Skip to content
Part 21 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Su Ayya basu isa Zaria ba sai wajen bakwai da rabi, dan ma yau a karo na farko ta ga Abbu ya taka mota sosai. Wajen su Rayyan suka fara biyawa saboda Ayya, maganar farko da Abba ya fara bayan sun shiga dakin shine,

“Me yasa zaku kawo shi wannan asibitin? Baku san na makaranta yafi kowanne kyau a Zaria ba? Kuma sai yafi samun kulawa fiye da ko Ina.”

Kallon shi Rayyan yayi kafin ya sauke kan shi, saboda shi dai asibiti yasan Bilal yana bukata, ko da asibitin kauye aka kaisu a daren jiya in dai zasu iya bawa Bilal din wani taimako a halin da yake ciki zai barsu. Bai iya magana ba saboda kan shi da yayi bala’in nauyi, ga ganin Abbu ya kara mishi nauyin kan da yake ji ba kadan ba. Ayya kam bata bi takan Rayyan ba, kujera ta ja ta zauna kusa da Bilal tana tunanin a fadin duniya wanne ciwo ne zai kwantar mata da yaro haka,

“Bilal…”

Ta kira da wani irin yanayi a muryarta dan tun suna hanya take tarbe hawaye, Abbu na kallon yanda lokaci zuwa lokaci take kai hannu tana goge gefen idanuwanta, gabaki daya hankalinta a tashe yake,

“Me suka ce yana damun shi?”

Abbu ya sake fadi zuciyar shi na kara shiga cikin wani hali, dan shima bai taba ganin Bilal din ya kwanta ba.

“Bashi da lafiya Abbu.”

Rayyan ya furta da kyar, kyale shi Abbu ya yi, duk da shikam daya ga Bilal din a zaune, zai je yayi magana a basu sallama su tafi asibitin makaranta gabaki dayan su. Amman a kwance yake da alamar bacci yake yi. Mami ba damuwa da Bilal bane batayi ba, amman sun gan shi, ya kamata su karasa su duba Layla itama tunda tasan da wahalar gaske daga Rayyan har Ayya subar gefen Bilal din.

“Bacci yake?”

Ayya ta tambaya tana kallon Rayyan da ya dan daga mata kai kawai. Gabaki daya zaman Abbu a dakin ya takura mishi, kan shi harya fara dawowa da ciwo. Wani abu yake tsikarin shi daya fita yabar dakin har sai Abbu ya tafi, amman saboda Bilal ba zai iya matsawa ko nan da can ba. Mami bata ce komai ba, saboda duk wata tambaya da zatayi su Ayya sun rigada sunyi. Rayyan din ba gaishe da su yake ba sai ta kama, zata iya haduwa da shi ya sadda kan shi kasa, ko yayi tsaye in da yake kan nashi a kasa har saita wuce sannan ya tafi inda zaije shima.

Kuma tun ranar da ta gansu da Layla sai ta kula kamar ya kara nisanta da ita. Ba abin bane ya dameta, amman bata son kowa ya kullace ta, Ayya ma dan babu yanda zatayi ne shisa suke wannan zaman doya da manjan. Amman iya soyayyar da zata iya nuna musu a lokacin shine a tsawatar musu. Idan basu fahimceta yanzun ba, wata rana zasu fahimce ta.

“Maimuna kina nan ne? Mu dubo Layla?”

Dan juyawa Ayya tayi ta kalli Abbu, sannan ta sake mayar da dubanta kan Bilal. Bata zaton akwai wani abu da zai faru wanda zai saka zuciyarta taso Layla, yarinyar batayi mata ba tun daga ranar farko da ta dora idanuwanta a kanta. Ta kara girmama tsanar da take mata daga lokacin da Bilal ya fara raba lokuttan shi tare da yarinyar da kuma Mami, har yana shiga bangaren su. Sai kuma take kara ganin yanda Rayyan yake bata lokacin shi cikin yanayin da ko ita bata samun shi. Babu wani abu da zai sa taji yarinyar a ranta, bata sonta, in zata iya nisantata da duka yaranta zata yi. Amman rashin lafiya ce, batama san dan ance Layla bata da lafiya zata ji wani abu ba.

Ganin yanda take tunani yasa Abbu fadin, “Ki zauna tare da Bilal din muje mu dawo.”

Kai ta jinjina ma Abbu da ya saka hannu a aljihun shi, dubu hamsin ce ya cire ya taho da ita ko da zasu bukaci wani abin, talatin ya kirga ya bawa Ayya da fadin,

“Ko da za’a bukaci wani abu.”

Zuciyar shi a jagule take, ba zai kara jagula yanayinta ba ta hanyar bawa Rayyan kudin da yasan da wahala ya motsa daga inda yake ballantana ya saka hannu ya karba, sai ya ga Rayyan yake tuna yanda yake son sakawa a taya shi a addu’a akan matsalar Rayyan din, ko da Nasiru ne yayiwa zancen, amman kamar wanda ake shafarwa kwakwalwa sai ya shirirance, sai ya sake ganin Rayyan din tunanin maganar ya dawo mishi, numfashi mai nauyi ya sauke yana juyawa, Mami na fadin

“Allah ya kara sauki ya bashi lafiya.”

Kafin ta juya tabi bayan Abbu suka fice daga dakin. Ayya kuwa Rayyan ta kalla, idanuwan shi duk sun shige ciki, bata ga sunyi ja ba balle ta alakanta abinda take gani a cikin su da rashin bacci, amman yayi duhu ya kuma fada da alamun rama.

“Yaushe rabon da kaci abinci?”

Numfashi ya sauke, “Na ci abu jiya da rana…”

Mikewa Ayya tayi, bai tambayeta in da zataje ba, ya gaji, a gajiye yake jin shi. Kan shi da kirjin shi kamar akwai wani a cikin su daya danne. Ga son ganin Layla da kewarta da suke nukurkusar shi. Ba zaice ga mintina nawa Ayya tayi a waje ba, amman da leda ta dawo, lemuka ne ta siyo na robobi sai kuma biskit.

“Ka zo ka dauka.”

Tace mishi, tsaye ya yi yana kallon lemukan, kafin ya kalli Ayya, kamar yana son sanin lokacin da ta kula, ko ya akayi ta sani.

“Ka zo ka dauka Rayyan, na san bakacin abinda baka san inda ya fito ba, Bilal ya fadamun.”

Ta karasa maganar da wani yanayi a muryarta, duk wani kusanci da yake tsakaninta da Rayyan, wanda ya kamata ace yana tsakanin uwa da danta, ta same shine a sandin Bilal. A cikin labaran shi yakan fada mata abubuwan da Rayyan yake so da wanda baya so, yanayin shi da duk wani babba da karamin abu da yake tunanin zata bukaci ta sani, ko kuma zata so ta sani din. Ko waya suka yi saiya fara bata labarin yanda ranar Rayyan din ta kasance, sannan zai bata labarin ta shi ranar.

“Rayyan ma yau ya yi lakca…”

Ya kan fara fadi bayan sun gaisa ko yace, “Sai da muka tsaya wani shago yau da muka fita da Rayyan ya siyi biskit, kin san halin shi ba cin wani abu yake a waje ba.”

Ya kan karasa maganganu irin wannan da dariyar da kan sakata yin dariya itama. A fadin duniyar ta Bilal daban ne, Bilal ya kan fahimci damuwarta a lokuttan da Abbu bai gane ba. Shisa hankalinta ya tashi, ta kasa samun natsuwa duk yinin jiya har zuwa safiyar yau, bacci ma sai dai tace barawo, da kuma ya fisgeta take farkawa saboda mugayen mafarkan da bata tunawa da suke addabarta suna sake sakata jin kamar wani abu mai girma ya sami yaranta. Rayyan daya karaso ya saka hannu ya dauki coke tabi da kallo, biskit din kwara daya ya dauka. Bata ce mishi ko me ba.

Tana ji da Bilal ba zata biye Rayyan ba, yana da girman da yasan cikin shi na bukatar abinci ko da bakin shi baya so. Batayi mishi magana ya zauna ba, tana kallo yaja kujera ya zauna. Suna nan su Abdul suka biyo, sosai Ayya ta jinjina karamcin su, sun siyo su Maltina da ruwa sun taho da shi. Ta kuma yi mamakin ganin Rayyan ya gaishe su, yana kula da kallon da take yi mishi, ko da yabar Zaria su Abdul na cikin jerin mutanen da ba zasu taba mantuwa a zuciyar shi ba, sun mishi kirkin da bai taba tsammani ba a lokacin da yake cikin tsananin bukatar taimako.

“Ka gaisa da kowa a mutunce ko baka so Hamma, ko mutuwa kayi kafin a kira su Ayya su din nan da muke waje daya zasu fara sani.” Bilal kan fadi amman baya jin shi, saboda yana ganin gaisuwar kanta a matsayin takurar sosai, gashi sai su dinga gaisawa da kai da sassafe hannun su duk ruwan da baisan kona mene ne ba. Yanzun kam in sun gaishe shi zai amsa ko da bayaso din, in yaso ya wanke hannun shi da sabulu kamar yanda yakan yi. Sai bayan sun tafi Ayya tace,

“Abokan ku suna da kirki.”

Kai Rayyan ya girgiza mata.

“Abokan Bilal ne, gida daya muke…”

Saboda shi yasan ba abokan shi bane ba, ya san ko da suka taimaka mishin dan Bilal suka yi. Kai kawai Ayya ta jinjina, ta dan gyara zamanta kenan taga Bilal ya motsa. Sake motsin ya yi yana jin shi kamar wanda ya yi tafiya mai nisan gaske zuwa wani waje, aka kuma dauke shi aka cillo da karfin gaske. Idanuwan shi da sukayi nauyi yake kokarin budewa a hankali saboda haske yayi mishi yawa. Yayi kokarin bude su ya kai sau biyar kafin ya samu ya bude su gabaki daya.

“Bilal…”

Yaji an kira cikin muryar da ta saka shi juyar da kan shi a hankali ya kalli Ayya, bakin shi ya yi nauyi balle ya kira sunanta.

“Bilal”

Ta sake fadi tana sauke numfashin da batasan tana rike da shi ba. Idanuwan shi ya mayar ya runtse, komai na dawo mishi cikin yanayin da y saka yan hanjin shi yamutsawa cike da sabon tashin hankalin daya dirar mishi. Ko su Ayya har sun sani ne shisa suka zo, da wanne ido zai kalle su, ta ina zai fara amsa tambayoyin su, da kyar ya iya sake bude idanuwan shi yana bin hannun shi da kallo, yaga karin ruwan da saura kadan ya kare, sosai yake karewa dakin kallo yana gane tabbas a asibiti yake, kamar sama-sama yaji muryar Rayyan, da ido ya lalubo Rayyan din da yake zaune kan kujera yana kallon shi.

“Hamma”

Ya furta muryar shi a hankali, amman Rayyan din yaji, fuskar shi ya saka cikin hannuwan shi yana wani irin sauke numfashi. Allah kadai yasan halin da yake ciki tun shekaranjiya, musamman jiya kuma zuwa safiyar yau. Komai karfin hali yake, sanin Bilal na da rai baya nufin hankalin shi ya kwanta tunda bai ga ya motsa ba. Wata natsuwa ce take dawo mishi, ya kai dakika biyar kafin ya bude fuskar shi yana mikewa ya karasa in da Bilal din yake,

“Bilal?”

Ya kira cike da alamar tambaya, duk da idanuwan shi a bude suke, yana son ya kara tabbatar da cewa da ya tashin.

“Hamma”

Cewar Bilal, wani numfashin Rayyan ya sake fitarwa, da wani yanayi a fuskar shi ya ke kallon Bilal.

“Karka sake tsoratani haka, Bilal karka sake tsoratani haka…”

Ya karashe maganar yana sake sauke numfashi, sai da yaga Bilal din ya dan daga mishi kai tukunna ya juya, hanyar kofa ya nufa yana budewa ya fita, hadi da ja musu kofar ya rufe. Anan bakin kofar ya tsugunna yana wani irin mayar da numfashi kamar yayi gudu. Godiya yakewa Allah da duk wani yare da yake fahimta, da zai iya kuka tabbas zai yi na saukin da ya samu lokaci daya haka. Ya kusa mintina biyar anan tsugunne kafin ya iya mikewa, kujerar da take ajiye irin na karfen nan ya zauna kan guda daya. Hutawa yake yi yasan Ayya da Bilal labari zasu fara, yanda kan shi ya yi nauyi sosai zai takura.

Yana nan zaune Abbu ya dawo.

“Ya mai jikin? Har ya tashi?”

Abbu ya fadi, kai Rayyan ya jinjina mishi, harya karasa ya murza kofar Rayyan yace,

“Ya Layla? Abbu ya take?”

Dan juyowa Abbu ya yi.

“Taji sauki, na barta da Maminta ma, abinci take ci sanda na fito.”

Kai Rayyan din ya jinjina zafin da kirjin shi yake yi yana yin sauki. Da Mami ta biyo Abbu sun dawo zaije wajen Layla. Amman yasan Mami bata son shi a kusa da Layla, saboda haka zai jira sai ta tafi, zai yi wannan hakuri. Wayar shi dai ya zaro daga aljihu yana tura mata sako.

“Baki kirani ba da kika ta shi.”

Yana shiga tana dawo mishi da amsa.

“Sai da su Mami suka zo na tashi Hamma, na ji sauki. Ya Hamma Bilal?”

Numfashi ya sauke.

“Ya tashi yanzun shima. Allah ya baku lafiya. Ki kula da kanki, zan zo in ganki anjima.”

Har yana shirin mayar da wayar aljihun shi yaji sako ya shigo.

“Ina son ka Hamma.”

Murmushi ya yi, abinda ya kwana uku rabon da yaji ko alamun shi, sosai murmushi ya yi har hakoran shi suka bayyana, a hankali wani sanyi yake sauka cikin kirjin shi, sake karanta sakon da ya zauna a kwakwalwar shi ya yi saboda yana jin muryarta a cikin kan shi inya karanta daga wayar. Ya jima kafin ya iya mayar da wayar aljihun shi, ya kasa daina murmushi. Yanayin da yake ciki baya son ya bar shi. Zai so ace kullum yana cikin yanayin, kafin yayi mata magana tunanin fita ya nemi sigarin da zai sha yake yi ko zuciyar shi zata kara rage zafi. Amman yanzun yaji baya bukata, dutsen da yake danne da kirjin shi ya daga da kalaman Layla.

Hamma ya yi alamar baccin da yanzun yake jin alamun shi, amman bashi da halin kwanciya. Natsuwa ce ya samu shisa ma har baccin ya samu zuwar mishi.

*****

Bacci ta sake komawa bayan tayi sallah, babu ciwon kan, sai zazzabi kadan da kuma duniyar da bata jin dadin ta. Ta so ta dan watsa ruwa amman bata jin karfin jikinta. Sai kuma lokacin Anisa tace zata je ta dawo, sanda ta dawo ta soyo mata kwai ta taho da ruwan zafi da kayan shayi data kullo su a ledoji. Sai kofi da cokali. Layla ta san tana da lakca shisa ta matsa mata ta tafi.

“Baki ga naji sauki ba, kinga an fara test, ana iya yin wani babu tsammani, kuma idan akwai wani abin zan kira wayar ki ai.”

Bata so tafiya ba.

“Dan Allah ki tafi, ni bacci ma zan koma.”

Sai da ta ga Layla din ta juya kwanciya da yake tun wajen karfe hudu da aka cire mata ruwan daya kare sai suka barta ta huta. Tafiya Anisa tayi don tayi shirin tafiya aji. Lokacin ne wayarta ta soma ruri, ganin Abbu a rubuce yasa cikinta hautsinawa, sabon zazzabi na dirar mata, amman idan taci gaba dakin daukar kiran su hankalin su zai tashi fiye da yanda tasan ya tashi. Batayi magana da Bilal ba, amman idan yaji zabinta na barin komai daya faru a tsakanin su tasan zai amince. Ta san boye komai shine saukin su, in ma sunce zasu fada ta ina zasu fara?

Kuma jiya Rayyan ya ce yana son ta, shi ya saukar da zazzabinta ya rage ciwon kan da takeji, ya rage kusan rabin damuwarta, shi ya bata kwarin gwiwar daga wayar Abbu har tana amsa sallamar shi.

“Layla… Ya jikin naki?”

Numfashi ta sauke, kenan sun san bata da lafiya, tana da tabbacin Rayyan ne ya fada musu.

“Da sauki Abbu, ina Mami?”

Ta tambaya.

“Gata nan tana jinki, yanzun zamu karaso ma, muna Zaria.”

Mikewa zaune tayi wata irin zufa na karyo mata, kanta take kallo tana neman alamun da zasu iya nunawa Mami wani abu ya faru da kuma yanda zata yi ta boye.

“Hello…”

Abbu ya fadi jin tayi shiru.

“Sai kun karaso Abbu.”

Tayi maganar tana mamakin yanda akayi muryarta bata rawa. Sauke wayar tayi daga kunnenta, tabbas idan bata saita nutsuwarta ba Mami zata gane akwai wani abu, karyar da zata yi take nema amman gabaki daya kanta ya kulle, tana nan zaune tana tunani sai ganin su tayi sun shigo.

Wani kuka ne yake neman taso mata da ta hango Mami, saboda a tsayin rayuwarta Mami ce komai nata, duk da Abbu ya zame mata mahaifin da ta rasa, Mami daban take. Ko da tana cikin damuwar da bata taka kara ta karya ba haka takan shige jikin Mami tana mata sangarta, Mamin kuma zata biye ta ta lallasheta a wasu lokuttan in ta kula da gaske akwai damuwa a tattare da ita.

Yanzun ma kasa daurewa tayi, suna karasowa ta zagaya hannuwanta tana rike Mami, hawaye masu dumi na zubo mata, numfashi sosai Mami ta sauke tana samun natsuwa da taga Layla din. Dagota tayi daga jikinta tana zama gefen gadon.

“Mene ne na kukan kuma? Ai gamu mun zo.”

Mami ta fadi muryarta na rawa, har cikin ranta take godewa Allah da yasa babu abinda ya sami yarinyarta. Jikinta ta taba tanajin da zazzabi.

“Kin ci abinci?”

Kai Layla ta girgiza tana share hawayen da yake fuskarta.

“Gashi Anisa ta kawomun shayi.”

Abbu ta kalla.

“Abbu”

Murmushi ya yi, “Sai yanzun kika ganni?”

Dariyar karfin hali Layla tayi, amman tanajin yanda wani abu yake budewa a cikin kirjinta. A lokutta da dama na rayuwarta ta saka kafa tayi fatali da duk wata tarbiya da suke dorata a kai, saboda tana ganin a kasan kaunar su akwai rashin wayewa, akwai dogon bambancin da take gani tsakanin yanda suka yi tasu rayuwar a baya da kuma yanda rayuwa take tafiya yanzun.

“Babu wani abu zamani Jabir, duniya bata canzawa, mutanen cikinta ne kawai suke canzawa, bambancin yanda muka yi tamu rayuwar da yanda ku kukeyin taku yanzun shine zabi…”

Mami ta taba cewa Jabir sanda yake mata maganar cewa zamanin su da kuma na yanzun daban ne, sun jima suna dariya bayan Mami din ta tashi, a ganinsu ba zata taba fahimta ba, ashe sune basu fahimceta ba, akwai tarin ma’anoni a kalamanta, ko kan maganar kaya da take yawan yiwa Layla din, ta dauki shekaru tana mata fada da nasiha a kai sai yanzun take kallon abin da kalar idanuwan da Mami ta ke taso ta duba. Abubuwa da damane suke ta mata yawo. A cikin abinda ya faru a kwanakin nan biyu ta daina kokarin gane ya akayi abinda ya faru ya faru, saboda bata da wannan amsar, ta dai san babu tirsasawa a al’amarin saboda rudanin da take ciki shi Bilal yake ciki.

Abu biyu zuwa ukku ta sani a yanzun, kafafuwanta ta dauka taje gidan su Bilal, da ta tura taga basa nan zata iya juyawa kamar yanda Rayyan ya taba balbaleta da fadan shi harda rankwashi da ta kai musu abinci taga basa nan ta zauna tana jiran su. Yana shiga ya ganta ya rankwasheta yana kama hannunta, da kyar ya bari ta saka takalma.

“Idan kika ga bama nan karki kara zama, baki da hankali ke kam sam ko? Baki san maza bane kawai a gidan? Karki kara zuwa ki zauna idan ni ko Bilal bama nan, dakin tura dakin ki juya ki tafi gida, kina jina?”

Harya rakata bai daina fada ba, da tabi maganar shi, tunda ko suna nan din baya bari ta zauna. Tana shiga zai mike, shisa ta daina sallamar masu abin hawa. Ko a ranar dan tana tsammamin zata same sune, shisa ta sallami mai napep din. Tunda tana son taga tafiyar Rayyan din in yaso ita da Bilal sai su koma makaranta. Amman da ta juya da taga basa nan, da ta janyo dakin ta juya, sai ta zabi ta shiga ciki harta zauna. Idan Mami taji tana da yakinin tambayar farko da zatayi mata shine, “Me kikaje yi gidan su Rayyan?”

Kuma bata da amsar wannan tambayar, uzurin duk da zata bayar a cikin kanta ma bamai karbuwa bane ba. Akwai abubuwa da yawa da ta fahimta yanzun, abubuwan da take dauka a matsayin takura da batasan kariya bane a wajenta. Tun jiya take daukar alkawurra kala-kala, ciki harda sauraren duk wani abu sa Mami zata fadi da kuma yin aiki da shi, dan taga alama maganganun na da karfin kareta daga abubuwa da dama. Da ta saurare su da bata zo inda take yanzun ba, amman tana jin kamar lokaci bai kure mata ba. Ganin Mami din ya sa duk ta kara jin karfin ta ya karasa karewa.

Ita ta taimaka mata taje bandaki ta kara kuskure bakinta suka dawo, likita ne ya shigo yin round da yake dakin su hudune a ciki, akwai dai yar tazara tsakanin wani gadon zuwa wani, kuma akwai wasu gadajen da babu kowa, su Abbu fita suka yi sai da aka gama sannan suka dawo.

“Wai idan naci abinci sai a kara sakamun ruwa yace, zan kara kwana sannan su sallameni.”

Kai Mami ta jinjina mata, tana daukar kofin da yake cikin kwandon da Anisa ta kawo. Shayin ta hada mata tana dauko yar kular ta bude mata wainar kwan, ta fara cine Abbu yace,

“Bari in koma wajen su Bilal in kara ganin ya nashi jikin tun da ita ta samu.”

Kai Mami ta jinjina.

“Kayi mishi sannu.”

Dubu sha biyar ya kirga ya bata yana barin biyar a jikin shi, karba ta yi hadi da yin godiya, ita da Layla suna mishi addu’a da bada sakon yiwa Bilal din sannu da jiki. Daurewa Layla tayi ta shanye shayin tas, wainar kwance ta kasa cinyewa, karfin hali take yi kar Mami ta fahimci wani abu, hira sukeyi a hankali, har akazo aka kara mayar ma da Layla ruwan, da yake an saka allurai a ciki, baccine ya dauketa. Mami na nan zaune Anisa ta dawo, gaisawa suka yi ta wuce da fadin zata dora girki.

“Kina ta shan hidima, idan akwai waje me kyau ki siyo kawai Anisa.”

Mami ta fadi tana bata dubu uku, tasan duk tsadar abincin dai nasu su uku ba zai wuce dubu dai-dai ba. Karba Anisa tayi dan kuwa da gasken a gajiye take jinta. Saida tayi sallar azahar sannan ta dawo, tana kawo musu nasu sallama ta kara yiwa Mami saboda tana da wata lakca har karfe hudu. Har tana saka Mami yin tunanin ya za’ayi yara ba zasuyi rashin lafiya ba da wannan zirga-zirgar da suke yi. Ga shi saika dawo daga daukar darasi zaka fara neman abinda zaka ci.

“Kullum daman sai kun dawo sannan kuyi girki?”

Ta tambayi Layla cike da damuwa bayan ta tashi, dariya Layla ta yi.

“Muna ci a cikin makaranta, mun mafi yin abincin dare dai, ko da safe mu girka kafin mu fita idan babu lakcar safe.”

Numfashi Mami ta sauke, babu wani abu a karatu nesa da gida banda wahala a nata ganin, saboda idan a gidane zakaje ka koma kuma ka sami abinci a girke, shisa duk in suka dawo sai taga sunyi zuru-zuru. Ayita maganar wahalar karatu ce, nan kuwa harda kujuba kujuba da rashin samun abinci akan lokaci.

“Kinga da kinyi zamanki BUK kikaki.”

Murmushin Layla tayi mai ciwo, saboda a karo na farko maganganun Mami din sun zauna mata, da ta zauna a BUK din abin nan da bai faru ba, saboda ina taga Bilal din ma in ba hutu ya dawo ba? Batason tsaurara tunani a kai har mami ta fahimci akwai wani abu.

“Kai Mami, baki ga su Hamma ba har sun gama, sauran fa sati uku a fara jarabawa…da an dawo an karayin wata nima aji uku zan shiga.”

Kallonta Mami ta yi.

“Babu in shaa Allah kamar ke ce da rayuwar.”

Dan murmushi ta sake yi.

“In shaa Allah.”

Ta fadi tana saka Mami fadin, “Hmm…”

Kawai saboda ganin Layla ya nutsar da ita, amman akwai wani yanayi da zuciyarta take ciki wanda ta kasa fahimtar shi, watakila yana da alaka da kalar rashin tarbiyar da ta dinga cin karo da shi tunda ta shigo makarantar, yara ne kala-kala, wasu matan kallo daya zaka yi musu daga fuskar su ka gane yaran Hausawa ne kuma musulmi, amman shigarsu tayi hannun riga da wannan, ga shi sai rike juna suke da maza kamar hakan bakomai bane ba, ga gungun dalibai duk an jera an taho tare anata hada kafadu da sunan za’a tafi aji. Addu’ar duk da tazo bakinta yinta take yi. Bata je jami’a ba, tana jin labari kala-kala da yake tattare da jami’a dai.

Amman taga yaran da suka shiga cikinta suka fita kalau, yaran da suka tsallaka kasar ketare sukayo karatun su batare da tarbiyar su ta sami tangarda ba, hakan baya nufin kowa ma zai kasance a haka, idan babu rashin ji kacokan na yaro, akwai mugayen abokai da tasirinsu mai girma ne. Illar jami’a zatayi dai-dai da rashin illarta idan ma illar batayi rinjaye ba kenan.

“Allah ya shirya mana, Allah ya tsare mana”

Shine abinda taita furtawa sanda suke hanya. Kusan har karfe shidda suna garin Zaria. Sosai Mami taso tafiya da Layla, amman taki.

“Nafa ji sauki Mami, kuma mun kusa fara jarabawa mu dawo gida hutu gabaki daya.”

Abbu kuma ya goya mata baya da fadin, “Nan da kwana biyu sai mu kara dawowa mu kara duba su.”

Zuciyar Mami ta kasa nutsuwa, Ayya ma da kyar Abbu ya rabota da asibitin bayan sunje daukarta. Can ma suka sami Aisha da wata kawarta sun zo duba Bilal din sunyo abinci sun kawo. Abbu najin labarin Aisha a wajen Ayya, amman yaune ya fara ganinta, yarinya ba dai kunya ba, dan da kyar ta gaishe da su, ko sallama bata yi ma su Bilal ba suka fice suka tafi. Sai da suka jira ta karbi lambobin abokan Bilal din, tana tunawa Mami da cewa itama zata saka Layla ta tura mata lambar Anisa. Haka suka bar garin Zaria da rashin nutsuwa daban da wanda suka shigo garin da shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.6 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 20Martabarmu 22 >>

1 thought on “Martabarmu 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×