Skip to content
Part 19 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

“Ahhhhhh! Wayyoh Allah naa!”
Kamar a mafarki Ziyada ta jiyo ihun Khamis a cikin ɗaki.

Tsam tayi guri ɗaya tana saurare, izuwa wannan lokacin hawayen idanunta sun ƙafe ƙaf, sai sauke ajiyar zuciya da take yi lokaci bayan lokaci. Kuka a cikin labarin rayuwarta ba sabon abu bane, baƙin ciki ne da ako wane lokaci ake yi ana sake maimaitawa. In bacin ma ɗan adam da ba ya sabo da mugun abu, ai da tuni ta daɗe da haddace salo-salo samfur-samfur na baƙin cikin da Khamis yake cusa mata ko wane lokaci babu ƙaƙƙautawa…

“Wayyoh… Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un…! Ziyadahhhhhh!”
Aka sake faɗe cikin ihu daga can cikin ɗakinsu da murya mai bayyana lallai fa mamallakin muryar na cikin tashin hankali.

Khamis ne ke ihu, a tsorace ta ɗaga idanu ta kalli agogo, ƙarfe uku da minti goma sha takwas na dare. Har ta miƙe da sassarfa za ta shiga ɗakin don duba halin da yake ciki, sai kuma karaf zuciyarta ta dawo mata da tunanin irin baƙin cikin da ya gama cusa mata bayan gama ɗawainiya da shi da rashin lafiyarsa.

A kasalance ta juya zuwa ɗakin yaranta, tana jinshi yana nishi yana salati yana cigaba da kiran sunanta, amma tayi kunnen uwar shegu, kamar ma bata san yana yi ba.

Mamaki da tsoro ne suka kusa kifar da ita a ƙasa sa’adda ta shiga ɗakin yaran taga fitilarsu a kunne, Munawwara wacce ƙanwarta Khadija saboda rashin iya faɗar sunan ta yanke ‘Mu’ ya zama Nawwara, da Khadija mai sunan Ummanmu wacce ake yiwa inkiya da Mannira suna zaune sun haɗe kai da gwuiwa suna rusa kuka.

Da sauri ta ƙarasa ta dafa kafaɗun su biyun, a wahalce suka ɗaga idanunsu suna kallonta.

“Kkkkkukan me kuke yi? Wace ba ta lafiya a cikinku?”
Ta tambayesu da tsoro ƙarara a fuska da muryarta, bakinta na rawa. Ɗabi’arsu ce idan ɗaya ba ta da lafiya sai su haɗu suyi ta kuka, don haka a tsammaninta yanzu ma haka ne.

“Mum…myyyy?”
Suka haɗa baki gurin kiran sunanta cikin kuka. Kafin ta amsa Nawwara ta cigaba da cewa.
“Daddy na ji shi yana ta ihu yana salati, mutuwa zaiyi? Aishan gidan Alhaji Mudan ta taɓa faɗa min da Babanta zai rasu haka yake ta ihu da salati, Daddy ma rasuwa zaiyi ko?”

Da wani irin sauri cikin rawar jiki ta make bakin yarinyar da ƙarfi. Ƙirjinta babu abinda yake yi sai bugawa fat-fat, bata taɓa tsammanin jin kalmar mutuwa ga Khamis zai ɗaga hankalinta haka ba.
“Nauwara? Wani irin banzan magana mare daɗin ji kike yi haka?”
Ta daka ma ƴar tsawa bayan ta zazzaro mata idanu alamar tsoratarwa.

“Ki-kiyi haƙuri Mummy bazan sake ba.”
Yarinyar ta faɗa a firgice haɗe da ja baya da sauri, bakinta da aka make sai zugi yake mata.

“Kar ki kuskura, kar ki kuskura ki sake irin wannan banzan maganar mai cike da firgitarwa da tashin hankali. Kina ji na?”

A tsorace yarinyar ta ɗaga kai. Jikinsu biyun sai rawa yake yi.

A hankali ta zame zuwa ƙasa ta zauna, idanunta a lumshe, har lokacin gabanta bai daina faɗuwa ba. Ta ɗauki tsawon wasu daƙiƙu a haka kafin ta buɗe idanu ta zuba kan yaran, sai taga har lokacin hawaye suke yi. A kasalance ta ɗaga hannu ta yafito su, kamar abinda suke jira kenan, da sassarfa suka ƙarasa gareta suka rungumeta, cikin raunin zuciya suka sake fashewa da kuka.

Bayansu take shafawa a hankali alamar rarrashi, tun suna kukan da ɗan ƙarfi, a hankali suka dinga rage ƙarfin kukan, har ya koma sai sauke ajiyar zuciya da suke yi akai akai.

“Kuyi haƙuri ƴaƴan albarka. Na sani kuna tsananin ƙaunar Daddy, ba kwa so ya mutu ko?”

Da saurin gaske suka ɗaga mata kai.

“To Daddy bazai mutu yanzu ba in Allah ya yarda, sai can can gaba shekaru masu yawa, idan yaga auren jikokinku. Ai kuna yi masa addu’ar ƙarin lafiya da tsawon kwana mai albarka idan kun yi sallah ko?”

“Eh Mummy, muna yi. Har da ke ma muna yi miki, ba ma so ku rasu ku bar mu yadda Aliyar ajinmu iyayenta suka rasu, kullum-kullum sai ta yi kuka a makaranta, tana faɗa mana…”

“Ya isa haka Nauwara. In Allah ya yarda baza mu mutu da wuri ba.”
Ta faɗa a hankali, zuciyarta cike da tunanika mabanbanta. Mutuwa, mai yankar ƙauna, ba ruwanta da tsufa ko yarinta, ba ruwanta da rauni ko ƙarfin iyaye, ba ruwanta da idan ta ɗauke jigon gida me zai je ya zo a rayuwar wannan ahali, duk sa’adda lokaci yayi kawai zuwa take yi. Sai fatan Allah yasa mu cika da imani.

Ta buɗe baki za ta sake magana sai suka sake jin gurnanin Khamis da ƙarfi, a tsorace ita da ƴaƴan suka kalli juna. Sai kuma suka sake kwaɓe fuska za su saka kuka.

“A’a, a’a! Kun ga, kar muyi haka da ku! Kuka ya ƙare daga yanzu, wanda kukai a baya ya isa. Kun dai san Daddy ba ya da lafiya ko? To jikinsa ne yayi tsami sosai, shi ne fa yake ɗan nishi da salati ku kuma kukayi tsammanin yana cikin wani mawuyacin hali ne. Kuyi haƙuri, sannan don Allah ku kwantar min da hankalinku, kun san dai bazan faɗa muku abinda ba haka ba ko?”

A tare yaran suka gyaɗa kai alamar eh!

“Yauwa ƴaƴan albarka. Yanzu abinda nake so da ku shi ne, ku daure ku shiga banɗaki kuyi tsarki, sai ku ɗauro kyakkyawan alwala. Sallar nafila raka’a bibiyu za kuyi ku roƙi Allah yaba Daddy lafiya, idan kun idar sai kuyi barci. In Allah ya yarda zuwa asubah za ku farka kuga Daddy jikinsa da sauƙi sosai. Kun ji ko?”

“To Mummy, za muyi kamar yadda kika ce.”
Suka amsa a ladabce, a take suka miƙe don cika umarnin da tayi musu.

“Allah yayi muku albarka, ni kuma bari in je gurin Daddy. Idan kun idar da sallah fa ku tabbatar kun kwanta kunyi barci?”

“To Mummy”

Ko da ta fito daga ɗakin yaran, kamar za ta ƙi zuwa gurin Khamis sai wata zuciyar ta taushe ta.
‘Idan fa wani mummunan abu ne yake faruwa da shi? Idan fa mutuwar ce ta kawo mamaya kamar yadda Nauwara tayi hasashe?’
Da yin wannan tunanin yasa ta ƙarasawa da sassarfa zuwa cikin ɗakin.

Kwance yake akan gado ya kifa ciki, sai wani irin numfarfashi yake ja da sauri-sauri kuma mai ƙarfi. Hannunsa biyu na riƙe da ƙirjinsa.

“Kkkk…Khamis? Daddyn Nauwara? Mmmme yake faruwa? Me yake damunka?”
Ta tambayeshi bakinta na rawa. Ko kafin ya amsa mata har ta ƙarasa inda yake kwance ta birkito shi da ƙarfin gaske ya juyo yana kallon sama.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!!! Khamis menene? Me zan gani haka?”
Tayi maganar a tsorace bayan ta ja da baya, ganin wani irin rama da yayi lokaci ɗaya, fuskarsa tayi zuru-zuru. Idanunsa sai buɗewa suke yi suna rufewa, kamar mai shirin mutuwa kamar yadda su Nauwara suke hasashe.

Daƙyar ya iya ɗaga hannunsa ɗaya ya yafito ta zuwa gare shi. Da sauri ta ƙarasa ta zauna a gefen gadon, hannayensa ta riƙo haɗe da tallabo kansa daƙyar ta kwantar da shi kan ƙafafunta.

“Ruwa… ruwa… zan.. sha… rrrrrruwah..”
Ya faɗa daƙyar, a galabaice.

Da saurin gaske ta sauke kanshi daga ƙafafunta ta fice zuwa falo ta ɗauko mishi ruwan gora, saboda sauri ta ma kasa tsayawa ta ɗauko mishi kofi. Tana shiga cikin ɗakin ta buɗe ruwan ta sake tallabo kanshi jikinta ta fara bashi a hankali cikin kulawa da tarairaya.

Lallai tsakanin mata da miji sai Allah, yadda take lallaɓashi kamar ƙaramin yaro, tuni ta manta da ɓacin ran da ya cusa mata. Hankalinta idan yayi dubu ya tashi, gefen hijabin jikinta tasa tana goge mishi bakinshi bayan ya kawar da kanshi daga ruwan.

Tana gogewa tana hawaye, hankalinta a bala’in tashe, a tsorace take da kalmar mutuwar nan da ƴaƴan suka ambata, idan fa suka faɗa a bakin ƴan Ameen?. Idan fa Khamis ya mutu a wannan gaɓar ina za ta saka kanta da waɗannan ƴaƴa? Ya rabb! Lokaci ɗaya ta fara tofe shi da duk wata irin addu’a da ta zo bakinta a lokacin, roƙonta ko ma menene Allah ya yaye mishi da gaggawa, idan ta ɗauki daƙiƙu tana addu’ar sai kuma ta tsaya tana jan shessheƙar kuka.

Shi dai tun da ya lumshe idanu bai buɗe ba, shi kaɗai yasan azabar da yake ji daga gefen haƙarƙarinsa, bayansa, zuwa ƙirjinsa, idan aka ɗan ɗauki daƙiƙu sai ya ɗaga hannayensa biyu ya ɗora akan ƙirjinshi ya ɗan matsa a hankali.

Abinda yasa Ziyada fahimtar nan ke mishi ciwo. Lura da haka da tayi yasa ta ɗora hannayenta a gurin tana danna mishi sannu-sannu. Cikin hukuncin Allah kuma sai taga alamun yana jin daɗin dannawar da take mishi, hatta numfashin da yake yi ya sauya, daga sauri-sauri zuwa a hankali.

“Ziyadah”
Khamis ya kira sunanta can ciki-ciki, bayan ta ɗauki ƴan mintuna tana mishi tausa.

“Na’am! Daddyn Nauwara, sannu, ya jikin?”
Tayi maganganun da yanayin da ke nuna da tana da ikon cire mishi ciwon da ke damunsa tabbas da tayi.

“Da sauƙi. Kiyi haƙuri Ziyada, ki ci gaba da yi min addu’a kin ji? Na san kina haƙuri da munanan halayena, in Allah ya yarda zan daina, wata rana, in sha Allahu. Don Allah kiyi haƙuri, kin ji?”

“Na ji Daddy, Allah yasa haka.”

“Ameen.”

Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na wasu ƴan daƙiƙu, har lokacin bata daina ɗan daddanna mishi ƙirjinshi zuwa gefen cikinshi ba.

“Ɗakko min madara a frig.”
Ya bata umarni.

Cikin daƙiƙu kaɗan taje ta kawo mishi, a wannan karon ta haɗo mishi har da kofi da wuƙan huda madara. Khamis ɗin yana da Ulcer, wacce duk sadda ta tasar mishi sam ba ta yi mishi da wasa, kamar yanzu dai. Har ya fara barci ya ma manta da al’amarin wata Ziyada ciwon ƙirjin ya tasar da shi, sai a lokacin ya tuna ai yinin da yayi a ofishin State CID bai ci abinci ba, ko kafin yayi wani yunƙuri tuni ƙirjinsa ya riƙe, bayan wata ƙaƙƙarfan masokiya ta cake shi daga bayansa zuwa ƙirji. A cikin ƙanƙanin lokaci ya galabaita kafin Allah yasa Ziyada ta kawo mishi ɗauki.

Yana da garin maganin da yake sha da madara aduk sadda ciwon ta motsa mishi irin haka, a yanzu ma bayan fasa madarar da juyewa a cikin kofi maganin Ziyada ta ɗakko mishi ya zuba kamar yadda yake sha, ta sa cokali ta jujjuya mishi ta bashi ya shanye.

Ance magani dace ne, shi dai Khamis ya dace da wannan magani, a cikin daƙiƙu kaɗan duk wani riƙewa, zugi, raɗaɗi da ƙirjinshi ke yi duk ya bari. Kakkauran tea Ziyada ta haɗo mishi yasha sannan ya rungumeta a hankali saboda ciwukan jikinsa suka bi lafiyar gado, duk da a lokacin ƙarfe huɗu da minti arba’in da biyu ne na dare.

Kalaman ban haƙuri da soyayya ya cigaba da raɗa mata a kunnuwanta yana shafa ƙananun kitson da suke kanta, cikin ƙanƙanin lokaci barci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Tsuru yayi yana kallonta, zuciyarsa cike da tunanin irin matakan da suka tat-taka shi da ita har zuwa wannan matakin. Allah ya sani yana tsananin ƙaunar Ziyada, har gobe, duk irin cuɗeɗeniyar da yake yi da mata bai haɗu da wacce ta ture gwamnatin Ziyada a zuciyarsa ba.
“Soyayyarmu daga Allah ce Ziya, ki cigaba da haƙuri da ni har zuwa sa’adda za mu cimma matsaya ni da ke.”
Ya faɗa a fili, da wani kwantaccen murmushi a fuskarsa. Lumshe idanu yayi, a hankali shi ma barcin yayi awon gaba da shi lokacin da Ladanin unguwar ya ƙwalla kiran sallar farko.

*******

“Yaya, na rantse da All…”

“Idan ka ƙarasa rantsuwar nan sai na kwaɗa maka mari Khamis”
Yaya Yusuf ya katse shi cikin wani irin matsanancin fushi da bai taɓa gani a fuskar Yayan nashi ba.
“Ka san Allah? Duk zille-zillenka sai ka kaini gurin Malamin da yayi asirinnan. Wuce mu tafi.”
Ya ƙarasa mishi da umarnin cikin tsawa.

Duk da ya tsorata sosai, amma shi ɗin gwani ne gurin taurin kunne. Don haka a maimakon ya wuce su tafi kamar yadda aka yi mishi umarni, sai kawai ya nemi gurin zama kan kujera ya zauna, ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana kallon kafet ɗin da aka shimfiɗa a tsakiyar falon.

“Khamis? Raini ne ya fara shiga tsakanina da kai ko kuma umarni ne ban isa in yi maka ba?”

“Babu ko ɗaya a cikin biyun Yaya. Don Allah kayi haƙuri.”
Ya amsa a ladabce, har lokacin bai ɗaga idanunshi daga ƙasa ba.

Da fushi sosai a fuskarsa ya buɗe baki zaiyi magana kwatsam ringing ɗin wayarsa ya karaɗe cikin falon. Kamar kumurcin maciji haka ya tsaya shi kaɗai yana huci, idanunsa akan Khamis da yake ji kamar ya janyo shi ya shaƙe shi, ko kuma yayi ta jibgarsa har sai ya faɗa masa inda malamin nan da yayi ma Firdausi asiri yake.

Daƙyar ya iya ɗaga wayar ya duba, mahaifin Firdausi ne yake kiransa. Wani irin rugurgujewa ƙirjinsa yayi ya buga daram! Duk zafin da ya ɗauka lokaci ɗaya jikinsa yayi sanyi kamar an sheƙa masa ruwan sanyi, a lalace yaja ƙafafunsa ya zuwa gurin kujera ya zauna. Yana niyyar ɗaga wayar kiran ya tsinke.

Ajiyar zuciya ya sauke, ya girgiza kai, ya ɗaga idanu ya kalli Khamis, sai kuma yayi ƙwafa, ya cije gefen bakinsa. Duk da hankalinsa a tashe yake da dalilin kiransa da Alhaji Lukhman yayi a wannan safiyar, ba shi da yadda zaiyi ya gujewa yin magana da Alhajin, don haka bai jira an sake kira ba, shi da kanshi ya danna ma lambar kira, ya saka a handsfree ya aje wayar akan kujera.

Abinda ya ci doma baya barin awai. A rayuwarsa bai taɓa sanin Alhaji Lukhman ba sai dalilin Khamis, don haka duk abinda zai sa Alhajin ya kira shi a yanzu dalilin Khamis da ƴarsa ce, shi yasa ya buɗe wayar a fili ba sai ya sha wahalar yi masa bayanin abinda ake ciki ba…

“Assalamu alaikum! Alhaji Yusuf barkanmu da safiya. Ina fatan kun tashi lafiya?”

“Lallllafiya ƙalau Alhaji.”
Ya amsa bakinshi na ɗan rawa-rawa. Allah ya sani a tsorace yake da jin dalilin kiran, shi yasa shi kasa faɗin komai bayan amsa lafiya ƙalau.

Acan ɓangaren Alhaji Lukhman ɗin ma bai jira komai ba sai cewa yayi
“Nace ba? Alhaji Yusuf ya ake ciki ne da maganar karya asirin nan? Ka ga yau kwanaki biyu kenan da muka daddale magana a gaban hukuma. Ga yarinya har yanzu tana cikin matsanancin hali, bazan ɓoye maka ba Alhaji, a kwana biyunnan yarinyar nan kulleta muke yi cikin ɗaki saboda yadda take zambarma tana ƙwacewa za ta taho gurin Hamisu, duk yadda muka kira ƙwararrun likitoci suka duba ta haɗe da rubuta mata magunguna ko kaɗan basu yi mata aiki ba, ya ake ciki???”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 18Lokaci 20 >>

1 thought on “Lokaci 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×