Skip to content

Kuskuren Wasu | Babi Na Daya

3.8
(4)

“Fatima wai me yasa ba ki da mutunci ne, ke kullum cikin ƙorafi ki ke? Ke wace irin mace ce ne? Haka ki ka ga sauran mata na rayuwar auransu?”

“Kabir ka kirani da duk sunan da ranka yake so, amma wallahi ka ji na rantse ba zan juri wannan cin fuskarba. Ka faɗamin wanne haƙƙi ne naka bana saukewa? Kawai saboda son rai irin naka ba siɗi ba saɗaɗa sai ka ƙirƙiri fitinar da bata da tushiya domin ka ɗagamin hankali? Wai me yasa baka da imani ne? Baka tausayina ko kaɗan wallahi.”

Duka ya kawo mata da bahagon hannunsa, a sukwane ta goce tana karewa da sirirraran hannunta. Ta kai kallonta kan dogon yatsunta, waɗanda suka ƙawatu da jan lallen da ta shafe lokaci tana manna salatif kawai domin ta faranta masa. Amma kuma dawowarsa bata amfana mata komai ba sai kayan takaici. Wanda da a bayane yana shigowa da kuzanta ƙunshin zai soma kafin komai.

Ja baya ta yi tana girgiza kai.

“Ka yi komai Kabir, amma kadda ka kuskura hannunka ya kai jikina da sunan duka! Zan baka mamaki fiye da…”

Tau! Ta ji saukar mari a kuncinta, wanda ya haddasa mata yin a hantsile bakinta ya bugu da kujera, kallonsa take, sai diri ya ke yi kamar mahaukacin kare. Gadan-gadan ya yo kanta kamar mayunwcin zaki, yana nufarfashi kamar matashin ɓauna.

“Bara na gwada miki tawa kalar tarbiyar kafin ki nuna min taku, wai ku kuna taƙama da boko da anyi magana ku kira ƴanci ko? Gaskiya sai yanzu na amince da batun Samir amma zan nuna miki kuskurenki. Ni ba sauna ba ne ba zan ɗauki cin kashin da ƴan gidanku ke yi wa maza ba!”

“Samir!”

Ta yi furucin tana ja baya, laɓɓanta na motsawa da wani irin karsashi, a saitin idanunsa ta ke ajiye masa kallo cike da tuhuma. Tabbas sai yanzu ta ƙara ganin wautarta na yanke auren Kabir. Kuskurenta na farko shi ne rashin sanin waye asalin Kabir ɗin, kawai ta na yi masa kallon da takewa tarbiyar ahalinsu ne kasancewarsa ɗan babban gida. Shi yasa babu wani jinkirtawa ta amince da shi. Ashe kallon kitse ne take yi wa rogo. Amma abu na farko da ya kamata ace ta duba shi ne, waye abokinsa? Zuciyarta ta tunatar da ita cikin raɗa.

‘Samir!’

Runtse idanu ta yi tana tuna waye Samir ɗin? A hankali ta buɗe tana saukesu akansa. Sun kaɗa sun yi jajjur. Murmushin tsakiyar laɓɓa ya saki, yana aje kallonsa a saitinta. Kallon tsakiyar ido ya yi mata, a wannan karon ya yi nasarar ganin muradinsa, wato rauni a tare da ita. Yana kallon yadda kowace gaɓa ke amsar saƙonsa, zagayeta ya yi na sakan biyu. Ya ƙyasta hannuwansa ƙyas! Ƙyass!! Ƙyasss!!! A lokaci guda cike da karkashi ya furta.

“Haba Fatima me yasa ki ka kasa fuskantar mu maza dangin gujiya ne?”

Murmushi ta yi mai sauti, ƙwallar data ke adanawa tsayin lokuta ta sami zubowa, yau ɗaya ta ji karsashi da muradin son maida masa martani.

“Tabbas Kabir Ka zamomin dungu acikin rayuwata, sai dai kasani ba kowa ce ba ce take zama…”

“Ƙarasa mana ba kowace mace ke zama namiji yana takata ba ko? Ai ban yi mamaki ba. tambarin ahalinku ne wannan.”

“Kabir ya isheka. Kana faɗin ahali! Ahali!! Shin kai kana da…!”

Bata sami zarafin ƙarasa abin da take san faɗa ba, ya kaɗa kai ya yi ficewarsa. Dubansa take, kowane motsi nasa yana ajiye mata tabo mai girma a ranta. Karo na barkatai ta sake kai idanunta, yana gab da fita, tafiyarsa yake hankali kwance, yana aje taku kan duga-dugansa cike da sarauta. Sautin muryarsa ke fitar da waƙar da ke nuna zallar nishaɗinsa, a hankali ta fashe da kuka mai cin rai. Lumshe idanu ta yi tana ayyana,

‘Lallai maza suna suka tara.’

Ta shafe mintuna uku a zaune ta ji sallamar Aunty Khadija. Hakan bai sa ta maida hawayenta ba, domin abokin kuka ake faɗawa mutuwa. Da sassarfa ta ƙarasa tana rungumarta. Kuka ta ɓale da shi kawai kanta yana wata irin sarawa.

“Aunty ko ban faɗa ba Allah zai saka min wallahi!”

Da hanzari ta kalleta, bakinta har rawa yake yi,

“Me ya sa ki ke haka ne Ukty? Kin san kuwa illar mace ta nemi sakayya akan zalluncin da mijinta ya aikata mata? Hmm! Ba fa komai ki ke yi ba face daɓawa kanki wuƙa!”

Taune gefan bakinta ta yi karo na barkatai, ta ɗora hannunta akan ɗan matashin  cikinta da ya soma girma, wanda har gobe wanda ya yi sillar samuwarsa bai san da zamansa ba.

“Kinga wannan abin da ki ke tare da shi”, bata bari ta amsa ba ta ci gaba, “ko badaɗe ko bajima shi ki ke nema wa makoma matuƙar za ki nemi sakayya. Ai abin cikin ƙwan ya fi ƙwan daɗi, kina roƙon ubangiji ya saka maki akan abin da ya akaita miki, sakayya kuma kan ahalinsa zata tabbata domin abin da ya taɓasu shi ya taɓa. Kina san ki haifi ɗiya ta tashi a irin rayuwar da ki ke ciki?”

Da hanzari ta girgiza kanta, ƙaunar abin da ke cikin nata na ƙara zagaya lungu da saƙo na zuciyarta. Kanta ta ɗora bisa kafaɗar ƴar uwarta. Wani kuka mara sauti na neman ƙwace mata.

“Aunty sam na kasa fahimtar dalilin da zai sa a kira mutum miji amma ace sai matarsa ta shata layuka tsakaninsu idan tana son zaman lafiya. A zatona aure amintacciyar tarayya ce tsakanin mace da namiji. Amma abin da nake gani yafi kama da mulkin mallaka.

Ubangiji fa da kansa ya ɗaga darajar maza akan mata, amma hakan ba yana nufin mace ta zama tabarmar zamansu ba. Komai namiji ya yi sai akirashi ado Yaya? Bayan kuma idan aka yi masa duban tsanaki dodon adone ga rayuwar ɗiyar mace. Wannan wace irin rayuwa ce da farinciki da nutsuwar mace basu da mahimmanci a gidan aure? Wace irin al’ada ce ke mantawa da cewa mace ma abar halitta ce mai zuciya a cikin ƙirjinta?”

Jijjigata ta shiga yi, tana jin wani irin karsashi a ƙasan ranta. Wai yaushe ne ɗiya mace da rayuwarta za su huta a doron ƙasa? ‘sai sun mutu.’

Wani sashi na zuciyarta ya bata amsa. Da hanzari ta girgiza kanta tana ƙoƙarin ɗago da ƙumajinta gudun raunannar ƴar uwarta. Bayanta ta ci gaba da bubugawa, murya a tausashe ta furta,

“Rayuwa ba komai ba ce, kowa ce mace da ki ka gani da irin nata ƙalubalan. Duk macen da ta ce miki bata da matsala a gidan auranta ƙarya take miki, yaudararki take yi. Rayuwa ce da lissafi baya haɗata, rayuwa ce da ta bambanta da kintacen zuƙatan masu shiryata. Kadda ki yi yaƙinin farata da matsala, haka kuma kadda ka yi ganganci ginata akan turbar da za ki yi danasani…”

Kai ta kaɗa kamar marayan ɗata, ta taune gefen bakinta har sai da ta soma jin gishiri-gishiri na bin tsakiyar wushiryarta,

“Me yasa ƴar uwa? Haka rayuwar mata zata kasance? Kullum su ne koma baya? Na ji aure shi ne mutuntakarmu, shin aljannah ba ta samuwa ga ɗiya mace ne sai dole ta hanyar aure? Idan ba ki yi aure ba ke ce lallataciya, amma kuma yayinda kika karɓi alamtuwar martabar auren sai ki zamo baiwa? Baiwarma ba irin wadda zata amsa sunan Baiwa mai bauta ba, sai ki zamo baiwar da zata karɓi kowace ƙasƙantaciyar rayuwa saboda kawai an maƙala miki kalmar nan ta mace matar aure…?”

Zuwa lokacin kuka ya ci ƙarfinta, ta zame daga riƙon da ta yi mata tana sassheƙa da girgiza kai,

“Gaba ɗaya rayuwar wata macen abar tausayi ce, ita ɗin bata tsinanawa kanta komai. Wata irin bishiya ce ga rayuwar na raɓe da ita da rassanta basa amfanar da ita sai dai wasunta. Ƙwarai ina tausayin rayuwarmu domin tattare take da masu buƙatuwarta da yawa. Bishiya ce guda ɗaya amma ƙarƙashinta zaka riski tarin masu buƙatuwar kusanci da shan inuwarta. Ba dan komai ba sai dan dukansu rayuwarsu na buƙatarta. Gata dai da rauni wanda ita tafi cancanta da a tausayawa amma kuma kash!

Sau tari zaki riski ɗiya mace yayinda take yarinta mahaifiya ke kulawa da ita, idan ta girma ta tasa kuma burinta shi ne ya zan kwatantawa mahaifiyata kulawar da take gwadamin? Wanda a wannan lokacin ita kanta mahaifiyar burinta kenan, ɗiyarta ta tasa itama ta samu abokiyar taya hidimar rayuwa.

Tafi-tafi ƙannanta na buƙatarta wajan hidimarsu. Yau da gobe sha’awa da burinta kan sauka akan ni ya kamata in ɗauki hidimar gidanmu ta fannin aikace-aikace badan komai ba sai dan yadda aka gindaya tunaninta akan hakan. A kwana a tashi a sadata da ɗakin aure, sannu-sannu sai girma ya hauta. Hidimar gida data maigida, kwanci tashi kuma hidimar ‘ya’ya rainonsu tarbiyarsu har zuwa girmansu. Yayinda suka tasa fargabarta kulawa da rayuwarsu, idan ta aurar da su kuwa inba dace akai ba tsugono bata karewa gareta. ‘Yayanta na buƙatarta, maigidanta na buƙatarta ƙannanta na buƙatarta. Shin Aunty ita kuma wa zata buƙata? Duk wannan bai isa ɗarsa tausayi da ƙaruwar mutuntakar mace a idanun wasu mazan ba? Sai ma zamowarta abar wofintarwa.Anya akwai mafi cancantar dacewa da a tausayawa sama da rayuwarmu.?”

“Fatima!”

Ta faɗa da murya mai zurfi, ido ta saka cikin nata na wasu daƙiƙu suka yi kallon ƙuda.
“Nasan ke ake zallunta, amma hakan ba zai sa in ƙi baki haƙuri ba, wata rana sai labari. Duk wani yunƙuri da zaki yi yanzu ba shi da wani alfanu.”

Kai ta kaɗa tare da lumshe idanunta. Sossai take jin tsanar hallayar mijinta har cikin ranta tare da soyayyar Aunty Khadija har tsakiyar ranta. Sake dafa kafaɗar Fatima ta yi, amma kuma ta kasa furta komai. Idanu ta runtse komai na wulga mata daki-daki. Da wani irin karsashi zuciyarta take matsewa. Karo na ba adadi take jin kewar kusanci irin na ƴan uwantaka. Ƙasan ranta tata rayuwar take haskowa. Tanajin ina ma tana da me ƙwarara mata guiwa kamar yadda take ƙarfafawa Fatima. Ina ma tana da wanda zata ɗora kanta aka kafaɗarsa ta yi kuka! Ya Allah koda bata sami mafita, koda bai share mata hawaye ba ya furta mata cewar,

“ki yi haƙuri ɗiyarki zata dawo gareki. Zata yafe miki kuma zata yi miki uzuri.”

Duk da ta shan jin kalaman daga umarnin zuciyarta, amma tana muradin me furta mata su cike da ƙarfin guiwa. Tana son a faɗa mata komai zai wuce kuma yaushe. Tana buƙatar nauyin da ƙirjinta ya yi ya sauƙaƙa. Tabbas tana buƙatar wannan. Tana tsoron ranar da haƙƙin Maryam zai soma walagigi da rayuwarta.

Ƙaddara

Sauri take kamar mai niyyar tashi sama, burinta kawai ta kai wajen da zuciyarta ke muradi. A zafafe ta ɗaga ƙafarta ta nufi tsallaka wawakekiyar kwatar, wani irin juyawa ƙoƙon gwuiwarta ya yi ya lanƙwasa take ta durƙushe. Wasu hawaye ne suka zubo mata, ba ta damu ta goge ba ta miƙe cike da ci-da-zuci ta cigaba da tafiya.

Ɗaiɗaikun mutanen da ke zaune a wajen suka bi ta da kallon tausayi, wasu kuma na ganin bekenta da ganin ita ta jefa kanta a duk yanayin da take ciki. Ƙofar wani nakasasshen gida ta ja burki, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar ya ɗauki shekaru. Ƙwaƙƙwarar tsawa mai ƙarfi za ta iya kai shi kushewa. Tura ƙyaure ta yi wanda ya kasance na langa-langa, ta shiga. Wasu yara ne guda uku suka nufo ta da gudu suka ruƙunƙume ta.

A karo na biyu kwalla ta sake biyo kuncinta. Ledar hannunta ta kunto ta miƙa musu suka soma cin abincin hannu baka hannu ƙwarya. Tana gefe tana dubansu. Yunwa take ji amma ganin halin da yaran suke ya sa gaba ɗaya ta ji komi ya fita a ranta. Kukan ƙaramar ta tsinkayo tana faɗin,

“Mamma ki ce shu baimin.”

Da muryar tsamin baki irin na ƙananan yara masu ƙarancin shekaru. Share hawayen ta yi tana murmushi,ta ce, “ku bar mata kun ji!” Kallonta suka yi kamar masu neman ƙarin bayani, sai suka saki ledar suna ja baya duk suka raɓe a bango kamar ƙadangaru. Ɗaya bayan ɗaya take sauke idanunta a kansu, wani na taɓa zuciyarta mai zafi.

Zuciyarta ta dinga tuna shuɗaɗun al’amuran da suka cakuɗa duniyarta da launin zafi irin na alƙalamin ƙaddara, wasu taurari masu ƙuna ne suke giftawa a idanunta. Abubuwan da suka gudana cikin rayuwarta sun bar mata tabo mara gogewa tamkar yau faifan yake gara mata. Sosai take ajiye shi a wani gurbi da take ganin ita kaɗai ta cancanci jin ɗacinsa, komai na yawo cikin kanta yana ƙuntata duniyarta tana kallon yadda al’amarin ya fara daga rubutu irin na alƙalaminƙaddararta, ya dinga juyin waina da rayuwarta duk da ƙanƙantarta.

Ta gamsu ƙwarai idan ya tashi rubutunsa ba girma ko cancanta yake dubawa ba. Ba zaɓi ake badawa ba bare ta ware kanta daga masu rungumo kundin da ke ɗauke da shafuka masu tsauri. Ta yi amanna kan cewa kowa da irin shafin da yake buɗewa kuma dole ya karanta, tana mamakin masu nuna yatsa kan rubutun da babu magogi a kansa. Komai nata ya zo mata a sabuntaccen al’amari. Takan ji an ce wai gidan aure shi ne mutuncin mace da duk wata martaba tata, amma nata gidan auren shi ne silar dagula rayuwarta.

Ta zaɓi aure matsayin mafitarta kodan cigaban marayun ƴaƴanta amma ya maisheta maƙiyiyarsa. Bata san me yasa san zuƙata ya gindaya tsakanin mu’amalar ahalinta ba sama da zumunta. Sai dai tana da yaƙinin komai nada nasaba ne da SHU’UMANCIN MATA. A wannan gaɓar tana buƙatar wanda zai sabunta rayuwarta fiye da tsumayinta. Ko ba komai tana buƙatar wanda za ta ɗora kanta a kafaɗarsa ta faɗa masa damuwarta. Ta na mamaki da sau tari al’umma kan manta cewa kowane giɓi ga rayuwarka yana da sanadi.

Tarko

Tunda motar da ta ɗaukota ta direta a bakin shigo-shigo ɗin wajen gyaran gashin mai ɗauke da tambarin MARWAKH ta ke jin idanun matan da ke tattare a wajen a kanta. Ba yau hakan ta saba faruwa gareta ba, musamman idan aka yi la’akari da yanayin motar da ta kawota da kuma suturar da take jikinta. Hakan ba baƙon al’amari ba ne gareta, sai dai maimakon ta ji ɗaɗin yadda idanu ke shawagi a kanta akasin hakane.

Taune gefan bakinta ta yi har sai da ta ji gishiri-gishiri yana bin tsakanin haƙoranta wanda bata tantama da cewar jini ne. Ɗauke idanunta ta yi daga kansa akaro na barkatai, ta tura murfin motar da zumar fita. Rafar kuɗi ƴan ɗari-ɗari ya ɗora mata kan cinyarta.

“Na san za ki shiga gida, a gaidamin su kafin na dawo ɗaukarki.”

Ɗauke kai ta yi tana ƙoƙarin maida ƙwallar da ta ke ƙoƙarin samun muhali a kuncinta, ta girgiza kai tare da tura murfin ba tare da ta ɗauki kuɗin ba, lokaci guda ta furta,

“Za su ji.”

“Alawiyyah!”

Bata jira cewarsa ba ta wuce, tana jin lokacin da ya yi ƙwafa ya bawa motarsa wuta. Hakan sam bai dameta ba, hasalima ya rage kaso mafi tsoka daga cikin nauyin da ya asassawa ƙirjinta. Bata daina mamaki yadda idanun tsarorinta mata ke yawo a kanta ba, tana da yaƙinin ayyana samun kwatankwacin rayuwarta suke yi a ƙarƙashin ransu. Murmushi mai sauti ta saki tana tunanin kowace mace dai da irin nata ƙalubalan.

A hankali ta sami matsuguni a cikin wajen da aka tanada saboda irinsu. Wadda suka saba sossai a wajen, ta nufota da kazarniyarta tana dariya,

“Hajiyarmu yau ma kin iso ashe? Lallai yau jakata a cike take da maƙuɗan kuɗaɗɗe.”

Dariya ta yi mai sauti, “daɗina da ke akwai ban dariya Hassana yau ban ga injilah ba.” Ta furta tana baza idanunta alamun nema. Matashiyar budurwa ce siririya kamar a busheta ta faɗi ta ƙaraso wajen, kallo ɗaya za ka yi mata ka sakata a sahun masu iyayi. Ɗan ƙaramin hancinta ta sosa tana faɗi,

“Ga ni nan ai tunda na hango Alhajinki ya ajiyeki naketa nishaɗi.”

Wannan karon bata tanka ba, ta ajiye murmushi mai sauti tare da miƙa musu kum da kibiyarta. Nan da nan suka soma yi mata abin da suka san ta fi buƙata. Suna yi suna jan ta da hira tana biyesu koba komai sun rage mata kewar abin da ya ke cin ranta.

Wani ƙamshi ne ya yi musu sallama, gaba ɗaya suka ɗaga idanunsu ba dan sun shirya wa hakan ba. “tubarkallah” Injilah ta furta a ranta daga nan ta maida kanta kan abin da take yi. Itama da ake wa tsifar daga kallo ɗaya bata kuma maida kanta sashin ba. Sai dai wani sashi na zuciyarta na mintsininta kan sake kallon sashin musamman yadda ƙamshin matar ya dinga haifar mata da wata irin kasala da nutsuwar da bata san dalilinta ba. Ƙarar takalma ɗas-ɗas ya ja hankalinta, kafin ta gama tantancewa ta ji mutum a mafi kusancinta, murmushin tsakiyar laɓɓa ta sakar mata tare da furta,

“Sannu”

“Yauwa sannunmu” ta maida mata amsa a yangance. Ta ci gaba da tauna cingum ɗinta, ƙas-ƙas-ƙas-ƙararras! Karo na barkatai ta ɗora idanunta akanta. Gabanta ya yi mummunar faɗuwa. Ta sakar mata murmushin da ya ƙarasa kashe gaɓan jikinta,

“Ku ɗan bamu waje!” Ta furta tana sauke idanunta akan matasan ƴan matan, zuciyarta cike da farin cikin samun alamun nasara, akaro na wanda bata san adadinsa ba na hallartarta wajen dominta kawai. Hannunta ta damƙa, take wani sanyi ya ziyarceta, ta ɗan murza shi a hankali tare da furta, “ko zaki yi min alfarma mu zama ƙawaye.”

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×