Skip to content
Part 3 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

A hanzar ce ya shigo gidan a soro ya yi kiciɓus da Abban su, ya rusuna ya gaishe shi. Maimakon ya amsa sai auna masa ta maguzawa da ya yi tare da yin waje ya bar shi a nan shanye da baki. Juyawa ya yi da sassarfa yana gwamma numfashi ya shiga gidan, da hanzari ta miƙe tana tambayar,

“Sauban lafiya?”

Ledar hannunsa ya miƙa mata,

“Mamma ku ci wannan zan koma tashar motar yanzun nan!”

Kai ta kaɗa tana dubansa,

“Aa Sauban bana ƙaunar zaman tashar nan wallahi…”

“Dola ce ta saka, ki yi haƙuri wata rana sai labari Mammah. Ga wannan ki bawa Afra da Afnan su tafi islamiyya. Kuɗin littatafansu ne. Abdallah da Madu kuma su yi haƙuri zuwa gobe muga abin da hali ya bayar. Tashar ce sai a hankali ta soma cushewa akwai irinmu mabuƙata da dama. Sai dai Allah Ya rufa asiri.”

Ido kawai take binsa da shi, duka-duka shekarunsa babu yawa amma hidimar ƙanne ta haye masa. Idan yana raba abu tsakanin su daki-daki ta kan manta da shekarunsa ta dinga hango shi tamkar wani magidanci.

Sai yanzu take godiya ga ubangiji daya zamto ta ɗora yaran kan turbar ƙaunar junan su ba tare da kalmar ƴan ubannci ta shata musu layi ba kamar yadda mahaifin su ya ƙudurta. Sosai Sauban yake ƙara samun matsayi a zuciyarta bayan gurbin daya cike na babban ɗa. Musamman da yanzu ya ƙara tsayi tsarara irin na wahalar rayuwa. A hankali kamaninsa suke shirin juyewa zuwa na mahaifinsa. Kafin ta yi aune ya fice yana faɗin,

“Sanyawar albarkar Jarumar uwa Mamma!”

Sauban na fitowa ya wurgawa Shamsu dake ƙofar gidan su harara, ya ɗaure fuska tamau yana kauda idanunsa daga kallon ƙurillar da yake yi masa. Bakinsa ya motsa alamar gunguni, ya yi ƙwafa yana sake jin haushin murmushin gefan baki da Shamsun ke masa tare da kashe masa ido da kuma ɗaga gira kamar wata budurwarsa. A filli Shamsu ya furta,

“Allah Ya kai damo ga harawa!”

Hayatu dake gefansa ya furta,

“Ko bai ci ba ya taka!”

Dariya su ka saki mai sauti.

*****
Ko da fitar Sauban Mamma ta saki murmushin da ba ta shiryawa ba, Sauban daban ne cikin yaranta. Sallamar ƙannansa ta yi ta soma ƙoƙarin haɗa surfan Alkamar gidan Alhaji Audi da matarsa ta aiko mata. Sake jawo taɓarya ta yi ta ci gaba da aikin zufa na ta keto mata.

A karo na uku da ta ɗaga taɓaryar wani sartse ya shiga tsakanin fatar hannunta da babban ɗan ya tsanta, wata marainiyar ƙara ta saki tana runtse idanu cike da fitar hayyaci. Wani tunani ya shigeta lokaci ɗaya. Take ƙwalla ta cika idanunta ta soma tuna rayuwarta ta baya daki-daki.

Wata Ƙaddara

Tun farfaɗowar Yaya Kulu bayan ƙaramin ɗanta ya yayafa mata ruwa ta tsunduma tunani kan yadda za ta shawo matsalar da ta tunkaro su. Babban baƙin cikinta asarar da ta tafka na maƙudan kuɗaɗɗan da tana da tabbaci kan ba lallai ta sake samun kamar su ba. Musamman yadda al’amuran plaza ɗinta su ka ja baya sosai akan shekarun da su ka shuɗe. Wayarta ta ɗauka jiki babu ƙwari ta dana kira. Bayan ƴan gaishe-gaishe ta ɗora da,

“Malam matsalar…”

“Buƙatarki ta iso tun tsayin lokuta, abu uku muke buƙata daga gareki shi ne. Za ki sayi baƙar saniya a yankata. Wanda zai yi yankan zai saka fararen kaya, a tara jinin a roba idan ya gama a cire kayan a tsoma su a jinin.

A je gidan tururuwa a yi rami ko suri a saka a ciki. Akwai layu guda biyu kan katangarku ta waje, kisa a ɗauko za ki sami tarwaɗa a cire kan ki buɗe ki saka a ciki kisa wani abu ki ɗaure bakin tarwaɗan.

Bakin Khadija zai rufe ruf kan batun ɗiyarta amma sai kin kula sosai. Domin a yanzu haka ɗiyarta na da kusanci da ku sosai tana nan cikin Katsina kuma tana buƙatar agaji kadda ki kuskura su yi gamo da juna ko wani nata.”

“Malam babu yadda za ayi ta bar garin?”

“Ƙaddararta na zama cikin garin mai girma ce, akwai tashin hankali ga duk wanda ya yi yunƙurin datse igiyar da ta yi naɗi wa zaren ƙaddararta.”

“Na gode Malam za ka ga saƙo!”

“Mun riga mun ɗauki saƙonmu, ki duba inda kika ajiye wata kaddara taki mai girma anan muka zari kasanmu bama aikin banza”

Ras gabanta ya faɗi da ta tuna da sarƙarta ta miliyan biyu da rabi. Baki na rawa ta yi nufin yi masa magana amma tsawar da ya daka ta dakatar da ita.

“Musunki na nufin ɓata aikinki”

Ɗif wayar ta ɗauke, runtse idanu ta yi ga mamakinta sai ga ƙwalla. Wata tsana me girma ta sake ƙabura a zuciyarta game da Maryam tana jin da tasan za ta zamo tarnaƙi ga rayuwarta da sun kauda ita tun kafin zuwanta duniya kamar yadda wasun su su ka bayar da shawara tun a baya.

Kai tsaye ɗakinta ta nufa ta soma binciken wajen da ta ajiye sarƙar. Sai dai sama ko ƙasa babu sarƙa babu dalilinta. Hannu ta ɗora aka tamkar za ta tsala ihu, sai dai shigowar babbar ‘yarta a yanayin da ya ja hankalinta ya sa ta maida hankalinta kanta.
“Kausar daga ina ki ke?”

Sai da ta yatsina fusk kamar ba za ta tanka ba, sai kuma ta fuske.

“Gidansu Naja’atu na je na karɓi na saƙo!”

Kamar za ta sake jefa mata wata tambayar, amma ba ta ba ta damar hakan ba. Ta yi saurin kara waya a kunnanta kamar an kirata. Wayar ƙarya ta kama yi a haka ta shige ɗakin tana satar kallon mahaifiyarta ta. Tana shiga ta danna sakata tare da zaro kwalaban maganinta. Ɗaya bayan ɗaya ta soma gwamutsa na gwamutswa tana jinta kamar wadda aka yi wa bushara da gidan aljannah.

*****

“Abba sannu da zuwa.”

Yaran su ka furta suna dubansa a ɗan tsorace. Kauda kai ya yi yana cin magani. Daidai lokacin da ta ajiye taɓaryar hannunta tana kwashe yajin da ta dakawa maƙotan su aka biyata.

“Madu maza zo ka kaiwa Indo dakanta, idan ta baka kuɗin ka siyo muku gari da ƙuli da mai a zo aci lokacin shiga karatu na ƙaratowa.”

Ba ta kali inda yake ba, har yaron ya yi abinda ta umarce shi. Hakan be dame shi ba burinsa kawai ta haɗa garin da shi. Yana kallo ta share zufa tare da sake ɗaukar masarar da aƙala ta kai tiya ɗaya ta juye cikin babban turmin ta soma surfawa.
“Ke Maryama!”

Ba ta amsa ba, amma ta dakata tare da zuba masa idanu alamar ina saurarenka. Tsaki ya ja tare da faɗin,

“Kin maidani ɗan iska saboda kin soma kama mutsabai ko?”

Takaici da mamaki ne su ka nemi kasheta. Idonta ya sauka kan Afnan da ta lura tana gunguni tare da aikawa mahaifin nata harara. Humairah kuwa murguɗa masa baki take, tana cuno baki. Ƙirjinta ya ɗoka, da wani maɗaukakin yanayi. Wani tsoro mai girma ya ɗarsu a ranta tana gudun a sake maimaita kuskuren baya.

“Me kake buƙata?”

“Abinci”

Ya faɗa kai tsaye, galala ta yi tana dubansa, a saninta rabon da ya ba ta sisi harta manta. Yaranta kuwa har tausayi suke ba ta. Hatta da sallah baɓsu san su saka sababin kaya ba sai dai kwance tsawan rayuwar su shi ne suturar da suka yi sabo da ita.

Ballantana ita kanta, ba ta taɓa ganin miji me ƙyashi da hassadar mijinta ba, ita kam ba dan tsananin rabo ba ba ta jin za ta haifi waɗanan ƴaƴan da su ka haifa tare kodan gudun rayuwar ƙaskancin da tun ba yau ba ta karanceta a idanunsa. Amma ƙaddara ta riga fata.

“Ka jira Madu ya dawo”

Ta furta tana ƙoƙarin maida ƙwallar idanunta,

“Wallahil azim Mamma ba zai ci shi ba, ki nema da guminki kuma ki ba wani ƙato? Ki ci da shi ki ci da ƴaƴansa amma a wofin ce!”

Saubahn ne ya yi furucin da murya mai zurfi, ga wata ƙwalla kwance a idanunsa. Ido ta zuba masa a tsorace, bakinta har rawa yake yi. Tasan halin Saubahn sarai. Akanta zai iya da kowa amma ba ta hango ɗa me ido a fafatawarsa da Nuhu. Humaira kuwa dake gefe, hannu ta ɗaga masa alamar jinjinawa.

“Lallai wuyanka ya isa yanka Sauban ni kake cewa ƙato? Kin gani ko Maryama kin ga abin da kika haifa ko? Lallai ne ko da yake babu haufi ga mutumin da ba asan asalinsa ba. Ai tsintaciyar magge ba ta magge. Dangin dangiroro ne ba haufi”
Wani ƙaton ramine ya sake buɗewa a zuciyar Sauban, ya ɗago da kai idanunsa jajir, tamkar ɗan bududugin kwaɗo a ruwan barkono.

“Ba asan asalinmu ba amma ana manne damu ana cin arziƙi..”

“Sauban dan ubanka zo ka bar gidan nan kafin raina ya ɓaci in nakasa ka!”

Ta yi furucin wani marayan kuka na taho mata. Da mamaki cikin kansa yake dubanta.

Zuciyarsa na tunasar da shi,

‘Wannan jarumar uwa ce fa, mai cike da zuciyar sadaukarwa. Ita ce ɗaya da yake kallo matsayin sanyin idaniya, ita ɗin ce madogara wa duk wani karsashi da muradinsa. A yau ita ce take iƙirarin ya fita ya bar gidan da da guminsa a cikinsa.

Da tabbatuwar yadda furucinta ke samun mazauni a zuciyarsa, yayin da wani sashi ke bauɗar da fahimtarsa yana sake jadadda masa kamar furucin na yi masa nuni ne da ta ga ji da shi a cikin ahalinta.

A karo na barkatai ya sake jinjina girman fifita mijinta akan kansa. Ba yau ne farau ba, amma duk da ƙanƙantar shekarunsa da take hangowa yana mamakin yadda makantar son rai take gindaya tunaninta.

Kallon Mamman yake da dukkan zuciyarsa, wasu shafukane suke sake buɗe masa tare da ajiye manyan taban da be san ranar cikar gurbin su ba. Be yi aune ba ya soma jin saukar duka ajikinsa.

Dukansa take da duk wani sauran ƙarfi da ya rage mata, sai dai duk duka ɗaya tana jinsa yana kai mata karo a ƙahon zuciyarta. Shi take duka, amma kuma ita ce take jin zafin, wanda ke tafe da duk wata gubar haƙuri da ta haɗiya a baya.

Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi, dukansa take ba dan ba ta sansa ba, sai dan guje masa baƙar zuciya irin ta Nuhu. Ita take dukan amma ciwukan a zuciyarta take jin saukar su. Yanayin da take kai hannu kansa kaɗai ya isa tabbatarwa me hankali ciwon daga zuciya yake.

Saubahn kuwa tsaye ya yi yana kallonta, tana dukansa, bai ko motsa ba kuma ba shi da niyyar hakan. So yake tabunan dake zuciyarta su ƙara kumburin da za su asassa ciwon da zai buɗe idanunta daga makanta kan mutumin da ba komai ba ne a rayuwar su. Wannan alaƙar yake san datsewa, yana so ta rayu a bigiren da babu nauyin maha’incin mutum kamar mijinta. Ya alla ko ba komai ƙuncin su zai sauƙaƙa fiye da kowa.

“Ka fita ko na yi maka baki Sauban!”

Duk wasu notika na jikinsa sai da su ka daina aiki! Dubanta ya ke yi amma idanunsa na lalluban idanunta dan san gasgata furucinta,

“Eh! Ka tafi ka yi nisa da rayuwarmu bama buƙatarka!”

Malam Nuhu kansa da kullum burinsa ganin ya nesanta ta da Sauban ɗin ne sai da ya girgiza. Be taɓa tsamanin ranar za ta zo masa a kusa ba, amma ba zai bari damar ta kuɓuce masa ba,

“Me ka ke jira ba ka ji abin da ta ce bane?”

“Na ji Baba kuma zan tafi ba anjima ba yanzu ma kuwa”

Karon farko a rayuwarsa ya kira shi da Baba tun bayan kashedin da ya yi masa kan kuskuren aikata hakan,

“Kadda ka sake kirana da babanka ni ban haifi ɗan iska irinka ba. Shege me idanun mayyu.”

Shi ne furucin da ya shata layi tsakanin su a baya dan haka be taɓa kuskuren sake kiransa da kalmar ba. A fusace yake da shi dan haka ya ci gaba,

“Mamma zan tafi zan yi nisa da ku, ba kuma za ki sake gani na ba har sai lokacin da ki ka gajiya wajen neman inda nake. Ina fatan kadda ki makara!”

Daga haka ya juya da sassarfa yana barin tsakar gidan akan duga-dugansa. Tafiya ya ke kan ƙafafunsa amma zuciyarsa ce take motsawa. Tana matsewa da wata irin kewa na ahalinsa. ya sani Mamma ta yi hukunci ne dan gudun abin da zai faru gareshi amma be taɓa tsamanin za ta iya nesanta shi da ahalinsa ba. Me ya sa za ta zaɓi alawa ta yasar da zinare? Bayan yana da yaƙinin zaƙinta ba zai dawwama a kan harshanta ba.
Kai tsaye tasha ya nufa. Ba shi da tabbaci kan garin da zai nufa dan haka motar da ta rage na neman cikon mutum guda ita ya nufa kai tsaye ta tashi da shi zuwa garin da za ta nufa.

Lokacin da Madu ya dawo ba ƙaramin mamaki ya yi ba ganin su Afnan na kuka.

Tambayar duniya sunƙi ba shi amsa sai shassheƙa da ajiyar zuciya. Kasancewarsa mutum me zuciya tu ni ya cika ya yi fam ganin hakan ya sa Humaira da suke kira da Afra ta daure ta yi masa bayanin abin da ya faru.

Ba don ya san Humaira ba zai iya cewa ƙarya take, duka dai gata shekarunta ba masu ya wa bane amma yana da tabbacin ba za ta yi wa mahaifiyarsu ƙarya ba. Da wani irin ɓacin rai yake kallon mahaifiyar tasu sai dai ba shi da ƙumajin tanka mata dan haka ya ajiye ledar garin jiki a sanyaye ya juya ya bar gidan.

Babu inda be zaga ba a tashar amma be ga ko me kama da yayansu ba. Zuciyarsa ta cika da ƙunci yayinda kansa ya soma barazanar buɗewa. Me ya sa Mamma za ta yi musu wani giɓin a rayuwar su? Ba ta san Sauban shi ne bangon rayuwar su ba? Wace irin rayuwa take buƙatar su yi? Ba shi ya koma gida ba sai goma na dare. Zuwa lokacin gaba ɗaya ƙannan na shi sun yi zuru-zuru. Da gudu Afnan ta rungume shi tana kuka,
“Baka gan shi ba ko?”

Ba shi da karsashin ba ta amsa dan haka ya jinjina kai kawai yana bubbuga bayanta,
‘La illah illalahu Maryama me zan gani zo ki ga yadda ɗanki ya ƙwaƙumemun ƴa dama zaluntata kuke?”

Jinkita babu inda ba ya rawa tsabar tashin hankali, domin ta gama fassara inda kalamansa su ka nufa. Musamman yadda ya buɗe murya maƙota na ji. Madu kuwa tsabar takaici sai ya sake matse Afnan a ƙirjinsa so yake sai ya gwadawa mutumin nan iyakarsa.

“Madu ka cikata idan ba so kake baƙin ciki ya ƙarasani ba!”

“Mamma ke kika si yi tikitinsa da kanki saboda ai kinsan zaɓin da kika yi rayuwarki ba shi ki ka zaɓa ba. Shi ki ka zaɓa akan gobanmu?”

Ya faɗa yana nunabshi da yatse tare da danne mikin kewar ɗan uwansa,

“Zamu barki da shi Mamma. Za mu barki da shi da halins..”

“Ba zamu barta da shi ba Madu.”

Abdallah ya furta yana auna masa mugun kallo,

“ai hakan yake buƙata tare da muƙarabansa ya kasheta har lahira. Ni zan koya masa hankali zan nuna masa mu ma ƙarfinmu ya kawo…”

Gabanta ne ya faɗi tasan halinsa. Ya fi kowa zuciya cikin yaranta yana da haƙuri da shanye abubuwa amma be iya fushi ba. Ba su yi aune ba ya ɗaga shi ya buga da kasa, gaba ɗaya su ka yi kansa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Wasu 2Kuskuren Wasu 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×