Skip to content
Part 9 of 10 in the Series Ma'aurata by Aisha Abdullahi Yabo

Tana zuwa ta tura k’ofar ta jita a rufe kwankwasa k’ofar ta shiga yi da k’arfi.

Habib da yake zaune kusa da amarya abokanan sa sai zuba suke da abokanan amarya anata raha. jin bugun k’ofan yayi yawa yasa ya mik’e tsaye yana fad’in, “Bara na duba mai bugun k’ofan dan Allah.” Ya yi maganar yana mai nufar k’ofar.

Yana zuwa yad’an bud’e k’ofar kad’an ganin ta tsaye awajan yasa ya yi saurin fitowa tare da janyo  k’ofar. Cikin murmushi yace, “Ranki ya dad’i afuwan na so na shigo k’ofarki a rufe.”

Harara ta danna masa kafin tace, “Bak’in munafuki, wato tun ba a je ko ina ba zaka fara nunan rashin adalcin ko?”

Rik’e kansa ya yi cikin damuwa yace, “Ya kike so na yi Ruk’ayya? Kin rufe k’ofa. Shin ta ina kike so na biyo?”

“Ohon maka ni bani hanya na wuce.”

Da mamaki yace, “A’ina na tare maki hanyar?”

Komai ba ta ce da shi ba tabi ta gefensa zata wuce ya yi saurin shan gabanta.

“Wai me ma ya kawo ki nan?”

“Meye na sauri duk abunda ya kawuni gani zaka yi idan ka kwantar da hankalinka.” Ta yi maganar tana ya tsinar fuska.

“Kin ga Ruk’ayya bana son neman fitina ki koma zan shigo.”

“Tab fitina ai kafi kowa sonta tunda ka aurowa kanka fitinar.”

“To na ji. Yanzu dai dan Allah da Ma’aiki ki yi hak’uri ki je kin ga bana so ki yada girmanki agabanta da abokanaina.”

“Daga girman har su duk sunci babba b….Kai ina zan iya fad’a wannan zage haka ganin tana neman d’aga masa murya yasa ya d’auketa akafad’a kamar k’aramar yarinya ya yi hanyar d’akinta ihu ta dinga yi masa tana zille-zillen son ta sauko ta kasa ta dinga dukan bayansa tana zunduma masa zagi.

Bai zame da ita ko ina ba sai uwar d’akinta ya ajiye ta kan gado bai ce da ita komai ba ya fita bayan ya ciro key d’in dake jikin k’ofan.

Da sauri ta sauko daga kan gado ta biyo shi da gudu kafin ta zo falon ya rufeta ta waje.

Ta dinga masifa, “D’an iska ashe matsoraci ne kai wallahi daga kai har ita sai kun san kun shiga gonata dukan ku nafi k’arfin ku wallahi sai naga bayanku!” Haka ta dinga sambatu kamar sabuwar hauka.

Habib yana tura k’ofa abokinsa Muhusin yana tsaye alamar fitowa zai yi.

“Kai har ka sa mun fara jin tsoro ko lafiya shiyasa nace bara na zo na duba ka.”

Cikin fara’a yace, “Lafiya k’alau, mu je.”

Suna zuwa addu’a suka yi tare da gabatar masu da kayan sayen baki.

Bayan tafiyar su ya umurce ta da ta yo alwala shikuma ya d’auki leda d’aya daga cikin kayan da suka shigo dasu ya nufi d’akin Ruk’ayya yana bud’ewa ya hangota rakub’e gefen kujera tasa kanta a tsakankanin gwuiwarta tana kuka.

Tausayinta yaji hakan yasa ya ajiye ledar kusa da ita tare da zama ya dafa kafad’anta cikin sanyin murya yace, “Haba Ruk’ayya! Me yasa kike son sawa kanki dani damuwa ne? Na fa fad’amaki ban k’ara auren nan dan bana sonki ba. Kin sani ni ba mazina ci bane bakya iya d’aukar buk’ata ta kinga dole ne na k’ara aure amma ban yi dan na wulak’anta ki ba.”

Cire hannunsa ta yi daga kafad’arsa tana fad’in, “Hum maza kenan halinku kenan. Ban yi aure dan nai maki kaza ko kaza ba haka kuke fad’a, babbak’un munafukai. Ba dai dan ta biya maka buk’ata ba yasa ka aureta, to zan gani d’in!”

Ta wuce shi fau a tunaninsa uwar d’aki zata shiga sai yaga tayi hanyar fita tsakar gidan. Da sauri yabiyo ta sai dai kafin ya k’arasu harta fita d’akin amarya ta fad’a. Maryama da fitowarta kenan daga toleit, taga mutum k’erere akanta. Ta yi mugun tsorata baya ta dinga yi tana kwalawa Habib kira.

“Hubby ina kake ne na shiga uku aljana!”

Shak’u wuyanta Ruk’ayya tayi tana fad’in, “Wuce uku dubu ma shiga zaki yi matuk’ar baki fita harkar mijina ba!”

Habib ne ya shigo d’akin ganin irin shak’ar da taiwa Maryama yasa ya nufeta cikin tsawa yace, “Miye haka Ruk’ayya kin yi hauka ne kasheta zaki yi? Za ki saketa ko sai ranki ya b’ace!”

“Uban hauka na yi, Habib. Sai na kasheta idan yaso nima akashe ni d’in!”

Fizgota ya yi da k’arfi tare da yarfa mata mari. Kallon sa ta yi da idanunta da suka yi jawur, hannunta dafi da kuncinta tace, “Habib ni ka mara saboda wannan bak’ar ballagazar!”

Ta yi maganar tana mai nunin Maryama da ke gefe tana mayar da numfashi tare da shafa wuyanta.

Habib yace “Eh an mare ki d’in wallahi Ruk’ayya ki shiga taitayinki. Ki daina ganin ina lallab’ar ki ki ce zaki mun abunda kikaga dama kuma wallahi maza kibar d’akinnan tun muna shaidar juna!”

“Ai idan kaga na bar nan to wannan mai kalar aljanu ta fita gidannan.” Tayo kan Maryama tana fad’in “Ke dan uwarki maza ki tattara tsumman karanki kibar gidannan tunda bada kud’in ubanki aka ginashi ba!”

Maryama ta kalleta shek’ak’e kafin ta matsa wajan da Habib yake tsaye ta rungumeshi ta bayansa cikin shagwab’a tace, “Oh Hubby, dama a gidanan da masu ciwon hauka. Ai bai kamata abarta a gida ba ya kamata aikaita asibitin masu tab’in hankal…”

Cakumar da Ruk’ayya ta kaimata ne yasa ta had’iye sauran maganar ba tare da ta shiryawa hakanba.

“Ni ce mai ciwon hauka ko! Ai kuwa zaki ga hauka dan ubanki!”

Habib ya d’auketa kamar d’azun ya kaita d’akinta bayan ya ajiyeta yace, “Wallahi abunda kike ba zai haifa maki d’a mai ido ba. Gara ki canza tun lokacin danasani bai zo maki ba.”

“Kaine dai zaka yi da nasanin, bani ba maci amana kawai!”

Key ya jiho mata “Gashi bazan sake rufeki ba ki yi duk abunda kika ga dama. Kuma wallahi kin ji na rantse matuk’ar kika yi gigin sake shiga d’akinta zaki sha mamakina”.

Yana gama fad’a ya ficewarsa ya barta nan tana zazzaga masifa da zage-zage, sai dai batayi gigin binsa ba dan tunda ya rantse tasani komai zai iya yi mata.

Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ma’aurata 8Ma’aurata 10 >>

1 thought on “Ma’aurata 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×