Skip to content
Part 2 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Ko da muka yi sallama ya tafi ni kuma na shiga gida a gaggauce na shige can ƙuryar ɗakina. Na lalubo lambar Malam da tun a waje na adanata na danna mishi kira.

“Assalamu alaikum wa rah-matullahi ta’ala wa barakatuh.”

Malamin yayi sallama daga can ɓangarensa da wata irin murya mai bayyana girma da kwarjinin malunta.

Lokaci ɗaya na ƙara nutsuwa, na gaishe shi a ladabce. Bayan ya amsa gaisuwar a nutse na kora mishi bayanin duk halin da nake ciki.

Ya fahimceni ƙwarai, ya kuma tausaya min. Malamin yayi min ƴan nasihohi kan muhimmancin bin umarnin iyaye, tare da tunasar da ni yana daga cikin rukunan imanin ko wane bawa yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau.

Ya tabbatar min zaiyi istikhara da addu’o’i. Yana fatan duk irin mijin da ya bayyana min da gaugawa zan karɓa hannu bibiyu inyi godiya ga Allah?

Na ce mishi babu matsala in Allah ya yarda.

Ya ce to madallah! Zai neme ni zuwa gobe.

Har zan katse wayar sai ya dakatar da ni da cewa,

“Nana Firdausi ki kwantar da hankalinki. Zanyi addu’a ta musamman kan mahaifinki, bazai ƙara matsanta miki kan ki fitar da miji ba har sai idan ke da kanki ne kika ce mishi ga mijin aure kin fitar.”

Wannan magana ta Malam ba ƙaramin faranta mini rai tayi ba. Godiya nayi mishi sosai, muka rabu zuciyata cike da matsanancin farin ciki.

Tsananin yarda da kalamansa har sai nake ga kamar na ma gama da babin wannan matsala.

Washe gari bai kira ni ba sai ƙarfe goma na dare. Bayan na gaishe shi abinda ya fara ce min shi ne.

“Firdausi lamarinki kina buƙatar kiyi amfani da magunguna. Za ki turo da dubu talatin yanzu ko gobe da safe, zuwa yamma saƙonninki za su isko ki har ƙofar gida.”

Bayan ya katse wayar ko minti ɗaya ba’a yi ba ya turo min akawun ɗin da zan saka kuɗin. A wannan dare kusan kwana nayi ina tufka da warwarar yadda zan sami dubu talatin da gaggawa.

A ƙarshe dai wani tsohon zoben gwal na Mamana na ɗauke ba tare da saninta ba. Na ba wani yaro a maƙwaftanmu yakai kasuwa ya siyar dubu hamsin da biyar. Na tura ma Malam dubu talatin ɗin.

Gaf da magriba sai ga wata baƙuwar lamba ta kira ni tana tambayata kwatancen gidanmu, wai an kawo min saƙo daga kano.

Ko da saƙo ya iske ni saboda mamaki haka na zubawa ƙullin garin maganin idanu da kuma wani ruwa mai kama da na rubutu a cikin galan.

“Yanzu ƴan waɗannan kayayyakin su ne dubu talatin?”

Nayi maganar a fili hannuna dafe da haɓa.

Kamar Malam yasan saƙo ya iske ni ga kuma irin tunanin da nake yi sai ga kiranshi cikin wayata.

“Nana Firdausi?”

Ya kira ni da wata irin murya mai bayyana duk abinda zai faɗa mai muhimmanci ne.

Nutsuwata na ƙara tattarawa guri ɗaya ina sauraren abinda zai ce bayan na amsa kiran da yayi min.

Tambayata yayi,

“A duniya bayan mahaifinki da ƴan’uwanki maza wa kika yarda da shi ɗari bisa ɗari?”

“Mahaifiyata.”

Na amsa kai tsaye.

“Ba a cikin mata ba, a cikin maza nake nufi.”

Daƙiƙu talatin na ɗauka cikin tunani sannan na amsa da

“Khamis ne, wani abokina…”

“Madallah! Wannan ƙullin garin maganin ki juye shi gaba ɗaya cikin galan ɗin nan! Ki girgiza ya haɗe sosai, gobe da yamma ki kira shi Khamis ɗin ki roƙe shi yayi miki wanka da ruwan rubutun…”

“Wanka kuma Malam? Khamis ɗin fa ba ɗan’uwana bane.”

Na katse shi ina zazzare idanu a tsorace, mamaki kamar zai kifar da ni a zaune.

“Ko me kika haɗa da shi mu ba damuwarmu bane. Ki roƙe shi yayi miki wanka da maganin, idan ya miki haka ina tabbatar miki miji ne zai fito miki da gaggawa, kuma miji ɗan gaske kece raini.

A istikharan da nayi an nuna min gaba na rayuwarki yana da haske sosai. Amma tsanin da za ki taka domin cimma wannan haske shi ne wankan maganin da shi Khamis zaiyi miki.

Nana Firdausi ruwanki ne ki bi umarninmu gurin amfani da magani kiga haske da cigaban da baki taɓa tsammani ba. Ruwanki ne kuma ki saka kunya ko jin tsoro ki ƙi amfani da magani kina ji kina gani damar da muka hango miki ta suɓuce daga hannunki.”

Ƙit ya katse wayarsa, ba tare da jiran ko zan sake cewa wani abu ba.

A wannan lokacin na shiga wani irin ruɗani da firgici da ban taɓa shiga ba a rayuwata. Kaso sittin na zuciyata na tunzura ni inyi aiki da maganin, na san Khamis bazai ƙi min wankan magani ba.

Kaso arba’in na zuciyata na hana ni, tana ta tunasar da ni Khamis fa ba muharramina bane. Ban haɗa komai da shi ba, yau ko da ɗan’uwana ne da muka fito ciki ɗaya yadda nake balagaggiyar budurwa yana balagagge bai kamata in tuɓe a gabanshi yayi min wanka ba.

Nan take shaiɗaniyar zuciyata ta tunasar da ni irin haske da cigaban da malam yace zan samu. Tana ƙara tabbatar min aikin Malam fa yana ci, ga Abbana tun shekaran jiya idan na gaishe shi da fara’a sosai yake amsawa.

Kuma ba ya ko tuna min batun fito da miji, saɓanin farko da yayi min maganar, kullum idan na gaishe shi zai tuna min saura kwana kaza fa lokacin da ya ɗibar min ya cika, in fito da wanda nake so ko kuma shi ya zaɓa min cikin waɗanda suke biyowa ta hannunshi.

Shirun da yayi min alamu ne na addu’ar Malam ta ci kan Abbana.

A ƙarshe dai haka na ɗaga waya na kira Khamis, da mamaki ina kakabin al’amarin na sanar da shi yadda muka rabu da Malam.

Da yake shaiɗani ne a siffar mutane buɗar bakinsa sai cewa yayi

“To miye a cikin ɗan wannan abin? Kin san na damu da lamarinki ko? Kuma ke kinsan kamar ƙanwata haka na ɗauke ki. Kawai ki haɗa maganin yau, gobe ki san ƙaryar da za kiyi a barki ki fita zan zo in ɗauke ki, muje Hotel ayi wankan da gaggawa kawai a wuce wannan gurin.

Ni ma wallahi na zaƙu kiyi aure. Idan Allah yasa kika ɓaro mana babbar harka ai kinga ni ma na samu gurin maƙalewa. Na san babu arzikin da za ki tako ki manta da ni ko Feedy ta?”

Haka ya kalallameni da daɗin baki har na daina wasu-wasi, zuciyata ta tsayu kan inyi amfani da maganin in taka tsanin da zai kai ni ga cigaban rayuwata.”

Firdausi tana kawowa nan a labarin ta ɗago idanunta da suka yi jajur, ta kama gefen ɗan siririn gyalen da ta yafa a kanta ta ɗauke wasu ƙananun ƙwallah a idanunta.

Ta ja shessheƙar numfashi sau biyu a jere, da ɗaci sosai a muryarta ta cigaba da bayar da labarin.

“Washe gari yazo ya ɗauke ni zuwa ɗakin hotel ɗin da ya kama. Yayi min wankan magani, kamar yadda Malam ya umarta.

Amma irin salon da yayi min amfani da shi gurin wankan maganin ya jefa ni a cikin wani yanayi ne da ban taɓa shiga ba, da haɗin kaina, jikina na so zuciyata na jin haushi…

A wannan ranar, a wannan lokacin, daga wankan magani Khamis yayi amfani da wannan dama gurin keta alfarmata…”

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.”

Alhaji Yusuf ya katse ta da salatin jikinsa na tsuma, fuskarsa na bayyana matsanancin tashin hankali. Saboda tsananin firgita da abinda ya ke ji ƙaninsa ya aikata sai da ya miƙe tsaye a zabure.

Khamis kuwa kanshi ya ƙara sunkuyarwa ƙasa cikin matsanancin jin kunyar Yayan nasa. Ya san ya daɗe yana jefa Yayan nasa cikin rikicinsa kala-kala.

 Amma ba’a taɓa fitowa fili an bayyana laifin da ya aikata ɓaro-ɓaro a gaban Yayan kamar wannan lokacin ba.

‘Ina ma ƙasa za ta tsage ya shige don kunya?’

“Uhmmmm”

Firdausi taja nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Ta sake share ƙwallah a karo na biyu.

Cikin sanyin murya ta cigaba da cewa,

“Sai da komai ya kammala hankulanmu suka dawo jikinmu, saboda tsananin ƙwarewa a yaudara irin ta Khamis a tare mu biyun muka fashe da kuka.

Ina furta na shiga uku yana furta ya shiga uku!

Hannayena ya kamo ya dinga gaurawa fuskarsa mari, da farko ƙyale shi nayi saboda matsanancin haushinsa da nake ji.

Amma da naga dukan yayi yawa, shatin yatsuna sun fito kwance ruɗu-ruɗu a kumatunsa sai na fincike hannayena, na zube a ƙasa ina cigaba da rusa kuka.

Nan gaba na yasa gwuiwa a ƙasa yana kuka yana rantse min da girman Allah bai taɓa yi ba, inyi haƙuri, in yafe mishi, tsautsayi ne. In yi mishi duk abinda nake so matuƙar hakan zai sa in huce. Idan kuma na amince shi zai aure ni.

Haka dai yaita amfani da kalamai kala-kala har na sami sauƙin damuwata. Ya taimaka min nayi wanka na tsaftace jikina, shima yayi wanka.

Muka fice daga ɗakin hotel ɗin zuciyata cike da damuwa da da-na sani mai tsananin yawa.

Ko da ya kai ni ƙofar gidanmu haka ya sake ɓata wasu lokutan masu yawa yana rarrashina. Magana ɗaya biyu sai ya share ƙwallah a idanunsa.

Sosai na gamsu da da-na sanin da yake nunawa. Bai bar ƙofar gidanmu ba sai da ya tabbatar na yi dariya, kashi hamsin cikin ɗari na damuwata ya yaye.

Muka rabu da shi kan cewa in je inyi shawara da zuciyata, in dai ina son shi, kuma zan iya aurenshi, ya rantse da girman Allah zai aure ni.

“Ni fa daman Feedy ina tsananin son ki. Amma na san kin fi ƙarfina shi yasa ma tun farko ban taya ba. Yanzu kuwa tunda wannan abu ya faru idan kin bani dama sai in shigo filin dagar yaƙin neman soyayyarki da dukkan ƙarfina.”

Waɗannan kalaman nasa su suka ƙara sanyayar min da zuciya.

Wasa farin girki…”

Sai tayi shiru tana girgiza kai, fuskarta na bayyana zallar yakaici da ɓacin rai, kamar a lokacin abubuwan suke faruwa.

Cikin zakwaɗi da son jin cigaban abinda ya faru Alhaji Yusuf da jami’an tsaron duk suka ƙara zuba mata idanu.

“Muna jin ki, sai aka yi yaya?”

Babba a cikin jami’an ya tambayeta. Domin labarin abinda ya shiga tsakaninsu a dunƙule Khamis ya faɗa kafin zuwan Alhaji Yusuf. Yanzu ne take warware duk abinda ya faru daki-daki.

A karo na barkatai ta ƙara sauke ajiyar zuciya.

“Tun daga wannan lokacin da muka aikata kuskure sau ɗaya, sai kuma na zama kamar wata mai shafaffiyar ƙwaƙwalwa.

Bana ji bana ganin komai a gabana sai Khamis. Zuciyata ta tumbatsa da matsananciyar soyayyarsa da sha’awarsa.

Kwana biyu tsakani wata muguwar sha’awarsa ta taso min, tun ina dannewa ina kawar da kai naji dai abu na ta ƙara haɓɓaka kamar zan mutu don sha’awa.

Ba shiri na lalubo shi a waya, cikin kuka na sanar da shi abin rannan nake so mu maimaita.

A ɓangarensa shi ma kamar mai jira, minti arba’in tsakani ya kira ni ga shi a ƙofar gida. Hotel ɗin da muka aikata kuskuren farko nan muka sake aikata kuskure na biyu.

Sai da komai ya kammala kuma ni da shi kamar ƴan dirama muka sake saka kuka. A wannan karon an rasa mai rarrashin wani. Muka sha kukanmu muka gode Allah, daga bisani muka yi wanka ya mayar da ni gida.

In taƙaice muku zance sai da muka kwashe shekara ɗaya cif a cikin wannan ƙazantaccen hali. Khamis ya mayar da ni kamar wata dadironsa, duk sadda sha’awa ta motsa min ina kiranshi zai taho da gaugawa.

a shima duk sa’adda sha’awata ta motsa mishi ako wane lokaci yana taɓo ni zan amsa kiransa.

Maganar aure tuni tasha ruwa a tsakaninmu, bai sake yi min maganar aure ba nima ban sake tuntuɓarsa ba, rayuwar bariki kawai muke bugawa a tsakaninmu.

Abinda ya fara kawo saɓani tsakanina da shi shi ne, bai kai watanni uku baya ba da Allah ya matsa bakina na faɗama wata ƙawata halin da nake ciki.

Allah ya sani abin yana damuna, ina aikatawa ne kawai amma wallahi tallahi zuciyata ba ta so.

Kuma wani abu da yake ɗaure min kai shi ne yadda idan sha’awar ta motsa min duk faɗin duniya babu wani ɗa namiji da nake so ya mu’amalance ni sai Khamis, wannan abu yana ci min tuwo a ƙwarya.

Ko da na gama zayyane ma ƙawata halin da nake ciki nan take ta ɗauke ni zuwa gurin wani malami can layin bayansu.

Tiryan-tiryan na faɗa mishi matsalata. Abinda wannan malami ya fara ce min shi ne, asiri ne wannan yaro Khamis yayi min. Amma in bashi kwanaki uku ya ƙara bincikawa.

Hankali tashe na ajiye mishi abin sadaka muka bar gurin. Saboda ina so in tabbatar da gaskiyar zance Kwanaki uku na cika ba tare da na tuntuɓi ƙawata ba na koma gurin malamin.

Ai kuwa ya sake tabbatar min da asiri ne a jikina. Kuma Khamis ne yayi min, ya harhaɗa min wasu magunguna ya ce inje inyi amfani da su, in Allah ya yarsa zan sami waraka.

Ko da na fara amfani da maganin na ɗan sami sauƙi ba kamar da ba. Amma fa duk da haka ban dena nemanshi idan abin ya motsa min ba, sai dai ba akai-akai kamar da ba.

Da naga haka sai na ƙara dagewa na fantsama neman magani a gurin malamai mabanbanta, ina kuma cigaba da addu’a.

Wani abin mamaki da ɗaure kai duk inda naje neman magani magana ɗaya ake ƙara tabbatar min, Khamis ne yayi min asirin da bazan iya mu’amala da ko wane namiji ba sai shi kaɗai, kuma duk sa’adda ya neme ni bazan taɓa yi mishi musu ba.

hi daga fara neman maganina zuwa yanzu na kashe kuɗi ya fi dubu ɗari uku. Wancan malamin da ya haɗa ni da shi kuma ko na kira lambarsa sam ba ta shiga.

Wata rana bayan mun gama mu’amala na tayar mishi da ballin cewa na san asiri yayi min, na gaji da wannan wulaƙantacciyar rayuwa da muke yi.

 da gaske yana so na ya fito muyi aure, sai in ƙara tabbata tasa har abada. Idan kuma ba son gaskiya yake min ba to ya karya asirin da yayi min ya fita daga hanyata.

Saboda wannan magana da nayi mishi sai da aka kwashe sati uku bai ƙara amsa kira na ba, bai neme ni ba. Har ciwo nayi na kwanta a asibiti saboda damuwa da sha’awarshi da take taso min.

In yanke muku labarin dai gaba ɗaya yanzu akan wannan gaɓar muke. Da naga ciwon sha’awa na neman kashe ni ne na sanar ma Mamana halin da nake ciki tsawon lokacin nan, ita kuma ta sanar da mahaifina, shi kuma hankali tashe ya kira Yayyena ya faɗa musu abinda yake faruwa.

Da fari su kansu sun so a sulhunta lamarin a gida ne ba tare da an sako hukuma cikin maganar ba. Ya fito a aura masa ni muje can mu ƙarata da iskancinmu.

Amma duk neman da suke ma Khamis ya ma ƙi yarda su haɗu balle har ya saurare su.

Wata rana dai Allah yaba Yayana sa’a ya tarfa shi a Mr. Biggs, yasa aka kama Khamis ɗin aka jefa cikin mota ya taho da shi gidanmu.

Amma saboda taurin kai irin nasa duk yadda Abbana da yayyena suka juya shi ya ce shi baiyi min asiri ba. Kuma wai shi bai san maganar malamin da nake cewa ya bani lambarsa ba. Shi ko kyauta aka bashi ni baya so bazai taɓa aure na ba.

Wannan shi ne abinda ya tunzura su aka kawo case ɗin nan.

Ga shi nan a zaune, wannan shi ne gaskiyar abinda ke tsakanina da shi. Idan nayi maka ƙarya Khamis don Allah ka musanta maganganuna.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.4 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 1Lokaci 3 >>

1 thought on “Lokaci 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.