Skip to content
Part 24 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Kow Ya San Cewa

Kowa yasan cewa zalunci bai dace ba

Kowa yasan cewa  ha’inci bai dace ba

Kowa yasan cewa cin hanci bai dace ba

Kowa yasan cewa munafunci bai dace ba

Kowa yasan cewa… Hmmm

*****

Kowa yasan cewa yin sata bai kyautu ba

Kowa yasan cewa yin fyaɗe bai kyautu ba

Kowa yasan cewa yin gulma bai kyautu na

Kowa yasan cewa yin ƙarya bai kyautu ba

Kowa yasan cewa… Hmmm

*****

Kowa yasan zagin shugaba bai dace ba

Kowa yasan cin amana bai dace ba

Kowa yasan cewa yin zato bai dace ba

Kowa yasan tauye ma’auni ma bai dace ba

Kowa yasan cewa… Hmmm

*****

Kowa yasan danne haƙƙin wani sam bai dace ba

Kowa yasan neman mata sam bai dace ba

Kowa yasan auren jinsi sam bai halatta ba

Kowa yasan cewa shaidar zur bata dace ba

Kowa yasan cewa… Hmmm

*****

Kowa yasan cewa Zubda jini bai dace ba

Kowa yasan cewa yin tsafi bai dace ba

Kowa yasan cewa maraya ai ba dabba ba

Kowa yasan cewa jaki ba bango ne ba

Sai dai kowa na son kansa… Hmm

Kuma bai son laifinsa… Hmmm

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 23Fasaha Haimaniyya 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×