Skip to content
Part 5 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Gabaɗaya Asabe da Malam Amadu sun kasa kunne suna jiran Jummai da ke zaune a gabansu, ta faɗa musu wanda ya yi mata ciki, sakamakon tsawon lokacin da ta ɗauka tana ɓoye musu.

Kan Jummai na ƙasa ta ce, “Habeeb ne.”

kusan duk ba su ji wanda ta ce ba, saboda murya ƙasa-ƙasa ta yi magana.

Cikin tsananin fushi Asabe ta ce “Wa kika ce?”

Jikinta na kyarma ta ɗago kai ta dube su, don har yanzu fargabar faɗa ta ke.

“Habeeb ne, kuma ya ce sai ya kashe ni idan na faɗa.”

“La’ilaha ila Llah….” Asabe ta shiga faɗi.

suka ƙarasa, Muhammadu Rrasulu Llahi Salallahu alaihi wa sallam” ita da Malam Amadu a tare.

Sanin waye Habeeb ya sa  Asabe kiɗemewa, bata san lokacin da ta ɗora hannunta a kai ta fashe da kuka ba.

“Na shiga uku ni Asabe!”

Ido Malam Amadu ya shiga warewa yana son sanin waye Habeeb.

Kafin ya ankare Asabe ta rufe Jummai da duka, tana faɗin, “Don ubanki! kafin ya kashe ki, ni zan kashe ki”

Gaba ɗaya Malam Amadu ya rikice, ya rasa ta ina zai ceto Jummai daga neman agajin da ta ke, domin Asabe ta danne ta, kuka da ihun ceto kawai take yi.

Sai da ya yi da gaske ya iya ɗaga ta, “Anya kuwa kina cikin hayyacinki Asabe?, Kin san me kike shirin aikatawa”

Cikin takaici da ƙunar zuciya ta ce,  “Koma me zan aikata gwara na yi, tun kafin mu ta kashe mu”.

Tana kaiwa nan ta fizge hannunta da ke riƙe a hannunsa ta yi kan Jummai.

Kafin ta kai gare ta ya yi saurin cafko ta.

Duk wani tunani nashi ya tsaya, burinshi kawai ya san waye wannan da ya gurɓata musu farincikin gida.

Idanunsa kan Asabe da ke ta huci kamar kububuwa.

Ya ce”Asabe, waye Habeeb?”

Ta ce “Ɗan gidan Kishiyar Uwani mana.”

Hannu Malam Amadu ya shiga tafawa, lokaci ɗaya kuma bakin shi yana salallami.

Jirin da ya saba ɗibar shi duk lokacin da ya ji wani tashin hankali, shine ya ɗibe shi.

A hankali ya bi bango ya zauna, yana jin dama ba’a haife shi a duniya ba, bare har ya ga ranar da abokin gabarsa zai samu nasara a kansa.

Waiwaye

Uwani ƙanwa ce a wurin Asabe, wadda suke uwa ɗaya uba ɗaya da ita.

Tana auren wani mai kuɗi, mai suna Alhaji Mainasara, wanda suke zaune a katafaren gidansu da ke birni.

Uwani ta haɗu da Alhaji Mainasara ne a kan hanyarta ta wucewa, lokacin shi kuma yana ƙofar gidan Iyayen matarshi wato Hajiya Mairo.

Tsaye suke a gaban motarsa suna hira shi da wani ɗan garin mai suna Labo.

Tunda Uwani ta doso wurin Alhaji Mainasara ke kallon ta, cikin ranshi kuma yana yaba kyawo irin nata, sai da ya ga ta tsaya kusa da su ne ya ɗauke idonsa, don bai so ta gane yana kallon ta.

Itama Uwanin Idonta na kan motarsa, wadda tunda take bata taɓa ganin Mota mai kyau irin ta ba.

Gaisawa ta yi da wasu mata tsofaffi ‘yan garinsu, bayan sun wuce ta juyo ta gaida Labo haɗe da Alhaji Mainasara a lokaci ɗaya, cike da jin daɗin gaisuwar suka amsa. 

Tambayar ta Labo ya yi, “Sai ina haka da yammacin nan?”

Amsa mashi ta yi da “Zan je gidan Yaya Kabiru”, lokaci ɗaya kuma kanta na ƙasa don ta fara tsarguwa da kallon ƙurillar da Alhaji Mainasara ke yi mata. 

Kai Labo ya gyaɗa, “Ayya, toh a dawo lafiya”, ta ce “Amiin”, sannan ta wuce.

Da ido Alhaji Mainasara ya raka ta, har sai da ta sha kwana sannan ya maido hankalinsa ga Labo tare da jefo mashi tambayoyi biyu a jere,

“Wace ce waccan, kuma tana da aure?”

Sai da Labo ya yi dariya, sannan ya tabbatar mashi da ‘yar garin ce, kuma bata da aure, mijin ta ya rasu sakamakon hatsari.

Alhaji Mainasara ya yi farinciki da jin haka, don haka ne ma ya nemi sanin gidansu Uwani a wurin Labo.

Bayan Sallar Isha’i tana zaune tsakar gidansu, sai ga ɗan aike, ana kiran ta.

Ɗan ɓata rai ta yi, cikin ranta kuma tana faɗin “Jarababbun sun fara”, a zahiri kuma ta ce ma ɗan aiken “Koma ka ce wane ne?”

Ɗan aiken bai daɗe da fita ba ya dawo, “An ce baƙo ne.”

Baki ta taɓe saboda ta gaji da wannan hirar marar amfani, kusan duk mazan ƙauyen son ta suke.

Kamar ta ce bata nan, sai kuma wata zuciya ta kwaɓe ta.

Cikin ɗaki ta koma ta ɗan gyara jikinta,

Kakarsu da ke zaune a kan abin salla na ganin tana shiri ta fara tsokanar ta, “Uwani mai zawarawa”.

Dariya kawai ta yi, ta nufi waje.

Ba ƙaramin Mamaki ta yi ba a lokacin da ta ga Alhaji Mainasara a matsayin baƙon da ya zo wurinta.

Tunda suka gaisa ta yi shiru, don gani take kamar almara, darajarta ba ta kai tsayuwa da mutum kamar Alhaji Mainasara ba, saboda kuɗin da yake da su, ita kuma gata ‘yar ƙauye.

Ni kuwa na ce, darajar ‘ya mace takai kalar kowane namiji ya so ta,  har ma ya aure ta.

Bai wani ɓata lokaci ba ya shiga bayyana mata sirrin zuciyarsa, cewar aure ya kawo shi a wurinta, tare da bata damar yin nazari, duk hukuncin da ta yanke, toh yana buƙatar jinsa a wurin Labo.

A wannan dare rutsum Uwani bata rumtsa ba, tambayar kanta ta shiga yi da “In amince, ko kuwa?”, kasantuwar ta san ko wacece matarshi, da kuma irin gabar da ke tsakanin a halinsu.

Tunda safe ta nufi gidan Asabe, neman shawara a kan ta amince ko kuwa?

Wata irin buɗa Asabe ta rafka lokacin da Uwani ta faɗa mata Alhaji Mainasara na son ta.

Leƙowa Malam Amadu ya yi cikin ɗakin, yana dariya ya ce “Abin daɗi ake ma buɗa, me ya faru ne Uwani?”

Dariya su duka suka yi, Asabe ta ce “Je ka dawo Malam, zan baka labari”

Yace “Toh shikenan”, yana faɗin haka ya juya yana dariya.

Duban Uwani Asabe ta yi, farin ciki fal da zuciyarta, “To Gwaggo ta amince?”,

Uwani ta ce “Eh ta amince.”

Asabe ta sake rafka wata buɗar “Na amince nima, muddin kina son Alhaji Mainasara, toh ki aure shi, ke ko baki son shi ki aure shi, don mu ƙumsa ma waccan matsiyaciyar matar ta shi takaici”.

Uwani bata baro gidan Asabe ba, sai da ta gama zuge ta a kan ta amince ta auri Alhaji Mainasara.

Tana komawa gida sai ga Labo ya zo, bayan sun gaisa ya ce “Saƙon Alhaji na zo karɓa, saboda zai tafi gida an jima.”

Cike da fargaba ta faɗa ma Labo amincewarta.

Labo na komawa ya faɗa mashi ta amince, aikuwa ya yi murna ba kaɗan ba, don fatanshi Allah ya bashi matar da zata share mashi hawaye, kuma da alama ya samu, don Labo ya bashi labarin Uwani, mace ce mai haƙuri da kamun kai.

Ba tare da wani ɓata lokaci ba ya samu iyayen Uwani, tare da neman su bashi auren ta.

wasu daga ciki sun yi na’am, wasu kuma suka ce kada ayi auren nan, saboda zai ƙara rura wutar gabar da ke tsakanin ahalinsu Uwani, da na matar shi Hajiya Mairo.

Waɗanda suka amince su suka fi rinjaye, kuma su ne dangi mafi kusa da Uwani, don haka aka sa ranar da za’a ɗaura aure.

Hajiya Mairo na zaune a gidanta ‘yan gulma suka zo mata da labari, cewar Uwani ƙanwar Asabe zata aure mata miji, da farko bata yadda ba, don gani take ba abin da mijinta zai yi da Uwani.

Tsaye abin ya yi mata a rai, ta ɗauki waya ta buga a gida don jin tabbacin abin, aikuwa aka tabbatar mata da haka ne.

Bala’i da zage-zage ta shiga yi a kan bai isa ya auro mata ‘yar matsiyata ba. 

Zaman jiran shi ta yi a falo, aikuwa har bayan Isha’i bai dawo ba. Kiran shi ta yi a waya “Wai kana ina ne?”, daga can ya ce “Na je ƙauye, amma ina hanyar dawowa gida”.

Ba tare da ta ƙara magana ba ta tsinke kiran, don tana da yaƙinin wurin Uwani ya je.

Fuu! Ta tashi ta nufi ɗakinta, sallar Magrib da Isha’in da taƙi yi saboda jiranshi, su ta gabatar.

Bata tashi daga kan abin sallah ba, ta ji shigowar motarsa.

Sai da ta ɓata lokaci tana tunanin matakin da zata ɗauka, sannan ta tashi tare da cire Hijabi ta nufi ɗakinsa.

Fuskarta ba annuri ko kaɗan ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, tsaye ta same shi, yana shirin aje babbar rigar da ya cire a kan gado.

Sanin abin arziki bai cika kawo ta wurinshi ba ya sa tunda ya kalle ta sau ɗaya bai sake ba.

Kamar abin arziki, ta karɓi babbar rigar ta aje.

Sannan ta kai hannu a wuyansa kamar zata ɓalle masa botiran riga.

Tunani ya shiga yi, yaushe Mairo ta chanja, wadda idan ya dawo ko sannu bata yi mashi, amma yau ita ce da taya shi cire kaya.

Tsinke tunanin ya yi lokacin da ya ji ta ci mashi kwalar riga, fuskarta ba annuri ko kaɗan ta ce “Munafikin Allah, me ka je yi a ƙauye?”

Da yake wannan ba sabon abu bane a wurinshi ya ce “Kin aike ni ne? “, lokaci ɗaya kuma yana ɓanɓarar hannunta daga wuyanshi.

“Eh na aike ka”, ya ce “Toh na manta saƙon ban kai ba.”

Ganin zai raina mata hankali ta ce cikin sababi, “Kada maida shi shashasha, duk munafuncin da kuke ƙullawa ya dawo mani, aure kuma baka isa ba wallahi, ba ubanda zai kawo mani irin matsiyata a gidannan.”

Sai da ya yi murmushin takaici sannan ya ce “Kai na yaba ma munafikin da ya kawo maki labari.

Aure kuma da gaske ne zan yi, kuma ba fashi, ga Uwani can ta shigo gidannan, sai dai ki yi duk abin da kika ga dama”,  yana gama faɗin haka ya shiga ingiza ta waje.

Aikuwa ta ƙulu, zagin Uwani ta shiga yi “Shaggu irin mayu, aurenta uku mazan na mutuwa, shine zaka auro mana ita.”

Da yake ya san sharri ne, sai ya kama dariya “Ko ita ce Uwar mayu, na ji na gani, idan ya so bayan ta shigo duk ta lashe ku mu huta”.

Yana gama faɗin haka, ya turo ƙofar ɗakin ya sa key.

Aikuwa kamar zata yi hauka, “Ni Asabe zata yi wa iskanci, ƙanwarta zata ƙaƙabawa mijina ya aura, toh wallahi ƙaryar bokayen naki, shegiya tsinanna”

Haka ta yi ta zage-zage har ta dawo falo. Tilon matashin ɗanta mai suna Habeeb na shigowa ya iske tana ta sababi.

Cike da damuwa ya tambaye ta abin da ya faru.

Ta ce “Alhaji ne zai ƙara aure.”

Fuskarsa ɗauke da mamaki ya sake tambayar ta “Aure Umma?”

Ta ce “Ƙwarai, kuma duk ya rasa wadda zai aura sai Uwani ƙanwar Asabe”,

Da yake ya san Asaben, kuma ya san irin gabar da ke tsakanin su ya ce “Tab, ai wallahi ba za’a auro mana waɗannan shaggun ba, kai ba su ba ma, ba wata shegiya da za’a kawo mana a gidannan, idan kuwa har ta kuskura ta shigo, toh ta shiga uku wallahi”.

Habeeb bai san babanshi na gidan ba, ya yi ta ɓarin magana da zage-zage,  kamar daga sama ya ji muryar shi yana faɗin,

“Habeeb, kai zaka saka matar da zan aura ta shiga uku, toh ga fili nan, da alamu uwarka ce zaka saka a cikin ukun, sakaran banza marar wayau, ta shi ka ɓace mani a gani”.

Kamar mai shirin tashi sama ya miƙe ya nufi ƙofa yana gunguni.

Duba Alhaji Mainasara ya kai ga Hajiya Mairo, da ke ta huci ya ce  “Ke kam an yi Uwar banza wallahi”.

Cike da masifa ta yo kansa da nufin sake ci mashi kwala.

Ja da baya ya yi tare da ware Hannaye, “Kada ki yi gigin sake taɓa ni, aure dai ba fashi, duk abinda kika ga dama kiyi”. Yana gama faɗin haka ya yi waje, ba tare da ya tsaya jin me take cewa ba.

Zagi ta uwa ta uba ta raka shi da shi, ganin ya maida ta mahaukaciya, sai ta ɗauki waya ta kira ƙawarta cewar da safe su yi mahaɗa a gidan Malam.

Kuɗaɗe ba kaɗan ba ta zazzage ma Malaminta a kan kada a bari mijinta ya yi aure, da yake abin a hannun Allah yake, ba hannun Malam ba, sai dai ta ji ana buɗa, dangin Amarya sun zo jere.

A ɗayan part ɗin da Alhaji Mainasara ya ware ma Amaryarsa mai rabo, nan ‘yan jere suka nufa.

Zumbur Hajiya Mairo ta yi ta miƙe, hannunta dafe da ƙirji ta ce “Na shiga uku.”

A hasale ta nufi ƙofa zata fita, karo suka ci da Habeeb zai shigo, ganin yadda ta hasala, ya san abin ba zai yi kyau ba idan ta fita.

Riƙe ta ya yi “Umma ina zaki je.”

Ta ce “Wurin waɗancan matsiyatan in ji me ya kawo su gidana”, tana gama faɗin haka ta fizge hannunta.

Aikuwa ya sake ruƙota tare da tura ta baya ya rufe ƙofar.

Kamar kuwa zata yi hauka, zagi kuwa ba wanda bai sha shi ba.

Su kuwa ‘yan jere ba wanda ya san wainar da Hajiya Mairo ke toyawa, haka suka gama jerensu suka tafi. 

Sai a ranar da Amarya ta tare ne aka yi abin da ba’a yi tsammani ba, domin gagarumin faɗa aka yi tsakaniin dangin Hajiya Mairo, da danginsu Asabe.

Ita Hajiya Mairo ta gayyato ƙawayenta da danginta suka shiga can sashen Amarya suna ta yada habaici suna faɗin “An bi malamai da bokaye, an liƙe ma Alhajin birni”,

Wasu kuma da suka ga yadda ɗakin Uwani ya ƙayatar sai suka riƙa faɗin, “Kai Alhajin birni fa ya yi ƙoƙari, ku kalli yadda ya zuba ma Amarya kaya.”

Asabe da a kan kunnenta wannan magana ta dira ta ce “Ai wannan ƙoƙarin na iyayen Amarya ne, ba na Alhajin birni ba.”

Wata daga cikin su ta yamutsa baki, “Anya kuwa, bamu ga wannan alama ba, an dai bi malamai sun bada laƙani, an yi ma Alhajin birni wayau.”

Asabe da abin ya zo ma wuya ta ce “Ƙwarai kuwa, malamai sun ci kuɗinsu, domin har yanzu makullin taska na hannunmu, muna kwasar rabonmu”.

Wata mai kama da tsohuwar karuwa ta ce “Irin matsiyata, ai mun san za ku aikata fin haka”.

Aikuwa Asabe ta fizgo ta tare da wanka mata mari “Gaku nan irin matsiyata, shegu irin karuwai”.

Sauran ƙawayen wadda Asabe ta mara suka shigar mata suna dukan Asabe, da dangin Asabe suka ga ana dukanta, sai suka shigar mata itama.

Kan ka ce me wuri ya rikice ana ta damben bala’i.

Da yake da biyu ƙawayen Hajiya Mairo suke faɗan, sai suka fara fashe kayan glass.

Asabe na gani ta ɗaga murya ta ce “Ba shakka, ku ce dama dai kaya suka tsone muku ido, shine kuka zo raba ta dasu, toh kun yi a banza wlh, ‘yan iska marasa….”

Kafin ta ƙarasa maganar  wata ta dunƙule hannu ta bugar mata baki.

Duk da zafin da ya ratsa mata baki, bai hana ta cakumar waccan ta inzigiza ta cikin fasassar kwalba.

Cak! Aka tsaya da faɗan, lokacin da waccan ta fasa wata irin ƙara.

Take zuciyar danginta ta harzuƙa, wasu suka yi kanta, wasu kuma suka rufar ma Asabe suna ta duka.

Dangin Asabe ma suka sake shigar mata, tun ana faɗa cikin ɗaki har ta kai ga an fito waje.

Amarya kuwa duk ta ruɗe, musamman da ta ga duk an ji ma wasu ciwo hada Asabe, kuka sosai ta riƙa yi tana faɗin “Wallahi da na san haka zata faru da ban yi wannan aure ba”

Ashe akan kunnen Hajiya Mairo, da ke tsaye gefenta take faɗin haka. 

Wata irin dariyar mugunta Hajiya Mairo ta yi “Nadama ki ke ko, toh da saura ma, ba ki ba zaman lafiya tunda kika shigo gidana wlh.”

Uwani ta buɗe baki zata yi magana kenan, muryar Alhaji Mainasara ta dakatar da ita.

Ranshi a ɓace ya nufo Hajiya Mairo “Kin yi daidai Mairo, kin nuna mana ke cikakkiyar dabba ce”.

Cike da tsiwa Hajiya Mairo ta buɗe zata yi mashi magana, aikuwa ya ɗaga mata hannu “Wallahi kina cewa tak a bakin aurenki”

Da ya ke tana son aurenta sai ta yi shiru.

Faɗa sosai ya riƙa yi, gaba ɗaya sai da ya kora dangin Hajiya Mairo.

Jiki a sanyaye suka fice mashi daga gida.

Dangin Amarya kuwa Haƙuri ya riƙa basu, don yana da yaƙinin duk abin da ya faru, jan su aka yi.

A ranar wasu daga cikin dangin Amarya suka tafi, wasu kuma suka tsaya don kimtsa ɗakin Amarya.

Asabe kuwa kasa komai ta yi don duk jikinta ciwo yake, ga bakinta ya yi suntum.

Da safe da Alhaji Mainasara ya ce yana son magana da ita ƙin fitowa ta yi, wai kunyar bakinta da ya kumbura take, sai dai ya ba Uwani saƙon kuɗi da godiya ta bata.

Motoci ya turo da zasu kai su gida, da zasu tafi Uwani ta yi ta kuka, Asabe ta ce ta yi Haƙuri, idan an yi hutu zata turo mata Jummai.

Bayan tafiyarsu Alhaji Mainasara ya ɗauke ta suka nufi kasuwa, duk abin da aka barnata sai da ya sawo mata wanda ya fi shi.

Suna dawowa suka maida komai a tare.

Halin kirki da iya kula da mace na Alhaji Mainasara, shi ya sa Uwani itama ta dage da bashi kulawar da tunda yake bai taɓa samun irin ta a wurin Hajiya Mairo ba.

Hakan ya sa kullum yake ji da Uwani, ko ɗakin Hajiya Mairo yake sai ya riƙa kiran sunan Uwani.

Hakan ne ya ƙara rura wutar gabar da ke tsakaninsu. 

Malamai Hajiya Mairo ta shiga bi a kan a raba Alhaji Mainasara da Uwani, amma a banza, don Uwani ba daga baya ba a wurin adduo’i.

A wurin Habeeb kuwa, duk wani mugun hali na uwarshi ya kwashe ya haɗa da na shi, shima yadda Uwarshi ta tsani Uwani, haka shima ya tsane ta.

Gaba ɗaya ya hana ta saƙat, da zaran mahaifinsa ya fita, sai ya shiga ɗakin Uwani ya riƙa zaginta.

Da yake bata da faɗa kamar Asabe, duk sadda ya shigo ko kallon shi bata yi, bare da shiga cikin sabgar shi.

Wata rana da tsiyarshi ta ciyo shi, sai ya zo neman abinci, da yake Hajiya Mairo ta yi tafiya.

Ba ko sallama ya shiga kwaɗa mata kira lokacin tana bedroom “Amarya.”

Asabe da basu daɗe da zuwa ba ta ce “Waye wancan ke kiranki haka?”

“Habeeb ne”, Uwani ta faɗa lokacin da ta miƙe.

Kai kawai Asabe ta girgiza “Zaka ci Ubanka.”

Uwani na fita, ta bi bayanta.

Habeeb da ke tsaye a tsakiyar falo, sai cika yake yana batsewa ya ce “Ina abincina.”

Uwani ta ce “Ban yi girki ba Habeeb, sai zuwa anjima.”

“Ba ki yi girki ba, ko dai kin kwashe ma mayun gidanku sun cinye.”

kai tsaye ya faɗi haka idanunsa na kan Asabe.

Toh dama Asabe jiranshi take, matsowa ta yi dab da shi sannan ta ce, “Yau ga shege mai baƙin hali irin na uwarsa, to ka koma wurin uwarka ka tambayeta su waye mayu.

Zaka ji ta ambaci sunan Mado, to shine Wanda ya haifi Uwarta, shi kuma maye ne, kaga ku ne kuka gaji maita”

Tamkar ya maƙare Asabe ya ce “Ubanki dai ne Maye.”

Da yake Asabe ba ta haƙuri ta biye mashi suka yi ta zage-zage, sai da Uwani ta yi da gaske, sannan ta tura ta bedroom.

Habeeb ya ce “Ki barta, in sake kumbura mata baki.”

Ashe ta ji, daga can tace “Sai dai ka kumbura na uwarka.”

Uwani ta ce kai yaya Asabe, don Allah ki yi shiru, kin biye ma ƙaramin yaro sai zaginki yake.”

“Ban gane in yi shiru ba, Wallahi da kin bar ni da na yi mashi hankali, shege mai gadon baƙin hali”.

Haka ta yi ta sababi, Uwani kuma na ta bata haƙuri, ƙarshe ma faɗan sai ya dawo kan Uwanin, wai ita ce ta ƙyale shi har yake shigo mata ɗaki.

Shi kuwa yana fita suka yi kiciɓus da Jummai a bakin ƙofa, zata shiga.

Ras!  Gabanshi ya faɗi, don rabon da yaga mace mai irin kyan Jummai tun sadda suka je Etophia shi da Babanshi.

Lumshe ido ya yi tare da raɓewa gefe, ya bata hanya.

Da ido ya raka ta har sai da ta shige.

Gaban shi na cigaba da faɗuwa ya nufi ɗakinshi, Samun kansa a cikin waigen ta ya yi ba tare da ya sani ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 4Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×