Skip to content
Part 6 of 22 in the Series Ko Ruwa Na Gama Ba Ki by Hadiza Isyaku

Kan doguwar kujera Habeeb ya kwanta yana mai fuskantar rufin ɗakin. Fuskar Jummai da ke ta yi mashi gizo a idanu ce ta disashe mashi ɓacin ran da ya fito da shi daga ɗakin Uwani.

Tambayar kansa ya yi, “Wace ce waccan?”

Nazarin kyakkyawar fuskarta ya shiga yi, yana mai son gane da wanda ta ke kama.

Wani dogon tsaki ya ja lokacin da ya gano da Asabe take kama, ƙoƙarin yakice ta a zuciya ya fara yi, don a rayuwarshi ba wadda ya tsana irin Asabe, saboda Ummanshi ta bashi labarin irin kitimullin da suka yi da ita a lokacin suna ‘yan mata.

Cike da son cire fuskar Jummai a zuciyarshi ya lumshe ido tare da gyara kwanciyarshi a kan kafaɗa, lokaci ɗaya kuma yana ta zagin Asabe a ƙasan ranshi.

Kiran da abokinsa Nasir ya yi mashi a waya ne ya sa shi tashi zaune tare da amsa kiran.

“Ya ne”, ya furta cikin dakusashshiyar murya.

Daga can Nasir ya tambaye shi “Ka na gida?”

Sai da ya ɗan ɓata lokaci sannan ya ɗaga kai “Yes ina nan”.

Ya ce “Toh zan shigo yanzu”,

Habeeb ya ce “Ok sai ka shigo”.

Katse kiran ya yi, tare da jefa wayar a kan gado, lokaci ɗaya kuma yana faɗin “Yanzu kuma wannan zai zo ya cika ma mutane kunne da zancen ‘yan mata”, jingina ya yi da bayan kujera tare da rufe ido kamar mai bacci.

Ba su fi minti goma da gama wayar ba sai ga Nasir, hannunsa ɗauke da leda.

Habeeb bai bari Nasir ya gane yana cikin damuwa ba, don muddin ya gane, toh sai ya yi mashi faɗa akan abin da yake ma Uwani na rashin kyautatawa.

Ganin Nasir ɗin nata washe baki ya ce “Uhm namamajo, hala daga wurin wata kake?”

“Kamar ka sani wlh”, Nasir ya faɗa lokacin da yake zama a kan kujera.

Ƴar dariya Habeeb ya yi ya ce “Allah dai ya sawaƙe maka”

Nasir ya ce “Ba amin ba wlh, ƴan mata rahama ne, kuma tunda kai tsoronsu kake ai shikenan”.

Dariya maganar Nasir ta ba Habeeb, zama ya yi shima kan kujera ya ce “Wlh ni ba tsoronsu nake ba, kawai dai bani da time ɗinsu”.

Dariya su duka suka yi, Ledar da Nasir ya shigo da ita Habeeb ya jawo “Me ka shigo mana da shi, yunwa nake ji wallahi.”

Nasir ya ce “Snacks ne da kunun aya Zee ta bani.”

Baki Habeeb ya ɗan taɓe yana ‘yar dariya, “Ashe Zee ɗin ta fara sonka”.

Nasir ya ce “Yo ta ga uwar bari, ƙawarta na koma mawa, ba arziki sai ga ta har gida tana bani haƙuri”,

Habeeb ya ce “Toh kaga abin da ni ba zan iya jura ba, shiyasa ba yarinyar da zan wahalar kaina a kan son ta, ta zo kuma tana mani wulaƙanci”.

Dariya suka ƙara yi, Habeeb ya fiddo cake da kunun ayar da ke cikin leda suka fara ci.

Hira sosai suka riƙa yi kasantuwar su abokan juna, Hakan ya sa Habeeb ya samu sauƙin damuwar da ke cikin ransa.

Suna gamawa Habeeb ya ɗauke Nasir akan mashin suka fita cikin gari.

Jummai ma tunda ta ji abin da Habeeb ya yi ma mahaifiyarta ta ke jin wata irin tsanar shi a ranta, domin bata haɗa mahaifiyarta da kowa ba, masifa ta shiga yi tana faɗin “Wallahi da ina nan sai ya ga ƙaryar fitsara, kuma ko yanzu bai tsira ba”.

Sai dai kuma duk da cika bakin da take ta kasa dena tuna lokacin da ya kafe ta da dara-daran idanunsa, tsaki ita ma riƙa ja tana yamutse baki.

Asabe da ke ta haɗa kaya tana shirin tafiya ta ce “Wai wannan tsakin na lafiya ne, ina jinki tun ɗazu kina ta cika mana kunne da shi”.

Jummai ta ce “Wallahi Inna wancan banzan Habeeb ɗin nake jin kamar in shaƙaro shi”

Baki kawai Asabe ta taɓe ta ɗauki hijabinta ta sa, don bata son tuna Habeeb saboda ranta ɓaci yake.

Canja maganar tayi da “Toh Jummai, sati ɗaya na baki, ki dawo gida.”

Uwani ta ce “Ina laifin sati biyu, tunda akwai sauran hutu.”

“Ko kuma wata biyu ba.”

Asabe ta faɗi haka lokacin da ta nufi ƙofa.

Dariya su duka suka yi, suka bi bayanta.

Har bakin gate Uwani da Jummai suka rako ta, suna tsaye sai ga Habeeb ya kunno kai cikin gate ɗin zai shigo.

Jummai na ganinshi ta haɗe fuska, ɗaga idanu ta yi da nufin wurga mashi harara, idanunsu na sarƙewa da na juna ta yi maza ta ɗauke kanta ba tare da ta hararenshin ba.

Shima kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai, inda suke aje motoci ya nufa tare da kafe mashin ɗin a can. 

Asabe da tunda ya shigo take ji kamar ta fizgo shi ta ce ma Uwani “Wancan marar kunyar sai kin ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansa, idan ba haka ba zaki kwana ciki”.

Idanun Uwani na kansa lokacin da ya nufi sashen mahaifiyarshi ta ce, “Ai babanshi zan gaya mawa ya yi mashi magana.”

Asabe ta ce “Hakan ne daidai.”

‘Yan maganganu suka ƙara yi, daga bisani suka yi bankwana, Uwani ta dawo ciki, Asabe da Jummai kuma suka fita.

Habeeb kuwa kallo ya kunna a palon Ummanshi, don ya kawar da faɗuwar gaban da ya shigo da ita sakamakon haɗuwa da Jummai a waje.

Ba laifi faɗuwar gaban ta ɗan ragu, domin abin da yafi so ne yake kallo, wato wrestling.

Sai gab da magarib ya kashe Tv din ya dawo ɗakinshi.

Yana tsaye yana cire agogon hannunshi ya hangi wulgin Jummai ta window.

Tsakin da ya fara zame mashi jiki ya ja, bayan ya cire agogon ya yi alwalla a banɗanki, yana fitowa ya canja manyan kaya ya nufi Masallaci.

A daren ranar kuwa shi da ita ba wanda ya runtsa, tun suna jin haushin tuna juna, har ta kai ga sun dena ji.

Ƙagara Jummai ta yi gari ya waye don ta sake ganin shi, duk da kuwa tulin haushinsa da ke ranta.

Shi kuwa bai taɓa tunanin nan ta kwana ba, don haka bai ma sa ma ranshi ba zai sake ganinta ba.

Washegari da safe Abbanshi ya kira shi ɗakin Uwani, saboda ta gaya mashi irin fitsarar da yake mata.

Zaune yake ƙasan carpet yana fuskantar Abbanshi da ke zaune kan kujera.

Uwani da ke zaune a gefe Abbanshi ya nuna, “Bin wannan tamkar bi na ne Habeeb, idan ka wulaƙanta ta, ko ka wulaƙanta danginta, tamkar ni ka wulaƙanta, don haka ya rage naka.”

Wani irin ƙululu ne ya taso ma Habeeb a zuciya, ƙasan ranshi kuma yana jin ba ranar da zai yi ma Uwani biyayya. 

“Ka bata haƙuri,” muryar Abbanshi ta dawo dashi daga tunanin da yake, fuskarsa murtuke ya ɗago kai ya kalli Abbanshi.

Shiru ya yi bai bata haƙurin ba, Abbanshi ya ce, “Ko baka ji me na ce ba.”

A hankali ya juya da jajayen idanunsa wurin Uwani, Daga can bayanta ya hangi Jummai ta fito daga kitchen zata shiga ɗakin da aka ware don baƙi.

Bai san sadda bakinshi ya suɓuce ba ya ce ma Uwani “Ki yi haƙuri.”

Saida Jummai ta shige, sannan ya ɗauke idanunsa, ƙasan ransa yana jin sassacin zafin da ya ke ji. 

Nasiha Abbanshi ya yi mashi akan ya watsar da duk wasu makaman faɗa, ya riƙi Uwani tamkar Uwa, domin bata da babanci da mahaiyarshi.

Da wani irin yanayi Habeeb ya fito daga ɗakin Uwani, shi ba murna ba, shi kuma ba haushi ba, ɗakinsa ya nufa ya yi wanka, yana fitowa ya chanja kaya, sannan ya ɗauki makullin motarshi ya nufi makaranta.

Tsawon sati ɗaya kenan Habeeb da Jummai suna haɗewa a cikin gidan, kuma duk sadda suka haɗu, sai sun ji wani abu ya tsarga zukatansu.

Habeeb tun yana  musun son Jummai yake, har ta kai ga ya yadda, gaba ɗaya sonta ya mantar da shi gabar da ke tsakanin ahalinsu, burinshi kawai ya samu damar da zai yi mata magana.

Samun Nasir ya yi har gida da maganar akan ya zai tunkari Jummai, don zuciyarshi ta matsu ta gansu shi da ita a tare.

Shiru Nasir ya yi yana nazarin abin da so ya hana Habeeb tunawa.

Daga bisani ya ce “Da alamun dai Habeeb ka manta daga inda yarinyar nan ta fito, ka manta irin rikicin da ke tsakanin family ɗinku da nasu.”

Habeeb ya ce “Wallahi ban manta ba Nasir, na so in cire ta a raina, amma na kasa, zan iya haƙuri da duk wani ƙalubale da zan fuskanta muddin za ta karɓe ni a matsayin masoyi.”

Murmushi Nasir ya yi “Toh Allah yasa ta karɓe kan, ka ga hakan zai iya rage gabar da ke tsakanin ku da su.”

“Fatana kenan wlh, na fahimci gaba bata da wani amfani, yanzu ga shi a dalilinta na kasa tunkarar wadda na gani ina so.”

Shawarwari Nasir ya ba Habeeb akan ya dake, don ya fahimci kamar yana jin tsoron tunkarar Jummai.

Cike da ɗaukar wannan shawara Habeeb ya baro gidansu Nasir.

Da yammacin wannan rana Habeeb ya fito waje, tsaye yake jikin Iccen turaren da ke ƙofar gidansu, ɓangare ɗaya hannuwansa na cikin aljihu, idanunsa kuma na kallon ababen hawan da ke ta wucewa a kan titi, da yake gidansu a bakin hanya yake.

A baɗini kuma Jummai yake tunani ba ababen hawan da ke wucewa ba, don duk wunin yau bai gan ta ba.

Ƙarar ƙofar gate ɗin ce tasa shi waigowa, wani irin daɗi ne ya ziyarce shi lokacin da ya ga Jummai ta fito.

Alwashi ya sha a kan yau zai fallasa mata sirrin dake cikin zuciyarshi.

Idanunshi a kanta har ta zo gabanshi zata wuce.

“Baƙuwar gidanmu,” ya faɗa ƙwarai, tare da yar dariya a fuskarsa.

Tsayawa Jummai ta yi tare da jefarshi da wani sassanyan murmushi, don tuni itama soyayyar Habeeb ta yi mata ɗaurin gwarmai a zuciya. 

Cike da mamakin tsayawarta ya ƙetara kwalbatin da ke gaban gidansu, ya je gabanta ya tsaya.

Idanunsa cikin nata ya ce, “Ina zaki je”

Wasu shaguna dake nesa kaɗan a tsallaken titi ta nuna mashi, “Can zan je.”

Sai da ya lumshe ido sannan ya ce “Toh muje in raka ki.”

“Toh” Jummai ta ce , suka tafi tare, ƙasan ranta tana jin wani irin daɗi, saurayi mai aji kamar Habeeb na mata rakiya.

Suna cikin tafiyar ya tambaye ta.

“Ya sunanki?” ta ce “Jummai”

Dakatawa ya yi da tafiyar, ganin ya tsaya itama ta tsaya.

“Gaskiya baki yi kama da jummai ba.”

Dariya ta yi “Toh da wa na yi kama”.

Shima dariyar ya yi “Da mai suna mai daɗi”, tare suka sake yin dariya,

Tabbatar mashi ta yi da haka ake kiran ta.

Ya ce “Na yadda haka ake kiran ki, amma ai ba shine asalin sunanki ba.”

Murmushi ta yi “Hakane, sunana Fatimah.”

Dubanta ya yi yana dariya “Yanzu na ji magana, amma kin dace suna fa.”

Ta ce “Toh na gode.”

Haka suka yi ta tafiya har ta kusa zuwa shagon, tsayawa ya yi daga ɗan nesa, ita kuma ta tafi shagon ta siyo abin da aka aiketa.

Tunda ta dawo idanunsa ke kanta.

Da murmushi ta ƙaraso wurinshi, suka juyo. hira sosai suka riƙa yi kamar dama sun san juna.

Sai da suka zo daidai gate ya ja tunga ya tsaya.

“Toh mu je mana” Jummai ta faɗa tana kallonshi.

“Wani wuri zan je,” ya bata amsa.

“Toh” ta ce tare da juyawa zata shige.

Kiran sunanta ya yi “Fateemah”

Tana waigowa ya kafe ta da idanu, itama idanun nata tasa a cikin nashi, take wani shauƙi ya dabaibaye su.

Cikin wata irin murya ya ce “Saƙo ne zan baki, ki bama zuciyarki, ki faɗa mata ina sonta.”

Baki Jummai ta buɗe, lokaci ɗaya kuma ta rufe bakin tare da lumshe ido.

“Zan isar maka da saƙonka Insha Allah.”

Tana faɗin haka ta juya ta shige ciki.

Dariya Habeeb ya yi tare da girgiza kai, karon farko kenan da ya samu kansa cikin farincikin da bai taɓa samun irinsa ba.

Tun daga wannan rana Jummai ta fara wasan ɓoyo da Habeeb, kunya da kuma rashin sanin amsar da zata bashi ne suka sa ta ke ƙin bari su haɗu.

Kullum tana maƙale jikin window tana kallon yadda yake ta raba idanu yana jiran fitowarta.

Tsakanin ta da farfajiyar gidan kuwa sai idan ta ga ya ɗauki mota ko mashin ya fita sannan take fitowa.

Shi kuwa hakan ba ƙaramar damuwa ya jefa shi ba, tun yana iya jurewa har ta kai ga ya kasa.

Tambayar kansa ya shiga yi “Toh ko dai ta tafi ne?

Sai kuma ya tuna ta ce sai hutu ya ƙare zata koma gida, kuma da sauran kwanaki kafin hutun ya ƙare.

Ingiza shi zuciya ta shiga yi akan ya je ɗakin Uwani, zai ganta a can muddin tana nan.

“Allah ya sawaƙe” ya faɗa a fili, don girman kan da ke tare da shi ba zai bari ya je can ɗin ba.

Haka ya yi ta dakon wannan damuwa ta rashin ganin Jummai a ransa, suna haɗuwa da Nasir a makaranta ya gaya mashi yadda suka yi da Jummai, amma kwana uku kenan bai sa ta a ido ba.

Sai da Nasir ya yi dariya mai isarshi sannan ya ce “So Manya, ka ga kuwa yadda ka fige.”

Ƴar dariya Habeeb ya yi “Bana son wulaƙanci fa, shawara zaka bani ya zanyi in sake ganin ta”

Kafaɗarshi Nasir ya dafa “Wai ramawa nake, nan a kan Zee ba irin dariyar da baka yi mani ba, kaga tun ba’a je ko ina ba Allah ya kama ka.”

Cike da damuwa Habeeb ya ce “Ban san haka so yake da naci a zuciya ba, ka san Allah, tun daga ranar da na ganta na kasa sukuni, gaba ɗaya komai ya fita raina, sai ita kaɗai nake tunawa kuma nake muradin sake gani.”

Murmushi Nasir ya yi “Ai abokina So ya wuce duk yadda kake zato.”

Maganganu suka yi sosai akan abin da yake damunsu, don shima Nasir har yanzu yana da tabon Zee, don duk da suna tare, idan tsiyarta ta motsa sai ta yi ta masa yawo da hankali.

Daga bisani kuma Nasir ya bashi shawarar akan ya cire duk wani girman kai ya je ɗakin Uwani.

Habeeb ya ce “Toh idan na shiga in ce me.”

“Nunawa zaka yi komai ya wuce tunda an yi maka faɗa, ka ga da haka zaka samu abin da ka je nema.”

Ba don Habeeb ya gamsu da wannan shawara ba ya amince.

Kwana ya yi yana saƙa yadda zai ga Jummai ba tare da ya shiga ɗakin Uwani ba, duk yadda ya saƙa sai zaren ya kwance, ƙarshe dai ta shiga ɗakin Uwanin ita kaɗai ce ta tsaya.

Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe ya tashi ya nufi ɗakin Uwani.

A hankali ya tura ƙofar falon ya shiga, ras!  Gabanshi ya faɗi lokacin da suka yi ido huɗu da Jummai, wadda ƙarar ƙofar ta sa ta juyowa.

Kasa ƙarasowa ya yi tsakiyar falon, daga can bakin ƙofa ya kafe ta da idanu wanda ya sa duk ta dabarbarce saboda ta san lafinta.

Shi kuwa ƙananun kitsonta da suka zubo har wuya ya ke kallo, kasantuwar yana son mace mai yawan gashi.

Fuskarsa a ɗan murtuke ya tako tsakiyar falon a hankali, sai da ya zo dab da ita sannan ya tsaya.

Ganin fuskarsa a ɗan murtuke ya sa ta ɗan marairaicewa, alamar ta amsa laifinta, kuma tana bada haƙuri, yana ganin ha ya saki wani sassanyan murmushi tare da ƙara kafe ta da idanu.

“Fatima na da kyau” ya faɗa a ƙasan zuciyarshi

A fili kuma ya ce “Kin kyauta Fateemah.”

“Da na yi me?” ta tambayeshi tana ƴar dariya. 

“Da kika jefa ni a damuwa mana, kin kuwa san halin da na shiga a kan rashin ganinki.”

Ɗan fari ta yi da idanu, sannan ta maida idanunta a kan Tv.

Sai da ya ɗauki ƴan daƙiƙu yana kallon ta sannan ya ce “Ina Aunty?”

“Tana ƙurya” ta bashi amsa a taƙaice.

Kai ya gyaɗa, sannan ya zo gefenta ya zauna suna fuskantar juna, don ya ga kamar hanlinta ya karkata a kan TV.

“Saƙona na zo karɓa, me zuciyarki ta ce.”

Idon Jummai ta ɗan zaro, ta fara yunƙurin tashi.

“Yi zamanki, tashi zan yi yanzu, amma sai kin faɗa mani saƙona.

Hanyar bedroom Jummai ta riƙa kallo, don tana tsoron Uwani ta fito ta gansu a haka.

A hankali ta juwo idanunsu a haɗe ta ce “Na isar maka da saƙonka, kuma ta ce ta amince.”

Tana faɗin haka ta tashi da sauri ta nufi bedroom.

Farinciki cike da zuciyar Habeeb ya dakatar da ita.

“I love you Fateemah”

Tana jin ya yi shiru ta yi sauri ta shige tana dariya.

Ido ya lumshe yana jin wani irin nishaɗi a ƙasan zuciyarsa, “Ashe haka so yake da daɗi” ya faɗa a ƙasan ransa. 

Ɗakinsa ya koma tare da kwantawa a kan kujera, ido ya lumshe yana ta tariyar Jummai yana murmushi.

Tun daga wannan rana soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Habeeb da Jummai, duk wani haushin juna sun dena ji, don gwiwa har ƙasa Habeeb ya ba Jummai haƙuri akan rashin kunyar da ya yi ma mahaifiyarta, tare da shan alwashin har gida zai je itama Asabe ya bata haƙuri.

Kusan Kullum sai sun haɗu sun yi zance, duk ranar da basu ga juna ba kuwa hankalinsu bai kwanciya.

Tsakanin shi da Uwani ma yanzu ba rashin kunya, sai ma girmamata da ya ke, duk da ita Uwanin taƙi sakar mashi jiki.

Idan yana son ganin Jummai kai tsaye ɗakinta ya ke zuwa, wani lokaci ya ga Jumman, wani lokaci kuma ta ɓoye bayan labule tana hangenshi yana raba idanu.

Wata rana kuwa ya shigo ɗakin suna hira jefi-jefi da Uwani, kamar ance ya kalli labulen dake bedroom, sai ya ga kan Jummai ta leƙo tana kallon shi.

Ɗauke kan shi ya yi kamar bai ganta ba, sai da aka ɗauki yan mintuna sannan ya sake kallon wurin.

Kashe mata ido ya yi lokacin da suka haɗa ido, aikuwa ta ruga ciki tana dariya.

Dariyar shima ya yi tare da maida hankalinsa ga Tv, don bai son Uwani ta fahimci wani abu.kuma ya yi ma Jummai kashe di a kan kada ta bari kowa ya san suna soyayya, har sai sun fara cusa fahimtar juna a tsakanin iyayensu, wanda kuma shine a bu mai matuƙar wahala.

Bayan sun sake haɗuwa ne ya ce mata “Malama ta ɓoye kin fito?”

Dariya ta kama yi “Malama ta ɓoye kuma?”

Ya ce “Toh na me ki riƙa ɓoye mani, bayan kin san wurinki na zo”.

Shiru ta yi bata ce komai ba, sai dai dariya.

Ƙuri ya yi ma fuskarta yana lissafa kwalliyarta, komai ya mata kyau in banda abu ɗaya, wanda shi kaɗai ne yake nuna daga ƙauye ta zo.

“Fateemah” ya kira sunanta.

Kallon shi tayi tare da aika mashi da saƙon murmushi.

Saida ya ɗan lumshe ido sannan ya ce “Kwalliyarki ta mun kyau.”

Wani irin fari da ido ta yi, wanda sai da gabanshi ya faɗi.

“Kin san me?” ta ce “A’a”

“Wannan baƙin da kike sawa a gira shi kaɗai ke ɓata maki fuska, me zai hana ki dena sanya shi, ko kuma ki riƙa sawa kaɗan, ina ganin kamar zaki fi kyau.”

Baki da ɗan turo “Ka ce dama kushe mani kwalliya zaka yi.”

“Ni na isa” ya faɗa yana dariya.

Dariyar itama ta yi ta ce “Toh shikenan, duk abin da ka ga na yi na kwalliya saboda kai nake yi, kuma Insha Allah zan kiyaye wanda duk bai maka ba.”

Habeeb ya ji daɗin maganarta “Yauwa Teeman Habeeb,” ya faɗa tare da shaƙar ƙamshin turarenta da ya game wurin.

Wannan kyakkyawar fahimta da kuma sauƙin kan Jummai su suka lunka son da Habeeb yake mata, soyayya ta gaskiya ya ke mata, ko a mafarki bai taɓa tunanin yi mata wani abu na ɓatanci ba.

Matsalar da ta fara jawo ma Habeeb ruɗani a zuciya ita ce, duk sadda zasu haɗu, toh sai Jummai ta fesa wani turare mai kashe jikin duk wanda ya shaƙe shi.

Sannan ga kuma sanya ƙananun kaya da take yawan yi, wanda a ganinta duk cikin wayewa ce, dama wasu matsalolin da duk ta same su sakamakon kallon films ɗin turawa.

Duk sadda suka haɗu da ƙyal yake iya shawo kan matsalar dake taso mashi a zuciya.

Babban abin da ranshi ke ruwaita mashi shine ya taɓa jikin Jummai.

Da zaran ya fara jin haka sai ya tashi, har hakan ya fara damun Jummai.

Da ta yi mashi magana me ya sa yanzu bai daɗewa suna hira.

Ido Jajur ya ce mata “Ke ce mana kike rikitamun lissafi.”

Bata fahimci inda maganarsa ta dosa ba, shi kuma bai yi mata ƙarin bayani ba ya tafi ɗakinsa ya kwanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 5Ko Ruwa Na Gama Ba Ki 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×