Skip to content
Part 11 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Idanun Habeeb cike da ƙwalla ya ɗago tare da duban mahaifinsa ya yi magana cikin rawar murya, “Abba don Allah kada ka rabu da mahaifiya ta.”

Murmushin da ya fi kuka ciwo Alhaji Mai Nasara ya yi, don ya fahimci in da ya dosa, “Zaka ɗauki Jummai da ɗanta ku tafi kenan?”

Kai Habeeb ya girgiza “Abba ai ba ɗana bane.”

Alhaji Mainasara ya ya ce “Wannan ai maganar banza ce, bari in faɗa maka wani abu. Zaman lafiyarka da na uwarka a gidannan shi ne ka ɗauki matarka da ɗanka ku tafi, idan ba haka ba zaku ga abin da zai faru.”

Tsaye Hajiya Mairo ta miƙe tare da zabga ashar “Alhaji duk abin da ka ga dama ka yi, amma wallahi sai ya sake ta, don ba matsiyata na haifa ma shi ba.”

Gwauron numfashi kawai Alhaji Mainasara ya sauke, tare da raka ta da idanu lokacin da ta juya ga Habeeb tana faɗin.

“Idan ni na haife ka, toh ka saki Jummai,”

Cikin kuka Habeeb ɗin ya ce “Toh Umma naki auren fa?”

Ta ce “Kada ka damu da ni, ka aiwatar da abin da nake umurtar ka kawai, ko kuma in tsine maka wallahi, don muddin ka ɗauki ɗan, toh kai ne ubansa ba kowa ba”.

A hankali Habeeb ya lumshe idanunsa, ƙasan ransa kuma yana jin wani irin tashin hankalin da bai taɓa tunanin zai samu kansa a cikin irinsa ba.

Shirun da taɗan ratsa ce ta sa shi buɗe idanun tare da ɗan marairaice fuska yana kallonsu, duk don su tausaya mashi.

Ganin fuskar kowa a murtuke ya tabbatar mashi da su duka suna a kan ƙudirinsu.

Tsawar da Hajiya Mairo ta daka mashi a karo na biyu ce ta ƙara gigita shi

“Kai nake jira Habeeb, ka rubuta takarda, sannan ka miƙa ma ubanka shima ya rubuta tashi”.

A yadda take maganar lallai ta kai maƙura a wurin ɗaukar zugar shaiɗan, don ji take mutuwar nata auren kawai take so.

Ido Habee ya sake lumshewa tare da matse hawayen baƙinciki, lokaci ɗaya kuma ya kalle ta don bai fatan auren uwarsa ya mutu, sannan a yadda yake son Jummai bai jin zai iya rabuwa da ita tunda har gashi Allah ya bashi ita. 

“Umma don Allah ki janye ƙudurinki na tsinuwa.”

“In janye Habeeb, ka yadda kai ke da ciki kenan?”

kai ya girgiza “Wallahi Umma ba nawa bane.”

A yadda yake ta rantsuwa akan ƙarya ne ya ƙara ma Alhaji Mainasara jin haushinsa, tunanin yadda ya chanja a lokaci ɗaya ya shiga yi, sam ba haka Habeeb yake ba, ko da yake da raina mutane, amma yana kwatanta bin dokokin Allah.

Yana cikin wannan tunanin ne Habeeb ya juyo gare shi tare da sake roƙon shi akan kada ya saki mahaifiyarsa.

Abbanshi ya ce “idan ka ga uwarka a gidannan, to ka yarda da ɗan Jummai naka ne, sannan ka tafi da ita.”

Shiru Habeeb ya yi tare da cigaba da magana da zuciyarshi “Tabbas idan na ɗauki ɗan Jummai, toh haƙiƙa na aikata abin kunyar da ban son mahaifina ya riƙa kallona da shi. kuma da mahifina ya riƙa yi mani kallon haka, gwara na haƙura da Jummai, domin farincikin da nake fatan samu ba zai samu ba tunda mahaifina na fushi da ni, sannan ga tsinuwar mahaifiyata wadda ko shakka babu sai ta kama ni tunda na aikata.”

Yana gama wannan tunanin ya dauki biro idanunshi na zubar hawayen Rasa Jummai domin ko da ya yi mata wulaƙanci ba don bai son ta ba, ya yi haka ne don gudun kada ya faɗa fushin iyayensa idan aka gane shi ne.

Abin da mahaifiyarsa take so shi ya aikata, saki ɗaya ya rubuta ma Jummai”  hannunsa na kyarma ya linke takardar tare da miƙa ma mahaifinsa.

Cike da baƙinciki Alhaji Mainasara ya karɓa sannan ya ce “Nagode da tozarci na biyu da ka yi mani, ka ɓata ƴar mutane, sannan ka nuna ma duniya ban isa da kai ba.”

Ƙafafunshi Habeeb ya ruƙo yana kuka “Abba don Allah ka saurare ni, bani bane wallahi.”

Fizge ƙafarshi ya yi tare da tashi tsaye “Ba zan muku baki ba kai da Uwarka, amma gaku ga duniyar na.”

Hajiya mairo ta ce ma Habeeb “Kai rabu da shi, ka wanke kanka a wurina, sauran yan sharri ma da sannu zasu gane gaskiya.”

Tana rufe baki Alhaji Mainasara ya ce “Toh ki je kema na sake ki saki ɗaya.”

Wanda shine cikon na biyu don dama akwai saki ɗaya a tsakaninsu.

Buɗa Hajiya Mairo ta rafka “Tafi nono fari wallahi, ni dama na gaji da wannan lalataccen auren naka.”

Bai tsaya jin me take cewa ba ya nufi ƙofa ya fita.

Da sauri Habeeb ya miƙe da nufin bin bayanshi, don ya ga tsananin fushi a tare da shi.

Dakatar da shi Hajiya Mairo ta yi tare da faɗin “Ƙyale shi don ba yin kansa bane, asiri ne suka yi mashi, kuma wallahi sai na ɗauki mataki a kansu.”

Lallashin sa ta riƙa yi akan kada ya damu tunda ba yin kan mahaifinsa bane.

Kasa dena kukan Habeeb ya yi, don ya san ba wani asiri, ƙarshe ma ɗakinsa ya koma ya cigaba da kukan a can.

Alhaji Mainasara kuwa ɗakin uwani ya nufa, a falo ya same ta tana rirriga Salim da ke ta faman kuka.

Damuwa bayyane a fukarsa ya tambaye ta “Kukan me yake ne?” Ta ce “Wallahi ban sanar mashi ba, rigimarshi ce kawai ta motsa.”

Karɓarshi ya yi tare da kwantar dashi a kafaɗarshi yana lallashi.

Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga shi ya yi bacci.

Alhaji Mainasara na gani ya ce mata “Kune baku iya lallashin yaro ba.”

Murmushi kawai ta yi, lokaci ɗaya kuma ta ɗauki takardar da ya aje akan kujera “Wannan fa?”

Ya ce “Takardar Jummai ce, da Uwar Habeeb ta sa shi ya rubuta.”

Wata irin faɗuwa gaban Uwani ya yi, hannunta na kyarma ta bude takardar ta fara karantawa, sallallami ta shiga yi bayan ta gama karance abin da ke cikinta.

“Alhaji wannan ƙaddara babu wata dubara da zamu yi mata, bamu isa mu rufa ma kanmu asiri ba, har sai lokacin da Allah ya rufa mana.”

Ajiyar zuciya ya yi “Gaskiya ne Gimbiya, amma yaran nan sun tozarta mu, yanzu auren ai shine rufin asirin kowa, amma saboda dabbanci irin na Mairo ta rusa komai, ko da yake kanta ta yi mawa, tunda har aurenta itama ya shafa.”

“Kamar ya ya shafi aurenta?” Uwani ta tambaye shi.

Ya ce, “Na sake ta.” Ruɗewa Uwani ta sake yi. “Alhaji me yasa?” Don ko shakka babu cewa za’a yi asiri suka yi ya sake ta, ita kuma abin da ta tsana kenan.

Alhaji Mainasara ya ce “Baƙinn halinta ne ya ja mata, ko ba wannan case ɗin na gaji da zama da ita.”

Sosai Uwani ta nuna rashin jin daɗinta a kan sakin, ganin haka ya sa shi labarta mata irin mugun halin Hajiya Mairo wanda ya daɗe yana kwasa.

Ya ce “Ni da gidana amma bani da iko da shi, daidai da girkin gidan ban ni da kaso a ciki, haƙƙin aure kuwa sai na yi kamar zan yi hauka sannan ta sauke mani shi, batun haihuwa kuwa maganin  tsarin iyali ta sha ba da sanina ba, ƙarshe ya zame mata illa a mahaifa, in taƙaice maki labari sai bayan na aure ki ne na san daɗin aure.”

Sosai Uwani ta tausaya mashi, tare da alƙawalin cigaba da faranta mashi har sai ya manta damuwar da Mairo ta ƙumsa mashi.

Rungumta ya yi haɗe da Salim ya ce “Allah ya baki iko”, “Amiin” ta ce, suka cigaba da maganar sakin, ƙarshe ya nemi alfarma wurin ta a kan kada ta fitar da maganar,  a bari a ga ko Habeeb zai yi nadama, don ya fahimci wani abu a cikin kukanshi.

A ɓangaren Habeeb kuwa Nasir ya kira a waya cewar don Allah ya zo. Amsa kiranshi Nasir ɗin ya yi, don dama yana da niyyar zuwa.

Ba’a ɗauki lokaci ba sai ga shi ya zo, ganin fuskar Habeeb a kumbure alamar ya yi kuka ya sa jikinshi yin sanyi.

Tun kafin ya zauna ya tambayi Habeeb “Wai me ke faruwa ne?”, don tun sadda ya ji Habeeb ya dawo ya shiga tunanin ko lafiya, saboda sun yi da shi ba zai dawo ba sai ya gama Masters ɗinshi.

“Ka zauna” Habeeb ya ce  mashi, zaman ya yi kusa da shi akan kujera, tare da maimaita tambayar shi abin da ya faru.

Ido Habeeb ya lumshe saboda azabar ciwon da kansa ke masa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya buɗe idon tare da kallon Nasir.

“Nasir na aikata zunubi mai girma a rayuwata, wanda ban san ta ina zan fara neman gafarar Allah da ta waɗanda na zalunta ba.”

Kallon shi Nasir ya riƙa yi da alamar yana son ƙarin haske, don shi dai bai san shi da wani mugun hali ba.

“Na yi Zina Nasir” Habeeb ya faɗa cike da baƙin ciki.

Ido Nasir ya zaro tare da dafe gabanshi da ya girɗe ya faɗi.

Zai yi magana Habeeb ya dakatar dashi da faɗin,

“A dalilin zinar da na yi an samu ciki, a dalinlin cikin an rasa rai, sannan na kashe auren mahaifiya ta, sannan na nuna ma babana bai isa ba, Nasir ka gaya mani yadda zan gyara waɗannan kusakuran a rayuwata”, kuka ya fashe da shi tare da ruƙo hannun Nasir.

Cije Leɓe Nasir ya yi, ƙasan ranshi yana jin wani irin tashin hankali, don shaƙuwarsa da Habeeb takai duk abin da ya samu ɗaya a cikinsu, tamkar ya shafi ɗayan ne.

“Duk garin ya haka ta faru?” Ya tambayi Habeeb a taƙaice.

Cikin Kuka Habeeb ya zayyana mashi komai, tun daga cikin da ya yi ma Jummai har zuwa mutuwar mahaifinta, da kuma sakin da ya yi mata wanda ya zama sanadin mutuwar auren mamanshi. Bai rage komai ba face sai da ya faɗa ma Nasir. Ya ce “Toh Nasir ka gaya mani ta ina zan gyara wannan kuskuren.”

Kai Nasir ya jinjina “Lallai ka aikata kuskure a rayuwarka, amma mafi girma a cikinsu shi ne sakin Jummai da ka yi, domin aurenka da ita ne kaɗai zai gyara kuskuren da kuka aikata.”

Ya ce “Toh Nasir ya zan yi idan ban sake ta ba, mahaifina fa zai riƙa yi mani kallon mazinaci.”

Nasir ya ce “Ai sakin ma ba zai hana ya yi maka wannan kallon ba, domin sai da ya samu ƙwƙƙwarar shaida sannan ya ce ɗanka ne.”

Faɗa sosai Nasir ya yi.

mashi ya ce “Baka kyauta ba, ka cutar da yarinya da iyayenta, yanzu kai namiji dubi halin da ka shiga sakamakon wannan ɓarna, toh ya kuma ga ita mace? Haba Habeeb” Kamar Nasir zai yi kuka ya ƙarasa maganar.

Shiru Habeeb ya yi yana Nazarin maganar Nasir, Lallai idan shi namiji na cikin wannan tashin hankali, toh ya Fateemah zata kasance, wani irin tausayinta ne ya kama shi, take allurar son da yake mata ta motsa tare da game dukka illahirin jikinshi.

Wata irin kyarma jikinshi ya kama yi, gaba ɗaya ba ta sakin mahaifiyarsa yake ba, don matsalarta mai sauƙi ce.

“Nasir, Lallai Fateemah tana cikin tashin hankali, ya zan yi in fitar da ita daga damuwarda na sa ta, ka bani shawara Nasir.” Yana gama faɗin haka ya miƙe tamkar zautacce.

Maida shi Nasir ya yi “Zauna, ka bi komai a hankali, ka ga yanzu ba wanda zai saurare ka daga mahaifinka har Fateemah, kuma uwa uba ga Umma, ko tsinuwar ta ka zaɓa ne?”

Ya Salam, kai Habeeb ya girgiza, lokaci ɗaya kuma idanunshi na fitar da ƙwalla, Nasir ya ce “Kuskure ne mai girman gaske ka aikata, wanda sai anbi a tsanake sannan a gyara shi, idan ba haka wurin gyaran wani, za’a kuma a ɓata wani”.

Lallashin Habeeb ya yi tare da magana mai daɗi, shawara ya bashi akan ya koma ya cigaba da karatunsa kada ya yi biyu babu, a hankali yana karatun komai zai iya daidaita.

Ba don Habeeb ya so ba ya bi maganar Nasir. Bayan ƴan kwanaki ya haɗa komai nashi da nufin barin ƙasar.

Haka ya je wurin Abbanshi da nufin bankwana. “A sauka lafiya” kaɗai Abbanshi ya ce mashi.

Jiki a mace ya baro ɗakin.

Wurin Ummanshi ya je, da yake ta koma gidan ƙawarta da zama tun washegarin da Alhaji Mainasara ya sake ta.

Bankwana suka yi, har ƙawar Ummanshi ta ƙara bashi haƙuri, tare da yi mata alƙawalin ɗiyarta idan ya gama karatu.

Murmushin yaƙe kawai ya yi, don a duniya ba yarinyar da yake so irin uwar ɗanshi Jummai, bankwana ya yi da su, aka sa Driver ya kai shi Airport.

A Ɓangaren ɓoyayyen masoyin Jummai wato Dr. Ameer, tun ranar da aka ɗaura auren Jummai zuciyarsa ta kaza sukuni, kullum cikin tausayin kansa yake sakamakon mugun kamun da son ta ya yi mashi a zuciya.

Gaba ɗaya bai kallon aibun da ke tare da Jummai sai ma tunanin yadda zai taimaka mata ta gyara kuskuren da ta aikata. Gashi kuma ya rasa ta.

Babban abin da yafi damunshi a rashin ta shi ne, aura mata azzalumin da ya gurɓata mata rayuwa da aka yi.

Zaune yake cikin office ya yi jugum, turo ƙofar da aka yi ce ta sa shi kallon ƙofar.

Ganin abokinsa Dr. Abdullahi Misau ne ya sa shi ƙaƙaro murmushi, duk don kada ya gane yana cikin damuwa, sai dai kuma haƙarsa bata cimma ruwa ba. domin sai da ya gane.

Zama ya yi suka gaisa, daga bisani ya ce “Anya kuwa abokina ba ka damuwa?”

“Me ka gani?” Dr. Ameer ta tambaye shi, lokaci ɗaya kuma yana ƙara ɓoye damuwar dake ransa ta hanyar murumushi.

“Na lura kwana biyu kamar baka da walwala, me ke faruwa ne?”

Girma da karamcin Dr. Misau ya sa Dr. Ameer ƙin ɓoye mashi damuwarshi ta son Jummai.

Sosai Dr. Misau ya tausaya mashi, don ya san ciwon so, sannan kuma ya nuna damuwa ga Jummai domin ya daɗe da sanin labarinta.

Aje rana suka yi akan zasu je garinsu Jummai su ga wane hali take ciki, duk da suna jin kamar ba zasu iske ta ba tunda an yi mata aure.

Ranar Asabar da yamma suka shirya, basu zame ko ina ba sai garinsu Jummai. Kai tsaye cikin gidan suka shiga da Sallama, kasantuwar Asabe ta san Dr. Ameer.

Tsakar gidan ba kowa sai yara, Basheer na ganinsu ya ruga ɗakin Asabe “Inna ga wannan likitan nan na birni.”

Fitowa ta yi dan ganin wanda Basheer ke nufi, tana ganinsu ta ƙaƙaro fara’a, don rabon fuskarta da walwala har ta manta.

Iso ta yi masu har cikin ɗakinta, bayan sun zauna kan darduma suka gaisa. Dr. Ameer ya ce “Dama zowa muka yi a gaisa.”

Ta ce “Aikuwa mungode”, waje ta fito tare da ba Basheer kuɗi ya siyo musu lemo, sannan ta nufi wurin da suke girki    tare da zubo musu Shinkafa da wake.

Soyayya da tausayin da suke ma mutanen gidan ya sa suka ci abin cin. Hira suka riƙa yi jefi-jefi da ita.

Shi kuwa Dr. Ameer sai raba ido yake bai ga Jummai ba, Asabe na fita ya tambayi Basheer “Ina Jummai?”, ya ce “Tana cikin ɗakinta.”

Ajiyar zuciya ya sauke, don ba abin da yake so sai ganinta, Asabe na shigowa ya ce “Bari mu leƙa wurin Jummai.”

Tashi suka yi suka fita tare da Basheer, “Wane ɗaki ne” Dr. Misau ya tambaye shi.

Wata irin faɗuwa gabansu ya yi lokacin da ya nuna musu bukka, tare suka kalli juna, kowa da abin da yake saƙawa a ransa.

Jiki a mace suka ƙarasa wurin bukkar, hankalinsu bai ida tashi ba sai da suka shiga ciki, a yadda suka ga Jummai ya fassara musu da tana cikin ƙunci, gaba ɗaya ta sauya kamannu, duk ta ƙara ramewa ta yi baƙi.

Ɗan raɓawa suka yi suka zauna, murya ciki-ciki Jummai ta gaishe su, kasantuwar yunwar da ke cikinta.

Amsawa suka yi, Dr. Misau ya karɓi yaron, ido ya lumshe ƙasan ranshi yana jin wani iri, “Lallai akwai matsalar yunwa a tare da waɗannan mutanen” maganar da ya yi da ransa kenan.

Ameer kuwa sai dai ya goge hawayen da suka malalo a idonsa, kasa zama suka yi suka fito. Ɗakin Asabe suka nufa suka ce zasu tafi. Kuɗi Dr. Misau ya fiddo ya bata, In da Dr. Ameer ya koma cikin bukkar.

Durƙusawa ya yi gaban Jummai ya fara magana ƙasa-ƙasa “Ki yi haƙuri kin ji, damuwarki gatanan a fili, Allah zai fidda ki kin ji ko”,  yana gama faɗin haka ya zaro kuɗi ya aje mata a gabanta, ƙwallan da ya gani a idanunta ne ya sa saurin ta shi ya fita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 10Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×