Skip to content
Part 5 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Minti ɗaya biyu uwar da ƴaƴan suke haɗa baki gurin cewa, fuskokinsu ɗauke da zallar tausayi da ƙaunarsa.

“Sannu Daddy. Allah ya yaye maka, muna roƙon Ubangiji ya baka lafiya da gaugawa.”

A sannu cikin kulawa da tarairaya suka ɗaga shi a hankali cikin lallaɓawa kamar wani ƙwai, cikin ɗaki suka shigar da shi.

Kan kujera mazaunin mutum uku suka kwantar da shi, Khamis an samu abinda ake so, sai ƙara narkewa yake yi yana langwaɓewa.

Cikin zafin nama Mummy ta surka ruwa mai zafi-zafi ta kai banɗaki.

Ta taimaka mishi yayi wanka, ta gargasa mishi jiki sosai yana ta  wash-wash, waiyo Allah, Ziya kiyi a hankali, har dai aka gama daƙyar saboda ƙorafinsa.

Da kulawa ta tallabe shi zuwa cikin ɗaki, bayan ta goge mishi jiki kamar ɗab jariri man zafin da ba ta rabo da shi ta ɗauko ta mulke mishi jiki. 

Ta ɗauko mishi kaya masu sauƙin nauyi ta taimaka mishi ya saka. Babu ɓata lokaci yabi lafiyar gado yana sauke ajiyar zuciya, ba tare da damuwar bashin sallolin da suke kanshi ko kuma tunanin rama sallolin ba.

Ko da ya nemi ina take bayan wasu mintuna da fitarta a cikin ɗakin Munauwa ce ta faɗa masa Mummy ta tafi Chemis ɗin Uncle Jamilu.

Wayarsa ya ba ta umarnin ɗauko masa a aljihun rigar da ya cire.

Tun sa’adda ya gama kiraye-kirayen Yayanshi jami’an tsaro suka kashe wayar. 

Tunanin kira masu yawa da ya rasa a dalilin wannan kashe wayar ya saka shi jan tsaki. Kamar yana ganin ƴan sandan a fili da ɓacin rai a muryarsa ya ce,

“Ƴan’iska kawai! Allah ya isa tsakanina da ku”

Minti uku da kunna wayar kira ya shigo mishi, fuskar waya ya ɗaga ya duba.

“Ƴar madara”

Shi ne sunan wacce take kiranshi.

Wani lallausan murmushi ya saki, lokaci ɗaya ya ji matsanancin ƙuncin da ke danƙare a zuciyarsa ya ragu kashi saba’in bisa ɗari.

Kafin ya ɗaga wayar sai da ya janyo bargo ya lulluɓa har kansa, ya ƙara yin luf akan gadon, sannan ya amsa kiran haɗe da kara wayar a kunnensa.

“Lolly…”

Kalmar da aka fara faɗa kenan daga can ɓangaren, da wata irin sassanyar murya mai  tsayawa a zuciyar mai sauraren mamallakiyarta.

“Ƴar madarata…”

Kafin ya aje numfashin maganarsa ta sakar mishi kuka mai bayyana zallar taɓara da shagwaɓa.

Sosai ya ƙara sakin jikinsa akan gadon. Yana riƙe da wayar yake jin yadda duk wata gaɓa da take jikinsa tana amsawa.

Baiyi gaugawar katse ta ba, domin a cikin kukan kissar ba ƙaramin madarar shauƙi yake kwankwaɗa ba.

Sai da ta ɗauki wasu daƙiƙu masu ɗan dama tana kokawa sannan ya fara rarrashinta da wasu irin tausasan kalamai.

“Ya isa ƴar madarata, Ummm? Babyna abar alfahari na. Zinariyar yarinya kyakkyawa mallakin Khamis shi kaɗai ƙwallin ƙwal! Kin san dai ina bala’i da masifar son ki ko?”

“Eh..”

Ta amsa a lalace.

“To kiyi haƙuri, ki daina kuka, na ɗan shiga cikin wani ƙaramin matsala ne yau ɗin shi yasa baki ji ni ba…”

“Matsala Lolly? Wace irin matsala? A duniyar nan wace irin matsala ta isa fuskantarka bayan da ni a tare da kai? Matsalar ta kuɗi ce?”

“Eh Madarata”

Ya amsa a raunane, ɓacin ran baro motarsa da makullinta acan hannunsu ya sake dawo masa sabo a cikin zuciyarsa. Kamar a lokacin lamarin yake faruwa.

Kafin ta ce wani abu ya ji alamun an shigo cikin ɗakin. A hankali ya yaye bargon daga kansa, idanu biyu suka haɗa da matarsa, idanunsa sun kaɗa sunyi jajur.

Ba tare da damuwar tsayuwar iyalinsa a gurinba ya sake jan bargon ya lulluɓa har kansa. Ya cigaba da amsa wayarsa cikin wani irin salo na soyayya da duk sakarci da rashin wayau na matar da yake aure a dole zuciyarta ta taɓu.

Idanunta ciccike da hawaye take kallonsa tana mirgina kai gefe da gefe, wani malolon dunƙulallen abu ya tokare mata wuya. Shi bai fito ba kuma shi bai koma cikin cikinta ba.Daga bisani da taji wayar ta ƙi ƙarewa ga kuma zuciyarta na daf da bugawa dole taja sanyayan ƙafafuwanta ta fice daga ɗakin, akai-akai take sharar ƙwallah.

Maimakon ta wuce falo gurin baƙon da ta bari a zaune da yara sai ta zame zuwa banɗaki. Famfo ta kunna ruwa ya fara zuba shaaa… Na tsawon minti uku ta ci kuka ta gode Allah, sannan ta kashe famfon.

Ta ɗebi ruwa ta wanke fuskarta sosai kafin ta fice daga cikin bayin. Murmushin yaƙe ta lalubo ta maƙala a fuskarta sannan ta sake komawa cikin ɗakin.

Har lokacin bai daina wayar ba. Izuwa yanzu ma likafa ce ta cigaba, ba kwance yake lulluɓe guri ɗaya akan gadon ba.

Juyi yake yi a hankali daga farkon gado zuwa ƙarshen gado. Da yanayi mai bayyana shauƙi da nishaɗin da yake ciki a fili. Fuskarsa ta gaza ɓoye farin cikin da zuciyarsa take ciki.

‘Naira dubu ɗari biyar Ƴar Madara tayi alƙawarin tura mishi da zarar sun gama waya. Wayarsa ita ce jarinsa na matakin farko, ga dai yadda cikin mintunan da basu wuce goma ba ya samu kuɗin fansar motarsa har da riba akai.”

Zuciyar Mummy ce ta ƙara yin baƙi-ƙirin. Lura da tayi duk juyin da yake yi kamar ma bai san da wanzuwarta a cikin ɗakin ba yasa ranta sake ninkuwa da ɓacin rai.

Yana daga cikin manyan sharuɗɗan da ya gindaya musu ita da ƴaƴan duk muhimmancin magana ko kuma matsalar da za’a sanar da shi in dai yana waya kar a kuskura a katse shi. Ko ma menene a jira shi ya gama waya a nutse.Haka kawai yau tayi sha’awar karya wannan doka tunda ba ta Allah ko ta Annabi bace.

Da ɗan ƙarfi ta bubbuga durowar jikin gadon.

Da sauri da ɓacin rai ya juyo don ganin a cikin ƴaƴan nasa wace mai rabon shan tsinannen duka a darennan ne take mishi wannan ƙwanƙwasar?

Sai suka haɗa idanu. Irin yadda ya ganta a kumbure ta cika tayi fam tana daf da fashewa yasa shi katse kiran. Harhaɗe giran gabas da yamma yayi don ma kar ta nemi kawo mishi wargi.

“Menene kuma? Wayar ma baza’a barni inyi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba…?”

“Abokinka Habibu mai Khemis, yana zaune tun ɗazu a falo yana jiran fitowarka. Ƙauna da tausayin halin da uban ƴaƴana ke ciki su suka ja min gora wajen yin gaugawar kiranshi.

Ba domin komai ba sai domin ya wanke ciwukan jikinka, ya kuma ba ka magungunan da za su taimaka maka wurin rage zugi da ciwon jiki. 

Ban sani ba ashe ni da ƴaƴana kaɗai muka damu da halin da kake ciki. Kai baka damu ba, ko a jikinka, ka warke har ka cigaba da tsula tsiyatakunka yadda kake so.

Ruwanka ne ka fito ya duba ka. Ruwanka ne kuma ka cigaba da kwanciya kana waya da ƴanmata. Khamis, a matsayinka na mijina, Uban ƴaƴana. Cikin sujadar ƙarshe ta salla ta ba na taɓa gajiyawa gurin yi maka addu’ar Allah ya shirye ka. Idan kuma kai ɗin ba mai shiryuwa bane…”

“Kin yi hauka ne?”

Ya katse ta cikin gigitaccen tsawar da har falonsu ana jiyowa.

Ko kallonsa bata sake yi ba, ta buga mishi tsaki haɗe da ficewa daga cikin ɗakin, saboda ɓacin rai ko gabanta dusu-dusu take gani. A dole ta nemi gurin zama a ƙofar bayi, kan dandaryar tiles. Ta jingina kanta da bango ta lumshe idanunta, zafafan hawaye na ta shatata kamar an buɗe famfo.

Ba shi da zaɓin da ya wuce fitowa a duba lafiyar jikinsa. Hakan ba kowa zai amfana ba sai shi da kansa. Da wannan dalilin yasa shi kiran Ƴar madara, a gaggauce ya gilla mata ƙaryar ta bashi awa ɗaya don Allah, Yayanshi yana kiranshi kan magana mai muhimmanci.

“Kin san tun kwanakin baya nake ta neman yadda zan samu damar tunkararshi da zancen aurenmu. To yanzu kam na samu wannan dama, ki kwantar min da hankalinki, kiyi farin ciki.

A wannan daren in Allah ya yarda zan shigar da zancen aurenmu a gurinsa. Muma dai muyi aurennan don mu ƙara tabbatar da me ake ji idan an shiga daga ciki…”

A tare su biyun suka kwashe da dariya, tayi mishi sallama zuciyarta cike da farin ciki mara ƙiyastuwa.

Da sauri ya nufi falon. Sai ya ga Habib ɗin zaune kan kujera, wayarsa na hannunsa yana ɗan dannawa. Ga ƙaramin faranti nan a gabansa an ajiye pure water guda biyu.

Ƴaƴansa gaba ɗaya suna zaune akan kujera mazaunin mutum uku. Sun takure jikinsu gaba ɗaya, a fuskokinsu kawai za’a fahimci suna cikin damuwa.

Haɗa idanu suka yi da ƴarsa ta biyu Mannira, ya ɗan sakar mata murmushi. A tare yaran suka haɗa baki gurin cewa

“Daddy ya jiki?”

“Da sauƙi Alhamdulillah!”

Ya ƙarasa gurin abokin nasa ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha.

“Na barka kana jira ko? Ayi min afuwa. Wani abu mai muhimmanci ne ya tsayar da ni a cikin ɗakin.”

Ya faɗa cikin dariya da basarwa.

“Ba damuwa! Me ya same ka Kham? Ka ga yadda kusan gaba ɗaya jikinka yayi dameji kuwa?”

Habib ya tambayeshi, fuskarsa na bayyana mamaki da damuwar halin da yaga abokin nasa. Ko da Ziyada taje da kukanta tana faɗa mishi irin halin da Khamis ɗin ke ciki bai yarda ba.

Ya zaci halin mata ne na kururuta ɗan ƙaramin ciwo zuwa babba. Yanzu da ya gani ra’ayil aini sai yaga ai ya ma zarce yadda ta suffanta masa.

“Hmmmm! Kai dai bari aboki. Na shiga cikin wani ɗan ƙaramin hatsari ne.”

Ya amsa tambayar tare da zama a kan kujera, nan kusa da Habib ɗin.

Wani kakkausan kallo ya aika ma yaran. A take da sassarfa manyan suka kama hannun ƙananan zuwa cikin ɗakinsu.

Ba tare da ɓata lokaci ba Habib ya fara aikinsa, wanke ciwukan yake yi ƙwarewa, in da ya kamata a saka bandeji ya saka, in da bai kamata ba kuma ya barshi a buɗe.

Sun ɗauki tsawon mintuna arba’in wajen aikinnan. Zuwa wannan lokacin sau goma sha uku ana kiran Khamis a waya, da lambobin abokan mu’amalarsa mabanbanta.

Magungunan da suka dace ya harhaɗa masa, sukai sallama ya fice daga gidan.

Duk da halin da yake ciki na zugi da jin sabon azaba saboda wanke ciwukan da aka yi, maimakon ya shige ɗaki ya nema ma kansa hutu sai ya fice tsakar gida.

Kafin yayi komai ƙofar gidan yaje ya kulle ya sa sakata. Da ya koma cikin gidan sai ya ɗauki ɗaya daga cikin kujerun roba guda biyu da suke ajiye gefe ya zauna akai.

Wayarsa da take riƙe a hannunsa ya buɗe ya fara duba lambobin da suka kira shi, lambar da ta kira mintuna goma sha biyar da suka wuce.

Wayar tana fara ƙara aka ɗaga daga can ɓangaren.  Da ɗoki da farin ciki a muryar matar da ta ɗaga wayar daga can ɓangaren ta ce,

“Khamis? Yinin yau ina ka shiga ne? tun ɗazu manyan kaya sun sauka…”

“Da gaske kike yi Babbar Aunty?”

Ya tambayeta cikin fara’a sosai, alamun ya ji daɗin labarin da ta bashi.

Tabbatar mishi da abinda ta ce tayi ta hanyar rantsewa da Allah. Ta ƙara da cewa,

“Da ganin yanayin wankan da irin girma da faɗeɗen ajin da suke ja duk cikin ƙannaina babu wanda ya faɗo min arai sai kai. Da gaske irin naku ne, ka gaggauta cikin daren nan ka baza koma ka kamo musu manyan kifaye, ka san ba mu da matsalar isar da Oder ko ƙarfe huɗun dare ne.”

A tare su biyun suka yi dariya. Ya sake gyara zama, zuciyarsa cike da tunanin wane babban kifin zai fara damƙowa cikin manyan kifayen da suke kwance a komarsa?

“Babbar Aunty ba ni minti biyar in haɗa wata waya, za ki ji ni yanzunnan.”

“Za ka iya ƙanina. Ni na san za ka iya. Idan ba kai ɗin ba ai babu wanda ya isa yayi irin wannan al’amarin na sha yanzu magani yanzu.”

Ta faɗa cikin karaɗin murna da yanayi na jinjina mishi. 

Kafin ya ce wani abu ta sake cewa,

“Shi kenan! Yanzu dai in kwantar da hankalina luf kamar tsumma a randa ko? In tsumayi kiran wayarka?”

“Eh babbar Aunty. Kafin in kira ɗin a sake sabunta ma hajojin gyara ciki da waje. A kuma yi musu gwari-gwari wajen ƙara fahimtar da su yadda harkar take tafiya. Idan sun amince da sharaɗin tabbas darajarsu za ta ɗagu, a cikin darennan kaɗai za su ƙara yarda da kalmar nan ta dare ɗaya Allah kanyi bature. Zan haɗa su da manyan kifayen da a cikin darennan kaɗai za su iya ƙwamuso abinda zai ishe su fantamawa har ƙarshen rayuwarsu. 

Ki kuma ƙara tunatar da su, a harkar nan idan aka miƙo wuya babu gudu babu ja da baya. Duk ta inda aka zo ta gaba ko ta baya su bayar da haɗin kai don gudun samun matsala…”

“Don wannan kar ka ji komai. Tun isowarsu bitar da nake ta musu kenan, kuma sun amsa, sun amince ɗari bisa ɗari. Har sun saka hannu a takardar yarjejeniya.”

“Dakyau!!!”

Ko da suka gama magana da wacce ya kira Babbar Aunty bai sake bi ta kan tarin lambobin da suka kira shi bai ɗauka ba.

Ma’adanar lambobinshi ya shiga, a sannu ya dinga bin jerin sunayen da suke gurin har yazo kan wata lamba da ya adanata da suna Babbar Harka 1, babu ɓata lokaci ya danna ma lambar kira.

Zuciyarsa cike da fatan Allah yasa a ɗauka. In dai aka ɗaga tabbas ko nawa ne cinikin zai faɗa, kakarshi ta yanke saƙa a darennan.

Kiran yana daf da tsinkewa aka ɗauka daga can ɓangaren. Wani abin mamaki ko da aka ɗaga wayar shiru aka yi, kuɗin na ta tafiya ba’a ce komai ba.

Da rawar jiki Khamis ya tattaro ɗan ragowar miyaun bakinshi ya haɗiye. Sosai ya ƙara shiga cikin nutsuwarsa, ya zamo gaba-gaba daga kan kujerar kamar zai duƙa a ƙasa, ya buɗe baki da wata irin sanyin murya mai cike da ladabi ya ce,

“Allah yaja kwana Ranka ya daɗe. Akwai manya manyan kaya fa irin wanda kuke buƙata…”

“Hamisu, nan da awa ɗaya a tabbatar guda uku sun isa gidan baƙin arewaci. Za ka ji saƙo, yanzu”

Ƙit aka katse wayar daga can ɓangaren.

“Yes!”

Khamis ya faɗa cikin ihun murna, tare da buga hannunshi da ƙarfi kan hannun kujerar da yake zaune akai.

“Ahhhhhh! ya faɗa da ƙarfi yana runtse idanu, saboda zafin fama ciwon da yaji ya ratsa mishi har tsakiyar ƙwaƙwalwarsa.

A can cikin ɗakin yara a zabure Munauwara ta taso da sauri za ta fito gurin Daddy saboda jin ihunsa da tayi. A bakin ƙofarsu tayi kiciɓis da Mummy, za ta fito ita kuma za ta shiga cikin ɗakin.

“Ina za ki?”

Mummy tayi mata tambayar tana tsattsare ta da idanu.

“Mummy, dama zan duba Daddy ne. Na ji yana ihu sai nayi tunanin ko yayi fami a ciwons…”

“Wuce ki tafi ki kwanta!”

Ta katse ta haɗe da daka mata tsawa.

Sum sum ta wuce zuwa cikin ɗakinsu jikinta a sanyaye, ta kwanta kan ƴar madaidaiciyar katifar kwanciyarta.

‘Ko me ya ɓatawa Mummy rai a darennan?’

Tayi tambayar a zuciyarta, fuskarta cike da kakabin mamaki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 4Lokaci 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.