Skip to content

List of Series

Abdulkadir by Lubna Sufyan

Kowa ya sha mamakin yadda aka yi har soyayya ta ƙullu a tsakanin Abdulƙadir da Waheedah saboda bambancin da ke tsakanin halayensu tamkar na ruwa da wuta ne. Yayin da wasu kuma ke tunanin halin da za ta shiga a zamantakewar aurenta da shi. Sai dai sun ba mara ɗa kunya sosai na tsawon wani lokaci kafin babbar ƙawar Waheedah da ake kira Nuriyya ta kutso kanta jikin Abdulƙadir tare da ƙoƙarin ganin ta aure shi.


Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Altaaf Tafida ya daɗe da yin aure amma har yanzu bai samu haihuwa ba, gashi kuma Allah ya jarabce shi da son yara. Kwatsam watarana sai ƙaddara ta sa ya ci karo da wasu ‘yan biyu waɗanda ko tantama babu nashi ne, sai dai karɓarsu daidai yake da neman jaki mai ƙaho. Rafiq ya kasa fahimtar dalilin da ya sa ba ya iya tuƙi, alhali kuwa yana iya tuna lokutan da yake tuƙa kansa a mota, tashin hankalinsa ya hauhawa ne ya yin da ya fahimci sabuwar amaryarsa Tasneem ta zo gidan shi ba tare da budurcinta ba. Kafin kuma ya gama ji da wannan, sai ga wani sabon asirin da ka iya rusa komai na rayuwarsa ya fara fitowa fili.


Aminaina Ko Ita? by Rashida Usman

Nafisa, kyakkyawar matashiya mai tashe da ji da kanta, ta ɗana wa ɗaya daga cikin ‘ya’yan Ambasada Ahmad Ɗangiwa mai suna Haidar tarkon soyayyar ƙarya domin ta samu maƙudan kuɗaɗe a wurinsa. Abin da ba ta sani ba shi ne, rikicin da ke kewaye da ahalin su Haidar ya sha gaban tunaninta, domin kuwa akwai waɗanda suka fi ta son kuɗin da take hangen samu, kuma har kisa za su iya yi domin su cimma burinsu.


Bakar Tafiya by Amina Abubakar

Basma, Jafar, Salma, Rabson Guy da Biba sun shirya tsaf domin yin wata doguwar tafiya, sai dai kafin su isa inda suka nufa dole sai sun bi wata shu’umar hanya wadda ta ratsa ta cikin wani baƙin daji da ake yi wa laƙabi da ‘Kai Ka Zo.’ Kowa a cikinsu tana da babban dalilin da ya sa zai yi wannan tafiya. Sai dai tun kafin a yi nisa kowannensu ya fara da na sanin yin tafiyar a lokacin da kwatsam direbansu ya mutu ba tare da sun san dalili ba.


Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Auren Asma’u da Abbas ya kusa, sai dai ko kaɗan ba ta son shi. Hankalinta na kan wani matashin mai kuɗi da ake kira Alhaji Nas, alhali kuwa shi bai san ma tana yi ba. A haka dai aka ɗaura auren ba don tana so ba. Kwaɗayin dukiyar Alhaji Nas da fafutukar ganin ta shiga rayuwar daula suka sa soyayya ta makantar da ita har sai da ta kashe aurenta ta fito domin ta auri Alhaji Nas. Burinta ya cika ta aure shi, sai dai irin halin da ta tsinci kanta a rayuwar zaman gidan ko a mafarki ba ta hango wa kanta hakan ba.


Daga Karshe by Khadija S. Moh'd

Fatima budurwa ce ‘yar kimanin shekaru goma sha bakwai. Shiririta, rashin hankali da tsiwa bayyanannu ne daga cikin halayenta. Kowa na ƙorafi da ita game da wannan, domin ko waye mutum za ta iya ɗaga ido ta kalle ka ta faɗa maka duk maganar da ta ga dama. Kafiya, kuwa sai ka ce kuturu. Jamilu ɗan uwan mahaifiyar Fatima ne, kuma shi take so ta aura, Mustafa kuma malamin Fatima ne na Islamiyya. Jamilu ya daɗe yana son Fatima amma bai faɗa wa kowa ba, ita kuma ta ce wa Mustafa ya turo manyan gidansu neman aurenta.


Gidan Gado by Zainab Muhammad

Kakan su Habiba ya mutu ya bar wa mahaifiyarsu wani makeken gida, sai dai ɗan uwansa Malam Umaru ya yi kane-kane akan wannan gida ya ƙi bari a raba a ba wa kowa haƙƙin shi. Duk wanda ya taso da maganar ma sai ya yi mishi barazanar ganin bayan shi. Magada dai sun sha alwashin ƙwato haƙƙinsu, shi kuma Malam Umar da matarsa Saude sun sha alwashin tauye wannan haƙƙi ta kowane hali.


Hakabiyya by Asma'u Abdallah Ibrahim

Yayin da fafutukar nemawa mijinta magani ya kai Zawwa zuwa ga tone kabarin wata budurwa mai ciki, hakan ya zamo matakin farko na cukurkuɗewar rayuwar Haƙabiyya tun kafin ta fito duniya. Hameedu, wanda ya canza sunan shi zuwa Huzaif yana ɗauke shi ma da wani ɓoyayyen sirri wanda ka iya fayyace komai ko ruguza komsi. Makirci ya haɗu da makirci, tsafi ya haɗu da mugunta, sirri ya ci karo da sirri, shin ko gaskiya ita kuma za ta yi halinta daga ƙarshe?


Malam Jatau by Haiman Raees

Rikita-rikitar Malam Jatau da rashin kan gadonsa na nema ya fi ƙarfin shi. Ga matansa su ma sun sako shi a gaba. Ko wa ya faɗa mishi mutum na iya yin faɗa ruwan sama? Ya gwada yin hakan kuma bai ji da daɗi ba.


Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Hajiya Beeba ta asirce Auwal domin ganin ta mallake shi ko ta halin ƙaƙa. A sanadiyar wannan asiri ne har ta raba shi da matarsa ta farko, kula da su ya dawo hannun Dawud duk da ƙarancin shekarunsa. Tashin hankali ya yi wa Labeeb yawa, abubuwa sun cukurkuɗe mishi. Dukkan ‘yan gidansu sun canza mishi. Ga Dawud na fushi da shi saboda cikin da ke jikin Zulfa, ga yaro an kawo mai da bai san daga inda ya fito ba, ga matarsa na neman rabuwa da shi, babban abokin shi ba sa ko magana, kwatsam kuma sai ƙaramin ƙanin shi ya mutu.


Tambaya by Haiman Raees

Kundi ne na rubutattun waƙoƙin hikima da jawo hankali waɗanda duk wanda ya karanta su zai fara sabbin tunane-tunane dangane da al’amuran yau da kullum da ma rayuwa baki ɗaya. Wane ne ni? Yaushe zan yi kaza? A ina ake kaza? Me ya sa abu kaza ke faruwa da dai makamantan waɗannan tambayoyi duk za su zowa wanda ya karanta su.


Voice of Love by Haiman Raees

Love is a living, breathing entity by itself. It is adorable to feel, but seldom to hear. These voices of love are yearning to be heard, so let’s hear them through this collection of poems.


Yes She Is by Fatima Abubakar Saje

A mother’s love is irreplaceable, her beauty is unimaginable and her heart is beyond this world.