Skip to content
Part 1 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Godiya ga Allah S.W.A da Salati ga Baban Abdallah da Ibrahimul Mu’azzam Annabi Muhammad S.A.W.

Fatan alkhairi ga ƴan ƙungiyata wato Hazaƙa Writers, ina mana fatan alkhairi da samun nasara bisa ga abin da muka sa gaba.

Wannan labari ƙirƙirarre ne, na yi shi don kawo gyara a cikin al’umma, ba don cin zarafin wani ko wata ba, Allah ya sa abin da ke ciki ya amfani Al-umma.

Sadaukarwa ga: Sirrin ‘Ya Mace Group

*****

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un! Na shiga uku ni Asabe, wanne irin bala’i na ke gani haka a jikinki Jummai?”

Cikin tashin hankali Asabe ke faɗin haka lokacin da ta yi arba da matashin cikin da zai kai wata biyar zuwa shidda a jikin ɗiyarta Jummai, wanda tunda take ba ta taɓa lura da shi ba sai yau, sakamakon kodayaushe, Jumman na cikin hijabin da ta fa ke da sanyin da ake ne ya sa ta sanya shi.

Jummai kuwa, da kullum ta ke fargabar ranar da wani zai gane tana ɗauke da ciki, ta raɓe jikin bangon ɗakinsu ta na ta muzurai, ƙasan zuciyarta kuma cike da firgici tare da kwancewar dabarar yadda za ta kare kanta.

Asabe da ta kasa yarda da abin da idonta ya gani ta matso kusa da ita, hannu ta sa, ta taɓa cikin, za ta janye kenan ta ji motsin ɗan da ke cikin Jumman wanda ya kusa tarwatsa mata zuciya.

Ɗif! wutarta ta ɗauke, wani mugun kallon tuhuma da kin shiga uku ta shiga yi ma Jummai. Da yake Jumman ta san irin wannan kallon, ta zaro ido ta fara ba ta haƙuri cikin muryar kuka.

Asabe ta ce cikin kaushin murya “Haƙurin Ubanki zan yi Jummai, ki jawo mana wannan bala’in sannan ki jefe ni da kalmar haƙuri, ki faɗa mani yadda aka yi haka ta faru.”

Jummai ta yi shiru tana share hawayen da ke gudana a fuskarta don ba za ta iya amsa tambayar da ta yi mata ba. 

Wta irin tsawa ta daka mata, wadda ba ita kaɗai ba, hatta awakinsu dake ɗaure a garke sai da suka firgita, “Ba magana nake maki ba”.

Ta buɗe baki za ta ƙara ba ta haƙuri kenan, ta ji saukar marin da sai da komai na ta ya tsaya, in ban da kunnenta da ke amsa sautin wannan  mari, ba ta gama jin wannan sauti ba kuma ta ji saukar icce ta ko’ina a jikinta, aikuwa ta fasa wata irin ƙara wadda ta sa mahaifinta Malam Ahmadu da ke zaure saurin ƙarasowa cikin gidan.

“Lafiya Asabe, me ke faruwa ne haka?”

Asabe na kuka ta jawo hannunshi “Malam wannan yarinyar ta jawo mana bala’i”.

Cikin rashin fahimta ya ce “Kamar ya bala’i?”

Ta ce “Ciki ne da ita Malam”.

Kamar saukar Aradu ya ji maganar Asabe, take duk wata wuta tashi ta ɗauke, ya shiga kallon Jummai da duka ya sa duk ta fita hayyacinta ta na kuka.

“Ciki fa ki ka ce Asabe?”

Cakumo Jummai ta yi, tare da yaye mata riga ta ce “Ka gani Malam”,

Yana gani ya yi maza ya rumtse idanunsa, ƙasan zuciyarsa ya na jin wani irin tashin hankali, da tunda ya zo duniya bai taɓa jin irin sa ba. 

Kan ka ce me jiri ya kwashe shi, ya na jin zai faɗi ya yi maza ya dafe bango, sannan ya lallaɓa ya shiga ɗakinshi, don ba zai iya tsayawa ganin wannan bala’i ba.

Jagwab!  Ya zauna kan gado tare da dafe kai ya shiga neman addu’oin yaye bala’i, duk wanda ya ɗauko karatunta sai ta ɓace mashi sai ya ɗauko wata, haka ya yi ta gwama farko da ƙarshen mabanbantan addu’oi a wuri ɗaya, ƙarshe da ta kakare mashi sai ya yi shiru tare da dafe kansa da duka hannayensa biyu.

Shi kuwa wacce irin ƙaddara ce wannan ta same shi, shi da ke cikin masu gyara ɓaraka a gari, ga shi shi kuma ɓarakar ta auku a gidanshi, ya na cikin wannan tunani ya jiyo ihun Jummai, da hanzari ya fito, ya kuwa iske Asabe ta shaƙare ta.

Tana faɗin “Wallahi ko ki faɗa mani wanda ya yi maki shi ko in kashe ki.”

Jummai da idanunta suka firfito saboda zafin shaƙara, ta yi ta miƙa mashi hannu tana son ya ƙwace ta, ya na zuwa ya shiga ɓanɓarar hannun Asabe a wuyan Jummai, sai da ya yi da gaske sannan ya ƙwace ta.

Zuciyarshi cike da ƙunci ya ce “Haba Asabe, kashe ta za ki yi?” 

Cikin masifa ta ce, “Toh menene amfaninta Malam? Gwara na kasheta na huta.” Tana kaiwa nan, ta dunƙule hannu ta bugar mata baki, aikuwa jini ya yi ta zuba.

Bangon dake kusa da ita ta jingina bayanta tana maida numfashi da ƙyar, ga zafin maƙara ga zafin ciwon da ya ratsa mata haƙori ya shiga cikin kanta.

Malam Ahmadu, da ya ga yanayin da ta shiga ya dubi Asabe ya ce “Kada ki sake taɓa ta, aikin gama ya gama, duka bai yi sai dai mu rungumi ƙaddara.”

Asabe ta ce bayan ta jefe shi da mugun kallo, “Wallahi Malam ba zan iya ɗaukar wannan ƙaddarar ba.”

Kai kawai ya girgiza don ya san halinta na kafiya da rashin haƙuri, idan an yi mata laifi, sannan ya ja hannunta suka nufi ɗakinshi. Kafin su shiga ta juyo ta ce “Wallahi kin shiga Uku a gidannan.”

Haƙuri da magana ya riƙa ba ta, amma kwata – kwata ta ƙi saurarar shi, ita babban tashin hankalinta jama’ar gari su ji wannan labari, don ta ga yadda aka yi ma wata da ta yi ciki, saboda tsangwama da kuma gulmar mutanen kauyen sai da suka canja gari, wanda hada ita Asaben a cikin waɗanda suka ɗora karan tsana ga wannan yarinya da iyayenta, don a ganinta sakacin iyayen ne ya sa har suka bari ɗiyarsu ta yi cikin shege.

Jummai kuwa zamewa ta yi ƙasa, haɗe da duƙewa ta haɗa kanta da gwiwa, kuka mai cike da zallar baƙin ciki da nadama ta riƙa yi, ita ba dukan da mahaifiyarta ta yi mata ne damuwa ba, gangancin da ta yi har ta ba saurayi kanta sakamakon romon baka tare da alƙawalin rayuwa mai cike da jin daɗi idan sun yi aure da ya riƙa yi mata, wanda sai bayan hakan ta faru ne ta gane ƙarya yake, don ko da yake ɗan birni bai mallaki abin da yake faɗa mata zai ba ta ba.

Kuma wani takaicin da kullum ta ke jin kamar ta kashe kanta shi ne, tunda ya gane tana da ciki ya yanke duk wata hulɗa dake tsananinsu, sannan ya yi mata kashedin idan ta sake ta ce shi ne ya yi mata ciki sai ya kashe ta, kuma idan ta sake zuwa gidansu, kai ko birni ma idan ya ji labarin ta zo sai ya haɗa ta da masu garkuwa da mutane sun sace ta, hakan ya sa tsoro ya shige ta, har take jin duk abin da za a yi mata ba za ta faɗi shi ne ya yi mata ciki ba.

Kuka sosai ta riƙa yi kamar ranta zai fita.

Asabe na fitowa ta ce “Kuka kam ai yanzu kika fara Jummai….”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 2 >>

5 thoughts on “Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×