Skip to content
Part 6 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

Kamar yadda rayuwa ta gadar game da zamantakewar auratayya a gidan malam Bahaushe haka ce ta kasance a gidansu Maryam. Kowa ce mace ita take ɗauke da ragamar ‘ya’yanta tun daga kan ci da sha da kuma sutura.

Tsakanin su da mahaifin su a sutura sai dai sallah. Ba damuwarsa ba ce ki ɗorawa ɗansa talla, abin da kawai ya sani shi ne zai baki tsabar hatsi don ki sarrafa abinci, ranar da yake ra’ayi ya ɗora kuɗin cefane ranar da baya yi ki nemo ko sata ce ki sarrafa ba damuwarsa ba ce.

Ɗa kuwa zai sa miki shi a makarantar islamiya amma hidimarsa ba za ta wuce ɗaya biyu ba zai ce ya gaji. Ire-iren wannan ya gadar da fitar mata ba iyaka a cikin gidansa, tare da haifar da yawaitar yara ƙanana marasa galihun kulawar iyaye mata kimanin guda ashirin da huɗu cif. Boko kuwa dama ba a yinta a gidansa.

Ga uwargida ba ta da matsala don yaranta sun tasa sun kawo ƙarfi shi ya sa take kallon kowa a ɗage dan ta miƙe ƙafa su suke komai, kuma ba ta lamunci su tallafawa ƙannen su ba. Sai dai ta maishe da duk wani yaro na cikin gidan bawanta ta hanyar ɗora musu talla kala-kala. Sana’a take kimanin kala goma a sauke wannan a ɗora wancan kullum yaran na tafe babu batun karatun addinni bare na zamani.

Mahaifin su bai damu ba sakammakon sauke masa kuɗin cefane da ta yi kai tsaye. Sauran iyayen yaran da ke gidan kuwa waɗanda ba su lamunci mai da na su yaran bayinta ba su ma su ka fantsama ɗorawa yaran su talla.

Hakan ya sa talla ta zamo kamar wani abu mai muhimmanci a cikin gidan, gasar fita ake, sai kuma sauyin sana’a a yayinda wanda ya fi kowa sai da kaya kan lokaci yake zama tauraro abin nunawa a cikin gidan.

Kamar yadda akasarin ɗabi’ar wasu cikin Hausawa ta kasance na rashin waiwayen yaran da su ka bari gidan tsofaffin mazajan su sakamakon ƙaddarar saki, haka ce ta kasance ga rayuwar Maryam. Tunda mahaifiyarta ta bar gidan mahaifinta ta manta da babin rayuwarta.

Maryam ta taso mace mai kamar maza, kaf cikin sa’aninta na gidan babu me cin galaba kanta. Haka kuma tana da naci da taurin kai musammn idan ya kasance tana da gaskiya. Mahaifinta yana kulawa da ita ba don komai ba sai don kasancewarta rigimammiyya ta gaske. Idan aka ce sallah ta kama bai mata ɗinki ba ta dinga kuka da birgima ke nan a tsakar gida har zuwa majalisa gaban abokansa, wanda hakan ke zame masa tonan silili. Shi ya sa da ta buƙaci abu yake yi mata.

A cikin gida kuwa sai ya zamana ta taso cikin tsangwamar matan uba, ba don komai ba sai don kasancewarta yarinya mai tsayuwa tsayin daka wajan kare mutuncinta ko da wasa ba ta yadda da raini ba tun tana ƙaramarta.

Dambe tsakaninta da yaran gidan ba kama hannun yaro, hakan ya sa yaran gidan su ka sa mata suna ‘Dage’. Lokacin da ta cike wasu shekaru a duniya a lokacin ne wani tunani ya soma ƙabura cikin duniyarta. Baban makaminta kuwa shi ne, mahaifinta na matuƙar ƙaunarta.
Ba kowane tunani ne ya soma ƙabura a duniyarta ba face shiga makaranta. Ta fara tunanin fara makaranta ne sakammakon ganin yaran maƙota da kuma na unguwaninsu na dabdalar zuwa makarantar boko da islamiyya. Mahaifinta shi ne mutum na farko da ta soma yi wa kukan sa makaranta, amma cikin ikon Allah sai ya wofintar da muradinta.

A wannan gaɓar ta yi kuka iya kuka amma abu ya ci tura a haka ta gangara zuwa shekaru takwas a duniya a wannan lokaci ne ta yanke fara ɗaukarwa matar mahaifinta talla saboda ta sami kuɗin shiga makaranta.

Ta fara talla cikin nasara, tana ɗaya daga cikin yaran gidan da ake wa kirari da mai kan sa a. Duk yawan tallan da ta ɗauka ba ta kwantai, haka kuma ba ta baro daidai da taro kasancewarta masifaffiya. Hakan ya ja mata soyayyar matar mahaifinta, tana ba ta abinci mai yawa ta ci ta koshi.

Haka ta kan siya mata gazal da hoda don ta yi kwaliyar da za ta fito a cikin sa aninta yantalla. Sai dai idan aka tona zuciyar Maryam babu abin da ta tsana sama da a kirata ‘yartalla ba don komai ba sai don yadda take ganin maza magidanta da akasari sun kai sa’annin mahaifanta suke wasa da su.

Babban mutum da gemunsa da komai ya yi jika da su, yakan yi ƙoƙarin ja musu mayafi ko wartar kudi a hannunsu musamman in canji ya haɗa. Haka ma samari ‘yan-bana-bakwai masu ƙarawa sama hazo, su kan taka muhimmiyar rawa wajen damuƙarsu da kai musu wawura da sunan wasa.

Ga duk ‘yartalla wannan ba baƙon abu ba ne a wajenta, wannan ya sa ta ƙara zama masifafiya ta ƙarfi-da-yaji wajen ganin babu wanda ya yi mata wannan wasan.

Babban takaicinta mahaifinta bai taɓa la’akari da fitarta da dawowarta ba, haka ma waɗanda take wa kallon manya a gidan. Wani lokacin takan tuna masu iyaye gidan ma ba su tsawatar musu ba ina ga ita? Idan ta yi irin wannan tunanin takan ji wani bigire na zuciyarta na neman ƙunsa mata ɓurɓushin tsanar mahaifiyarta, da ba ta barta a gidan mahaifinta ba da ba ta yi rayuwa irin haka ba.

Takan tambayi kanta wai me ya sa iyaye mata ke barin ‘ya’yan su a gidajen mazajen su bayan rabuwar aure? Bayan ta taɓa ji wata rana a bakin masallaci wani malami na faɗar musulunci ya ba su damar ɗaukar yaran na wani lokaci. Idan tana irin wannan tunanin zuciyarta kan ƙuntata matuƙa da gaske.

Ta ɗauki tsawon lokaci wajen samar da kuɗin da su ka samar mata da abin da zai isheta ɗinka kayan makaranta, a wannan gaɓar da kanta ta kai kanta makaranta. Bayan bincike malaman makarantar su ka nemi ganin mahaifinta, sai dai ƙiriƙiri ya nuna shi ba shi da hannu kan kawota.

Tausayi da duba yadda take ƙulafucin karatun ya sa malaman ɗaukarta, abin ka da makarantar gwamnati aka ba ta litattafai kyauta, da sauran kayan buƙatu sakammakon adalci irin na gwamna mai ci a lokacin.

Kasancewar ta yi girma aka yi itifaki aka saka ta aji huɗu, cikin ikon Allah ta dage da naci da binbinin ‘yan ajin masu ƙoƙari har ta soma fahimtar karatun yadda ya kamata. Sannu a hankali ta fara karatu cikin nasara.

Hakan ya sa ta soma ja baya da tallan Mama Sumaye. ba ta ɗauka sai ta dawo makarantar boko wadda ake taso su karfe sha biyu na rana. Da zarar azahar ta yi kuma za ta dawo ko ba ta siyar ba ta ajiye ta tafi makarantar Malam Lamiru.

Sauyin da aka samu game da tallanta ya haifar mata da baƙin jini fiye da baya, ba ta samun isasshen abinci sai ranar Juma’a shi ma saboda ana raba musu abinci ne a ranar a makaranta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fita hayyacinta ta kaɗe ta koma kamar tsumagiya.

A gidan su ba ta da sakewa cikin ‘yan’uwanta da ta zauna za su soma tonanta suna faɗin ‘yar bokon ƙarshen zamani. Da gayya za a ɗauki littafinta a yaga ko a yi makamashi da shi, babu damar ta yi magana sai su yi mata taron dangi sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi haka za su turmurmushe ta su yi ma ta duka. Sai dai ta koma gefe ta raɓe tana ajiyar rai amma hakan baya hanata idan ta samu faragar ganinsu a ɗaya-ɗaya ba ta kama yaro ta yi masa duka.

Kwanci tashi a haka Maryam ta shiga ajin matakin ƙarshe a makarantar firamare, wato aji shida. A wannan lokaci ne ta soma fuskantar ƙalubalen rayuwa mataki na biyu, kuɗin zana jarrabawa da aka nema su bayar shi ya soma dagula kwanyarta, domin kwata-kwata Mama Sumaye ta daina ɗora mata talla a cewarta ba za ta tsaya jiran gawon shanu ba.

Tunda garin Allah ya waye ta takura kanta da tunanin yadda za ta sami mafita. Wannan yanayi ya sata kasancewa mashau-mashau, tun safe har zuwa yammacin ranar da ta samu kwanyarta ta yanke mata tunanin da take ganin zai fissheta.

A daren ta kasa runtsawa saboda neman mafita, washegari da sassafe ta shirya ta kuma durfafi cika muradinta. Sai dai tun kafin ta kai wajen da zuciyarta ta kai ta ƙirjinta ke duka, yayin da gaɓɓan jikinta su ka yi sanyi. Ba ta da wani kuzari ko kaɗan a tare da ita, a haka ta zauna kan dakalin kofar gidan tun La’asar ta baza idanu tana hango ta ina madogarar da take ganin za ta ɓulle mata za ta ɓullo.

Tun da ya shawo kwanar gidan yana saɓa babbar rigarsa gabanta ya yanke ya faɗi, a karo na farko ta sami kanta cikin shakka da kuma tsoron tunkararsa da buƙatarta duk da ba sabonsa ba ne sauke nauyin buƙatunta.

Wani irin lugude ne ke wanzuwa a kowace gaɓa tata. Aro juriya ta yi ta yafa ta nufeshi duk da bugawar da kirjinta yake yi, bakinta na rawa ta yi tsaye a gabansa kamar itaciyar da aka dasa. Kamar wadda aka yi wa umarnin sai ta ba wa guiwowinta umarnin ladabtuwa ta zube a gabansa, wanda sai a lokacin ya lura da ita.

“Ba…Ba…Sannu…da zuwa!”

Ƙuri ya yi mata da idanu kamar me karantar wani abu cikinsa,

“Maryama lafiya ki ka wani tsare ni da idanu kamar an jijjiga ɓera a buta”

Gabanta ya sake bugawa, ta sunkuyar da kai ƙasa, “Babanmu kudin zana jarrabawa aka ce mu kawo naira dari uku. Shi ne…Shi ne…na…”

Take fuskarsa ta sauya kamar wanda aka yi wa aiken mutuwa, idanunsa su ka kada jajur da su kamar gauta.

“Na taɓa yi miki kama da me ƙaunar karatun bokoko a wuta? Ba ma boko ba kin taɓa ganin na sa ɗana a makaranta? Ko ni na saki a makarantar?”

Ƙyaƙƙyafta idanu ta soma yi kamar wadda ta yi wa maigari ƙarya. Kanta a ƙasa zuciyarta na ƙara ƙuntata tana tuna wai yau ita ce take ladabi a yi mata abu? Kafin ta ɗago ya shuri takalminsa ya yi cikin gida. Tun daga bakin babban zaure yake kwarara faɗan da ya jawo hankalin kowace mace ta fito. Mama Sumaye ɗaure da zani tana jan majina,

“Malam lafiya kake ta kwakwazo kamar wanda aka kama….”

Kallon da ya wurga mata ya sa maganar maƙalewa, abokiyar zamanta ce ta leme baki tana faɗin,

“Yo ke ma Yaya banda abin ki ai sanin hali ya fi…”

“Dakatamin malamai wani shashashanci na ji yana ɓullowa a gidana, wai Maryama in ba ta kuɗin zana jarrabawar share fagen shiga babbar makaranta ta ‘yan mata! Yo ni na sa ta makarantar?”

A sukwane Mama Sumaye ta saki shewa, ta kaɗa tafi tare da buga cinya daga bisani ta rangaɗa guɗa. Hakan ya yi dai-dai da shigowar Maryam. Ba kuma ta fasa ba.

“Ahayye nanaye! Allah nawa Annabi na uwata daɗina da gobe saurin zuwa. Ai wanda bai ji bari ba ya ji ho ho, kai sarki ubanka talaka. Babu yadda ban yi da yarinyar nan ba ta dinga ɗaukar mini talla amma ƙemadagas ta ƙeƙashe ido ta ƙiya saboda ta raina ni. Koda yake ai raini gado aka yo tun daga tushe. To uwar mutum ma dai haka ta ƙaraci maitarta ta gama kuma ta barmana gida…!”

Maryam ta waro idanunta daƙwa-daƙwa kanta, ta soma ƙunƙuni tana cuno baki, ganin mahaifinta na harararta ya sa ta yin ƙasa da kanta tana share hawaye. Tunani take wai ma wane ganganci ya sa mahaifiyarta tafiya ta bar ta cikin ɗimbin jahilci? Bayan da bakinta ta ji ana faɗar Mamarta ta yi makaranta?

Wai ma me ya sa ta auri mahaifinta ta haifeta a wannan rayuwar? Karo na farko ta soma tunani anya mahaifiyarta na ƙaunarta? Ita fa tashin birni ce ta san gardin ilmi fiye da yadda malaman su ke kwatanta musu.

Tunaninta ya tsaya cak! Sakammakon hango Salmanu ɗan amaryar maƙotan su da aka saka cikin kwatamin gidan su ya faɗa yana kuka. Zuciyarta ta ba ta da mahaifiyarsa ba ta tafi ta bar shi ba da aka saketa da bai faɗa kwatami ba. Tunaninta ya sake katsewa jin Mama na faɗin,

“Yo malam daina ta da jijjiyar wuya mana, ai karatun bokokon ba dole bane ga sa’aninta nan duk a ɗakunan aure har ma da zuri’a, gara ta fitar da miji a yi mata aure mu huta kada ta jawo mana abin faɗa!”

Ras! Gabanta ya faɗi da ta tuna ita ba mai ma kulata sai Sa adu mai faskare, wani almajiri da aka kawo almajiranci kusa da su. Wani miyau ta haɗiya muƙut kamar zai yaga mata maƙoshi. Ta ɗago kai idanunta taf hawaye,

“Mama dan Allah ko rance ne ki ba ni wallahi zan yi talla na tara miki kuɗinki. Ina son karatun nan sosai don Allah Baba ka ka ka yi min aure wallahi bana son aure yanzu, na yi ƙanƙanta!”

“La’ilah ilalah! Ƙarshen zamani ya zo malam ɗiya kamar wannan tana furta ba ta son aure”

Mama Sumaye ta faɗa tana tafa hannuwa da riƙe haɓa. Kuka Maryam take rirris zuwa yanzu ji take kamar ta shaƙota ta kasheta ta huta da maganganunta ta take jin sun fi takobi kaifi wajan yanka burukan rayuwarta.

Wata wawar mangara mahaifinta ya kawo mata, sai ta yi gefe bisa tsautsayi zaninta ya harɗeta ta yi taga-taga sai ta kifa. Bakinta ya fashe, haƙoranta su ka karci ƙasa ta ɗago bakinta ya haɗe da ƙasa da jini babu kyawun gani. Nan da nan ƙananta su ka zagayeta suna dariya suna tafa hannuwa.

Kafin ka ce kwabo sun ƙara yawa. Da wannan damar mahaifinta ya fice, akan idanunta tana rakashi da kallon tsana da baƙin ciki mutum mafi zallunci da ya ƙuntata rayuwarta. Ta cikin dishi-dishin idanunta da hawaye ya gama ɓatawa ta ke ganin wulgawar rigarsa.
Ta lumshe idanu tana fatan mutuwa ta ɗauketa ta huta. Wai a haka ita ce mi sauƙi-sauƙi da baya duk. A baya tfi kow samun gata da kulawa wurinsa, sai dai laifin mhaifiyarta da ya shafeta shi ya sa take fuskantar waƙi’a.

Ranar kwana ta yi tana kuka, wani lokacin ta yi jim tana tunanin mafita. Wata zuciyar na faɗa mata ki je wajan mahaifiyarki wata kuma na tuna mata wai ma ina mahaifiyartata take? A haka ta tsinkayi kiran assalatu ta miƙe da ƙyar jikinta duk ya yi tsami. Bakinta kuwa ya haye suntum da shi kamar zunguru.

Da sassafe ta isa makaranta duk da kayanta ba wanki saboda ba kudin omo amma ta ji daɗi tunda ƙarshan sati ne za a ba su wanki idan za a rufe makaranta. Haka ta kasance a makarantar ba ta tsinci komai ba daga karatun da aka yi musu kan bayanin yadda zasu gudanar da jarrabaa.

Lokaci zuwa lokaci takan share ƙwalla. Malamin lissafi da ya zama shi ne ƙarshan shiga ya ankare da ita. Sai dai duk tambayar da ya yi mata ba amsa ƙarshe ma ce masa ta yi faɗuwa ta yi daya tambayi dalilin kumburin bakinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Wasu 5Kuskuren Wasu 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×