Skip to content

Martabarmu | Babi Na Biyar

3
(2)

<< Previous

Kwanakin shi a lissafe suke, yana son makaranta, har kasan ran shi yana son makaranta. Yana kuma son karatu, musamman yanda Allah ya bashi baiwar kwakwalwa, da wahalar gaske ayi abu sau daya a gaban shi bai dauke ba. Kawai abu dayane ya kasa fahimta a shekarun shi goma sha bakwai yanzun a duniya. Duk lokacin da Abbu ko Ayya zasu nuna suna son abu, lokacin zaiji har ranshi babu abinda ya tsana sama da abin, yana so ya bari, yana so yaso abinda suke so ko dan yanda yake ganin halayen shi sun kasa raba zukatan su da tarin kaunar da sukeyi mishi.

Ya wuce Bilal da aji daya, amman zai iya tuna lokuttan da Bilal din yake daukar nashi litattafan ya duba ko an basu wani aiki da baiyi ba dan ya taya shi. Da gangan zai bar takardun shi babu rubutun komai, kawai dan yanda Abbu ya nuna yana bala’in kaunar su da karatu, bawai dan tambayoyin sun gagare shi amsawa ba. Ba a makaranta kawai hakan ya tsaya mishi ba, duk wani lamari na rayuwa da zamantakewar yau da kullum, kar dai Abbu ko Ayya su nuna ga yanda suke so, dan zaiyi abu daban da wannan din ne. Bai fara kawo sakamako mai kyau ba sai da yazo aji hudu a makaranta, ranar da kalaman Abbu suka tunzura shi.

“Nasan asarar kudina kawai nakeyi Rayyan, da ka daina zuwa makarantar nan zaifi mun, amman dai zanci gaba da biya dan in nunawa Yaya Ayuba cewa zancena gaskiya ne, babu abinda zaka iya ganewa indai bangaren makaranta ne.”

Daga ranar hatta Malaman shi mamaki sukeyi, irin yanda lokaci daya ya canza haka. Har kaguwa yayi lokacin jarabawa yayi dan ya kawowa Abbu, aikam na biyu yazo a ajin nasu lokacin. Da kan shi yazo ya nunawa Abbu, karba yayi batare daya nuna wani jin dadi a fuskar shi ba

“Dan kayi wannan baya nufin za’a dore.”

Shine kalaman Abbu, sune kuma kalaman shi a duk lokacin da zai kawo mishi wani abu daya danganci kokarin da yayi a makaranta. Tunda ko hira baya zama suyi, idan hirar shi tayi tsayi da wani to Bilal ne. Yanzun ma makaranta zasu tafi, harya gama shiryawa tsaf, amman Bilal ko wanka bai fito ba. Takalman shi ya dauko yana fitowa bakin kofa ya ajiye, silipas din da yake ajiye ya zira ma kafafuwan shi da nufin ya shiga bangaren Ayya ya dauko musu ruwa. Shi kayan sanyi ba damun shi sukayi ba, bama yaso sam, da an kawo pure water yake zuwa ya sungomo leda daya yazo dakin su ya ajiye. Ya duba ya kare shisa ya fito.

Yana karyo kwana suna cin karo da Layla da tsayin shi bai hana idanuwanta sauka cikin nashi ba.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Ya furta da karfi, zuciyar shi na wani irin dokawa, bayason ganin yarinyar sam, sai yaga kamar mage ce ta gitta mishi, yanzun ma ko ina na jikin shi bari yakeyi, har zuciyar shi.

“Ina kwana.”

Ta furta a hankali, duk da tasan ba amsawa zaiyi ba, zuwa yanzun da zata iya hana kanta gaishe da Rayyan ko shiga sabgar shi da ta daina. Amman duk abinda zata shirya ma kanta da ta sauke idanuwanta kan Rayyan din komai yake kwance mata. Kallonta yayi ran shi a bala’in bace.

“Dan ubanki ban hanaki zuwa inda nake ba? Mayya ce ke? Sau nawa zan gaya miki idan ina waje ki daina zuwa?”

Rayyan ya furta har lokacin zuciyar shi bata daina dokawa ba. Wasu irin hawayen bakin ciki Layla taji sun taru a cikin idanuwan ta, bashi bane mutum na farko daya kirata da “Mayya” ba, ba kuma shi bane zai zama na karshe, ko Ayya takan fada wasu lokuttan, su kadai ne suke fada a cikin gidan gabaki daya. A waje kuwa da wahalar gaske ka furta kalmar bata fasa maka baki ba, ta karfi da yaji ta zama mafadaciya ta gaske. Kullum saiya mata kashedin zuwa inda yake, amman a haka yake aikenta, a haka yakan sakata aiki, tana iya dawowa daga aiken shi ya hauta da masifar ta daina zuwa inda yake kamar bashi ya kirata ba. Har mamakin shi takeyi, sai kace mai jinnu.

Bata zabi zuwa duniya da kalar idanuwanta ba, asalima idan da an bata zabi zata dauki irin na kowa, bata kuma zabi fitowa daga jikin mahafiyar ta ba, balle a dinga alakanta su da Maita, kalma mafi ciwo a duniyarta gabaki daya.

“Hanya ce, kuma kowa wucewa yakeyi Hamma…”

Layla ta fadi itama nata ran a bace.

“Rashin kunya zakiyi mun?”

Rayyan ya bukata yana sata kallon shi da idanuwanta da bayaso, tana kara hautsina mishi lissafi, ita kadai ce ta raina shi haka duk gidan, ita kadai ce take kallon shi kamar bata tsoron shi, take kallon shi kamar shi din bai isa ba.

“Idan nace ba rashin kunya nai maka ba zaka yarda ne?”

Tayi tambayar tana sake tsare shi da manyan idanuwanta, kamar da take mishi da mage na kara bayyana, baisan lokacin daya dauketa da wani irin mari ba. Kafin ta wartsake ya kara dora mata wani duk a kunci daya. Ba marin shi bane ba ta saba sha ba, kawai a lokutta irin haka sai ta rantse da Allah a duniya babu wanda ya tsaneta sama da Rayyan, kullum kuma neman dalilin tsanar takeyi ta rasa.

“Matsa daga nan kafin in tattakaki, wawiya kawai.”

Rayyan ya karasa maganar da wani irin tsaki, yana saka hannu ya tunkudeta harta kusan faduwa tukunna ya wuce. Gabaki daya ta hargitsa mishi lissafi, da yasan zai ganta, sam ba zai fito ba, ruwan daya hakura saiya dawo makaranta sai ya dauka. Abbu yagani, ran shi a bace yake ko magana bai mishi ba ya raba zai wuce.

“Rayyan gaisuwar ma ba zan samu ba kenan yau ko?”

Baice komai ba ya shige abin shi, kai kawai Abbu ya jinjina. Da gaske ne jarabawa ta rayuwa takan zo ma bawa ta fanni daban-daban. Inda wani ya bashi labari tashi jarabawar zata so ta bangaren Rayyan ne ba zai taba yarda ba. Yana tuna kalar shakuwar shi da yaran a lokacin da yake dan karamin shi. Sai da ya dauka a cikin yaran shi gabaki daya mazan babu wanda zasu shaku dashi kamar shi da Haris, lokaci daya Rayyan ya sauya kamar wanda jinnu suka shafa.

Yanzun Rayyan ne zai nuna sam bayason magana da shi, zai karya idan yace abin baya mishi ciwo, yana kula da yanda idan ya nuna yana son abu to Rayyan din yaki abin kenan, kamar a duniya yana rayuwa ne dan ya bakanta mishi. Karatun shi ma sai da dabarar da Yaya Ayuba ya bashine da yai amfani da ita tukunna ya samu kan shi. Shisa ko da wasa yaki nuna mishi yana jin dadin yanda yake maida hankali. Yanzun ma ya kula sam ya daina jin ya Rayyan din yake ciki a makaranta. Ko wani abin akace su siya saidai Bilal yazo ya fada mishi.

Bai cika tashi tsayuwar dare ba, amman matsalar Rayyan tasa dare dai-dai ne baya tashi dan kawai yayi mishi addu’ar samun salama. Zuciyar da yake da ita tafi komai dagama Abbu a hankali, zuwa yanzun ko sallama akayi dashi a unguwa yasan ba zai wuce an kawo karar Rayyan din ba. Ko lokacin samartaka fada bai taba hadashi da wani ba, ammam sai gashi zuwan shi police station takwas duk akan Rayyan. Kuma ba yan waje kawai ya tsaya ba har cikin gida babu mai rabar shi, kusan kullum sai yayi ban hakuri cikin gidan akan Rayyan.

Yama daina mishi fada, nasiha ce wasu lokuttan, wasu lokuttan kuwa sai dai yabi shi da addu’a kawai, yanzun ma.

“Allah ya shirya”

Ya fadi yana wucewa. Rayyan kuwa dakin Ayya ya shiga, idan kasan gidan su a baya, kazo yanzun zakayi mamakin yanda aka gyara ginin yayi dai-dai da zamani, saboda rufin asiri dai-dai misali Abbu yana da shi. Ya taka matakin Professor kamar yanda burin shi yake, ga kasuwancin shi da Allah yake saka mishi albarka saboda shi mutum ne mai yawan taimako da kyautatawa iyalan shi. Shisa sam baya kukan rashi, rayuwa sukeyi mai natsuwa. Duk da tsayin shekaru bai canza zaman da yake tsakanin Maimuna da duka yaran suke kira da Ayya sai kuma Maryama da suke kira da Mami.

“Rukayya babu ruwa ne a dakin?”

Rayyan daya shiga kitchen ya duba bai gani ba ya fito falon yake tambaya. Da saurinta ta mike, har ranta tana kaunar Yayan nata, haka ma sauran yan uwan nasu, amman baya shiga cikin su, baya shiga sabgogin su, zatayi karya idan tace batajin kishin Bilal wani lokacin, saboda kusancin da yake tsakanin shi da Rayyan din. Ayya ba fada takeyi ba, amman sunsan cewa ba daga jikinta Bilal ya fito ba, saboda ko a makaranta da asalin sunan Baban shi yake amfani. Sai take ganin kamar ya kamata ace sunfi shi kusanci da Rayyan din.

Fridge taje ta duba tana dauko mishi leda daya na ruwa ta fito ta kawo, tun kafin ya karba yace

“Ba mai sanyi ba Rukayya… Bana son ruwa mai sanyi.”

Kai tadan rausayar, bai shiga cikin su bama balle su san me yake so ko meye baya so.

“Hamma duk an saka a fridge… Sai dai ko idan zaka ajiye ya huce…”

Karbar ruwan yazo yi

“Kabari in kai maka daki.”

Kai ya girgiza yana karba

“Zaka karya in hada maka tea?”

Kai ya sake girgiza mata, saboda ya fara jin maganar da sukeyi tayi mishi tsayi. Bayason kananun surutai marassa dalili

“Ko zaka ci wani abin”

Daga idanuwan shi yayi yana mata wani irin kallo daya sata komawa ta zauna. Kusanci take nema a tsakanin su ko yayane, kamar ko da yaushe bai bata wannan damar ba, zai fita daga dakin kenan Ayya ta fito daga dakin baccin ta.

“Rayyan…”

Ta kira tana saka shi runtsa idanuwan shi kafin ya budw su a hankali

“Ayya ina kwana…”

Ya fadi yana dan juyawa

“Kaci gidan ku… Daka shigo bakasan inda nake ba halan?”

Kai ya jinjina

“Ayya….ruwa kawai na zo dauka, ban san kin tashi ba kuma.”

Kallon shi kawai tayi, tasan karya yake, da bata fito ba sam ba zaije su gaisa ba. Idan zaiyi yini biyu bai sakata a idanuwan shi ba baya damuwa, Bilal ne idan shigowa goma zaiyi gidan saiya zo ya nemota, wani lokacin sai taga kamar yana son rage mata damuwar Rayyan ne, musamman idan yasan Rayyan din yayi wani laifi. Haka zai wuni yana lallabata kamar shi yayi mata wani abu. Kuma da gaske yana rage mata damuwa ba kadan ba.

“Allah ya shirya mun kai”

Cewar Ayya, Rayyan na ficewa daga dakin. Kan shi tsaye dakin su ya wuce ya ajiye ruwan. Dai-dai shigowar Bilal

“Yaushe zaka daina cin zalin yarinyar can ne? Kai baka duba maraicin ta?”

Dan fitowa yayi yaga Layla na tsaye tana hawaye, ga yatsun Rayyan kwance a kan fuskarta. Bai tambayeta me ya faru ba, hakuri kawai ya bata dan yasan a gidan babu wanda zai daketa idan ba Rayyan din ba. Duk idan kaga hawaye a idanuwanta to shine.

“Karka kara batamun rai Bilal…”

Rayyan ya fadi, shiru Bilal din yayi ya kyale shi. Idan ma surutu yayi yana iya kara jama Layla wani dukan. Duk saurin hannun Rayyan saika shiga harkar shi tukunna. Amman banda Layla, da alama ko numfashi tayi kusa dashi laifine. Har mamaki Bilal yakeyi, kuma ko aike Rayyan din zaiyi, gashi tunda yasan idan ya aike shi ba zaiki zuwa ba, takanas zai leka ya kira wani yaro cikin gidan ya bashi kudin yace a kai Layla ta siyo mishi, kuma da wahala aiken ya kare da dadi, dan sai ya nemi wani dalilin da zai daketa.

Kuma na rana daya bata taba kin zuwa aiken shi ba, duk wasu kananun ayyukan shi ita din yake sakawa. Shirin makaranta ya karasa suna fita tare da Rayyan din, su duka sabon sune sai sunje makaranta suke karyawa. Gara Rayyan ya siyi biscuit a hanya.

“Hamma kai da biscuit”

Bilal ya fadi yana dariya. Ba zaka taba raba aljihun Rayyan da biscuit ba, ko jakar makarantar shi ka duba zaka samu, kuma bayason mai zaki. Haka zai ta daukar abin shi dai-dai yana ci. Babu wanda baisan amanar da take tsakanin shi da biscuit ba, har Abbu wasu lokuttan yakan siyo sai ya baiwa Bilal din yace yaba Rayyan. Yanajin wani iri duk lokacin da Abbu ko Ayya zasu kyautatawa Rayyan din sai abin ya biyo ta hannun shi. Sai yake jin kamar suma zasuji ya kwace musu kusancin daya kamata ace yana tsakanin su da dan nasu.

“An hana ci ne?”

Kai Bilal ya girgiza mishi

“Kaima idan kana ci kasa hannu, ban hanaka ba ai.”

Kai dai Bilal din ya sake girgizawa, shi bama komai yake ci ba. Babur suka tare suna hawa su biyun zuwa makaranta daya kamar yanda suka saba.

***** *****

Bilal bai bude ledar da Aisha ta bashi ba sai da yazo gida. Harya natsu ma, duk gidan shi da Bilal ne suka fara makaranta daya daga firamari har yanzun suke sakandire a ALIC. Kuma yasan Aisha tun tana firamari, yana mata magana ne saboda tana mishi yanayi da Layla, daga rawar kanta har idan tayi dariya. Idan alewa yagani zai siya yakan siyi guda biyu ya bata daya. Aji dayane a tsakanin su, yanzun yana aji hudu ita kuma tana aji uku, kusan duk wanda yake ALIC yasan Aisha da Bilal. Danma shi wani lokacin yana tare da Rayyan, ita kuma tsoron Rayyan take ji, ba ita kadai bace, kusan duk wani wanda yake cikin makarantar tsoron Rayyan din yake ji.

Garama Aisha saboda Bilal yana dan mata magana wasu lokuttan. Amman idan baka ganshi da Rayyan ba zaka gan shi da Aisha. Wata irin shakuwa ce mai karfi a tsakanin su, zuwa yanzun har yan gidansu sun san Bilal, musamman wani lokaci da tayi rashin lafiya ta kwanta asibiti, yaje yafi sau biyar, hatta da Baban Aisha sai da yasan shi a lokacin. Da yake yana da wani irin shiga rai, haka cikin kankanin lokaci ya shiga ransu suma. Har wata Yayar Aisha din ta dinga tsokanar shi

“Bilal din Aisha…”

Murmushi ya dingayi saboda kunyar da ta dinga sakawa yanaji. Yanzun ma bude ledar yayi, biskit ne kala-kala da cin-cin, a cewarta bikin abokin wasanta akayi. Kayan bikin ne ta kawo mishi. Bayason kayan zaki haka, kawai dan Aisha ce shisa ya dauki cin-cin daya ya saka a bakin shi. Baiji shigowar Rayyan ba sai hannun shi da yagani cikin ledar yana daukar biskit guda biyu

“Kai ba zakai sallama ba”

Waje Rayyan ya samu ya zauna, kamar baiji maganar da Bilal din yayi ba

“Ina ka samo biskit kai kuma?”

Murmushi Bilal yayi

“Aisha ce sukayi biki, shine ta kawo mun.”

Kai Rayyan ya jinjina

“Yara kanana daku wai soyayya. Allah ya shirya.”

Yanayin yanda Rayyan din yai maganar ne ya ba Bilal dariya. Zaka rantse da Allah wata shekara goma ya bawa Bilal din ba daya da doriya ba

“Waye yace maka soyayya mukeyi?”

Tabe baki Rayyan yayi

“Zan fadama Ayya su fara shiri, ba zakai karatu ba, gara Abbu ya kaika kasuwa kawai a aurar da kai…ka kawo biskit din nan ko guda biyu a kai ma Ayya dan ta ga abinda surukarta ta bayar…”

Dariya Bilal din ya sakeyi yana fadin

“Hamma…”

Dariyar shima Rayyan yakeyi

“Jibi yanda idanuwanka suka cika da kunya. Bilal… Allah ya shiryeka to.”

Biskit daya Bilal ya dauka yana jifan Rayyan din da yake dariya dashi. Bai cika magana ba, amman randa duk ya saka shi gaba da tsokana sai ya rasa bakin ramawa. Musamman yanzun akan Aisha yafi samun damar tsokanar shi da yawa haka. Ko Rayyan din aka tsare ba zaice ga asalin yanda soyayya take ba balle kuma shi. Kawai yanajin Aisha har ran shine, baisan ko haka soyayya take ba, amman yasan ko dariya tayi sai ya ga kamar Layla, idan tana mishi surutunta ma, kominta yana mishi kamar Layla. Zai rantse lokutta da yawa har idanuwan Layla yake gani a cikin nata.

Shi dai yasan Layla ce dalilin kusancin shi da Aisha, Layla ce sanadin fara maganar shi da Aisha, idan akwai wani abu bayan wannan baisan shi ba. Saboda duka gidan Layla ce kawai take kula da ran shi ya baci, kowa kawai dauka yake ran Bilal baya baci, ba’awa Bilal laifi, ba zai manta ranar da tace mishi

“Hamma na rana daya ka nuna ranka ya baci, ka daina bari a cikin ka.”

Murmushin da yakan yi ko da ranshi a bace yake shi yai mata

“Waye yace miki raina ya baci.”

Dariya tayi

“Murmushin ka baya kaiwa cikin idanuwanka. Idan kayi murmushi ko kayi dariya harda idanuwan ka kakeyi, idan ranka ya baci idanuwanka basa dariya… Bansan ya zan maka bayani ka gane ba.”

Numfashi kawai ya sauke

“Me yasa ba zaka fadama Hamma Rayyan ya bata maka rai ba?”

Kai kawai ya jinjina mata. Kuma tun daga ranar ko a haduwa sukayi tai mishi magana yanayin murmushi zata ce,

“Waya bata ma Hamma Bilal rai?”

Ita kadai take ganewa, kuma ita kadai yakan fadama ran shi ya baci wani lokacin. Ayya damuwar Rayyan kawai ta isheta, shisa baya taba nuna yana cikin matsala, ko rashin lafiya saiya kwanta sosai da sosai ake ganewa. Sai yayi ciwo a tsaye ya warke babu wanda yasani sai Layla. Yanzun ma mikewa yayi yana ficewa daga dakin, wata irin yunwa yake ji, bangaren Mami zashi yaga ko ta dafa wani abin da yake ci, tuwo Ayya tayi miyar taushe, bayason dafaffiyar albasa, ko a dafaduka aka saka saiya tsince tas yake iya cin abincin. Yanzun tunda Rayyan ya zuba yaga tayi yawan da baisan ya zaiyi ya tsince ba, shisa ya hakura ya fito kawai.

Bai karasa bangaren Mami da yake lallabawa kar Ayya tagan shi ba, yasan bataso yana cin abincin Mami din, amman zuwa yanzun sai dai ta bishi da ido kawai, tunda taga ba zata iya hana shi ba, shine abu guda daya da Bilal ya taba gardama mata a kai, ta hana shi yaki hanuwa, amman kome zatace yayi baya taba nuna mata bayaso ko a fuskar shi kuwa. Layla yaci karo da ita.

“Hamma…”

Ta furta da fara’a a fuskarta

“Me kuka dafa Layla?”

Bilal ya tambaya

“Wake da shinkafa ne, akwai miya. Amman yayyanka kayan miyar Mami tayi, bari ingani dai…”

Ta furta tana juyawa ta koma ciki, ta kai mintina kusan goma kafin ta fito da filet a hannunta da abinci harda cokali a ciki.

“Na ciccire albasar, amman saika duba akwai kadan a ciki…”

Karba yayi yana murmushi

“Ni nace bana cin albasa?”

Dariya Layla tayi

“Ba saika fada ba, kana barin shi a plate din abincinka da yawa….”

Wannan karin shi yayi dariyar

“Ke kam Allah ya shiryeki”

Yanajin dariyarta harya wuce, tun a hanya ya fara cin abincin saboda yunwar da yakeji, harya karasa daki

“Kai ba zaka daina cin abincin matar can ba, Ayya ta hana, sai an barbada maka abu tukunna ko?”

Saida Bilal ya hadiye abincin da yake bakin shi tukunna yace

“Abu nawa Ayya ta hanaka baka daina ba? Kuma kasan zato babu kyau ko a addini…”

Cewar Bilal din yana kara cakuda abincin hadi da diba ya saka a bakin shi.

“Ni daban, kai daban, bana so kana cin abincin ta, amman ba zaka jini ba.”

Shiru yayi ya kyale Rayyan din, idan wannan maganar ce sun saba, Ayya tagaji, shi dinne ya kasa hakura har yanzun. Duk cikin karatun duniya da ake mishi babu wanda ya rike da kyau irin cewa Mami zata barbada mishi abu yaci. Abincin shi yaci gaba daci kan shi a tsaye, yana ganin Rayyan din ya mike ya dauko uniform din shi da safa.

“Wanki zakayi?”

Kai Rayyan ya girgiza

“Me yasa zan wanke, Layla zata wanke mun.”

Yanda yayi maganar zaka rantse da Allah Layla din yar aiki ce a gidan ba ‘ya ba.

“Layla baiwar kace? Me yasa kaci ka takurama yarinyar nan ne wai?”

Kallon shi Rayyan yayi

“Me yasa ita bata damu ba sai kai?”

Kai kawai Bilal ya jinjina, yana kallon Rayyan din ya fita. Ba shiga bangaren Mami yakeyi ba, idan ba wani yaron zai daka ya ruga ya shiga bangaren nata ba, itama sam bata shiga harkar shi tunda rashin kunya yake mata kamar zai daketa.

“Layla!”

Ya kira, itama sai lokacin da ta zubama Bilal abinci ta samu ta zuba nata, tana zaune da remote a hannunta da ta kasa tsayawa waje daya taji ya kwala mata kira.

“Rayyan ne ko?”

Mami ta tambaya, duk da muryar su shida Bilal din ba ko yaushe ake banbance taba, amman tasan idan Bilal ne zai shiga har ciki, ba zai tsaya daga bakin kofa yana kwala ma Layla kira haka ba. Cokalinta ta mayar cikin abincin tana mikewa, marin da yayi mata yau da safe ta fadama kanta tana zaune zai zo nemanta, zatayi banza da shi, haka ma tacewa Mami data shiga tana kuka.

“Ina zaune zai kirani, kinsan Allah Mami ba zanje ba nima, kowa yayi harkar shi.”

Murmushi kawai Mami tayi, ita yanzun ta daina tsoma bakinta a tsakanin su. Tun tasowar Layla idan Rayyan din yai mata wani duka har ranta Mami take ji, tayi fada da Ayya yafi a kirga kan cin zalin Layla da Rayyan yakeyi. Sau biyu ta taba kaiwa Abbu kara, duka lokutta biyun kuma tana shan kunya, dan ko muryar Rayyan din Layla taji da gudu take fita, sai ta dauki ido kawai ta saka musu. Yanzun zata shigo tana kuka shabe-shabe, tana fadar yanda ita da Rayyan sun raba hanya, sai ya aiko kiranta ta ajiye koma meye takeyi ta tafi.

Kamar yanzun da ta ajiye abinci, jikinta har kyarma yakeyi ta fita.

“Ki wanke mun”

Ya fadi yana ajiye uniform din a kasa

“Yanzun idan na gama cin abinci”

Kallonta yayi

“Idan ba zaki wanke mun ba ki fadamun, tun dazun bakici abincin ba sai yanzun?”

Kayan ta tattara tana turo labbanta gaba, ta wuce ta koma ciki, tana jin tsakin da Rayyan din yayi. Sai da ya dafe kirjin shi duk da yayi kokarin ganin bai hada idanuwan da ita ba, amman sai da taja zuciyar shi ta doka. Ita kuwa cikin daki ta shiga

“Ni fa zan taimaka in wanke mishi Mami, amman shine wai ba zan gama cin abincina ba, zaiyi fushi ya dauka”

Murmushi kawai Mami tayi tana kallon Layla harta wuce da wankin tana kuma cigaba da mita.

“Allah ya kyautata kaddarar da take tsakanin ku Layla. Allah ya kare maraicin ki”

Shine addu’ar da Mami take bin ta da ita a lokutta irin haka. Har tsoro takeji idan taga sunyi wani abin ita da Rayyan. Ko yara batajin suna cewa Hamma Rayyan ya basu abu, amman wani lokacin zakaga Layla da abu kuma tace shi ya bata. Har kudi a cikin aljihun makarantar shi duk idan ya bata wanki

“Ki mayar mishi da kudin shi”

Mami kance idan ta nuna mata ta tsinta, amman sau biyu ta gwada tana shan maruka, yana fada mata yanda bayaso tana zuwa kusa da shi.

“Hamma zai sauke Jujun shi a kaina Mami.”

Ta bawa Bilal kuma sau biyu shima ya mayar mishi, saiya Bilal din ya dawo mata dasu yace mata ca yayi ta rike, yana sane yake bari, ba zai bata da hannun shi bane ba. Ba kuma zai bude baki yace ta dauka ba. Shisa har a ranta Mami tana tsoron kaddarar da take tsakanin Layla da Rayyan din. Bata da wanda zata furtawa ne kawai, tunda ita ba wasu kawaye gareta ba, sirrinta yana cikinta, gara ta zanta damuwarta da Haris da ta fadawa wani can. Shikuma yanzun ya sami gurbin karatu a Zaria, duk da yakan yi kokarin zuwa wani lokacin duk karshen wata, idan karatu yayi tsanani kuma sai yakai wata uku ma bata saka shi a idanuwanta ba.

Tana nan zaune, sai da Layla ta gama wankin tukunna ta dawo ta zauna tana daukar abincin

“Har abincina yayi sanyi”

Ta furta cikin yanayin mitarta

“Ki dumama”

Cewar Mami, kai kawai ta girgiza

“Nifa bama na son wanki, Mami kinsan bana son wanki, shine Hamma yake sakani” Murmushi kawai Mami tayi, indan Layla ce ba gajiya takeyi da mita ba musamman akan Rayyan. Haka ta gama cin abincin tana mitar ta tashi ta wuce kitchen, kwanonin ba yawa garesu ba, ta daifi so ta wanke, sam batason aiki a kanta. Duk da akwai miya da yawa, Mami tace ko taliya sai a kara dafawa, gara tayi wanke-wanken saita fi jin dadin zama tayi kallonta a nutse.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×