Skip to content

Ma’aurata | Babi Na Biyu

Bookmark

No account yet? Register

<< Previous

Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu’an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar matacce.

Kaɗaa kanta kawai tayi ta miƙe ta nufi ban ɗaki ta ɗauro alwala sannan tayi raka’atainil fajar bayan ta idar tajima asujjada tana addu’a da nemawa mijinta shiriya.

Tana idarwa ta fara karatun ƙur’ani mai girma ganin ankusa atayar da sallah ko motsi baiyi ba yasa ta tashi dan ta tayar dashi.

Duk da kashedin da yayi mata idan yana bacci ba atashinsa hakan bai hanata tashinsa ba.

Buɗe idanunsa yayi cike da bacci ya ce, “ke lafiya?”

Cikin rawar murya ta ce; “uhm um da…ma. lokacin sallah ne naga yayi shine nace ko zaka tashi kar jam’i ya wuce k…

Marin da ya kaimata ne yasa ta haɗiye sauran maganar ba tare da ta shuryawa hakan ba.

Cikin masifa ya ce; “wai Fatima meyasa kika raina ni?”

Idan kika kuskura kika sake tashina bacci Allah sai na lahira ya fiki jin daɗi shasha kawai!”

Daganan ya miƙe fau ya wuce ɗakinsa yabarta zaune awajan tamkar mutum mutumi.

Jin an tayar da jam’i yasa ta miƙewa jiki asanyaye ta bi jam’i.

Da safe bayan ta idar da haɗa abun karin kumallo ta sake gyara gidan ko ina tsab sannan ta yi wanka bayan ta shirya ta ɗauko abincin ta tana ci tana kallon tashar larabawa.

Bata ji motsin fitowarsa ba sai ganinsa tayi tsaye akanta fuskar nan ba annuri.

“Ke kiyi abincin rana da yawa zanyi baƙi.”

Cikin ladabi tace dashi “to ina kwana?”

Bai amsa mata ba yayi hanyar fita falon  da sauri ta ce, “ga abincinka ko na kawoma ɗakin ka?”

“Barshi acan” yayi maganar yana  mai ƙarasa shigewa ɗaki.

Sai wajajen goma ya sake fitowa kai tsaye dani ya wuce ya cika cikinsa sannan ya tashi zai fita ya ƙawala mata kira

“Ke kina ina?” Fatima dake ɗakinta kwance ta fito da sauri kamar zatayi tuntuɓe ta ce, “ga ni.”

“Sakwara nakeso kiyi anjima koma dakan hannu na keso na kimanin mutum goma bana son na na’ura.”

“To Insha Allahu.”

Fita yayi ba tare da ya amsa addu’an da take masa na Allah ya tsare ba.

Koda akayi sallah azahar ta kammala komai sai dai kam tasha wahala dakan sakwara.

Uku dai dai ya shigo tare da ƴan mata uku da samari huɗu dukansu ba mai shiga ta kirki,da kagansu kaga ƴan bariki.

Lokacin da suka shigo Fatima tana ɗaki tana karatun novel a wayarta sam bataji shigowarsu ba sai muryarsa da tajiyo yana kiranta da sunan da ya saba “ke ke kina ina?”

Da rawar jiki ta ajiye wayarta tare dasa hijab har ƙasa ta fito turus tayi ganin waɗanda ke zaune a falon sai wata budurwa da tayi shigar banza kwance ajikin mijinta tasani bata son Fahad amma dole taji ba daɗi tunda mijinta ne.

Tsawa ya daka mata “ke baki da hankali ni zaki zo kiyi mana tsaye aka da Allah wuce ki kawo mana abinci!”

Cikin kirma  tabar wajan kitchen ta nufa tana zubar hawaye tana jin dariyar abokan.

“Man baka da kyau miye dan Allah matsalar yarinyar nan ba laifi tana da kyau da diri sai dai da gani ƴar ƙauye ce.”

Ɗayan yace, “tasa wani hijab kamar matar Liman.”

“Hahahaha Man kace ustaziya kake aure” cewar budurwarsa.

Tsaki yayi kafin ya ce, “ai kawai ku bari Dady ya gama dani ya rasa wacce zai had’ani da ita sai wannan bagidajiyar!”

Share hawayen da ke fuskarta tayi kafin ta ɗauko babban  farantin da ta haɗa abincin da sallama ta shigo falon ta ajiye a gabansa sannan ta koma ta ɗauko abun sha ta kawo har zata   wuce ya daka mata tsawa,

“Ke zo nan!”

Da rawar jiki ta dawo ta sunkuya gabansa. “Ga ni.”

“Ubanwa kika ajiye da zai zuba abincin?”

Cikin kirma ta ce, “Kayi haƙuri bara na zuba.”

Tana buɗawa da sauri Sumeey tace, “Kutt! Waye zai ci wannan?”

“Gaskiya Man bana cin wannan abar kuma yunwa nakeji.”

Sauran ma duk sukace ba zasu ci ba dan ba cimarsu bace, Ali wanda tun shigowarsu tausayin Fatima ya cikashi daganin yanayinta mai sanyi sam bata dace da mutum kamar Fahad ba.

Kallonta yayi cikin tausayi ya ce, “Fatima zubo mun.”

“Toh” ta amsa jiki asanyayi bayan tazuba ta kaimasa Man ya ce, “Gayu me kuke buƙata ta girka maku?”

Wannan ta ce, “Tuwon samu wannan taliya wannan jalof d’in shinkafa.”

“To kinji maza kije ki girka masu kuma karki kuskura ki ɓata mana lokaci.”

Haka ta shiga kitchen tana aiki tana mamakin almubazzaranci irin na Fahad sabida Allah abinci kala huɗu awuni Allah ya kyauta.

Haka ranar ta wuni cikin bautawa Fahad da abokanan sa sai Isha suka bar gidan bayan sun gama jin kaɗi-kaɗinsu sallah kuwa ko sau ɗaya bataji waninsu yayi ba.

Ranar kam jam’i ko ɗaya bata samu ba saboda ƙaran kiɗan da suka sa sai ita kaɗai tayi sallah.

Tana jin fitarsu ta fito falon ko ina kaca kaca abinci kowa gashinan ba awani ci abincin kirki ba dama da hijab ajikinta fitowa tayi tabawa mai gadi abincin tace idan wanda ta kawo masa bai ishe shi ba ya ƙara sauran ya kai makarantar almajiran da ke bayansu.

Ƙarfe bakwai na safe yagama shirinsa zai wuce wajan aikinsa ta shigo ɗakin ba ko sallama, 

“Habib ina so zanje gida.”

“Kije makarantar koyan sallama idan kin koyo mayi magana.”

Yayi maganar batare da ya kalleta ba ya ɗauki jikka laptop ɗinsa zai wuce tayi saurin shan gabansa cikin masifa ta ce,

“Wallahi Habib kana da matsala to naji salamu alaikum.”

Girgiza kai yayi kafin ya amsa da, “Amin alaiki salam.”

“To tunda nayi sallama sai abani amsa kuma ina son kuɗi dubu goma zan biya kasuwa.”

Murmushi yayi aransa yana mamakin halin Ruƙayya wai ta manta abun da tamasa jiya

“Kayi shiru.”

“Bazaki ba, kɗ’i kuma bazan ce babu ba bayarwa ne dai bazanyi ba.”

Daganan yasa kai ya fita yana jinta tana magana cikin ɗaga murya

“kada Allah yasa kabayar ɗin maƙo kawai!”

Haka tabar ɗakinsa zuciyarta na suya.

Ranar kam a office yasa sakatirinsa ya sayo masa abinci ya karya.

Ku saurari baba na uku in shaa Allah.

Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)

Next >>

How much do you like this post?

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found this post interesting...

Follow us on social media to see more!

nv-author-image

Aisha Abdullahi Yabo

Share the post on social media.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.