Skip to content
Part 25 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Maganganun Ayya ne suke mishi yawo, kafin ya zare hannun shi daga cikin nata, yana kallon Layla da jin an kira sunan shi ya sakata bude fuskarta, idanuwanta har sun kumbura saboda kukan da takeyi. Tana jin su, bata san kalar tunanin da ya kamata tayi ba, duniyar duka take ji ta hade mata waje daya. Ta rasa da wanne zata fara, tashin hankalin abinda yake faruwa da ita karon kanta, halin da su Mami suke ciki, Abbu da take ganin ba zuciyar shi kawai ta taba ba, harda Martabar shi, ko kuwa Rayyan da take ji suna lakabama laifin da ba nashi ba?

Ko yanzun da yazo yake kallon ta, yake neman amsa a cikin idanuwanta, a hankali take ganin yanda komai yake shirin canzawa a tsakanin su. Duk a cikin abinda yake faruwa shi tafi ji, shi tafi tunani, in zai rike hannunta, ya kasance da ita, hargitsin zai mata sauki, amman tana ganin yanda wasu katangu suke fara ginuwa a tsakanin su, wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata, tana runtsa idanuwanta ta bude su a kan Rayyan. Dan kallon ta yakeyi, wannan karin ta cikin idanuwanta yake son tabbatar da gaskiyar abinda kunnuwan shi suka jiye mishi kafin yasan matsayin kalaman a zuciyar shi, kamar ciki yaji ance tana da shi, kamar ji yayi ana kiran cikin da yake jikinta da nashi.

“Hamma…”

Labbanta suka motsa, muryarta sam bata fito ba, amman shi yajita a cikin kan shi, yaji ta a cikin zuciyar shi inda wani abu yake bubbudewa da ciwo na gaske.

“Rayyan…”

Yaji muryar Ayya da take kallon shi cikin tashin hankali, saboda shirun shi yana nufin abubuwa da dama, shirun shi yana nufin daukar laifin da ake so a makala mishi, bata san lokacin da ta kama hannun shi tana jijjigashi ba.

“Kana da matsala kala-kala tun tasowar ka. Rayyan ka bude bakin ka kace mun ba kayi ba, ka fada kowa yaji wannan matsalar ba taka bace ba.”

Wani abu yake ji tokare da makoshin shi, amman baisan ta yanda zaiyi ya hadiye shi ba, bakin shi ya kafe kamar ya kwana biyu bai sha ruwa ba. Baisan yanda akayi jikin shi baya rawa ba, saboda gabaki daya zuciyar shi jijjiga takeyi tana rarrabuwa sashi-sashi.

“Ciki aka ce… Rayyan ciki. Ciki ake magana a kai ba abu na wasa ba.”

Ayya ta karasa muryarta na karyewa, idanuwanta sun fara cikowa da hawaye saboda tashin hankali. Dan daya fito daga cikinta ba zaiyi wannan barnar ba.

“Rayyan”

Ta kira cike da roko wannan karin, hawayenta na zubowa, kallonta yayi cikin ido, abinda yakan dade baiyi ba, kafin ya kama hannunta da yake damke da nashi ya sauke. Kan Layla ya sake sauke idanuwan shi da suke cike da tarin tambayoyin da baisan ta inda zai fara yi mata su ba, guda daya yake so tayi duk yanda zatayi ta amsa mishi duk da bai furta a fili ba, da dukkan muryar zuciyar shi yake tambayar.

“Ciki gare ki? Cikine a jikin shi?”

Bata san ya akayi ba, amman ta fahimci neman tabbaci Rayyan yakeyi, kai ta dan daga mishi a hankali, wasu hawaye na zubo mata. Hawayen da suka hana ta fara ganin wani yanayi da bata da kalmar fassara shi cikin idanuwan Rayyan din, kafin ya dauke idanuwan shi daga cikin nata. Numfashi yake fitarwa a hankali a hankali saboda yanda yake ji kamar baya shiga inda ya kamata, kamar yau akwai abubuwan da suke cunkushe mishi hanyar shiga da ficen iska. Juyawa yayi da nufin barin wajen ko zai samu maganar ta natsa mishi da kyau, ko zai tattara hankalin shi wajen gane girman da maganar take da shi, karfin da yake tare da maganganun da yake barazana da dan zaman lafiyar daya fara samu a duniyar shi.

“Rayyan…”

Wannan karin muryar Abbu ta tsayar da shi cak, tana kuma saka shi juyowa ya kalli Abbu din ido cikin ido.

“Ka ce baka taba mun amana ta ba, ka bude bakin ka kayi mun Magana.”

Wani numfashi Rayyan yaja a wahalce, bashi bane ba, ko zai taba Layla, ba zai taba zama ta wannan fannin ba. Ko kwayoyi yasha ba zai taba ta haka ba. Saboda tunanin abinda yake faruwa yanzun, saboda yanda mutanen da suka fi komai muhimmanci a rayuwarta ne zasu fara dora ayar tambaya akan ta, kafin mutanen da basu taba bada gudummuwar komai wajen tarbiya, ci, sha da sutturarta ba su fara zagayawa da maganganu kala-kala akanta, akan Martabar gidan su. Shisa bayason mutane, wannan halin shine, ko kadan baya son su. Mutanen da yake so basu da yawa, saboda matsalolin da suke tattare da mutane yawa gare su.

“Bani bane Abbu.”

Ya furta kalaman cikin kan shi, dama ta farko daya samu tsaye a gaban Abbu, yayi magana da shi kamar yanda kowanne da yake magana da mahaifin shi tazo mishi a haggunce. Martabar Layla zata fi karuwa idan suna tunanin cikin jikinta nashi ne, ba za’a fara mata dukan da yaga ana yiwa wata a film din Hausa da Bilal yake kallo wani lokaci ba, kan sai ta fadi uban cikin da yake jikinta. Idan sun karbi abin, tashin hankalin su ya sauka zasuji a bakin Layla, shikam yanzun ba zasuji komai banda shiru ba. Numfashin daya sauke mai nauyine, kafin yakai hannu yana dan murza goshin shi, kan shi kamar zai tarwatse haka yake jin shi.

“Rayyan rokon ka nakeyi…”

Cewar Abbu, kirjin shi zafi yakeyi, zuciyar shi ciwo takeyi har ko ina na jikin shi yana amsawa. Gara ace wani ne a waje, wanda zai iya shari’a dashi daga filin duniya har zuwa na lahira inda ba zai taba yafe mishi wannan laifin ba. Idan ya zaman Rayyan ne baisan yanda zaiyi ba, bai sani ba kam. Amman tabbas komai zai iya faruwa.

“Idan kaci gaba dayin shiru zan dauka da gaske laifin naka ne.”

Shirun dai Rayyan ya sakeyi, yana sadda kan shi kasa, kirjin shi Abbu ya dafe, ya dauka hawaye sun mishi kaura a shekarun shi, sai yanzun da yake jin taruwar su a cikin idanuwan shi.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Ya furta yana dafe fuskar shi da duka hannuwan shi, wani irin numfashi yake ja yana fitarwa kafin ya bude fuskar shi ya kalli Rayyan da yake tsaye a gaban shi, daga yanzun zuwa wani lokaci da bai hango shi nan kusa ba idan yana ganin Rayyan din zai mishi baki, sosai yake danna zuciyar shi da kalaman da take son furtawa.

“Ka fitar mun daga gida Rayyan, ka tafi kawai.”

Ba Rayyan bane kawai ya dago da kai yana kallon Abbu, hatta da Mami sai da ta dago. Ayya ma kallon shi takeyi tana son jin ya sake furta kalaman ko zata yarda da taji su daga farko, Rayyan daya fara magana ne ya sata kallon shi.

“Ka nuna mun wani uban, Abbu a yanzun nan idan ka nuna mun wani uban ko jakar da take kafadata ba zan sauke ba, zan fita in bar maka gidan ka, zanyi nisa da gidan ka, zanyi nisan da ko nemana kayi ba zaka ganni ba…”

Numfashi Abbu ya sauke yana kallon kasa, kafin ya sake dagowa, baisan lokacin da ya daga hannu ya dauke Rayyan da mari ba, karar na amsawa a ko ina na wajen kafin Bilal ya motsa kafafuwan shi yana karasawa ya shiga tsakanin Abbu da Rayyan din, dan harya sake daga hannu zai kara dauke Rayyan da yake kallon shi ido cikin ido har lokacin da mari.

“Abbu… Dan Allah Abbu.”

Bilal ya fadi a wahalce, wani nishin wahala na kwace mishi, tunda suka fara magana yake so kasar wajen ta bude ya fada ciki ta rufe da shi, rufewa na har abada ko zai gujema fuskantar kowa da kowa. Amman yaki faruwa, tunda suka kira sunan Rayyan komai ya karasa kwance mishi, kalaman Abbu suke mishi yawo har lokacin, babu tunanin komai a ran shi sai na yanda idan mutuwa ba tazo mishi ba, tabbas karshen zaman shi tare da su yazo. Idan Abbu yace Rayyan ya fita yabar mishi gida a haka, tabbas shi zai saka a rakashi waje ne.

A tsorace yake, tsoron da ya saka shi tunanin akwai sauki mai girman gaske a tattare da mutuwa, wani tsoron na daban yana kara bugar shi, saboda hango kwanciyar kabarin shi da yake cike da kokwanto da yayi, a da laifukan shi yana jin tsakanin shi da Allah ne, yanajin suna da sauki mai girma saboda Allah Mai Rahma ne. Amman yanzun laifin shi nacin amana ne, kuma bayason fara tunanin makomar masu cin amana. Bayaso sam, gabaki daya jin shi yakeyi a gigice kamar zai shide.

“Matsa mun Bilal…”

Abbu yayi maganar da wani yanayi da Bilal bai taba ganin shi a ciki ba, kai Bilal yake girgizawa.

“Abbu ni ne, ni ne Abbu.”

Ya furta a razane, saboda ba zai tuna ranar karshe daya ga Abbu ya dagama wani daga cikin su hannu ba, amman a idanuwan shi yake ganin inda abun duka a kusa da shi yau zai saka shi ya jibgi Rayyan din, ba zai kara wani laifi ba, bayan cin amana ba zai shiga tsakanin mahaifi da dan shi ba, ba zai iya kara daukar wani tashin hankalin ba, kamar zai fashe da kuka yake kara fadin.

“Ni ne Abbu.”

Kai Ayya ya dafe, hawaye masu zafi na zubo mata, Mami ta kalla, duk ita ta shigo rayuwar su, ta shigo musu da Layla har suka zo inda suke din nan yanzun. Bilal take kallo da gabaki daya ya rikice, tun tasowar su, ko Rayyan zata daka haka yake shiga tsakani, ko da zata rufe ido taci gaba da kai duka ba zai matsa ba, zai amfani da jikin shi ya kare na Rayyan din yana kuka yana bata hakuri. Akwai tarin lokutta da tasan Rayyan ne yayi laifi amman Bilal din zai dauka. Shine yake faruwa a gaban idanuwanta yau, amman ba zata bar shi ba, ba zata kyale shi daukar wannan laifin ba.

“Karya yake, ya saba Ahmadi, ya saba daukar laifin Rayyan.”

Ayya ta karasa da wani yanayi, kanta sarawa yake ta kowanne bangare, tana tunanin rashin amfani na Malaman duk da tayita asarar kudinta a kansu, duban su da bugun kasar su ya tashi a banza da suka kasa hango mata wannan tashin hankalin, da basu fada mata ko da bata iya kauce mishi ba tasan yanda zata karbe shi tunda wuri, hawan jinin da bata da shine yake son kamata lokaci daya.

“Bilal ka matsa kafin in wanke ka da mari kaima.”

Cewar Abbu, jiri yake gani sosai zuwa yanzun, amman so yake Bilal ya matsa ya kara ganin Rayyan.

“Abbu wallahi ni ne.”

Wani murmushi mai ciwo Abbu yayi.

“Karyar ce kake bi da rantsuwa Bilal? So kake in yarda da kai haka?”

Kan shi Bilal ya sadda kasa yana rasa inda zai saka ran shi yaji sauki-sauki. Komai ya cunkushe mishi, yana ganin Abbu ya juya ya fara takawa, sai dai ko taku biyu baiyi ba ya yanke jiki ya fadi. Kan shi sukayi gabaki dayan su cikin karaji banda Rayyan da Layla, shi yana nan tsaye inda yake, yana rasa kalar tunanin da yakeyi ko ya kamata yayi. Layla kuma tashin hankali ne ya sake dirar mata, shikenan ta kashe mutum daya da ya karbeta a lokacin da kowa yakita, mutumin da bai taba sakawa taji maraicin da take tare da shi ba. Kuskure daya ya canza mata komai.

Bilal da Jabir ne suka kama shi suna yin dadin Ayya da shi, dan tunanin asibiti baizo musu ba. Jabir ne yayi tunanin samo ruwa ya shafama Abbu a fuska kafin ya bude idanuwan shi yana kokarin mikewa

“Abbu faduwa kayi fa, ka kwanta dan Allah.”

Jabir yayi maganar kamar zai saka kuka, baisan tashin hankali ba duk tsayin rayuwar shi sai yau. Ko abokai ne in ka nemi daga mishi hankali zaka neme shi ka rasa ne. Sam baya zama, shisa abin yake tabashi sosai da sosai.

“Idan na kwanta ba zai canza komai ba Jabir, kabar ni in tashi in fuskanci matsalar nan.”

Mikewa Bilal yayi, ba zai iya dauka ba, zuciyar shi ba zata iya dauka ba sam. Ficewa yayi daga dakin zuwa nasu. Rayyan kuwa yana inda suka bar shi, Layla yake kallo har su Mami suka bi bayan su Bilal suna barin su kadai a wajen .

“Hamma”

Layla ta kira tana son ya taimaka mata, ko da zai zama lokaci na karshe a tsakanin su, ya taimaka ya fahimce ta, saboda tasan babu wanda zai taba fahimtarta. Yanzun a kan idonta taga rashin yarda a idanuwan kowa kan cewa cikin na Bilal ne, kowa yaki yarda, tana kuma ganin katanagar da Rayyan yake ginawa a tsakanin su, idan ta bude bakinta, idan ta fada musu cikin na Bilal ne duka zasu yarda, dole zasu yarda. Amman idan suka ce ta auri Bilal fa? Tunanin kawai ya girgiza duka ilahirin zuciyarta balle ya kasance ya tabbata, da gaske mutuwa zatayi idan ta rasa Rayyan.

Watakila tana da sauran rabon zama da Rayyan shisa yaki musa cikin jikinta ba nashi bane ba, so take ya bude bakin shi yayi mata Magana.

“Hamma”

Ta sake kira, dafe kan fuskar shi Rayyan yayi da hannuwan shi duka biyun, yakai mintina biyu a haka kafin ya bude su akanta, a karo na farko yana tsintar kan shi da kin son ganinta. Har a zuciyar shi bayason ganinta.

“Dan Allah Hamma…”

Ta fadi cikin kuka, kai Rayyan yake girgiza mata.

“Bana son ji, koma menene, ba zai canza komai ba Layla.”

Ya karasa yana juyawa, baisan yana cikin tashin hankali ba saida ya karya kwanar da zata kai shi dakin su yaji kafafuwan shi sun kasa daukar shi, a wajen ya tsugunna ya dafe kirjin shi yana jin kamar zai rabe gida biyu. Bude bakin shi yayi yana fitar da numfashi saboda ta hancin kofofin sun toshe mishi, cikine a jikin Layla. Yaron wani ne yake rayuwa a jikinta, yaron da ba na shi ba. Layla, Laylar shi ake magana a kai ba wata ba. Waye zai musu wannan abin? Waye zai taba mishi ita haka, runtsa idanuwan shi yayi yana kuwa bude su babu shiri saboda kazantar hoton daya hasaso cikin kan shi.

Koma wanene tare da Layla suka ci amanar shi. Abin da yafi tsana a rayuwar shi, ya bude baki ya fada mata yana son ta, Layla da ya dawo da burin fuskantar kowa da sunan soyayyarta ce da dan wani a cikinta. Bangon wajen ya dafa ya samu yana mikewa, so yake ya karasa daki ya kwanta, jiri yake gani a tsugunnen ma. Dakyar ya iya mikewa yana shiga dakin su inda ya samu Bilal a tsaye.

“Zuciyata zata fashe Bilal, kirjina ciwo yakeyi.”

Rayyan ya fadi, in bai gayawa wani ba da gaske zuciyar shi fashewa takeyi. Bakin shi ba zai iya shiru a gaban Bilal ba, wannan abin ya mishi girma ya dauka shi kadai, so yake a lallashe shi, kamar karamin yaron da yayi mummunar rauni haka yake ji, a hankali Bilal ya juyo yana sauke idanuwan shi akan Rayyan da yake fitar da numfashi kamar mai ciwon asthma. Shima yana gab da fara fitar da numfashi ta wannan sigar idan wani bai yarda dashi ba, idan bai fadama wani laifin shi bane, saboda shi kowa yake cikin rudani, tashin hankalin zai mishi yawa.

“Hamma…”

Bilal ya kira da wani yanayi a muryar shi da yasa Rayyan kallon shi, abinda yake kan fuskar shi na saka zuciyar Rayyan wani irin dokawa, tun kafin ya bude bakin shi Rayyan yake girgiza mishi kai yana rokon shi, baisan kafafuwan shi sun gaji ba sai da yaji gwiwoyin shi a kasa.

“Dan Allah Bilal…”

Ya furta a hankali, na shi kan Bilal yake girgiza ma Rayyan din shima, dole ya fada mishi, idan yai shiru bashi da hope akan Rayyan din zai yafe mishi, idan ya fada musu, idan kowa ya sani wata rana zasu ji rokon gafarar shi.

“Ni ne Hamma, cikina ne a jikin Layla.”

Kan shi Rayyan ya durkusar kasa sosai yana wani irin maida numfashi, watakila haka ake ji yayin fitar rai, saboda wani abu ke fisgar shi da kalaman Bilal. Da kyar bakin shi ya iya furta.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Yana dagowa ya dafe fuskar shi da hannuwan shi ko inya bude zai farka daga wannan mummunan mafarkin. Bilal ma kasa yayi.

“Hamma idan nace kuskure ne zaka yarda?”

Bude fuskar shi Rayyan yayi.

“Kuskure? Cikin ne zaka dauka ka dora akan kuskure? Layla fa… Bilal ba wata bace Layla.”

Rayyan ya fadi yana kallon Bilal, har lokacin yana son ya san me ma yake ji gabaki daya.

“Kuskure n…”

Mikewar da Rayyan yayi na katse ma Bilal maganar daya fara. Hannu ya mike mishi.

“Bani mukullin mota…”

Da wani yanayi Bilal yake kallon shi.

“Baka iya tuqi ba Hamma, me zakayi da shi?”

Yanda Rayyan din yake kallon shi ya saka shi mikewa.

“Ni ya kamata in bar maka dakin.”

Ya karasa yana ficewa, ko takalmi babu a kafar shi, komawa Rayyan yayi ya zauna, kan shi ya dora jikin gadon dakin yana jin kamar zai mutu. Kwanan shi biyar yau rabon da ya busa hayaki, saboda yana son ya bari, baima yi tunanin akwai wahala sosai a barin shan tababa sai da yake son bari. Jakar shi da sai lokacin ya sauketa daga kafadar shi ya bude, jikin shi har rawa yake lokacin daya dauko kwalin tabar, a yanda yake jin shi zabi biyu yake da shi, ko tabar ko kwayoyin da yayi ma Bappa alkawarin zai sha su kan ka’ida a kowanne yanayi.

“Abu daya zai iya sa ka koma Rayyan, dan Allah ka kula, kaga su da taba ne kawai matsalar ka yanzun.”

Ya kan ga Bappa din ya dauki robar maganin na shi yana lekawa, kamar yana son kirga su batare daya fito da su gabaki daya ba, ba zai iya surutun maimaita magana daya ba saiya kyale shi. Shisa yanzun ya zabi tabar, kunnawa yayi kuwa, sai da yaja kara goma amman a banza, banda zafin da kirjin shi ya kara har tari yake kamar sabon shiga a shan sigarin. Ko dan yana kokawa da numfashin shine bai sani ba. Amman ya kasa samun sauki ko yaya. Yanda duk yaso ya hango Layla da Bilal ya kasa, idan wani ne daban zai iya lakaba mishi kowanne sigar laifi.

Zai iya cewa tursasa Layla yayi, zai iya cewa ya bata wani abune ta sha. Zai iya cewa komai, amman Bilal ba zaiyi abu daya daga cikin duka tunanin shi ba, gabaki daya Bilal bashi da wani dalili da zai iya tunawa nayin abinda yayi. Shisa baiga dalilin da zai saurari komai ba, iya abinda yaji ya ishe shi har karshen rayuwar shi. Kirjin shi zafi yake kamar ana hura wuta a ciki. Shisa ya sulale ya kwanta, babu abinda yake mishi yawo sai Bilal da Layla da ya kasa haskowa saboda tabbas zuciyar shi tarwatsewa zatayi. Mutum biyun da yafi yarda dasu akan kowa, mutum biyu da suka fi kowa kusanci a rayuwar shi.

Bilal yana fita a bakin kofa ya zauna, hawaye yake nema ko zai samu sauki amman ya rasa su yau.

“Kaina kamar zai bude nake ji.”

Muryar Jabir ta daki kunnuwan Bilal din, gefen shi ya samu shima ya zauna. Kowa da abinda yake ji, kowa da abinda yake tunani. Yanayi ne da babu wanda zai iya lallashin wani.

“Na kasa yarda Hamma Rayyan zai mana haka, zuciyata ta kasa yarda…”

Numfashi Bilal yaja yana saukewa.

“Bashi bane ba, ni ne.”

Murmushi mai kunar rai Jabir yayi.

“Idan kace kaine sai kake tunanin abin zai mana saukin dauka? Ka daina dan Allah Hamma, kabari muji da abu daya.”

Jabir ya karasa yana mikewa, gara ko ruwa yaje ya dauka ya sha, koya watsama jikin shi. Koma me da zai dan saukaka mishi abinda yake ji, bin shi da kallo Bilal yayi, wato babu wanda yake son sauraren shi, haka girman yardar da sukayi mishi yake daman? Haka suke ganin ba zai taba cin amanar su ba. Kamar an dora dutse a kirjin shi haka yaji. Kafafuwan shi ya kara ja yana hade su da kirjin nashi ko zai ji dama-dama. Kan shi ya dora a jikin gwiwar shi yana sauke numfashi a hankali.

*****

Zaune Ayya take akan kafet, sai yanzun komai yake tabata, yanzun girman abin yake yawo a kwanyarta. Layla da Rayyan, kaddarar su mai girma ce haka ashe? Duk yanda taso ta shiga tsakanin su alkalami ya gama rubutun shi akan su, sai kawai tunanin farraqun da tayi musu ya fado mata. Zuciyarta na wani irin tsalle ta koma cikin makoshinta, daman ance wani rabon har kisa yakeyi. Ko nasu ne yazo a haka? Raba sun da tayine da rabo a tsakanin su shisa ya kullu ta wannan gurbatanciyyar hanyar da take jin gara mata auren, komin yanda zuciyarta bata so zata koyi jure ganin su a tare kamar yanda take ganin Mami da Abbu.

Batason laifin ya zagayo ya dawo kanta, bataso saboda hakan na sakata jin kamar an tsomata a ruwan kankara. Zuciyarta ta tsinke daga inda take a kulle lokacin da taga Abbu a kasa, dan tana jin yanda zuciyar ke mata barazanar daina bugawa a mintunan da Abbu yayi bai tashi ba, yaran da take karewa da kominta, yaran da take jin zata iya komai dan nisanta su da juna, sune hanya irin wannan ta hada har suna neman kashe mata mijin da take so fiye da su, mijin da take kauna fiye da yanda take son kanta.

Yanzun ma kallon shi takeyi, yanda yake durkushe kan gwiwoyin shi yana sharar kwalla, zuciyarta kamar zata fito waje.

“Dan Allah Ahmadi kayi hakuri, kar wani ciwon ya shigeka lokaci daya, bansan ya zanyi ba… Kayi hakuri dan Allah, komai zai zo da sauki.”

Take fadi tana kokarin tarbe nata hawayen, tasan mijinta, ta san shi din mai rauni ne akan lamurran duniya. Sau nawa ita take nakuda amman take samun karfin halin bashi hakuri duk idan ciwo ya kwanta mata, kuka riris haka Ahmadi yakeyi duk idan ta fara nakuda, balle takan yi mai dogon zangon da sai an fara fidda rai da ita. Yana da raunin da batasan ya zata misalta a fahimta ba, shisa tasan da wahala ya iya daukar wannan kaddarar salin alin. Bata su Rayyan ko Layla takeyi ba yanzun, ta mijinta takeyi, ta tunanin halin da yake ciki da wanda zai shiga anan gaba.

Watakila da batayi katsalandan a cikin al’amarin ba da haka bata faru. Akwai abinda ya girmi tsanar da tayiwa Mami, akwai abinda zai iya tabata fiye da kaddarar da ta hada Mami da Abbu waje daya. Yanzun take gani, abubuwa ne masu tarin yawa suke mata yawo, lokuttan da tayi kokarin shiga hurumin da ba nata ba, canza lamurran da bata da iko a kan su. Zuciyarta da tsoro take bugawa, da kokwanto mai girman gaske kan makomar ayyukanta, kan inda kaddarar da tayi komai dan ta canza take son ta kai ta.

“Idan mutuwa ta daukeni yanzun fa Maimuna? Ni ya zanyi? Me zan fadi akan amanar da ban rike da kyau ba? Ke da kanki kin gano mun matsala a rikon da nayiwa Layla, Allah da yake ganin komai fa?”

Sai Ayya taji kamar da ita yake, kamar ya watsa mata ruwan gishiri a ciwukan ta haka taji. Idan ita tata mutuwar ta dauketa kafin ta mike fa? Ya zatayi ita? Me zata fada akan katsalandan da tayi ma kaddara? Wanne hujjoji zata labe a bayan su? Hawayen da suka zubo mata masu zafi ne na gaske.

“Ba kai bane baka da abin fadi, nice. Wallahi nice ban da abinda zance, ya zan kalli yan uwana? Me zance musu ya faru?”

Mami da ta samu bakin magana tayi jero tambayoyin wani sabon tashin hankalin yana dirar mata, tunda suka shigo dakin ta jujjuya maganganun da Ayya ta fada mata. Idan tace ga dalili daya da ya saka ta barin Layla komawa Zaria zatayi karya. Bata san ya akayi ta yarda ta koma ba, a wannan halin ma ba zata iya dorawa kaddara ba, ba kuma ta son yin amfani da kalmar sakaci da take ta mata yawo. Gani tayi kamar akan tarbiyar duka yaran tana iya yinta. Yaune take gane baka taba yin iya yinka a tarbiya, saboda ba abu bane na lokaci daya, ba kuma abu bane iri daya.

Tarbiyar jiya takan banbanta da ta yau, saboda a duk rana halaye kan canza, yanayi mai girma ko karami, bakon yanayi kan samu wajen zama da dan adam. Shisa tarbiya zata zamana yau da kullum. In kayi jiya, yau ma ka kara, saika hada da addu’ar samun karfin yin fiye da ta yau a goben da zaka samu aronta.

“Nayi iya yi na.”

Da iyaye da yawa kan fadi ba uzuri bane ba, ba kuma lallai ya zama hujja ba a gaban Allah, su yaran amana ne. Mutum ma ya baka amana kaci ya kake karewa, balle Allah da kan shi da ya zabeka a cikin mutane da dama ya baka amanar yara, ya baka aron lokaci, lafiya, da wadatar kula da su. Soyayyar Layla ta rufe mata ido.

“Rikon maraya da wahala.”

Shine kalaman da mutane kan furta a duk lokacin da tarbiyar marayun da suka dauki amanar kula dasu ta sami matsala. Kusan shine hujjar da suke kafawa, har wanda basa rike da maraya ma suna hasaso wahalar da take cikin rikon maraya. Yau ta canza mata tunani gabaki daya, babu wani riko na yaro da yake da sauki, babu kuma wani kalar yaro da baya bukatar tarbiya. Maraya ko mai iyaye, musamman maraya da tausayin rashin iyaye kan saka iyayen rikon sakaci kan tarbiyar shi. Bata san me yasa duk wannan tunanin yazo mata a kurarren lokaci ba, babu wanda zai mata uzuri kamar yanda ta kasa yiwa kanta yanzun.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Ta furta a fili wani kukan na kwace mata. Ayya ma duk yanda take saka hannu tana share hawayenta basu daina zuba ba. Na Abbu sun tsaya daga idanuwan shi, a zuciyar shi suke zuba da ciwo na gaske, da kuma tunanin ta inda zai fara bullowa abinda yake faruwa dan bai sani ba, yaran shine karfin zuciyar shi, sune kuma raunin shi.

****

Iyaye,

Iyayen riko,

Jinjina da lokuttan da baccin ku baya tsawaita saboda tunanin tashin hankalin da yake tare da amanar da take karkashin kulawar ku.

Fatan alkhairi da tarin sadaukarwar ku.

Addu’ar karfin gwiwar ci gaba da kular da kuke.

Ta yau tafi ta jiya.

Ta gobe ta dara ta.

Kuna kokari mun sani.

Idan bamu yaba yau ba zamu yaba gobe, kar tunanin rashin jin dadin mu na kankanin lokaci ya rufe idanuwan ku da hango gaba.

Rabbi Ya tayaku, Ubangijin da Ya baku amana ya tayaku rike ta.

Amin thumma amin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 24Martabarmu 26 >>

1 thought on “Martabarmu 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×