Skip to content
Part 23 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

“Layla ta dawo ko?”

Naadir ya tambaya yana shigowa dakin, murmushi Mami tayi,

“Bata dawo ba.”

Ta amsa shi, kallon ta yakeyi da murmushi a tashi fuskar kafin ya wuce kitchen, bude-bude ya fara yana ganin wake da shinkafa, sai sauce din manja da ta sha kifi, yana zubawa yake fadin,

“Layla ta dawo Allah Mami…ni na sani.”

Dariya tayi wannan karin, da yake nan BUK Naadir din yake yi, kuma duk a cikin yaranta shine makaranta take wahalar wa, saboda kokarin shi bai kai nasu ba, yana cikin gari amman ba kullum yake kwana a gida ba, musamman lokacin jarabawa irin haka, a makaranta yake kwana suna dan taba karatu, wani lokacin har tausayin shi take ji, akan Naadir ta yarda kokari halitta ne, amman babu wanda zaice baya fahimta, idan harka sakawa zuciyarka hakuri da juriyar bibiyar abu, hatta da Marwan tana kallon shi ya ajiye islamiyya, gashi da kokarin amman karatun bawai ya dame shi bane can-can. Yafi gane harkar kasuwanci da yakan bi Yaya Ayuba.

Amman Naadir na zuwa islamiyya har yanzun, idan zaibi abu sau hamsin kafin ya fahimta baya gajiyawa. Yanda ake yaran suna gane Layla ta dawo har mamaki yake bawa Mami, shisa Naadir na fitowa daga kitchen din tace,

“Wai ya ake kuna gane ta dawo ko baku ganta ba?”

Dariyar shi Naadir ya yi.

“Kamshi Mami, kamshin turare.”

Dariyar tayi.

“Wato ni bana saka turare kuke nufi ko mene ne?”

Kai Naadir ya girgiza, yana ficewa, Mamin su na kokari matuka wajen tsafta, amman turarukan da Layla take amfani da su daban ne, duk idan ka shigo zakaji su. Su suke fara sanar da kai tana cikin gidan. Sai kuma abinci da manja yawanci, su duka yaran suna so, ita kuma Mami bai dameta ba, kuma ba zata iya wahalar girki kala biyu kamar yanda Laylar take yi ba, idan miya ce tana iya yiwa Mamin tata daban da babu manja, su kuma tayi musu mai manja. Kuma tana iya binsu a waya tana tambayar me suke marmarinci, Mami abinda taga damar dafawa shi takeyi, ko Abbu baya mata zaben girki balle su.

Layla ma daga dakinta ta fito dan yunwa ta korota, tunda tayi azahar ta kwanta tana bacci, bata tashi ba sai da la’asar din, jikinta da yayi nauyi yasa ta watsa ruwa bayan ta idar da sallah.

“Wai ina kike siyen turaren wutar da kike zuwa da shi? Yafi na nan da mukan siya dadewa a dakuna.”

Mami ta tambaya.

“Wajen wata Kamshi by Saffad, Anisa ce take zuwa da shi tana saka mana a daki, kamshin yana mun dadi, shine ta bani lambarta duk idan zan dawo nake siyo mana fa, kuma babu tsada Mami.”

Layla ta karasa tana shigewa kitchen, sai da ta zuba abinci ta kai daki sannan ta daukowa Mami kwalbar turaren wutar tana dawowa ta kawo mata. 07010137848 Lambar wayar Mami ta duba, Layla kam yunwa takeji shisa ta koma cikin daki abinta, yau da ta tashi ji take a duniya idan bata ci miyar kifi da manja ba komai zai iya faruwa, shisa ta kira Jabir a waya tace ya siyo musu kifi. Da yake yafita kwadayi ko awa daya ba’a hada ba ya shigo dakin da kifi mai yawa, sai da ta saka wani a fridge ma. Abincin take ci tana duba text tsofin texts din su ita da Rayyan, ba sosai suke waya ba tunda ta dawo saboda Mami.

Shisa kusan wuni sukeyi suna musayar text, baya gajiya da saka mata kati ko da tace mishi tana da saura, yi yake kamar baijita ba, ta dai rasa ya zatayi da shi akan waya. Duk idan tayi mishi zancen waya sai yace ta kyale shi, ba zai barnar kudi ba akan waya. Kewar shi na danneta, in da ya siyi babbar waya zata saka shi ya dauko manhajar IMO dan su dinga video call ta nan, ta ga fuskar shi, ko hotunan shi basu kai goma ba wanda take da su, na ranar da ya gama jarabawa, sai kuma ranakun da yazo wajenta ta daga camera bai fisge wayar daga hannunta yana hada mata da rankwashi ba saboda zata dauke shi hoto.

“Ko aljanu sukan rabo a dauki hoto da su wani lokaci Hamma, amman ace kai baka da hotuna saboda Allah.”

Ta taba ce mishi, murmushi yayi kawai yana girgiza mata kai, akwai hoton su ita da shi da take so, saboda ranar tayi sa’a ya tsaya sosai, kuma manyan kayane a jikin shi harda hula. Har ranta take jin Rayyan, kamar yanda har a zuciyarta take jin shine cikon farin cikin ta. Abincin ta karasa cinyewa ta dauki plate din ta mayar kitchen ta koma ta kwanta abinta. Idanuwanta take ji suna mata nauyi da alamun bacci, ba dan bata kwanciya ba, amman a yan kwanakin nan sai take ganin kamar baccin da takeyi yayi yawa. Shisa da ta idar da sallar asuba take shiga kitchen tayi abinda zatayi, saboda Mami bata tashin ta, idan tayi aiki shikenan, idan kuma bata fito ba ita zatayi da kanta.

Shekaranjiya wata irin kasala ta dinga ji har cikin kasusuwan ta, shisa ta kasa fita tayi kwanciyar ta, sanda ta tashi karfe goma na safe.

“Mami baki tasheni ba, shine kikayi aikin ke kadai.”

Murmushi kawai Mamin tayi mata.

“Rai na son hutu Layla, kuma motsa jiki na da kyau, tunda kika zo bana wani aikin komai, sai kin shagwabani ki koma makaranta abinki.”

Dariya tayi, ko da babu makaranta tasan Mami ba zata tasheta ba. Wayarta da harta fara subucewa daga hannunta saboda bacci ta dago, haka kawai sai idanuwan ta suka sauka kwanan wata, period biyu kenan batayi ba, wannan karin ma har wajen kwana takwas kenan ta kara. Farkon da sukaje makaranta, daga ita har Anisa sun sha wahala saboda infection da suka kwasa na amfani da bandakin makaranta, gara ma ita ciwon mara ya kara mata sai kuma period daya dinga mata wasa, da kyar Anisa ta samu ta sakata taje asibiti.

“Ni fa in zan shekara banga period ba zaifi mun, Allah ya kawomun saukin wahala ne.”

Har duka Anisa ta kai mata tana fadin,

“Ke daman ai baki da hankali.”

Amman da gaske takeyi, babu wani ciwo da yake bata wahala banda period, har zullumi take yi idan taga tsakiyar wata ya kusa, tana hasaso kalar wahalar da zata sha. Shisa yanzun ma bata damu ba, daman Anisa na mata fadan ta dinga tafiya da tsintsiya bandaki, ta wanke wajen kafin ta tsugunna, shisa rashin period din bai wani dameta ba, tasan ba zai wuce infection din da har a asibiti aka fada mata idan bata kiyaye ba zai iya dawowa, saboda babu matsalar da take damun mata irin wannan, babu kuma abinda yake da wahalar sha’ani kamar shi. Idan ta koma makaranta sai ta sake zuwa asibiti, zuwa yanzun kam zata shana abinta.

*****

Fitowa tayi daga bangaren ta, tana jin Intisar na fadin,

“Ayya ko ina ne fa babu network din Glo, ga nawa ma ya dauke.”

Bata bi ta kanta ba, cigaba tayi da tafiya tana daga wayarta, sai kuwa ga tsinke daya ya kawo ya sake daukewa, a ranta take fadin,

“Ga shi na fara zuko shi, amman yaran nan sai suce maka ai ko ina ne babu network.”

Bilal take ta kokarin kira tunda ya fita, sai take ganin kamar ya koyi yawo yanzun, duk da yakan ce mata wajen tirenin din kwallon kafa yake tafiya, ko wajen Aisha. Fitar tashi tana mata yawa, sam baya son zama a gida kamar yanda sukan yi, ta kira MTN din shi bai daga ba, tasan karamar wayar na tare dashi, nan ne kuma glo din su yake, dabarar ta gwada kiran shi da wata lambar bata zo mata ba sam. Intisar da taso fada mata zagi ta sha, sai tayi shiru tana dariya. Harabar gidan ta fita sosai, kamar daga sama taga giccin Layla, yanayin da ya sata raba idanuwanta da wayarta tana kallon yarinyar.

Ba cika kallonta tayi ba saboda yanda bata cikin yan kayanta, amman yau wani irin bugawa taji zuciyarta nayi, fara ce dan fara, Layla na da hasken fata kamar su Rayyan, amman sai taga ta kara yi mata wani sanannen haske, hasken da bata fata ya kasance tare da budurwa kamar Layla. Sosai zuciyarta take bugawa, musamman yanda Layla ta dawo ta wuce cikin wani irin rashin kuzari da ba nata bane, ita din mai kazar-kazar ce, bata san kiyayyar da takewa Maryama bata mamaye dukkan zuciyarta ba sai yau, sai yanzun da ta tsinci kanta da furta,

“La hawla wala quwwata ila billah.”

Tana saurin kauda zargin da yake son darsuwa a cikin zuciyarta. Kafin ta dora da addu’ar neman tsari daga shaidan da kan jefa zato kala-kala a zuciyar dan adam. Tsoron da taji ne ya mantar da ita neman Network din da ta fito yi tana komawa ciki. Duk surutun da Intisar takeyi mata bata jiba balle tabi ta kanta, sam zuciyarta ta kasa samun natsuwa, ko dan kacokan rayuwarta akan yaranta ne? Takan san basu da lafiya kafin ma su farga da basu da lafiya, ko jikin Rukayya ya taba nata takan gane idan zafin jikin dai-dai yake ko akasin haka,

“Ayya lafiyata kalau fa, ina ga gajiyar makaranta ce.”

Rukayya kan fadi wasu lokuttan idan tace mata ta sha ko panadol ne, sai ta barta, karshe da safe zaka ji tana cewa,

“Kinga zazzabi ya dameni ko Ayya?”

Harararta takan yi ta share, sai ta fara dariya, a cikin yaranta kaf Rayyan ne kadai bata gane wani abu a kan shi. Shisa yanzun tasan akwai abinda yake damun Bilal da yake boye mata.

“Akwai wanda zai san damuwar ka idan ban sani ba Bilal?”

Ta bukata bayan ya dawo da kwana biyu, amman murmushi yayi mata.

“Bakomai Ayya, idan akwai zan fada miki kinsani.”

Kai ta jinjina, bai saba mata karya ba, a yanda sautin muryar shi ta fito tasan karya yakeyi. Bata ja maganar bane saboda batason ta saka shi sake yi mata wata karyar akan wadda yayi mata. Fatanta matsalar kar ace daga wajen Aisha ne yake fuskantar ta, saboda damuwa ba abokiyar Bilal bace ba, banda ita Rayyan ne kawai take tunanin zai san damuwar Bilal, shikuma ba zai taba fada mata ba. Addu’a kawai takeyi Allah yasa ba wata damuwa bace mai girma. Shisa take son yakice Layla da ta tokare mata makoshi daga ranta, saboda bata bukatar wata damuwa ta rashin dalili a kwanakin nan.

Har dare ma bayan tayi isha’i taci abinci nan falon tayi zamanta tana kallon wata dirama a tashar Dadin Kowa. Amman hankalinta rabi ne a kai, rabin na wajen kofa tana jiran ta inda zata ga bullowar Bilal, har Abbu ya riga shi dawowa yau. Bai shigo ba sai wajen tara na dare, sallamar shi ta amsa a hankali tana kallon shi ya wuce kitchen ya zubo wani abinci da ko Huda yayiwa kadan ya dawo falon ya samu kujera ya zauna.

“Me ake kallo ne Ayya?”

Numfashi ta sauke tana nazarin yanayin shi, gashin daya ajiye a fuskar shi bai hanata ganin ramewar da yayi ba, yau sai take ganin kamannin da akan ce yanayi da ita sun fito sosai, saboda ramar ta kara fito da hancin shi.

“Wata dirama ce fa, kamar ma kullum sukeyi.”

TV din Bilal ya dan kalla, yana mayar da hankalin shi kan abincin da yake ci, yasan jikin shi na bukata, amman tunda yazo gidan ba gane kan abinci yakeyi ba. Texts din Rayyan suke tuna mishi wasu lokuttan.

“Kaci abinci Bilal.”

Shine abinda yake rubutowa da safe, da rana, da kuma dare, bai taba kara wani abu a kai ba, ko ya rage, in sukayi waya kuma baya tambayar shi yaga sakon ko me yasa bai bashi amsa ba, ko da bai tuna mishi ba yana kokarin ganin ya saka wani abu a cikin shi ko da sau daya ne a rana. Duniyar ce yakeji ta hade mishi waje daya. Idan zaka tambaye shi ya yake kwanciya ya tashi da safe ba zai iya fada maka ba, wata rana akan darduma in da yakan yi salloli nan bacci yake dauke shi, ya fara sallolin ne saboda tunanin neman wani abu ya sha dan ya taimaka mishi wajen bacci ya fara damun shi.

“Muryar ka na mun kama da wanda depression yake shirin kamawa Bilal, idan ba zaka iya mun magana a dan uwanka ba, kai mun magana a matsayin likitan da zai iya taimaka maka…”

Rayyan yace mishi jiya da safe, yana kara saka shi jin babu dadi, saboda ya saka shi cikin damuwa, bayan abinda yakejin yayi mishi.

“Ban san me zance maka ba… Idan na kara ce maka babu abinda yake damuna zai zamana wata karyar akan wadda nake tayi a kwanakin nan, saboda haka zan fada maka gaskiya Hamma, wani abu na damuna, amman bana son inyi magana a kai, dan Allah ka daina tambaya, kana karamun nauyi da tambayoyin ka.”

Yanajin numfashin da Rayyan ya sauke ta dayan bangaren, runtsa idanuwan shi Bilal yayi yana bude su

“Ba zan sake tambaya ba, in kayi mun alkawarin ko da kaje asibiti sun baka wani abu karka sha sai naga mene ne.”

Dan murmushi Bilal yayi, shi me zai ma kaishi asibiti. Har yanzun duk yanda ake magana kan mental health bai shiga zuciyar shi ta yanda zai dauki kafafuwan shi yaje asibiti a kai ba.

“In shaa Allah. Lafiyata kalau da gaske, damuwa ce kuma kowa na tare da ita yanzun…”

Ya karasa da yar dariya dan ya saukaka musu yanayin daga shi har Rayyan din.

“Zan zo karshen wata In shaa Allah… Zan zo in ganka.”

Kai Bilal yake girgizawa.

“Kar ka baro hidimar ka nace maka lafiyata kalau Hamma.”

Wayar Rayyan ya kashe a kunnen shi alamar ya rigada ya gama yanke hukuncin zuwa, babu kuma abinda zai sake hakan. Tun jiyan yake lissafa kwanakin da suka rage a cikin watan, yana ganin saura kwana tara, tabbas nauyin da kan shi yayi zai karu idan Rayyan da Abbu suka kasance waje daya yana ganin su a duk rana. Tunda yazo ya kasa bari idanuwan shi su shiga cikin na Abbu sam, ko hira mai tsayi ya kasa zama suyi, kullum cikin uzuri yake dan yabar dakin Abbu din. Ga Aisha yanzun da fada suke na rashin dalili, ko yau sai da sukayi kafin ya taho.

“Damuwar ka na damuna duk da ban santa ba, amman baka mun adalci ka sani…”

Ta fadi tana tashi tabar shi a wajen, ya rasa yanda zai ya dinga bata hankalin shi kamar da, ko waya suke yakan shiga wani tunani sai taita magana bai san tanayi ba, haka idan suna chatting yakan manta ya ajiye wayar, wasu lokuttan sai ta kira sannan yake tunawa, banda hakuri babu abinda yake da shi da zai bata, amman yana bukatar duk wasu kalamai na hakuri da zai iya adanawa, saboda yanajin yanda shine kawai abinda ya rage a tsakanin shi da mutanen da suka fi kowa kusanci da shi.

*****

Ganin karfe sha biyu saura yasa Mami sake tashi dan taje ta duba taga ko lafiyar Layla. Bataji motsin ta ba da asuba sai da ta tasheta, wajen tara na safe ma ta sake tashin ta dan ta karya. Tana tura dakin kuwa taga bacci takeyi, karasawa tayi tana dan bubbugata.

“Layla…”

Mami ta kira a dan tsorace, da kyar Layla ta bude idanuwanta, da zazzabi ta kwana ga kasala, jikinta kamar ta aro takeji, da tana sallah da asuba sai takejin jiri na dibarta, raka’a ta biyu a zaune ta karasa ta da kyar.

“Lafiyar ki kuwa?”

Mami ta tambaya tana taba jikin Layla da taji kamar wuta,

“Subhanallah…”

Ta furta tana kama Layla ta dago ta.

“Mami bani da lafiya.”

Cewar Layla tana sake komawa ta kwanta saboda yanda take jinta, tana zazzabi kala-kala, amman wannan daban yake, tunda take a duniya bata taba jinta a irin yanayin da take jinta yanzun ba, ko dazun da Mami ta shigo ba bacci takeyi ba, maganar ce take mata wahala da ta fada mata bata da lafiya. Gabaki daya Mami ta gama rikicewa, tashi tayi tana wucewa ta dauko hijabi ta saka a jikinta tana dawowa dakin Layla da take jin wani sanyi na ratsa sassan jikinta, lokaci daya tunanin mutuwa na gifta mata, yana sakata jin ko dai ciwon ajali ne ya kamata

“Ko mutuwa zanyi Mami? Jikina baya mun dadi.”

Zuciyarta Mami taji tayo wani tsalle tana dawowa makoshinta

“Wacce irin magana ce wannan? Jiba shirme.”

Ta karasa tana daukar wayarta da take kan gadon Layla tana rasa waya kamata ta fara kira, Haris dai baya garin ma, sunje wani Seminar a Katsina. Idan ta kira Jabir da wahala yana kusa, lambar Bilal ta lalubo tana kiran shi, sai da tayi tunanin ba zai dauka ba sannan taji sallamar shi cikin kunnenta

“Dan Allah Bilal idan kana kusa kazo ka kaimu asibiti, Layla bata da lafiya…”

Da sauri ya amsa da,

“Gani nan… Bari in shigo.”

Sauke wayar tayi daga kunnenta tana mikewa, hijabi ta samo ta kama Layla ta dago ta tana saka mata, duk ta langabe a jikin Mami, ga amai da yake tukarta amman yaki fitowa, tunda asuba take jin shi. Gabaki daya sama-sama take ji, kamar rabinta a duniya rabinta a wani waje da bata san ina bane ba. Ko minti goma ba ayi ba sai ga Bilal din ya shigo bangaren Mami da sallamar shi, dan a kwance yake sanda kiran Mami ya shigo, da kamar ba zai daga ba, baisan me zaice mata ba, tunda ya dawo sau biyu ya ganta, yana duk kokarin shi wajen ganin basu hadu ba, sai dai Mami ba zata taba kiran shi babu wani dalili mai karfi ba.

Yana dagawa kuwa yaji dalilin ne mai karfi, motar su ta sami matsala tun shekaranjiya daya ajiyeta wajen gyara bai waiwayeta ba sam. Kuma yaji muryar Mami kamar hankalinta a tashe yake, shisa yana fitowa ya wuce dakin Ayya, a Kitchen ma ya sameta

“Bilal… Lafiya?”

Ayya ta tambaya, ganin yana balle maballan rigar shi kamar a hanya ya Sakata.

“Mukullin mota zaki bani Ayya, yanzun Mami ta kirani inzo in kaisu asibiti Layla bata da lafiya.”

Wani irin kallo Ayya takeyi mishi, duk yaran Maryama din sai ta kira Bilal saboda gulma da neman dalili, Haris baya nan tasani tunda ko da safe sunyi waya. Amman Jabir aikin me yakeyi.

“Ina Jabir? Sai kaine zaka kaisu asibiti? Ita ina motar hannun ta?”

Numfashi Bilal ya sauke.

“Ayya dan Allah, tun da kikaga ta kirani watakila basa nan ne shisa.”

Karamin tsaki Ayya taja.

“Kinibibi ne dai da neman magana irin nata, sai kaje ka dauka yana kan drawer din gefen gado, in ka kaisu ka dawo mun da motata zan fita.”

Wucewar yayi ya dauko, yanajin Ayya na fadin,

“Kabi a hankali kaketa rawar jiki…”

Baiko juya ba harya fice ya na nufar dakin Mami. Aikam yanayin da ya ga Layla din ya daga mishi hankali.

“Ki taso Mami.”

Ya fadi, kama Layla tayi suna fitowa, sunzo harabar gidan dan ya dauki motar Ayya, sai ga Jabir ya shigo shima da motar Mami din da Ayya take magana a kai.

“Bilal ga Jabir nan ma ya dawo, bari sai mu tafi kawai.”

Kai ya jinjina mata.

“Bari in maidawa Ayya mukullin dan zata fita sai in zo mu tafi.”

Wannan karin kai Mami ta girgiza mishi, daman saboda tana tunanin idan ta tsaya jiran Jabir za’a bata lokaci shisa. Tasan halin Ayya, zata iya fadar maganganu idan Bilal din ya bisu asibiti, kwana biyu basuyi ba, bata neman tashin hankali.

“Nasan muma ba jimawa zamuyi ba In shaa Allah…ka koma kawai dan Allah.”

Dan juya zancen yayi, kafin ya jinjina kai.

“In dai sun rike ku dan Allah a kirani.”

Ya fadi yana rakasu har wajen motar, sai da yaga sun shiga har sun juya sannan ya koma ciki. Kai tsaye Aminu Kano Jabir ya nufa da su, in da ba’a bata lokaci ba, basu ma samu layi ba, Jabir ya sai musu kati, mutum daya aka gani sai su da suka shiga, Mami ta zaunar da Layla da take jin kamar zata shide akan kujera ita tana tsayawa, tambayoyi likitan ya fara yi kamar yanda sukan yi.

“Tun yaushe kike zazzabin?”

Ya tambaya, dan jim Layla tayi, takan kwana da shi tun dawowar ta, amman baya damun ta, tun da sai ta farka ko fitsari taji shi, in ta samu ta koma bacci kuma da safe ya tafi, yaune kawai ya kwantar da ita haka, cikin rawar murya ta amsa shi

“Na kai sati, amman da dare ne kawai. Yaune har yanzun bai tafi ba”

Sosai yaci gaba da mata tambayoyi kala-kala, jin ance za ayi awon jini dana fitsari yasa Mami fadin,

“Bata da aure fa.”

Murmushi kawai likitan yayi.

“Za’a duba komai ne Hajiya, babu wata matsala.”

Haka kawai sai ta tsinci kanta da shiga damuwa, tare da Jabir sukaje aka dibi jini da su biyan kudi, zuwa duk wani abu da ake bukata suka dawo suka zauna suna jiran results din.

“Ko zaki sha wani abu in siyo miki?”

Kai Layla ta jinjina.

“Ka siyomun Sprite”

Da mamaki Jabir yake kallonta

“Yaushe kika fara shan sprite?”

A shagwabe ta kalli Mami.

“Ka wuce ka siyo mata bata da lafiya karku sakani surutu.”

Dan tasan halin Jabir baya gajiya da tsokanarta, kawai dan yaga tana mitarta da kai kara. Wucewar yayi, bai jima ba ya dawo. Mami yasan ba sha zatayi ba, ruwa ya siyo mata, shi ya siyowa kan shi coke. Suna zaune aka ce musu result din ya fito.

“Mami kiji me zaice, jiri nakeji Allah.”

Kai Mami ta daga mata, nan ta ajiye robar ruwan da ta fasa ta dan sha, sai Layla take jin ta dan samu, ba kamar sanda suka fito daga gida ba, har ranta ta dauka ciwon ajaline ya kamata. Zaune sukayi abinsu ita da Jabir yana mata hirar wani film da suke kalla su dukan su mai suna Blind spot

“Hamma banyi nisa ba, kabarni, bana son jin me zai faru…”

Dariya yayi, ya bude baki yayi magana ya hango Mami, yanayin ta na saka shi mayar da bakin shi ya rufe, saboda a hargitse take, a hargitse kuma ta karaso inda suke.

“Ki bude bakin ki Layla, ki fadamun karyane, ki ce mun likitoci da kan su nayin kuskure, na’urar su na samun tangarda…”

Cike da rashin fahimta suke kallon Mami da take magana kamar ta sami tabin hankali.

“Mami…”

Jabir ya fara magana Mamin ta katse shi ta hanyar daga mishi hannu, idanuwanta kafe suke cikin na Layla.

“Ki tashi muje ki fada mishi ke din budurwa ce, ki kalli idanuwan shi ki fada mishi babu yanda za ayi ki samu ciki!”

Wannan karin har mutanen da suke wajen sai da hankulan su ya tattaru ya dawo kan su, robar lemon da take hannun Jabir tana subuce mishi.

“Ciki? Mami ciki? Bashi da hankali? Wanne irin ciki kuma?”

Layla tun daga kalmar “ciki” komai ya daina karasawa kwakwalwar ta, in dai ciki likita ya gano mata tasan inda ta same shi, in dai da gaske akwai wani abu a cikin ta tasan ya akayi, ba karya yayi ba, na’urar su bata da matsalar komai, kwakwalwar ta ce ta samu tangarda, tunaninta ne ya yaudareta da alamomin duk da ta dinga gani amman ta kasa fahimta, ba infection bane ya dauke mata al’ada, shigar cikine.

“Layla…”

Mami tayi maganar tana girgizata cikin yanayin da ya sata daga ido ta kalli Mami din.

“Ciki Mami… Ciki ne da ni.”

Ta karasa cikin wata irin murya da yasa wani abu kullewa a cikin Jabir, yaune ya fara sanin tashin hankalin, Mami kuma da ta yanke jiki ta fadi tana kara mishi wani sabon tashin hankalin, ya sha ganin yanda duniya take birkicewa mutane a fina-finai. Yau a gaske yake ganin yanda duniyar ta karkata ta juya da shi a ciki, kamar film haka wani gefe na kwakwalwar shi yake daukar hoton komai, kafin ya tsugunna a kasa cikin lemon daya zubar yana kama Mami, magana yake amman sautin muryar shi baya fita saboda tashin hankali.

Cikin Nurses din wajen ne wasu suka rugo dan su taimaka mishi, har aka dauke Mami yana tsugunne a wajen, Layla na zaune ko motsi ta kasa, tun tasowar shi duk wata damuwa tashi kafin Mami ta sani Abbu ya sani, ya saba abu koya kai ko bai kai ba ya nemi Abbu, shine babban abokin da yake da shi saboda mutum ne shi da yarda da mutane takewa wahala, shisa yanzun ma wayar shi ya laluba yana kiran Abbu.

“Abbu kazo Aminu Kano, Layla bata da lafiya.”

Ya iya fadi saboda kirjin shi da yayi nauyi, bayason fadama Abbu cewar Mami ta yanke jiki ta fadi, baima ji me Abbu yake fadi ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana sakata a aljihun shi. Yana wani irin sauke numfashi yake kallon Layla.

“Ciki gare ki Layla?”

Ya bukata yanajin maganar ta fito mishi kamar da wani irin yare, saboda kalamai ne da baisan yanda za ayi ace sun gifta tsakanin shi da kanwar shi ba, tsakanin shi da Layla, sai da ta dago kanta tana kallon idanuwan shi da suke rokonta da ta karyata maganar, ko da ta zamana da gaskene ta saukaka mishi tashin hankalin da yake ciki ta karyata. Amman bata san ta inda zata fara ba itama, ta dauka ta gama fahimtar menene shock, sai yau tasan da gaske komai zai iya tsaya maka cak, ciki harda emotions Dinka.

“Ciki ne da ni Hamma.”

Ta karasa maganar da dariyar da batasan ta inda ta fito ba, duk da kuwa tana jin idanuwanta cike suke taf da hawaye.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Jabir ya furta yana zama a kasa, cikin asibiti, batare daya damu da cewa cikin lemar lemon daya zube bane, balle kuma ya damu da cewa fararen kayane a jikin shi. Tarin tashin hankalin daya kunno musu yake hasasowa, MARTABAR SU da ta samu gurbata ta fannonin da ba zasu misaltu ba ke mishi yawo, rayuwar kanwar shi da ta canza har mutuwarta yake dubawa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 10

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 22Martabarmu 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×