Skip to content
Part 2 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

May 1985, Kano

Da gaskiyar iyaye da kance kukan yaro yafi komai daga hankali, har kasan ranta take jin kukan Rayyan, a gaggauce ta karasa wankan, sabonta ne sai ta saka hijabi idan ta daura zani sannan take fitowa daga wanka, kamar yanda takan shiga da ita. Amman yanzun kam haka ta fito, hijabin ma a bandakin ta baro ta. Ganin ta lallaba Rayyan din yayi bacci shisa ta lallaba tadan watsa ruwan ta fito, ashe ba nisa baccin yayi ba. Tana daga labulen gabanta nayin wata irin mummunar faduwa ganin Maryama data mika hannu tana shirin daukar Rayyan

“Me kike kokarin shafa mishi?”

Ta furta tana karasawa da sauri ta hankade Maryama da take tsaye. Sallar la’asar ta idar, tana zaune tana jan casbi kamar yanda takan wuni tanayi, ko karanta wani littafin da take tunanin zai amfani rayuwarta tunda ta shigo gidan. Da yake da ta gama firamare tayi makarantar kwana har aji uku, da maganar auren su da Ahmadi a kanta ma ta karasa aji ukkun. Bata tsammaci tarbar kwarai a wajen Maimuna ba, amman tayi mamakin kalar kiyayyar da take nuna mata kamar itace mace ta farko data fara shiga gidan aure a matsayin mace ta biyu. Ba zata manta ranar da aka shiga da ita dakin Maimuna watanni ukku da suka shige dan karrama Maimuna a matsayinta na uwargida kamar yanda tsarin al’ada yake.

Sam bata ga fuskar Maimuna ba tunda kanta a rufe yake kasancewarta amarya. Kalaman Iya Asabe da take fadin,

“Wanda duk yake a dakin nan yasan halin da kike ciki, dan kishiyar nan anyi mana, wasun mu fiye da daya. Sai anyi hakuri, ko da babu tsira mai nisa tsakanin ki da Maryama kanwa ce a wajenki a gidan aure. Saboda haka ga amanar ta…”

Iya Asabe bata karasa maganarta ba Maimunar ta katse ta da fadin,

“Iya ki takaita kalamanki, indai amanar Maryama ce ban dauka ba, karku doramun nauyin da ba zan sauke ba…”

Daga inda Maryama take zaune tana jin salallamin da duk wanda yake cikin dakin yakeyi cike da mamaki.

“Inda amana ba zaku rako Maryama dakina ba wallahi, ba zaku dauketa ku liqawa Ahmadi ba…”

Ba zata manta yanda taji takun tafiya ana barin dakin daya baya daya ba. Har Iya ta kamata suka fice saboda yanda Maimuna sam taki sauraren nasihar da Iya taso tayi mata, tana barinta da furta,

“Allah ya saukaka.”

Kafin su fita daga dakin. Maimuna bata canza kalamanta ba ko bayan da Ahmadi ya hadasu da sunan yi musu nasiha.

“Ka dauki matarka ku fitar mun daga daki Ahmadi, ku fita ba sai kun haskamun yanda zaku kasance da juna tsayin daren yau ba, wallahi hakurina yana gab da karewa…”

Maimunar ta karasa maganar da rawar Murya alamar kukan da take kokarin tarbewa. Ita kam zatace firgicin da ta tsinci kanta ya girmi wanda kowacce mace take tare dashi a darenta na farko. Daga ranar kuwa har yau babu wata magana ta arziqi data hadata da Maimuna, banda mugayen kallo da takan watsa mata duk idan ta wuce, tana jin labaran kishi, amman na Maimuna daban ne, ga yan uwanta da taga alama wajen zaman jegon Rayyan suna tayata.

Ba tsoron biye rigimar da Maimuna takan takaleta da ita a duk rana takeyi ba, kalaman Ahmadi ne suke tausarta.

“Da bana sonki ba zan aureki ba Maryama, kamar yanda kauna ce tasani auren Maimuna kema haka. Idan ina da mutunci a idanuwanki zaki tayani kaucewa rigima da Maimuna, dan Allah ki kauda kai daga lamurranta, ki tayani wanzar da zaman lafiya a tsakanin ku gwargwadon iyawarki”

Tun kafin zama karkashin inuwar aure ya hadata da Ahmadi ta tabbatar da nagartar shi. Ta dauka tasan soyayya a iya tsayin lokacin da suka dauka kafin auren su, sai yanzun take ganin banbanci. Yanda Ahmadi yake kula da ita, yake gudun duk wani abu da zai sosa ranta ya kara daga daraja da matsayin shi a zuciyarta. Saboda shi zata cigaba da kauda kai daga halayen Maimuna har Allah ya fahimtar da ita cewa su dukansu zaman aure sukeyi, kuma ita da niyyar mutu ka raba ta shigo gidan, babu inda zata tafi.

Shisa take kokarin ganin bata shiga harkarta ba, bata taba ganin gidan da keda kishiyoyi kowa na abincinta daban ba tun tasowarta sai a nasu gidan. Ta dafa sau biyu, ba zatace ga abinda ya faru ba, Ahmadi ya ce mata kowa abincin shi zai dinga dafawa, abin har yanzun wani iri yakeyi mata. Ga yaran Maimuna da shiga rai, musamman Zubaida, ko dan Ahmadi har ranta take jin yaran. Kiri-kiri Maimuna ta hana mata rabarsu, ko inda take basa zuwa, buta wannan idan tata ce basa tabawa, in ta dan samu sunje kusa da ita to Ahmadi ya dawo gidan, kuma ranar itace da girki, shima kome zata basu kai suke girgiza mata a tsorace.

Yau ma kukan Rayyan da take tajine yai mata tsaye, taso ta share, amman taji shigar Maimuna bandaki, kuma tasan sauran yaran suna makaranta. Tunanin ko an dora shi a samane ya fado shisa yake wannan gigitaccen kukan yasata tashi ta shiga bangaren Maimuna din, komin yanda basa ga miciji yaron baisan me duniyar take ciki ba balle zafin kishi irin na mahaifiyar shi. Tana shiga taga kuwa wajen mitsilniya yaja zanin shimfidar ya nade fuskar shi da shi, samu tayi ta cire mishi, ta gyara ne zata dauke shi taji shigowar Maimuna, bangazar da tayi mata da babu bango a kusa zata iya faduwa. Rayyan din Maimuna ta dauka tana saka shi a jikinta hadi da jijjiga yaron.

“Kashe mun shi zakiyi Maryama? Meya kawoki dakina?”

Kalaman Maimunan taji har ranta, sun mata zafi matuka.

“Wacce irin magana ce wannan? Kukan shi naji yayi yawa, kuma naji kamar kin shiga bayi shisa nazo in duba.”

Cike da rashin yarda Maimuna take kallonta, Gwaggo Bare tayi mata kashedi karta bar Maryama na rabar mata yara, kafin ta shafa musu abinda in rayuwar su bata salwanta ba za’a sabauta su. Yanda tayi nasarar mallake Ahmadi ba zata bari tayi nasara a kanta ba sam. Karfi da yaji jituwa ta musu karanci tsakaninta da Ahmadi, laifinta yake gani yanzun a duk wata karamar magana da zasuyi. Ranar da aka daura mishi aure da Maryama ne rana mafi muni da tashin hankali a rayuwarta. Ba zata manta bayan fitar su shi da Maryama daga dakin yanda ta dafe cikinta tanajin kamar zai fito duniya ranar saboda yasan kalar tashin hankalin da take ciki.

Kwanciya tayi a kasa tana sakin wani irin gunjin kuka zuciyarta kamar zata fado, a haka Ahmadi ya shigo dakin yana kamata.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Maimuna me kikeyi haka? Dan Allah ki rufamun asiri, kinga bake kadai bace ba… Kiyi hakuri, kiyi hakuri kisawa ranki salama, inda nasan kishinki yakai haka wallahi dana hakura da auren nan… Oh Allah na.”

Yake fadin yana sake riketa a jikin shi ganin yanda numfashinta har sama-sama yake saboda kuka.

“Wata zaka raba, Ahmadi wata zata dandani soyayyarka yau, dan Allah karkaje, karka hada mun jikinka da nata, karka cakuda kaunata data wata, Ahmadi mutuwa zanyi Allah idan nasan a wajen wata zaka kwana.”

Maimuna take maganar kamar bata cikin hayyacinta. Har yau ba zatace ga yanda akayi ya sulalace yabar dakin ba, bama zata tuna ko ta runtsa ko bata runtsa ba, a satin farkon nan ta wahala. Tayi mamaki da mata suke kiran nakuda tafi komai ciwo a sha’ani na rayuwa. Zata zabi haihuwa goma a jere indai za’a koma baya a goge Maryama daga rayuwar Ahmadi, ko haihuwar Zubaida data kwana hudu cikin matsananciyar nakuda kamar ba zatai rai ba bai kai mata zafin ciwon da takeji a zuciyarta duk idan Ahmadi ya kasance a dakin Maryama ba.

A kwanakin bakwai bata tsaya tasan me suke ci shida Maryama ba, dan batai mishi karyaba washegari daya shigo mata daki kamar bai hada shimfida da wata ba.

“Idan abin kari kake jira zaku wuni da yunwa daga kai har ita, wallahi zan zabi mutuwa akan in dafa abincin da Maryama zataci.”

Da suka kwana bakwai ma ta karbi girki ko lafiyar kirki bata da ita, tana ganin Maryama da salo dan ta zuba mata wani abu tace zatayi girkin. Su Zubaida gidan Yaya Ayuba ta turasu sukaci abinci, itama daga can din aka kawo mata, washegari da taga ta shiga ta dafa tazo tayi mata maganar da ko amsa bata iya bata ba, Ahmadi na dawowa ya shiga dakinta da ya duba karfin jikinta tace mishi.

“Ba zan iyacin abinda duk ya fito daga hannun matarka ba, yarana ma ba zasuci ba ballantana a barbada mana abinda aka baka aka mallake ka.”

Yanda yake kallonta rai a bace bai ko girgizata ba.

“Maimuna yaushe ne zakiyi sanyi akan maganar Maryama? Da kika taso gidanku abinci kikaga an raba? Me yasa nine zan fara wannan al’adar dan kawai kin dauki zafin kishi kin saka a ranki.”

Batasan ko yanda ya nuna dan Yayya tayi hakurin zama da kishiya itama ya zame mata dole tayi wannan bane a fakaice ya taba zuciyarta, ko kuma maganganun da yake mata a fadace saboda Maryama sune suka tunzurata ba, amman bataso hawayen da suka zubo mata ba.

“Ni dai na fada maka, kai za’ayiwa asarar abinci saboda wallahi ni ba zanci ba…”

Runtsa idanuwan shi Ahmadi yayi yana bude su a kanta.

“Idan akayi hakan shikenan? Idan kowa ya dafa abincin shi yayi miki?”

Kai ta daga mishi, bai sake furta wani abu ba yasa kai ya fice daga dakin. Idan fushi yayi ma shiya jiyo. Ita kama tasan ba zataci duk wani abu da zai fito daga bangaren Maryama ba, su Khalifa ma daki ta sakasu taja kunnen su akan Maryaman ganin yanda take wani jansu a jiki. Dan Zubaida ma ca tayi mata Dodo Maryama take zama da dare, idan ta karbi abin hannunta zata zo ta cinyeta tana bacci. Yaran kuwa har ransu suka dauki hudubar mahaifiyar tasu.

“Bana so, karki sake shigomun daki, idan siqewa kikaji yanayi bance ki taimaka mishi ba….idan burgeni kike sonyi Maryama dan girman Allah ko numfashi karkiyi kusa dani…”

Murmushi mai ciwo Maryama tayi, wani bangare na zuciyarta takeji a gajiye da halayyar Maimunar.

“Duk yanda bakyason ganina Ahmadi ya hadamu…”

Ido a bude Maimuna take kallonta.

“Magana zaki fadamun? Dakina zaki shigo ki fadamun magana?”

Wani murmushin Maryama ta sakeyi da yasa Maimuna takeji kamar ta dauketa da mari, kafin ta kai hannu a cikin ta tana shafawa, haka kawai yau sai takejin tana son bakantawa Maimuna rai ko yayane.

“In Allah ya yarda na dan yan watanni da nawa a hannuna.”

Tana karasa maganar ta juya da shirin fita daga dakin, tanajin tsakin da Maimuna taja a fili.

“Aikin banza aikin wofi, sai kin haifo ukku a tare zan san dai-dai kikejin kanki dani a cikin gidan nan.”

Labulen Maryama ta daga tana ficewa daga dakin, Rayyan da yayi shiru a jikinta ta mayar kan bayanta tana daukar zani ta goyashi. Zatayi karya idan tace bata girgiza dajin cikine a jikin Maryama ba, duk da bata saka idanuwa akan lamurranta, ko yawu bataga ta tsartar ba. Ta rasa dalilin da yasa maganar take daga mata hankali haka, nan gefen gado ta zauna duniyar nayi mata shiru. Yara uku ba wasa bane, ko da ukkun Maryama ta ajiye a gidan Ahmadi ba masu shekaru kamar nata ba, tunda ko yanzun tana morar yaran nata da dauke mun wannan, mikon mun wancen. Amman batason kwan Ahmadi a cikin wata macen, batason ya daga idanuwan shi ya kalli wasu yara a cikin gidan nan banda nata.

Malamin Khadi ma ba haka ya buga mata kasa ba.

“Ki kwantar da hankalinki, ba wani dadewa zatayi a gidan ba tunda ba wai son gaskiya Ahmadi yake mata ba, kuma yanzun haka sati mai zuwa aljanun da Malam ya aika can kasar Masar zasu dawo da hadin turaren da zai karya sihirin.”

An kuma kawo mata turaren da ta yarfe gadonta da shi Ahmadi ya kwanta, duk wani magani da aka bata tayi amfani dashi tayi, amman ko ran girkinta Ahmadi ya leqa Maryama idan tayi magana saiya nuna rashin jin dadin shi.

“Kema ina zuwa dubaki ranar nata girkin, me yasa abin magana baya miki wahala?”

Haka yace mata kwana uku da suka wuce, ganin washegari Maryaman zata karbi girki, kuma ya yini zir baya gidan, ta dauka ba zai kwasar mata mintina cikin lokacinta da sunan duba Maryama ba.

“Namiji kenan…”

Maimuna ta tsinci kanta da furtawa, ashe ciki Maryama take dashi amman ko da wasa Ahmadi bai furta mata zancen ba, sai yayi shiru abin shi, watakila da bataji a bakin Maryama ba sai ya nuna kanshine zata gani. Ahmadin ta da komai ya danganci rayuwar shi itace ta farkon sanin shi, da ita yakan shawarta sanar da Yaya Ayuba ko Nasiru wani lokacin. Rana daya wata ta shigo tsakiyar su da hakan.

“Allah ya kwashe miki albarka Maryama.”

Ta sake furtawa hawaye cike taf da idanuwanta, duk mazan duniya ta rasa wa zata kyalla idanuwa a kan shi sai Ahmadi.

***** *****

Da yake yau girkin Maimuna ne, kai tsaye dakinta Ahmadi ya wuce bayan ya dawo sallar Isha’i. Ya siyo kankana, da kan shi ya tashi ya fita zuwa kitchen ya dauko faranti da wuka ya dawo ya zauna.

“Ina Khalifa da Zubaida? Ba dai sunyi bacci ba.”

Kai Maimuna ta girgiza mishi.

“Yau ma gidan Yaya zasu kwana kenan.”

Ahmadi ya furta da murmushi a fuskar shi kafin Maimuna ta sami damar fada mishi, yanajin dadin kusancin da makotakar su da Yayan shi ta wanzar tsakanin yaran su. Shi kanshi ma yanzun ma sai sukai karfe tara a waje da Yaya Ayuban suna hirar su wasu lokuttan. Hakan ba karamin dadi yake mishi ba, a lokuttan da Maimuna ta hada mishi zafi sai yaji zuciyar shi ta sanyaya idan sunyi hira da Yayan. Duk da bayason rage mutuncinta a idanuwan dan uwan nashi, shisa ko da wasa bai taba gwada fadar laifinta ba ballantana ya nemi shawara.

Duk fadan da zasuyi, sukan shirya, kuma yana yafe mata ko da bata nemi hakan ba, son da yake mata mai girmane. Yana gudun kar ya fadama Yaya Ayuba wani laifin Maimuna din, shi yazo ya yafe mata, Yaya Ayuban na kallonta da abin, sam ba zaiji dadi ba. Kankanar ya raba gida uku, ya dauki kashi daya ya saka a ledar, yanda yake jin wata irin gajiya jar a kasusuwan jikin shi yau zaiso ace zai iya baiwa Maimuna kankanar dan ta mikawa Maryama. Amman mitarta zatayi karshe harda rashin kunyar da ta koyi yi mishi tace ba zata kai ba. Shisa ya mike da kan shi yana kuwa cin sa’a Maryaman ta fito rike da buta a hannunta, murmushin nan nata tayi mishi.

“Maryama…”

Ya furta cike da jin dadin ganinta, yana mika mata kankanar da ta ajiye butar hannunta tana dan tsugunna ta saka hannuwa biyu ta karba cike da girmamawa.

“Allah ya saka da alkhairi. Sannu da kokari.”

Murmushin shi Ahmadi ya kara fadadawa.

“Ya zazzabin? Yayi sauki ko?”

Ya tambaya kamar dawowar shi bai dubata ba, kulawar shi daban take.Kai ta daga mishi cike da jin nauyi, tunda taga har wannan watan bata ga al’adarta ba, ta tabbatar da zarginta na cewa ciki take dauke dashi, ba wani canji takeji a jikinta ba, banda yawan kwadayin abinci mai manja, sai zazzabi da takan kwana dashi wani lokacin, amman lafiya kalau take jinta, wasu amaye amaye ko tashin zuciya duk Allah bai daura mata ba. Tana taso ta fadama Ahmadi zargin da takeyi amman nauyin hakan takeji sosai, banda yau da kishi yasa tayi ma Maimuna burga da cikin, ita kadai tasan da abinta.

“Sai da safe, kisha maganin da na siyo indai kinji ya dawo, da safe sai mu fita a dubaki asibitin wajen aikin mu.”

Kai ta iya jinjina mishi.

“Allah ya hutar da gajiya.”

Ta furta tana juyawa daki, labule kawai ta daga ta ajiye ledar kankanar ta dawo ta dauki buta, kasala takeji yau sosai, dan tun taliyarta data dafa da manja ce da tayi saura taci da daren nan. Kan kunnenta aka kira isha’i tana kwance tana juye-juye a daki sai yanzun Allah yai mata fitowa. Alwala ta daura ta koma daki abinta. Ahmadi ma dakin Maimuna ya koma, yana karbar Rayyan daya saka babban yatsan shi a baki yana ta tsotsa.

“Gaka da alamomin hakuri amman sai rikici ko?”

Ahmadi yai maganar kamar yaron zai fahimci me yake cewa, Maimuna da ta sakko kasan itama ta dauki wuka tana karasa gyara kankanar daya yanka, ta dauka tana mika mishi, hannun shi ya duba saboda yayi gaishe-gaishe da mutane.

“Ban wanko hannu ba.”

Dan kara matsawa tayi tana fara zare kwallayen jikin kankanar ta mika saitin bakin shi daya bude ta saka mishi a ciki, taunawa yayi yana jinjina kai.

“Wai… Daman yace mun me kyau ce wallahi, dana sani kwallo biyu na siyo…”

Kallon shi Maimuna ta.ke.yi.

“Da zaki? Naga batai ja ba sosai.”

Ta karasa tana sakawa a bakinta itama, sake gyara wata tayi tana kara ba Ahmadi.

“Aikam da zaki…”

Cewar Maimuna, kafin Rayyan daya fara mutsilniya a jikin Ahmadi yana kwakkwabe fuska yasata furta,

“Wallahi karka dagamun hankali, na rasa inda ka kwaso rigima.”

Dariya Ahmadi yayi.

“Me kake nufi?”

Ta furta tana kallon shi, kai yake girgiza mata yana kawo bakin shi ganin ta gyara kankanar da ke hannunta, a nata bakin ta lunkuma.

“Ka wanko hannuwanka ka sha da kanka, so kake kace ni ya biyo da alama.”

Dariya yake sosai, dariyar da ta kwana biyu bata gani ba, gyara Rayyan yayi yana amfani da dayan hannun shi ya riko nata da take kokarin kwacewa tana dariya. Yayi kewar wannan rahar a tsakanin su, yayi kewar matar shi, kallonta yake da wani yanayi a fuskar shi.

“Nayi kewar ki.”

Cikin idanuwan shi ta kalla, ita kadai ce macen da take iya hada idanuwa dashi kai tsaye haka, har maza kance yana musu kwarjini, ko Maryama bata iya kallon shi haka. Maimuna kan ce,

“Kai din nawa ne, nawa ne ni kadai Ahmadi.”

Kuma ya yarda shi din nata ne, duk da bai kasance nata ita kadai ba kamar yanda taso, amman natan ne.

“Kaji ka, abinda muna tare a gida daya ko da yaushe, me yasa kake magana kamar ka dade baka ganni ba?”

Numfashi mai nauyi ya sauke.

“Dan Allah mu daina fada, ki daina mun rigima, mu koma zaman mu kamar da.”

Murmushi tayi kawai, murmushin da yake ganin kamar yana da wata manufa data wuce nishadi. Haka suka kasance daren kamar satin amarcin su, har wajen biyun dare, da Maimuna lafe a jikin shi suna bacci. Da yake shi bamai nauyin bacci bane, kwakkwaran motsi ma yakan ji, cikin baccin yake jin kakarin aman da ya sashi bude idanuwa yana saurarawa, sosai yake jin ana kakarin, yaso zame Maimuna a hankali ba sai ta tashi ba dan ya fita ya duba, amman itama din ba nauyin baccin gareta ba.

“Ina zaka je?”

Ta furta muryarta cike da bacci tana murza idanuwa.

“Kamar Maryama ke amai, bakiji bane ba?”

Ya amsa kasa-kasa saboda dare, tsaki Maimuna ta ja.

“Munafuncine kawai, dan Allah ka koma ka kwanta.”

Da mamaki yake kokarin ganin idanuwanta saboda duhun da yake dakin. Rigar shi da yake tunanin tana ajiye wani waje kan gadon yake lalube har ya samota, kokarin sakawa yake a jikin shi Maimuna ta tashi zaune.

“Fitar zakayi kenan?”

Ta bukata a harzuqe, hakafa kwanaki ta fito tana wannan kakare-kakaren, Ahmadi ya kwana zarya yana fita dubata. Shine yau daga dawowar shi dakinta zata sake bullo da wannan sanaben

“Kasan dai yau kwanana ne ko? Halin matane baka sani ba Ahmadi? Munafuncine ba wani abu ba.”

Kai kawai ya girgiza yana sauka daga kan gadon.

“Bari in dubata….”

Itama saukowa tayi, zuwa lokacin idanuwanta sun saba da duhun tana dan ganin shi, aikuwa hannu yaji ta riko mishi.

“Babu inda zakaje fa, kanajin ma kamar ta koma daki. Wannan ai shiga hakki ne.”

Fisge hannun shi Ahmadi yayi.

“Me yake damunki ne wai? Ina tausayinki ya tafi? Ko ta tafi daki bazan duba yarinyar mutane bayan naji sarai amai tayi ba? Kinga Maimuna ki fita idona kafin in saba miki.”

Ya karasa yana fara tafiya zuwa hanyar kofa, yanajin ta biyo shi, baibi takanta ba ya fice daga dakin, hasken farin wata ya haske tsakar gidan, ko takalma bai saka ba ya nufi bangaren Maryama, yana shiga ya sameta a zaune da fitilar kwai a dakin.

“Maryama? Jikin ne?”

Kai ta girgiza mishi.

“Aa wallahi. Amai ne kawai, inajin kankanar dana sha na kwanta ce ta juya mun ciki.”

Kuma da gasken take, dan karatun littafin tarihin Annabi (SAW) Kamalalle takeyi bacci ya dauketa anan kasa inda ta saka filo, kawai farkawa tayi tana zufa, kafin taji wani amai ya taso mata, dakyar takai tsakar gida. Duk wani abu da yai saura a cikin nata kuwa saida ta fitar dashi, kuma garas take jinta banda yar galabaita da tayi. Ahmadi bai yarda da ita ba, tsugunnawa yayi yana saka hannu ya taba wuyanta ko da zazzabi, amman lafiya kalau yaji jikinta.

“Sannu…”

Murmushi Maryama tayi.

“Yawwa… Kaje ka kwanta, kaga da safe zaka fita, gara ka huce gajiya.”

Kallonta yakeyi yana son tabbatar da lafiyarta.

“Babu wani abu da yake miki ciwo dai ko?”

Kai ta jinjina mishi.

“Kin tabbata? Ki fadamun dan Allah.”

Murmushi takeyi sosai.

“Allah babu inda yake mun ciwo…dan Allah kaje ka kwanta.”

Numfashi Ahmadi ya sauke.

“Shikenan, Allah ya kara lafiya, idan da wani abin dai kizo ki tasoni kinji ko? Allah ya tashe mu lafiya…”

Kai Maryama ta jinjina mishi, tana kara ganin dalilin da yasa kaf dangi kowa yakejin daman yar shi ce a gidan Ahmadi, ba zata gaji da godewa Allah da wannan damar da ta samu ba, har zai fita ya kara juyowa.

“Ko in miko miki ruwa?”

Kai ta girgiza mishi tana nuna kwanon sha da yake a rufe.

“Kagan shi nan na dibo fa tun dazun…”

Sannun dai ya sake yi mata kafin ya fita, ya gyara mata labulen dakyau saboda sauro. Kafin ya wuce inda ya samu Maimuna a bakin kofar dakinta tsaye.

“Idan cin amana dai kasa a gaba babu inda zai kaika wallahi.”

Ta karasa maganar ranta na suya, sai takejin kamar kamshin turaren da Maryama kan hayaqa a zuwan turaren wuta a jikin shi. Watakila wata sa’ar Malamin ta ya bata na fito da Ahmadi tsakiyar dare ta goga mishi wannan shu’umin turaren.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Dan girman Allah Maimuna ki saka ma ranki salama.”

Ahmadi yai maganar cike da gajiya, yana mamakin kishi irin nata, wani lokacin yana jin daman ya hakura sun rayuwa su kadai kamar yanda taso, daya kaucewa duk wannan rigingimun.

“Ta ina zan fara sakama raina salama bayan baka bani wannan zabin ba? Bance maka munafunci bane, kawai bata kaunar ganin na kebance dakai saita tsiri wani abin da zaka ha’ince ni”

Rabata yazo yi, gara ya wuce ya kwanta, inya tsaya biye mata zaiyi. Kamar ba ita bace tagama mishi alkawarin zasu zauna lafiya dazun nan. Amman sai ta tare kofar, wani irin kishine turnuke da zuciyarta, kamshin turaren Maryama da hancinta yake jiye mata sai take ganin kamar wani abin sukayi a yan mintina daya dauka a dakin nata da sukai mata nisan awanni, tare mishi hanya ta yi.

“Ka koma dakin nata mana, ka koma inda ka fito Ahmadi tunda haka kake so tun daga farko.”

Ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata, yana da nashi dakin, kudine da sun shigo hannun shi akwai hidimar da zaiyi dasu, bai karasa bangaren ba, kuma duk da haka akwai wani dakin da zai iya zuwa ya kwanta a bangaren Maimuna, dakuna uku yayi mata, harda dakin girki, bangaren Maryama dakuna biyu itama da na girki, har lokacin akwai tankamemen fili da katanga kawai yaja mishi, banda filin tsakar gida, wannan sai a hankali zai dinga gine kayan shi tunda ba sauri yake yi ba. Hannun ta ya kama ya cire daga kofar yana shigewa cikin dakin da ta bishi.

“Wallahi Allah zai kamaka idan baka mana adalci”

Runtsa idanuwan shi yayi yana bude su hadi da sauke numfashi, kukan da takeyi na kara taba zuciyar shi.

“Kamshin turarenta kakeyi fa, Ahmadi kamshin turarenta kakeyi ranar girkina. Wanne irin rashin adalcine wannan? Ko cikin da take dashi ne yasa kake wannan rawar kafar?”

Juyowa Ahmadi yayi yana kallon Maimunar da mamaki.

“Ciki kuma?”

Hawaye ne suka kara tsiyayo mata.

“Kana nufin kace mun baka sani ba?”

Mamaki yake kan mamaki.

“Maryaman ce take da ciki?”

Ya kara tambaya, kai kawai Maimuna ta jinjina tana rabashi ta wuce kan gado ta kwanta. Ya dade a wajen yana jinjina maganar, ko dan ita Maimuna macece shisa ta gane Maryama na da ciki. Har ran shi kuma yaji dadi, yanzun yake fahimtar kwadayin manjan da ake ta mishi abinci da shi kwana biyu. Murmushi kawai yayi yana karasawa kan gadon. Kukan da Maimuna takeyi na kara dagula mishi lissafi, matsawa yayi daf da ita yana rikota jikin shi, tun tana kwacewa harta hakura.

“Kamshin ta fa kakeyi.”

Ta sake fadi tana zame jikinta, mikewa zaune yayi ya cire rigar ya cillar a kasa, yana kara komawa kan gadon ya rikota.

“Ki yi hakuri Maimuna…”

Kuka takeyi sosai, ya rasa kalar kishin nan nata, abin kuma yafi karfin shi, addu’a yake mata na samun salama, amman kamar tunzura abin yake karayi. Ya jima yana lallashinta.

“Karka kara zuwa wajenta in kama dakina.”

Amsata yayi da to, dan a zauna lafiya, da duk wasu sharudda da taketa kafa mishi, sannan tadan ji nutsuwa, ko rubutun data diga mishi a ruwa dazun ya fara aiki, na kokarin kwato shi daga hannun Maryama ne, Allah ya fara taimakonta da alamu, zatayiwa Khadi maganar wannan turaren na Maryama dan bata yarda dashi ba. Da zata iya ma da kanta zata tambayi Ahmadi taje gidan Khadi din suje wajen Malam tare, amman tsoro takeji, ta gwada sau daya, ta kasa karasawa, sai take ganin kamar wani zai ganta, kamar za’aje a fadawa Ahmadi inda taje. Tafi gane duk yan kudaden da zata samu ta ba Khadi din, duk wani abu da za’a karbo mata a karbo. Da wannan tunanin a ranta bacci yayi awon gaba da ita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 1Martabarmu 3 >>

1 thought on “Martabarmu 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×