Skip to content
Part 7 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Ita da ma dai Yusuf ɗin ne Ziyada ta ce tana so. Wallahi a guje za ta bashi aurenta. Ba tun yanzu ba take matuƙar yabawa da halayen yaron, yana da kaifin hankali da hangen nesa. A unguwarsu yaron ya samu kyakkyawar shaida, lamuransa na aiki da hankali har sun zarce shekarunsa.

Amma Khamis, inaaaa.. Baza ta cusa kanta a cikin lamarin da tun farko bata yi mishi hangen zai haifar da ɗa mai idanuwa ba. Lumshe idanu tayi a hankali tana tunanin ta inda za ta ɓullo ma Ziyada su warware al’amarin lafiya ba tare da tashin tashina ko tashin hankali ba.

Aunty Rukayya da tafi kowa zafi cikin ƴaƴan ita ce ta taso daga mazauninta a fusace. Tun ɗazu irin rainin da Ziyada take yi da yadda take mayar da magana harshe a tsattsaye ba rusunawa yake taɓa zuciyarta, ranta a ɓace, hannayenta har wani ƙaiƙayi suke yi wajen son taɓa lafiyar Ziyada.

Kusa da Ummanmu taje ta tsaya ta fara magana a zafafe.
“Ummanmu ki daina biye ma wannan yarinyar mai kunnen ƙashi fa. Ziyadan da kika sani da ba ita bace yanzu. Wancan yarinyar taki mai sanyi hali, kunya, yin abinda aka umarceta ko da zuciyarta ba ta so ba ita bace yanzu, wannan wata sabuwar fitsararriyar Ziyada ce Khamis ya canzo mana.

Ki ƙyale mu da ita, karen bana shi ke maganin zomon bana. Ki kawar da kanki ko na wasu ƴan mintuna ne don girman Allah. Za mu dakata ta nuna luguf, ta yadda ko cewa aka yi ta kalli ɗan iskan yaronnan da ke kallon mata yana wani lumshe idanu baza ta iya kallonshi ba.”

Ummanmu dai ta kasa cewa komai, sai bin ƴaƴan nata da idanu take yi ɗaya bayan ɗaya zuciyarta cike da tunanin hanyar ɓullewa.

Aunty Karimatu da take da sanyin hali a tausashe ta kalli Ziyada ta ce
“Auta kin kuwa san a unguwarnan ba ke kaɗai bace budurwar Khamis? Ke me ya kaiki yin sake har zuciyarki ta kamu da son wannan mayaudarin yaron? Aishan gidan Baduku budurwarsa ce, Bintan Inna mai koko budurwarsa ce, Aliya Tanimu budurwarsa ce, Habiba…”

“Aunty Karima duk fa waɗannan da kika lissafo tsofaffin ƴanmatansa ne. Kuma su suka fara nuna mishi suna son shi, gudun wulaƙantasu da gudun mayar da martanin soyayya da ƙiyayya yasa shi fara kula su sama-sama. Daga baya kuma ya rabu da su tunda dama ba son su yake yi ba, kin ga kuwa baza’a ce ya yaudare su ba.

A yanzu kam Wallahi tallahi ni kaɗai yake so kuma yake niyyar aure. Idan kuma baki yarda ba kije ki tambayeshi ko ki tambayi ƴanmatan idan har yanzu yana tare da su.

Ke kuma Aunty Rukayya gaskiya kar ki ƙara ce mishi ɗan iska, ehe!. Da baki kalle shi ba ta ina za ki san yana kallon mata har za ki wani ƙara mishi da sharrin yana lumshe idanu…”

Saukar wasu zafafan maruka a kuncinta hagu da dama yasa wuta ya ɗauke mata na wucin gadi ba tare da kammala maganar da take yi ba.
Ɗif tayi, bakinnan gum, ta ƙura ma guri ɗaya idanu kamar mai karanta wani abu.

Amma a zahirin gaskiya abinda take gani kawai suna gilmawa a cikin kallonta wasu ƙananun taurari ne masu tsananin haske da sheƙi. Wani azababben zafi da raɗaɗi ke ratsa kumatukanta daga ko wane ɓangare har gefen kunnuwanta.

Ta ɗauki daƙiƙu a cikin wannan yanayin, sai kuma ta dawo cikin hayyacinta ta hanyar ƙwalla wani gigitaccen ihu mai barazanar fasa dodon kunne. Nan ƙasan kafet ɗin da ya malale ko ina na cikin falon ta zube tana tumami da birgima kamar wacce aka kawo ma saƙon rasuwar iyayenta ba tare da sunyi jinya ba.

Wannan ihun kuka da ta saka shi ne abinda ya tunzura zuciyar Ummanmu. Ya ƙara fusata Aunty Rukayya da Aunty Karima da suka sauke mata tagwayen maruka. Umarni Ummanmu tayi musu kan su wujijjiga mata Ziyadar ko za ta san lallai Baba ma da Babansa.

Masu nema a duhu balle sun samu a sarari. Dorina mai baki bibiyu da Ummanmu take ajiye da su tun suna ƙanana suka kwaso a guje. Ziyada da ta saki jiki a ƙasa tana burgima da ihu har da na taɓara bata san hawa ba balle sauka sai fara jin saukar ruwan bulalu tayi a jikinta.

Habawa! Daga ihun wasa ba sai ga shi tana na gaske ba. A haukace ta miƙe tsaye ta ruga da gudu za ta rungume Ummanmu don samun tsira da saurin gaske Rukayya ta riƙo ta. Ta cigaba da zabga mata dorina Karima tana taya ta.

“Na tuba bazan ƙara ba. Wayyo Allah na.. Don girman Allah kuyi min rai. Me nayi muku za ku kashe ni? Duk wannan dukan mutuwan kan Khamis ne? Na haƙura da shi. Wallahi na daina son shi. Daman shi ne ya ce min idan banyi muku hauka-hauka ba baza ku bari ya aure ni ba. Don Allah kuyi haƙuri…”
Ire-iren maganganun da ke fita a bakinta kenan cikin matsanancin kuka da gunji mai tsananin ƙarfi.

Ta ko ina yayyin sunyi mata ƙofar rago. Sun hana ta samun matsera ko ƙanƙani. Duk da waɗannan kalamai na ban haƙuri da take furtawa da irin alƙawurran da tayi ta ɗauka kan baza ta sake kula Khamis ba basu ƙyaleta ba sai da suka yi mata lilis. Izuwa lokacin ta daina ihu sai gurnani kawai take iya yi, nan tsakar falon suka watsar da ita a wulaƙance suka shige ɗakinsu.

Ummanmu ƙofar falon ta kulle ta ciki ta zare makullin sannan ta shige ɗaki don gabatar da sallar la’asar. Babu ko ɗigon tausayin Ziyadar ta tsallaketa ta wuce ciki, tana ganin yadda wasu sassan jikin Autar nata suka faffashe da sashin dorina amma ko kallonta bata yi ba.

Sai da ta gama gunjin da take yi da gurnani ta rarrafa a wahalce kuma a tsorace zuwa cikin ɗakinsu. Fitsari ne cike dam da mararta, in banda haka babu abinda zai shigar da ita cikin ɗakin balle har yayyinta su ƙara akan dukan da suka yi mata. A gaban Ummanmu sunyi mata irin wannan duka na kawo wuƙa ina ga a bayan idanunta?.

Babban ɗaki ne wadatacce da ya ɗauke gadajen kwanciyarsu madaidaita guda uku. Sai ƙaton durowar zuba kaya ko wacce da ɓangaren kayan sakawarta. Da ƙaton madubi a tsaye mai ɗauke da ƴan ƙanunu durowa a jikinsa.

A ɗarare ta ɗan leƙa kanta cikin ɗakin, sai ta hangi yayyin nata suna sallah. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Ta runtse idanu wasu zafafan ƙwallah suka sake silalo daga cikin idanuwanta.

Ta rarrafa da sauri duk da yadda take jin gaɓɓanta na amsawa da azaba. Babban burinta ta shige ta rage nauyin mararta ta fice daga ɗakin kafin su idar da sallar su ƙara yi mata wani dukan.

Shaƙuwa da ƙauna mai girma ke tsakaninta da ƴan’uwanta. Da wayanta dai baza ta iya tuna wata rana da Ummanmu ko yayyinta suka mare ta ba, balle har a kai ga irin wannan dukan kamar sun samu jaka.

A kullum tattalinta suke yi suna yi mata abinda take so. Ita ce ƙaramarsu, mafi rauni a cikinsu. Da wannan dalilin yasa sai dai idan bata furta tana son wani abu dangin ci, sha, sutura ba. Matuƙar ba ya fi ƙarfinsu bane ko ba a wannan lokacin ba sai sun mallaka mata abinda ta ce tana so.

A yanzu kam wani gagarumin tsoronsu ne ya cika zuciyarta. Wani sashen na zuciyarta ma har ta fara tantamar anya kuwa daman ƙaunar da suke gwada mata a baya ba na bogi bane?

“Auta”
Ta ji muryar Aunty Karima ta kira ta a tausashe, a lokacin da take gaf da ficewa daga cikin ɗakin.

A tsorace ta tsaya a inda take, ko kafin ta waiwaya ta fuskanci mai kiran har idanunta sun tara ruwan hawaye.
“Ku… ku… kuyi haƙuri… Fitsari ne ya shigo da ni ba wani abu ba. Don Allah kuyi haƙuri..”
Ta ƙarasa maganar a raunane haɗe da saukar hawayen cikin idanunta.

“Zo nan”
Rukayya ta kira ta da ɗan zafi-zafi a muryarta.

Kallon cikin idanun Aunty Rukayyar tayi, ganin ba wasa kuma babu wani sassauci yasa ta janyo ƙafafunta a sanyaye tana hawaye ta rarrafa zuwa gabansu.

Wani abu da yasa ta kusa sakin ihu shi ne yadda yayyin suka yi a tara a tara gurin ɗaukarta cak kamar ƴar jinjira zuwa banɗaki. Cikin kulawa da nuna ƙauna suka ajiyeta kan abin zama.

Ruwa mai zafi suka haɗa suka gargasa mata jiki. Alwala suka umarceta da yi sannan suka sake ɗaukarta zuwa cikin ɗakinsu. Kan katifarta suka zaunar da ita.

Aunty Rukayya tana mutsuka mata man zafi a sassan jikinta. Aunty Karima ta buɗe gurin kayanta ta ɗauko mata sassauƙan doguwar riga da hula aka saka mata.

Sallaya suka shimfiɗa mata sannan suka umarceta da yin sallah a zaune. Babu wata magana a tsakaninsu ukun, amma irin yadda suka tarairayeta da nuna mata kulawa shi ne abinda yasa ƙwalla kasa tsayuwa a idanunta. Akai-akai take kai babbar yatsarta tana ɗauke hawayen, suna kallonta. Cikin su biyun babu wacce ta tambayeta kukan me take yi.

Kafin ta idar da sallah har sun haɗo mata tea mai kauri cike da kofi. Tana idarwa suka bata tasha sannan suka bata ƙwayoyin paracetamol biyu da pain reliver guda biyu.

“Na gode ƴan’uwana.”
Ta faɗa a raunane tana kallon cikin idanuwansu.

Kawar da fuskokinsu suka yi basu ce komai ba. Cak suka sake ɗaga ta zuwa kan katifarta suka kwantar.
“Kiyi barci, idan kin farka za ki ji sauƙin ciwon jiki.”
Cewar Aunty Karima.

Sun juya za su bar mata gurin da saurin gaske ta riƙo hannayensu ɗai-ɗai.
“Kuyi haƙuri don Allah, ku daina fushi da ni. Bazan sake ba in Allah ya yarda.”
Sai kuma ta saka musu kuka a raunane, har lokacin ta ƙi sake hannayensu.

Haɗa idanu suka yi, sai kuma suka mayar da kallonsu kanta. Fuskokinsu da wani irin yanayi mai wuyar fassara.
“Idan kuka za ki tasa mu gaba kina yi sakar mana hannayenmu.”
Cewar Aunty Rukayya.

Da saurin gaske ta haɗiye kukan, sai sauke ajiyar zuciya da take yi.

Gefen gadon suka zauna kusa da ita.
“Kina so mu daina fushi da ke?”
Suka haɗa baki gurin tambayarta.

Da saurin gaske ta dinga ɗaga musu kai, alamar eh! Wani irin zafi zuciyarta ke mata, duk da mugun dukan da suka yi mata soyayyar Kham na nan danƙare a cikin zuciyarta. Amma irin yadda suka nuna mata ƙauna bayan azabtarwar shi ne abinda ya sanyayar da jikinta. Har ta dinga tunanin irin matsananciyar ƙauna da shaƙuwar da ke tsakaninta da mahaifiyarta da Yayyinta. Da yadda kusan ako wane lokaci suke zaɓan farin cikinta a saman nasu farin cikin. Yadda suke sadaukar da abubuwansu da dama a kanta, in ba akan lamarin soyayyarta da Khamis ba babu wani abu da ta taɓa kawowa kai tsaye suka ce mata bazai yiwu ba.

Sai a lokacin ta gane lallai fa ta tafka kuskure, irin hanyar da ta biyo na aro halaye marasa kyau ta ɗora akan nata kyawawa ba shi zai sa ayi mata abinda take so ba. Sai kuma yadda suke ɗaure mata fuska ya fara taɓa mata zuciya, ko sun barta kwance tabbas baza ta iya barcin ba saboda tunanin matsanancin fushin da Ummanmu da su yayyinta suke yi da ita.

Gara ta nemi afuwarsu tun kafin lokaci ya ƙure mata. In yaso daga baya sai ta sake sabon lale ta hanyar bin su da lalama da tsantsar ladabi da biyayya. Khamis ne dai tana son shi, ko kusa bata hango akwai wani turjewa ko duka ko ɗaukar mummunan mataki a kanta da zai sa ta daina son shi ba.

“Tunanin me kike yi haka?”
Aunty Rukayya ta tambayeta tana kallonta da idanun tuhuma.

Ƙwal-ƙwal tayi da idanunta sannan ta buɗe baki da ƙyar ta ce
“Ba komai! Don Allah ku daina fushi da ni.”

“Za mu daina fushi da ke. Amma sai kinyi mana alƙawarin daga yau babu ke babu Khamis. Baza ki sake shiga harkarsa ba, ko a hanya ya tare ki baza ki taɓa nuna kin san shi ba balle har ki saurari ƙarerayinsa da kalamansa na yaudara. A gidannan kuma baza ki sake tayar mana da maganarsa ba. Kuma za ki kwantar da hankalinki ki cigaba da harkokin rayuwarki da karatunki cikin walwala da kwanciyar hankali kamar babu wani abu da ya taɓa faruwa.”

“Na yi muku alƙawari. In Allah ya yarda duk abinda kuka ce zan kiyaye.”
Ta amsa kai tsaye. Aka ce wanda ya faɗa ruwa ko takobi aka miƙa masa zai kama. Yafiyarsu take nema, don haka za ta amince da duk abinda suka ce ba tare da ko kaɗan a zuciyarta tana jin za ta aikata ba.

Jin da suka yi ta amince cikin farin ciki suka rungumeta. Nan take fuskarsu ta faɗaɗa da matsananciyar fara’a. Kama ta suka yi zuwa ɗakin Ummanmu don su taya ta bata haƙuri kan irin ɓacin ran da tayi ta saka ta tun daga ɓullowar zancen Khamis ɗin har zuwa yanzu.

Malam bahaushe ya ce kaza tana taka ɗanta ba don ba ta son shi bane. Ummanmu bata ja da nisa ba itama ta yafe ma Ziyada. Nan kan gadon Ummanmu suka kwantar da ita, su ukun suna zaune a gefenta cikin hikima da salo na balagar iya magana suna nunar mata irin matakan da za ta bi a sauƙaƙe wajen yin fatali da Khamis da guntuwar soyayyarsa daga zuciyarta.

Da bakinta ta faɗi shi yake zugata, da wannan dalilin yasa suka yi ta jaddada mata kar ta kuskura ta sake saurarenshi balle har zantukansa suyi tasiri a kanta.

Wanda yayi nisa ba ya jin kira, mai rabon shan duka ko ana muzuru ana shaho sai ya sha. Duk maganganun da suke yi ga Ziyada dai kamar tatsuniya suke karanta mata. Maganganun suna shiga ta kunnen su fice ta kunnen hagu, ko kaɗan bata ji a zuciyarta ta gamsu da maganganun ba balle har ta samu ƙwarin gwuiwar aikatawa. Daga bisani ma dai da ta gaji da saurarensu lumshe idanu tayi ta fara barcin ƙarya.

A dole suka ƙyale ta. Suka fice daga ɗakin, Ummanmu ta ja ƙofar a hankali don kar ƙaran ƙofar ya tashe ta. A hanlali ta buɗe idanunta, ganin babu kowa a ɗakin sai ta saki murmushi, a hankali ta ɗaga hannunta na dama ta ɗora a saitin zuciyarta. Ko rantsuwa tayi babu kaffara, ta tabbata duk bugu ɗaya na zuciyar tana fita ne da sautin sunan Khamis, ta ina za ta iya rabuwa da wanda zuciyarta ke bugawa dominsa?

Bata fara son Khamis don ta daina ba. Amma ya zama dole daga ita har shi su canza salon takunsu. Matakai ɗaya bayan ɗaya har matakai goma ya shirya musu, matakan da za su taka don cimma burinsu na auren juna.

Tunda mataki na ɗaya da na biyu basu yi aiki ba. Lokaci yayi da za su tsallaka mataki na uku, matakin da ta tabbatar zai jijjiga zukata da yawa, matakin da bayan aukuwarsa ba ta jin akwai wani shamaki da ya isa ya hana iyayensu ɗaura musu aure a gaggauce.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 6Lokaci 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.