ahamad suka tafi.

Bayansu yabi da kallo, cikin ransa yana jin wata irin ƙaunar ɗansa, ido ya lumshe lokacin da suka ɓace ma ganinsa.

Su Basheer na zuwa gida Ahamad ya ce “Umma, Abba yana gaida ci.”

Baki ta taɓe ta ce “Wahalallen banza da wofi, bazan amsa ba.”

Aisha ce ta ce Ahamad ɗin “Toh tana amsawa.”

Can wurin ƙarfe biyu Habeeb ya shirya ya nufi gidan Asabe, tunda ya shiga gidan yake ta raba idanu, sai dai bai ga Jummai ba, sai muryarta da su Aisha suna ta shewa, da yake can ɗakin Malam Amadu suka tare.

Cikin ɗaki ya samu su Asabe, da girmamawa ya gaishe su, ƴar hira suka taɓa da Uwani, Asabe kuma ta fito don bata da abin da zata ce.

Da zai tashi ne ya ɗauki Salim suka fice, a waje kuma ya tarar da su Ahamad.

Jansu ya yi suka je shago, biscuits da chocolates ya siyo musu, sannan suka dawo.

Jummai ana bata ta ce “In yi me da shi?” Uwani ta ce “Ke don Allah abu bai wucewa ne, a yafe ma juna mana don Allah.”

Wasu hawaye ne suka ga suna fita a idonta, wanda ita kadai ce zata iya fadin ko na miye. 

Da yamma ne kuma Uwani da Alhaji Mainasara suka shirya zasu koma gida, shi kuma Habeeb anan garin zai zauna har ranar da Hajiya Mairo zata koma, sai su tafi tare. 

Har kofar gida su Jummai suka rako Uwani ita da su Aisha, Habeeb na ganin Jummai ya kara faɗaɗa fara’arsa, ita kuwa duk sai ta yi kicin-kicin da fuska.

“Fateema” ya kira sunanta cikin raunin murya, amma ta yi kamar ba da ita yake ba. Allah ya kiyaye ta ƙara yi ma su Asabe, motar na tafiya ta juya zata shige gida.

“Don Allah ki saurare ni Fateema” ya faɗa tare da bin bayanta.

Ganin ta ƙi tsayawa sai ya juyo ga su Aisha, Salma ya kalla ya ce “Don Allah ƙawata ki yi kata Magana.”

Ɗan haɗe fuska ta yi, don me zai ce mata ƙawata.

Marairaicewa ya yi ya ce “Please.”

“Ok tam” ta ce, bayan Jummai suka bi, shi kuma ya tsaya a bakin zauren gidan.

Tsaye suka same ta a zaure na biyu tana jiransu, Aisha ta ce “Don Allah ki saure shi ki ji me zai ce maki.”

Ƙara haɗe rai ta yi don har yanzu ta kasa mantawa da tozarcin da ya yi mata.

Cewa ta yi “Ba wani abu da zan iya saurara a wurin wancan azzalumin mutumin, don haka ya yi ta kansa ma.”

Akan kunnensa Jummai ta faɗi haka. Ido ya lumshe tare da haɗe wani gululun baƙinciki.

Tamkar zuciyarsa zata fito ya juya ya tafi.

Salma na leƙowa ta hange shi ya sha kwana.

Sadda ta dawo har sun shige cikin gidan “Ya tafi ma” ta faɗa tana kallon su.

Asabe dake tsaye ta tambaye su. “Wa kenan?”

kamar Jummai zata yi kuka ta ce “Wancan banzan Habeeb ɗin mana, Allah kuwa idan ya cigaba da matsa mani sai ya ga rashin mutunci.”

Baki kawai Asabe ta ta6e don bata da abin cewa anan.

Habeeb kuwa juwa na dibar sa ya isa ɗakin da yake kwana, zama ya yi jikin bango tare da haɗe kai da gwiwa “Me ya sa Fateema take da riko ne, me ya sa ba zata saurari nadamata ba” hawaye ne suka cika mashi ido, kuka mai tsuma zuciya ya rika yi tare da neman agajin Allah.  

Alhaji Mainasara ya ga sadda Jummai ta share Habeeb a lokacin da zai tada mota, kuma abin bai masa daɗi ba. Sai da suka yi nisa da tafiya ne ya ce ma Uwani “Ban san ya zan yi da lamarin Habeeb ba, ya kai maƙura a wurin son yarinyar, gashi kuma ta samu miji, sannan na fahimci fushi mai tsanani take da shi”, cike da damuwa ya ƙarasa maganar, don yana ji a jikinsa ko da Jummai bata samu miji ba, toh abu ne mai wahala su daidaita ita da Habeeb.

Ƴar ajiyar zuciya Uwani ta yi sannan ta dube shi “Wannan lamari a bar ma Allah kawai Alhaji, sannan batun fushi zata gaji ta huce ne, Allah ma muna masa laifi ya yafe, bare kuma mutum.”

Maganganun da zasu kwantar mashi da hankali ta ciga da faɗa mashi, don ta fahimci tsantsar damuwa a tare da shi.

Cikin ikon Allah kuwa damuwar da ke ransa ta ragu, hira suka cigaba da yi, har Allah ya sa suka isa gida lafiya.

Habeebullah bawan Allah! Soyayyar Jummai ta yi girman da cire ta zai iya jijjiga zuciyarsa har ma da zuciyoyin da ke tare da shi, don haka ko da wasa bai taɓa gigin fara cire ta ba, sai ma neman hanyar da zata ji daɗin zama a muhallin da ya yi mata yake.

Tabbas ya yadda ya zalunci Jummai, mafarin ya ƙara jin ƙarfin zuwa neman afuwarta, tare da tabbatar mata da zai karɓi duk hukuncin da zata yi mashi, matuƙar daga baya zata amince da soyayyarshi.

Shawara zuciyarshi ta bashi da ya je wurin mahaifiyarta domin ta sa baki a wurin bata haƙurin, kuma ya karɓa, saboda gani yake shawara ce mai kyau. Cike da ƙwarin gwiwa ya tashi ya nufi gidan, sai dai tun a zaure jikinsa ya yi sanyi.

Jummai da Ameer ya gani suna ta sheƙa soyayyarsu, kallo ɗaya zaka yi musu ka tabbatar da suna cikin nishaɗi.

Wata irin faɗuwa gabansa ya yi, wadda bai san sadda ya dafe kirji ba. Daga can cikin zuciyarsa kuma ji yake kamar zata rabe gida biyu.

Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci idanunsa suka kaɗa kamar garwashi.

Jummai da Ameer kuwa mamaki ne ya kama su, don sai dai suka ganshi tsaye a gabansu yana ta huci.

Haɗe fuska suka yi, barin Ameer da ya ji a jikinsa wannan ne Habeeb, wanda kuma a duniya ba wanda ya tsana kamarsa, domin shine musabbabin lalacewar Jummai.

*Ni kuma na ce shine sanadin haduwarka da Jummai, da bai ɓata ta ba, toh da ba inda zaka ganta, tuna maka na yi Ameerin sarkee*.

“Malam lafiya ka shigo ma mutane ba ko sallama,” Ameer ya faɗa cikin fushi.

Hannu Jummai ta ɗaga ma Ameer ɗin, wanda yake nufin ya barta da habeeb.

Habeeb kuwa bai ma san me Ameer ke cewa ba saboda tsananin tashin hankali, cikin wata irin murya mai raunin gaske ya ce “Fateemah waye wannan?”

Idanunta cikin nasa ta bashi amsa da “Wanda zan aura ne bada jimawa ba,” don dama neman hanyar da zata ƙumsa mashi baƙinciki ta ke.

Kaifin wannan magana da Jummai ta faɗa mashi ya fi na sabuwar reza, hakan ya sa maganar ta shiga datsar zaren da ke ɗinke a jikin zuciyarsa.

Wani mugun kallo ya yi ma Ameer da ke ta huci kamar kububuwa, sannan ya sake dubanta ya ce “Fateema da gaske shi zaki aura?”.

Cikin masifa ta ce “Na taɓa yi maka ƙarya?”,ya girgiza kai “A’a”, ta ce “Toh ka san na yi, babu sauran lokacinka a wurina.”

Lumshe idanunsa ya yi lokacin da wasu zafafan hawaye suka cika su, a hankali ya buɗe su sannan ya juya ya fita.

Ameer ya ce “Wai wannan marar kunyar me yake nufi ne?” Baki ta taɓe “Ina fa zan sani, can matsalarsa ce.”

Kishi ne ya turnuƙe zuciyar Ameer, don ya ga zallar son jummai a tare da Habeeb “Ban haɗa ki da kowa ba, kuma wallahi tsaf zan bige shi idan ya ƙara ko kallonki ne.”

Ita dai haɗe fuska ta yi, don Habeeb ya ɓarar mata da farincikinta.

Jefi-jefi suka cigaba dayin hirar, ganin duk ba daɗi Ameer ya ce “Bari in dawo.” yana faɗin haka ya fita, ita kuma ta dawo ciki.

Wurin Dr. Misau dake ta ƙoƙarin shawo kan Aisha ta karɓi tayinsa Ameer ya nufa, don tunda ya ganta ya ji duk duniya ba tauraruwar mace irin ta.

*Na ce sholy wallahi kada ki wahalar min da ɗaa, Abdullahi namijin azo a gani ne, idan kika same shi toh kin gama morewa*

Aisha na ganin Ameer ta ce “Tafiya zan yi”, ya ce “Ok toh, zamu yi waya.”

hararar wasa Ameer ya yi mata, ta tafi tana dariya.

Labarin abin da ya faru  Ameer ya faɗa mashi.

Dr. Misau ya ce “Na kuwa ga shigarshi, da alamu ma kamar bai da lafiya.”

Ameer ya ce “Ko gawa ne ni bai dame ni ba, tsaf zan saɓa masa kamannu wallahi.” dariya ce su duka suka yi, daga bisani suka ɗora hirarsu ta abokai, har misau ɗin ke bashi labarin ya shawo kan Aisha da ƙyal.

Dariya Ameer ya yi sannan ya ce “Ai mata ba’a samun su a ɓagas Dr., Kafin ka je wurinsu ne zaka ga abin zassauƙi, sai ka je ka ga ba haka bane”, dariya su duka suka yi, Dr. Misau ya ce “Na yadda abokina.”

Habeeb kuwa yana can ya rikice ma mahaifiyarsa, kuka kawai yake yana faɗin “Umma mutuwa zan yi idan na rasa Fateema.” Yana cikin magana tari ya sarke shi,

Hannu ya sa ya goge yawun da ya jalalo mashi daga baki, yana dubawa ya ga jini, wanda kuma Hajiya Mairo ta riga shi ganinshi.

Cikin tashin hankali ta sa hannu ta gogo jinin, lokaci ɗaya kuma bakinta na faɗin “Innalillahi wa inna ilaihi raji’una.”

“Kin gani ko Umma, mutuwa zan yi” ya faɗa yana ƙara gogo jinin shi ma. 

Tamkar zuciyarta zata fashe itama. riƙe shi ta yi tana kuka ta ce “Habeeb duk ni naja maka wannan lalura, da ban ce ka sake ta ba, da haka bata faru ba.”

kuka sosai suka rika yi hada gwaddo, duk wanda ya ga yanayin Habeeb dole ya tausaya mashi.

Gwaggo na kuka ta riƙa basu haƙuri, sannan ta dangwalo ƙasa ta dafa ƙirjinsa ta cigaba da yi mashi addu’a, domin daidai gwargwado tana da sani.

Ido Habeeb ya lumshe yana jin raɗaɗin dake zuciyar yana ragewa, domin addu’ar da Gwaggo ta yi mashi kamar yankan wuƙa take, muddin dai an yi ta da yaƙini.

Kwatar da kansa ya yi kan cinyar Ummanshi tare da lumshe ido, ita kuma ta cigaba da shafa mashi kai haɗe da lallashinsa.

Tana ganin ya fara samun nutsuwa, ta ce gida zasu, kayansu gaba ɗaya suka haɗa tare da barin ƙauyen

So manya! Ko kashe shi, ko ya kashe ka.

Maman Mu’azzam

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×