Skip to content

Kuskuren Wasu | Babi Na Biyu

4
(6)

<< Previous

Zaune take yayinda hannuwa biy-biyu ta buga tagumi tun bayan dawowarta gidan Fatima. Babu abin da ya ke bijiro mata a rai sama da ɗiyarta tilo da ta bari. Shin wace rayuwa take? A kintacenta zasu yi sa’ani da Fatima. Ras! Gabanta ya faɗi yayinda wata zuciyar ta raɗa mata,

‘Kenan ita ma ta yi aure! Wa take aure? A wane matsayin rayuwa take?’

Bata ankara ba ƙwalla suka soma zarya a kuncinta. Yayinda wani duhu ya gilmawa tunaninta. Numfashinta ya soma yin sama da ƙasa. Bata ankara da shigowar maigidanta ba tsabar fitar hayyaci. Ya kai mintuna huɗu da shigowa ɗakin amma bata sani ba, idanu ya tsura mata cike da takaici, ba wai dan ganin halin da take ciki ba sai dan ɓata masa lokacin da ta yi yana ta magana babu amsa. Ji yake kamar ya shaƙeta ta mutu tsabar baƙin ciki. Doka stool ɗin mudubi ya yi da ƙarfi. Firgigit ta juya,

“Alhaji sannu..Kai ne..? Ban san…”

“Dakata Khadija, ba uzurunki nake buƙata ba.”

“Wallahi ban san ka dawo…”

Sake katseta ya yi a tsawace, ke ki ka sani, ni ba damuwata bace. Na shigo ne in faɗa miki zamu tafi Saudiyya hutu gobe ni da Hajiya Hauwa da yara so abin da ki ke buƙata ki yi magana.”

Wannan karon ba ƙwalla bace kaɗai, kuka ne ya ke shirin taho mata. Yayinda wani miki ya shiga famuwa a tsokar dake tsakanin a wazunta. Wai sai yaushe zata zama kamar kowace mace mai cikakken iko a gidan mijinta? Shekaru goma sha takwas tana zaman bauta amma tamkar an shuka dusa. Ta sani cewa kuskurenta ya isa girbar fiye da abubuwan da take riska, amma bata yi tsamani za a samu naci wajen zamansa a gurbin rayuwarta ba. Duka kuskuren nata ne, amma girbar laifukan da ba ita ce tushan dasa su ba.

Ta lura tsaf rayuwarta neman zama turken kare take yi, shi wanda take yi dominsa baya ta tata yayinda a idanun ƴan uwanta yake nuna babu ya ita har suna ganin ita ce mowar gida. Wawan tsakin da ya ja ne ya juyo da hankalinta amma kafin ta farga ya wula mata damin kuɗi ya fi ce fuu! Kallonsu ta yi tare da ɗauka ta yi wurgi da su ta fashe da kuma kamar ƙaramar yarinya. Ba sune muradinta ba, ba su ne za su bata abin da take ganin ya yi wa rayuwarta giɓi na har abada ba. Yau ɗaya tana jin kewar giɓin da bata da tabbacin cike shi. Tana jin kamar bata cancanci girbar wannan shukar ba. Ba nomanta bane, akwai girbin da ahali ke gadarwa da makusanci shi bisa kaifi irin na alƙalamin ƙaddara.

Ta jima anan zaune tana jin hayaniya da karakainar mutanan gidan amma bata jin fitowarta zata haifar da alfanu dan haka ta zauna tana jan istigifari. Ba ita ta fito ba sai magarba bayan ta idar da sallah saboda yadd take jin ranta ya yi sanyi. Gaba ɗaya mutanan gidan suna fallo, kowa da abinda yake yi.

Mashiɗa tana gam a laptop ɗinta tana haɗawa da cin ƴaƴan itacen data sa aka tanadar mata. Tun fitowar Mama Khadijan ta kalleta sheƙeƙe kamar wata sa’arta ta watsar. Karima ce ta taho da ɗan gudunta. Ta turo baki gaba,

“Mama tun ɗazu nake zuba ido ban ganki ba, gashi gobe zamu yi tafiya ba mu yi hirar da zan dinga tunaki ba.”

Kalaman yarinyar sun ɗauke kaso tamanin na damuwarta. Aranta ta ji ashe ita ma uwa ce. Sai dai ƙarfin tsakin da Hajiya Hauwa ta saki ya ankarar da ita mafarki take yi. “Wallahi Karima saina buge bakinki ya yi taɓon da duk ranar da wannan matar tabar gidan nan zaki dinga tuna ita ce sila! Dan annamimmanci ita uwarki ce?”

Rau ta yi da idanu, kamar zata yi magana sai ta juya da gudu ta shige ɗakinsu. Ji ta yi ƙafaffunta sun ƙara nauyi kamar ba zasu ɗauketa ba. Zuciyarta na matsewa da wani irin tashin hankali da ba sabo ne a duniyarta ba. Tabbas ta zauna da abokan zama masu baƙin jahilin kishi irin na matan ƙauye amma bata taɓa gamo da muguwa kuma makirar mace kamar Hajiya Hauwa ba. Wankakiya ce fes a idanun danginta saɓanin cikin rayuwar auranta. Sallamar Baba maigadi ce ta katse mata tunani, ta amsa masa da hanzari sanin babu wanda yake da ƙimar yin hakan duk cikar fallon.

“Hajiya Mama wai gashi daga gidan barrister…”

Kafin ya ƙarasa Mashida ta kwashe da dariya, “An dai yi girman kwabo. Gemai-gemai ana bin gidan matasan yara abin hadda ƙwaɗayi.”

Saroro ta yi tan dubanta daga ita har Baba maigadin. A haife ta haifeta hasalima ita ce mutum na farko data yi mata wanka tana jinjira amma saboda ƙasƙanci ita ce ta ke mata wannan furucin. Ɗauke kai ta yi ta karɓi saƙon kamar bata ji ta ba. Hakan ɗabi’arta ce ta ji, amma kuma ta nuna kamar bata jin ba. Ta gani amma sai ta zama makauniya duk dan a zauna lafiya.

Tana hango tausayinta a idanun tsohon ya girgiza kai ya fita. A ransa yana jinjina rashin tarbiya irin na yaran gidan da mahaifiyarsu ta zamo tsani. Shi kansa bai tsira a wajensu ba amma yana mamakin yadda take shanye duk wani abu daga faninsu. Tsayin shekaru ashirin yana aiki agidan, a lokuta mabanbanta alaƙar mutunka ta sha haɗasu tun kafin ta zamo ƙarƙashin ikon maigidan har zuwa matakin da suka zamo inuwa guda. Sai dai ba zai iya cewa ga rana guda ta ya tsinkayi murmushi a saman nutsattsiyar fuskarta ba wanda bana yaƙe ba. Tabbas cikin mutane ma irinta ƙayadaddu ne.

Da sassarfa ta wuce ɗakinta ko buɗe saƙon bata tsaya yi ba, tana jiyo shewarsu tare da mahaifiyarsu har zuwa lokacin da ta jiyo sautin mahaifinsu suna murna. Idanunta gaba ɗaya sun rufe mafita kawai take nema. Kai tsaye ta ɗauki wayarta ta kira layin babbar yayarsu. bugu biyu ana uku ta ɗaga, “Kaga matan many..”

Aka faɗa daga ɗaya ɓangaren, sai da ba a kai ga ƙarasawa ba ta katse a zafaffe. Karon farko data tunkari yayar tasu da irin wannan zafin da ya sakata ɗaurewar mara.

“Dakata Yaya Kulu, wallahi na kira ne in shaidamiki yau na gaji da cin kashin da Yaya da matarsa suke min. Abu har kan ƴaƴan da a cikina na haifesu. Tabbas ku shirya gani na a gida koda wane lokaci. Kadda ki yi min barazana da cewar Baba ba tsina, ba ko tsireni zai yi wannan karon na kai maƙura. Da girmana da komai na zama ƙasƙantaciyar baiwa. Kuma ku sani daga ranar dana dawo zan nemo ɗiya ta duk inda take zan gyara kuskurena wannan a rubuce yake. Tabbas zan nemo Mar…”

Ga mamakinta ta kasa ƙarasawa. Sunan ya tokare mata maƙoshi tan jin yadda take kokawa da numfashinta. Ba wannan ne karon farko ba duk lokacin da taso furta abin da ya shafi rayuwar ɗiyartata hakane yake faruwa da ita. Wayar ta suɓuce a hannunta ba tare data sani ba.

Sunkuyawa ta yi hannunta a wuyanta data shaƙe da tunanin hakan ne zai kawo mata sassucin raɗaɗin da yake neman fasa mata maƙoshinta. Daidai lokacin Karima ta shigo da zumar bata haƙurin abin da ya faru a fallo.

Halin data ganta ya sanya ta shigo da gudu da ƙyar ta ɓamɓare hannuwanta a wuyanta. Suna maida numfashi tare. Kallonta ta yi a ruɗe sai huci take yi yayinda ƙwalla suke sunturi kan kumatunta. Wayar ta ɗauka tare da datse kiran da har lokacin yake a kunne. Ba tare da ta jira cewarta ba ta shige bedroom ɗinta ta bar Karimar a zaune.

A can ɓangaren yaya Kulu kuwa tsabar kaɗuwa da mamaki ne ya daskarar da ita har ta kashe wayar bata san amsar da zata bata ba. Babu abin da ya soma faɗo mata a rai sai gargaɗin da aka yi mata kan ta kiyayi asara da durƙushewar rayuwa duk ranar da Khadija ta sa ɗan bar neman ɗiyarta.

Musamman akan dukiyar data mallaka a sillar auren ita Khadijan. Dan haka hankali ta she ta hau lallubar wata lamba a wayarta. Sai dai kafin ta dana kira wata lamba ta shigo a wayarta ta, ta ɗaga da faɗuwar gaba.

“Madam miliyan huɗun da aka haɗa za a kai banki ƴan fashin sun shigo ɗazu sun karɓeta ba jimawa”

Yaraf! Ta faɗi ƙasa ba ta motsi.

*****
Kaico!

“Alawiyya akwai tafiyar da za mu yi yau dan haka me k ike buƙata?”

Sai da ta haɗiyi wani kakkauran miyau sannan ta furta, “Bana buƙatar komai ma, kuma ma mene ne abin gagawa ba anjima zaka dawo gidan ba?”

“No ba zan dawo ba daga office zan wuce, dawowar bata da wani muhimmanci.”

‘Muhimmanci?”

Zuciyarta ta yi mata raɗar kalmar a kunnuwanta. Wani abu ta ji ya daki ƙirjinta, girmnsa har ya shallake tunanunta. Murɗawar da mararta ta yi ya tuna mata tarin abubuwan da ta yi ta ɗirkawa kanta saboda tana yaƙinin daren yau zau iya zama tsaraba gareta. Shekaran jiya ya dawo, kuma yana bata tabbacin yau zai koma. Ba wannan ne takaicinta ba, inda zai tafin ya fi yi mata ciwo fiye da wofintar da ita da yake yi, “Ba ki ce komai ba!”

“Abin cewar ne babu.”

Ƙit ta kashe wayar tare da dannawa Haj Zali waya.

“Kina gida?”

“Ina gidan ko kuma kango?”

“Bana sn shirme Zali ina san ganinki!”

“Baki da matsala ke tawa ce zan yi komai domin farin cikinki.”

Wani matsuguni me girma kalaman nata suka samu a zuciyarta. Hakan ya ɗarsa mata mamaki, a duniya babu mutumin da yake yi mata kwatankwacin kalaman ta ji sun tafi da duniyarta sama da Aliyunta amma mene ne yake shirin faruwa da ita?

Cikin hanzari ta shirya ta ɗauki mota ta fita. Har ta isa gidan nata bata daina mamaki ba, tana da yaƙinin amincewarta na zama ƙawaye ne mafari. Amma ko alamu bata jin danasanin faruwar alaƙar. Sai yanzu ta ke jin dama tun asali wannan rayuwar ce ta kamaci mai matsala irin tata. Sai dai a wasu lokutan takan ji an ya ba ta tafka kuskure ba? A haka ta gangara da motarta layin gidan. Maigadi ya buɗe mata ta shiga.

Ɗaya bayan ɗaya take kallon mutanan da sukw cikin gidan, yayinda zuciyarta take kisima mata akwai waɗanda irin tata rayuwar ce ta kawosu gidan. A babban fallon gidan ta samu masauki, amma sai ta samu umarni daga Hajiya Zali na cewar a kaita ɗakinta na musamman. Haka ta miƙe tabi yarinyar kamar raƙumi da akala. A ranta tana ƙara yaba tsaruwar gidan duk da ba shi ne shigowarta ta farko ba. Suna shiga yarinyar ta juya.

Idanunta ta janye daga bakin ƙofar ta ɗora su kan Hajiya Zali. Take ta sake jin wani karsashi na ɗaukarta. Hannuwanta ta ware mata, babu musu ta miƙe kan duga-duganta cike da sassarfa ta isa gareta.

Lumshe idanunta ta yi, wani sasshi na zuciyarta ya kwaɗaitar da ita,

‘ina ma Aliyu ne!”

Dum! Wani sauti ya ziyarci masarafar sautinta, ɓurɓushin murmushin dake tsakiyar laɓɓanta ya soma zangwayewa yana gushewa zuwa bigiren da ya saba zama a irin yanayi.

Hannunwan Zali da suka sami matsuguni a wasu sassa na jikinta suka soma saukar mata da wani irin hucin da ya tilasta mata hanzarta barin jikinta. Da ido ta dinga binta, ta taɓe baki tana taunar cingum ɗinta a nishaɗance,

“Ke dai Alawiyyah kin ji ɓutur wallahi, ki zauna ɗa namiji ya dinga watangaririya da rayuwarki kamar ɗiyarsa. Kin gani nan bani da ƙulafuci kan namiji tunda na gano wajen ragema kaina zafi. Tsakanina da ɗa namiji abu biyu ne, shi ɗin waigi ne ga rayuwata, sai kuma kadaran-kadahan idan ya ce kulle in ce cas!

Ga inda zan je ana mararina ana tattashina kawai in tsaya ina ɓatawa kaina lokaci. Ke fa bama irin namu ki ke ba, an yi anyi a gwada miki kina dojewa to mene ne matsala a harka irin taki? Abu ne fa na sirri daga ke har shi kun sauƙaƙawa juna ba tare da shi ya fuskanta ba. Kawai dai zai wayi gari kin zama irin yadda yake so, kin sakarmasa mara ya yi fitsari ke kuma kina nan kina sha’aninki!”

Ƙarasowa ta yi kusa da ita tana rangwaɗa, yayinda ta sassauta murya da wata irin ƙaramar murya me haɗe da wani irin maganaɗisun da suke jan hankalin abokan harkarsu. Hannunta ta shiga murzawa da wani irin sallo na ban mamaki.

“Please ki yi wani abu dan Allah. Ki bani dama ko ban baki farin ciki ba zan zamo tsani.”
Kallon data yi mata ba iya kashe jiki bane kawai, akwai wani abu. Wani abu da taso mata wanda yake kwance tsayin shekaru a ƙirjinta. Binta ta yi da idanu, sai kuma ta gyaɗa kai tana kasa kowane harafi na ta a mazaunin da ya dace a ƙasan ruhinta.

Take zuciyarta ta amince da abin da ta faɗa. Dan haka ta shiga sakin murmushi tana jin duniyarta sabuwa. Shewa wasu ƴan mata biyu suka saki, suna shigowa maƙale da juna. Kauda idanunta ta yi akansu tana jin zata amince da shirin Hajiya Zali na samun farin ciki amma ba zata iya irin rayuwar da suke yi ba.

*****
A hanzarce ya shigo gidan a soro ya yi kiciɓus da mijin Ummansa ya rusuna ya gaisheshi. Maimakon ya amsa sai auna masa ta maguzawa da ya yi tare da yin waje ya barshi anan shanye da baki. Juyawa ya yi da sassarfa yana gwamma numfashi ya shiga gidan, da hanzari ta miƙe tana tambayar, “Sauban lafiya?”

Ledar hannunsa ya miƙa mata,

“Mamma ku ci wannan zan koma tashar motar yanzun nan!”

Kai ta kaɗa tana dubansa,

“Aa Sauban bana ƙaunar zaman tashar nan wallahi…”

“Dola ce ta saka, ki yi haƙuri wata rana sai labari Mammah. Ga wannan ki bawa Afra da Afnan su tafi islamiyya. Kuɗin littatafansu ne. Abdallah da Ahmad kuma su yi haƙuri zuwa gobe muga abin da hali ya bayar. Tashar ce sai a hankali ta soma cushewa akwai irinmu mabuƙata da dama. Sai dai Allah Ya rufa asiri.”

Ido kawai take binsa da shi, duka-duka shekarunsa babu yawa amma hidimar ƙanne ta haye masa. Idan yana raba abu tsakaninsu daki-daki ta kan manta da shekarunsa ta dinga hangoshi tamkar wani magidanci.

Sai yanzu take godiya ga ubangiji daya zamto ta ɗora yaran kan turbar ƙaunar junansu ba tare da kalmar ƴan ubannci ta shata musu layi ba kamar yadda mahaifinsu ya ƙudurta. Sossai Abdul yake ƙara samun matsayi a zuciyarta bayan gurbin daya cike na babban ɗa.

Musamman da yanzu ya ƙara tsayi tsarara irin na wahalar rayuwa. A hankali kamninsa suke shirin juyewa zuwa na mahaifinsa. Kafin ta yi aune ya fice yana faɗin,
“Sanyawar albarkar Jarumar uwa Mamma!”

Abdul na fitowa ya wurgawa Shamsu dake ƙofar gidansu harara, ya ɗaure fuska tamau yana kauda idanunsa daga kallon ƙurillar da yake yi masa. Bakinsa ya motsa alamar gunguni, ya yi ƙwafa yana sake jin haushin murmushin gefan baki da Shamsun ke masa tare da kashe masa ido da kuma ɗaga gira kamar wata budurwarsa. A filli Shamsu ya furta,

“Allah Ya kai damo ga harawa!”

Hayatu dake gefansa ya furta,

“Ko bai ci ba ya taka!”

Dariya suka saki mai sauti.

*****
Koda fitar Abdul Mamma ta saki murmushin da bata shiryawa ba, Abdul daban ne cikin yaranta. Sallamar ƙannansa ta yi ta soma ƙoƙarin haɗa surfan Alkamar gidan Alhaji Audi da matarsa ta aiko mata. Sake jawo taɓarya ta yi ta ci gaba da aikin zufa na ta keto mata. A karo na uku da ta ɗaga taɓaryar wani sartse ya shiga tsakanin fatar hannunta da babban ɗan ya tsanta, wata marainiyar ƙara ta saki tana runtse idanu cike da fitar hayyaci. Wani tunani ya shigeta lokaci ɗaya. Take ƙwalla ta cika idanunta ta soma tuna rayuwarta ta baya daki-daki.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

6 thoughts on “Kuskuren Wasu | Babi Na Biyu”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×