Skip to content
Part 1 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

January 1985, Kano, Nigeria

Tsaye yake bakin kofar gidan shi da yake haya anan unguwar Fagge, gidan da shine na biyu da ya kama duk a cikin unguwar a shekaru kusan hudu da auren shi saboda halin matar shi Maimuna. Halin da yanzun ya saka shi zullumin shiga cikin gidan, ko da wasa bai hasaso rana irin wannan zata zo mishi a rayuwar auren shi ba, ranar da zai tsaye a kofar gidan shi yana tattaro duk wani kwarin gwiwar da zai iya wajen shiga gidan. Dakyar ya iya sauke numfashi yana taka cikin soron hadi da shiga cikin gidan da sallamar da yasan ba lallai bane ta amsa.

A zaune ya sameta kan kujera a tsakar gidan tana yanka alayyahu. Jikinta sanye da atamfa mai zanen tabarma da ta karbi farar fatarta, bakin nan dauke da janbakinta ja da a lokacin ko baka maya saka shi ba sai yai kwanaki biyu kan labbanka da alamun shi. Tayi mishi wani irin kyau, duk da cikin jikinta yasa kuraje fitowa a fuskarta. Ahmadi ya kasance cikin jerin mazan da kance

“Farar mace ko da mayya ce….”

Indai zasu samu suna so, tun bayan mallakar hankalin shi daya dora idanuwan shi akan Maimuna yasan tana cikin jerin matan da yake son kasancewa da ita har karshen rayuwar shi.  Shisa baiyi nauyin bakin fadin yana son ta ba, da yake ahalin Dikko gabaki daya abune mai wahala daga mazan su har matan su ace gashi yau sun fita daga gida sun auro bare. Koya ka shiga gida ka duba miji da mata sai ka samu wata halartacciyar alaka ta jini a tsakanin su. Ita kanta Maimuna din da shi Ahmadi dan mace da yar namiji suke, iyayen nasu ma in aka duba duka cikin ahalin Dikkon ne, ta bangaren mahaifiyar shi abokiyar wasa ce, ta bangaren mahaifin Ahmadi kuma Maimuna ‘ya ce a wajen shi.

Da yake su din boko ta shige su, sai aka dinga jinjina karancin shekarun Ahmadi duk da bayan karatun da yake shekarar shi ta karshe lokacin yana da tsayayyen hanyar samun shi ta kasuwancin takalma na manya da yara da Babban Yayan shi Ayuba ya saka shi a hanyar yi tunda kasuwanci ne silar arziqi kuma abin tinqaho ga ahalin Dikko gabaki daya. Ko da aikin gwamnati ka sami wani namiji nayi inka duba sai kaga ya hada da kasuwanci ko yayane. Hakan yasa ba’aqi bashi auren Maimuna ba. Amman surutun ya kara samo asali da Yayan Ahmadi wato Bala da yake nashi kasuwanci a asalin tsatson su wato jihar Katsina da bai ko da maganar aure ba.

Amman wata goma cif bayan auren Ahmadi da Maimuna kowa ya fara sambarka, ba’a maganar komai sai albarka da take cikin auren wuri, gasu yanzun da dansu da yaci sunan Mahaifin Ahmadi din wato Mutaqqa suke kiran shi da Khalifa. Lokacin ne kuma Ahmadi ya kammala karatun shi da yake a bangaren lissafi inda aka tura shi yin bautar kasa a jihar Katsina. Ga albarkar kyautatawa iyali da yake gani ta wajen nasara kan duk wani al’amari da zai saka a gaba.

Da yake Maimuna tana cikin matan da suke haihuwar da Hausawa kan kira gwarne, cikin yarinyarta ta biyu Zubaida ya shigane ko watanni takwas cikakku Khalifa baiyi ba, wayewar da suke da ita yasa suka dauki shawarwarin likita, Khalifa da lafiyar shi dimir har aka yaye shi. Yanzun ma tana shayar da Zubaida lokacin da ta sami ciki na ukku da yake a jikinta a yanzun. Da tsohon cikin Zubaida dole suka tashi daga gidan yawan da yake haya saboda rikicin da aka kwasa tsakanin Maimuna da daya daga cikin yan hayar.

Sai bayan auren su ya fahimci ita din bamai hakuri bace ba, akan magana kalilan ma bakinta baya shiru. Dole ya samu wannan gidan mai daki biyu da suke a ciki yanzun suke zamansu su kadai, daman saboda tunanin bautar kasar da zai tafi da zaman kadaici da bashi da dadi shisa ya kama cikin mutane. Yanzun ma dai komai ya kusan zuwa karshe tunda tun kafin auren shi da Maimuna yana da filin shi da Yaya Ayuba yasa ya siya kusa da gidan shi. A cewar shi su kadaine maza da suke gari daya cikin yaran Alhaji Mutaqqa, shi Bala yana Katsina, kuma acan yake zaune da matar shi bayan auren shi. Ya kamata ace suna kusa da juna.

A lokacin ma rabin kudin ne yake da shi, da yake Yaya Ayuba yana da hali saiya cika mishi, a hankali ya biya shi yake kuma gina tanqamemen filin da taimakon Yayan nashi.

“Maimu uwargidan Ahmadi, fara jinin Dikko….fara hasken idaniyata”

Ahmadi yai mata kirarin da yakanyi mata tun lokacin amarcin su saboda tayi mishi kyau ba dan kadan ba duk da babu jituwar kirki a tsakanin su kamar da

“Hasken da ya kasa hanaka hango Maryama…”

Ta karashe maganar kanajin daci da zafin kishin da yake dauke a muryarta, kai kawai Ahmadi ya jinjina, indai rikicinta ne kan karin auren da zaiyi ba sabon abu bane ba. Shidin tunda ya fara amsa namiji ya tsara rayuwar shi da mata biyu, ko da wasa baya hango kanshi zaune da mace daya tal. Sanin hakanne ya fadawa Maimuna tun lokacin hidimar bikinsu, amman dariya kawai tayi. Yanzun ne ya fahimci ma’anar dariyarta, bata dauki maganar tashi da muhimmanci ba sam a wancen lokacin.

“Ina yaran?”

Ya tambaya cikin son sauya zancen, bai jira amsarta ba ya wuce cikin dakin da jan kafet ne shimfide. Sai yaga dakin yayi mishi girma saboda babu jere, a hankali harsun fara kwashe kayayyakin su zuwa sabon gida tunda abu kadan ne ya rage a dayan bangaren da Maryama zata zauna. Shigar shi tayi dai-dai da tasowar Khalifa yana mishi oyoyo, Zubaida na son maimaita abinda Khalifan ya fadi cikin wani yare na daban. Dariya yayi sosai yana kamata ya dagata, duk lokacin da ko idanuwan shi ya dora kan yaran sai yaji wani nishadi na daban ya ziyarce shi.

Yana son Maimuna, yayi wayon sanin dadin iyaye, amman yawancin kaunar shi ta yan uwace ya sani. Sai yanzun da yakejin kaunar Khalifa da Zubaida da bai taba sanin kalarta ba, da Zubaida a jikin shi ya zauna, dai-dai shigowar Maimuna da farantin da yake jere da kwanoni, karba yayi ba saita tsugunna ba saboda cikin jikinta. Aikam dakyar ta samu waje gefen shi tana zama. Abincin ya bude yana ganin shinkafa da miya harda naman kasuwa da ya saka shi jero addu’ar godiya ga Allah da ni’imar da ya wadatasu dashi.

Musamman a lokacin da tattalin arziqin kasa ya shafi jihar Kano matuqa, mutane na cikin yanayi na rashi, idan ka samu abinda zaka mai bakinka koya yake ba karamar ni’ima bace, balle shi harda nama. Cokali ya dauka ya dibi miyar yana zubawa a gefe ya cakuda ya diba yakai bakin shi bayan Bismillah, lumshe idanuwan shi yayi saboda dadin abincin, indai ta wannan bangaren ne bayajin Maimuna. Yana kuma jin dadin yanda duk kalar rikicin da zasuyi baya shafar abincin shi da shimfidar auren su. Lafiyar shi na da muhimmanci a wajen ta kadan ba

“Ko zaka ci abincin ne?”

Ahmadi yai maganar yana kallon Khalifa daya girgiza mishi kai, shima yayi ma yaron tayine kawai dan sabo dayi badan zaici ba. Inba yana gida lokacin abinci yayi ba su hadu suci, sam Maimuna bata yarda da su saka mishi hannu a cikin abinci bayan sunci nasu har sun ture. Ba’a bata wannan tarbiyar ba, ba zata bari yaranta su dauka ba. Duk kaunar shi da su kuwa baya mata katsalandan akan tarbiyar su saboda zaiyi mata shaida tsaye take wajen saka su hanya me kyau.

“Maimunata in dai girkine… Anya akwai abincin da zanci yakai naki dandano kuwa?”

Ya fadi cike da kauna da yabawa, baki kawai ta tabe, tun haihuwar Zubaida kaf dangi da kalar soyayyarta da Ahmadi suka tafi a bakinsu. Yanda ko kunyar lokacin baya nunawa, a gaban kowa yake bata kulawa da dukkan zuciyar shi, sai ake alakanta hakan da zurfin boko da yayi. Shi kanshi bai hango tsayawar karatun nashi a Degree kwara daya kawai ba, yana da burin yin karatu mai zurfin gaske. Maimuna zata shiga aji biyu sakandire aka tsigeta aka aura mishi. Ganin kaunar da yakewa boko yasata nacin koyon turancin da baya gajiyawa da bata darussa akan shi wajen shi.

Batason ko da gaba yaga wata a hanyar bokon nashi yaji ita din kamar ta gaza ta wani fanni, musamman yanzun daya sami aikin koyarwa a jami’ar Bayero din da taimakon wani Malamin su da jinin shi ya hadu dana Ahmadi din, shekarun zaman su kuwa da nacin Maimuna yasa ta kalaman da suke mata wahala a harshen turanci kadanne, lokutta da dama takan yiwa Ahmadi magana cikin harshen dan kawai tanajin dadin yabawar shi da kalar kwakwalwarta.

Wani irin so takewa mijin nata da bata hadashi da komai ba, tun da karanci shekaru take da kishi na fitar hankali, kishin da ko kaya iri daya bataso ana hada mata da sauran yan uwanta, jibga kuwa tasha ta babu adadi lokacin da take gida kan ta kafe ba zata saka kaya kala daya da sauran yan uwanta ba. Kaf dakinsu itace yarinya tilo da take taya mahaifiyarta da suke kira da Yayya kishin matar Baban nata Inna da bata komai sai kokarin kyautata musu. Ita kanta Yayya takanyi mamakin inda Maimuna ta kwaso dabi’unta saboda tana da yakinin ba kalar tarbiyar da tayi mata bace wannan din.

Maimunar ma inda zaka tambayeta lokacin da ta fara qin Inna ba zata iya tunawa ba, kawai ta wayi garine da tsanar yanda take ganin Inna ta saka kalar kayan da Yayya ta saka, ko kuma Baba ya siyo abu ya baiwa Inna a tsakar gida gabansu. Har ranta takanji tuquqin bakin ciki, da Inna bata aurewa Yayya miji ba, sam ba zata zo tana daga kafadu ta saka kaya kala daya da Yayya ba. Takan tuna kalaman mahaifiyarta lokacin da take da rai

“Maimuna na rasa inda kika kwaso wannan kishin naki, wallahi na rasa. Allah ya rangwanta miki shi karya zame miki matsala”

A zuciyarta bayan amin takan raya

“Ni kadai zan zauna a gidan mijina, babu macen da zata zo ana siyo mana kaya iri daya da ita.”

Tun kafin tasan dadin auren kenan, ballantana yanzun da takejin kaunar Ahmadi na ratsa duk wani sassa na jikinta. Lokacin hidimar auren su da yace mata

“Kinsan Ahmadin ki na mace biyu ne ko?”

Dariya tayi sosai, duk zancen da yai mata na zama da mata biyu raha ta dauke shi, a zatonta labarin kalar kishin da take dashi yaji shisa yake zolayarta. Sai ranar daya dauketa dan suje taga ginin shi da yayi nisa ne tashin hankalinta ya fara ganin kalar tsarin ginin, a gigice suka dawo gida. Inda tai wani irin zaman dabas a kasa tana sakin kururuwar da Ahmadi yaga ko lokacin da labarin mutuwar Yayya ta riske su batayi irinta ba tana fadin

“Tozartani zakayi? Ahmadi asirina zaka tona shisa kake tunanin hadani da wata? Ashe soyayyar da kake mun duk karyace? Kulawar nan taka duk yaudara ce?”

Sosai kalamanta suka girgiza shi dan ya dauka sanar matan da yayi tun kafin auren su zai rage kadan cikin kishin daya kula tana dashi a kan shi, dan ko yan uwanshi da suke ciki daya bataso suna rabar shi. Balle kuma ayi maganar wasu can daban. Ranar ya dauka ya gama ganin tashin hankalinta, kwanaki biyu sukai cur bata bari sun runtsa ba a gidan. Shikuma lokacin ya kyalla idanuwan shi kan Maryama harma Yayanta yasan yana ciki, manya sun sani, an dai boye zancen ne saboda ya fada musu bai gama shiri ba sai ginin shi ya kara nisa za’a tsayar da zancen auren sosai.

Da yake itama Maryama duk ahalin Dikkon ne, alakarsu tafi karfi da Maimuna akan shi, tunda Kakkanin Maimuna na wajen uwa da kuma na Maryama itama na wajen uwa abokan wasa ne na kusa, ba bare bace zai auro. Yanda Ahmadi ya dauka zancen sanin kowanne lokaci zai iya kara aure shine tashin hankali mafi girma da zasu shiga dashi da Maimuna, sai da aka tsayar da ranar auren shi. Sai da Maimuna tasan wa zai aura asalin tashin hankali ya fara.

Ranar inda Allah yasota daga Khalifa har Zubaida suna gidan Yaya Ayuba. Dan ko gida bata kulle ba, kuka take wiwi, da kafafuwanta ta isa gidansu Maryama inda ta shiga babu ko sallama sai ruwan tijarar da ta sauke musu

“Ashe kasa kuke jira ta rufe idanuwan Yayya kuci amanata, tunda kuke zuwa gidana badan zumunci bane da shirin ku aurawa yarku mijina ne…me yasa duk mazan dangi sai Ahmadi na? Me yasa zakuci amanata haka?”

Duk yanda suka so ta kwantar da hankalinta fur taqiya. Kuka take musu tana surutai harda zagin da batasan lokacin da taji shi kwakwalwarta ta nade mata su ba. Sai da kowa a gidansu Maryama yai tunanin ko Maimuna tana da iskokai da ba asan dasu ba. Duk da akance kowacce mace nada nata, dalilin bayyana ne wasu da yawa basu samu ba. Sai da aka kira Gwaggon Maimuna din Bare da take aure nan kasa dasu, tukunna ta samu ta fitar da Maimuna daga gidan tana janta zuwa nata gidan.

“Gwaggo auren cin amana zasuyi, Maryama fa suke neman aurawa Ahmadi na”

Lallashinta Gwaggo takeyi sosai kafin ta kara fada mata maganganun da suka sake firgitata

“Waye baisan Karime da shige-shige ba? Kaf dangi fa kowa yasan gidansu da bin bokaye. Kina ganin ita taki barin kishiya ta zauna a nata gidan. Biyu fa ta fitar, wallahi idan akace miki Ahmadin ma basu kyale shi haka ba ba’a musu. Babu wanda bai shaida kaunar da take tsakanin ku da Ahmadi ba…”

Ai sai Maimuna ta kara dora hannu a kai tana rushewa da wani sabon kukan, sai yanzun take gane menene firgici

“Na shiga uku ni jikar Hanne… Gwaggo karsu fitar ni daga gidana, karsu rabani da Ahmadi…”

Kara riketa Gwaggo tayi

“Ki share hawayenki, wacece Karime ballanta Maryama, ke kinsan in ba anbi ta karkashin kasa ba, mai Ahmadi zai da wata Maryama….yarinya duk ta gandame a gida ba mashinshini. Karki damu akwai Malamina dana aminta dashi, shine yaimun aikin wannan yarinyar da aka hada da baqar iska…”

Hannu Maimuna tasa tana share hawayenta, dan indai Malamin da Gwaggo take magana shiyai mata aiki ya raba babbar yarta da bakar iskar da aka tura mata har tayi aure, to aikin shi naci. Dan tunda suka tashi tasan duk sa’annin yar Gwaggon suna da yara wajen hurhudu a dakunan mazajen su, a tarihin ahalin Dikko matansu da wahalar gaske su cika shekaru sha biyar ba a dakin mazajan su ba, wasu ma tun suna shekara sha uku, lokacin da za’ayi shabiyar din da goyon yaro. Amman yar Gwaggo takai shekara ashirin da bakwai kafin tayi aure.

Bata bar gidan Gwaggo ba saida kwarin gwiwar Malamin Gwaggon zai mata maganin matsalar auren nan da Ahmadi yake so ya jajibo musu. Dan ko da ya dawo gidan ya rufeta da fadan da tunda suke duk tarin laifukan da takeyi bai taba mata irin shi ba akan zuwan da tayi gidan su Maryama hakuri ta bashi. A ranar kuwa ta kwana tayi juyi tana zubar da hawaye, tana kara tabbatar da asiri akayiwa Ahmadi, inda babu asiri shidin bazai taba daga mata murya akan wata mace ba.

Ba’a cika sati biyu ba Gwaggo tazo gidan ta kawo mata magunguna da rubutun da zata sha ta shafe jikinta, sai maganin kuma a barbada a abincin da Ahmadi zaici.

“Kinji asiri ne ko? Turaren ne ta goga tazo nan gidan dashi, har a kofar gida tayi miki barbade ya tsallaka”

Kada kai kawai Maimuna tayi, mutum ba abin yarda bane, shisa kawarta daya Khadi tun tasowar ta, saboda rashin yardar da take da ita. A shekarar da ta wuce Maimuna ba zata manta ba, wajen sau hudu Maryama na zuwa gidan da sunan zumunci, ashe duk karyace, mijinta take kokarin aurewa. Wasu cikin kudaden da Ahmadi kan bata da ba wani abu take siye ba dan shidin mai kyautatawa iyalin shine ta diba tabawa Gwaggo dan ance gaba harda na tsari za’a karo mata da wanda za’a turo aljanin da zai katange gidan ko da su Maryama zasu gwada wani asirin.

Ranar jikinta har bari yake da Ahmadi yakai lomar abinci, sai tashi tayi tabar mishi dakin tana wucewa bayi ta kulle, inda tai zaune tana garzar kuka, sai takejin kamar taci amanar zaman su, kamar bata kyautawa kaunar da Ahmadi yake nuna mata ba da ta barshi yake aikawa cikin shi abincin da yasha garin magunguna har kala biyu, ga lamurje da ta hada mishi da ruwan rubutu.

“Kaga abinda hange-gangen ka ya janyo mana ko Ahmadi?”

Ta furta tana wani irin kuka mai taba zuciya, sai takejin kamar ta tsallaka wani waje yau mai wahalar komawa baya. Sai dai me babu abinda ya canza, da duk rana da yanda maganar auren Ahmadi take kara kusantowa. Maganar tashin hankalin da Maimuna take ciki ba’a fadi. Ga laulayin ciki daya sakata a gaba lokacin, kalar kulawar da Ahmadi yake mata na kara hura wutar kishin shi, ko rufe ido tayi ta kwatanta raba kaunar shi da wata Maryama sai zuciyarta tayi kamar zata tarwatse. Sai yanzun take ganin gaskiyar Khadi, take ganin wautar da tayi wajen kokarin hanata shiga Malamai saboda rashin kyawun hakan a addinance.

Khadi itace ta ukku a wajen mijinta, shigarta sai da tayi nasarar fitar da ta biyun daga gidan. Bayan fitarta ne yai dai-dai da rabon cikin da Khadi din ta samu, dan ta fadawa Maimuna cewa Malamanta sunce mata kishiyarce ta qulle mata mahaifa. Da tana ganin kamar haihuwa nufin Allah ne, sai yanzun ta gasgata zancen Khadi, kishiya ba abinso bace ko da ta batumbatumi ce. Ranar da kanta ta sami dan aike har gidan Khadi tace inta sami dama ta leqota. Kwanaki biyu tsakani kuwa Khadi tazo gidan.

Kuka sosai Maimuna ta tusa mata

“Khadi ki taimakeni, Malaminkin nan da yayi miki aiki kije mun wajen shi ko zai taimaka mun akan Ahmadi, dan Allah Khadi, wallahi ya kara auren nan zuciyata bugawa zatayi”

Dariya Khadi tayi har tana saka Maimuna jin haushi

“Ai gara da kika farka, idanuwan ki suka bude… In anyi duniya da Manzo kin kawo kukan ki inda za’a share miki”

Wannan maganganun sun kara karfin amintakar da take tsakanin su. Kudade Maimuna ta baiwa Khadi masu yawan gaske, dan idanuwan ta sun rufe da zafin kishin da bata tunanin addu’ar neman sauki akan shi, ta saki Allah ta komawa yan tsubbun da ta aminta sune kadai maganin matsalar da take fama da ita yanzun. Sai dai wani sabon tashin hankalin ta shiga dan Malamin Khadi ya hango dole sai Maryama ta shigo gidan sannan zata iya nasara a kanta

“Da ayaba akayi mishi wannan mallakar, da ace baki ma farga da wuri ba da yanzun sun shiga tsakanin ki da Ahmadi, dole sai ta shigo gidan za’a san yanda za’a karya sihirin…”

Ya kuma tabbatar mata dole saita kara jajircewa daga ita har yaranta. Kullum cikin boye-boye magunguna take da take bankadawa ma cikinta da yara a matsayin karya tambaya da kuma kaikayi koma kan masheqiya. Wasu da inta jika Ahmadi yagani sai tace mishi maganin shawarane da Gwaggo ta hado mata, wani lokaci harya karba kanshi tsaye yasha shima, tunda ta gano wannan hanyar cewa bokon shi bata rabashi da magungunan gargajiya ba take bashi wasu kanta tsaye da sunan maganin Basir ko shawara ko sanyi.

Kishin da yake cinta ne yasa ta zabi daga musu hankali daga ita harshi ko zai kara saka tai gabala akan shi ya fasa auren nan, amman kullum nuna mata yakeyi asirin da su Maryama sukayi mishi mai karfine dan bazai taba iya fasa aurenta ba. Yanzun ma kallon shi take yanda yake yabonta kamar ita kadai din ta ishe shi, harya karasa cin abincin yanayin hamdala

“Sannun ki da kokari, Allah yai miki albarka”

Ahmadi ya karasa yana mikewa ya tattara kwanukan ya fita dasu dan ya taimaka mata, duk idan ta wuce da turtsetsen ciki haka, koya dawo yaga gidan qwal saiya kara jinjinawa mata, ko a tunani ya hasaso kanshi da cikin jikinta sai ya hango yanda zai wuni shame-shame a kwance, amman ita harda kokarin girki, ko da tana laulayi sai yayi da gaske take kinyin girki, koyane saita lallaba ta dafa mishi abinda zaici. Shisa darajarta a zuciyar shi mai girma ce. Ganin da yayi magriba ta karato ya saka shi daura alwala kafin ya karasa dakin yana fadin

“Bari in fita masallaci….”

Batace mishi kanzil ba, sosai yake kewar hirarrakin su da yanda halin ko in kula din da take nuna mishi yake ci mai tuwo a kwarya. Haka yasa kai ya fice daga gidan. Ko da sukai sallar Magriba nan suka tsaya da wasu cikin unguwa danjin labarin Makka daga sabon Alhajin daya dawo satin daya fita wato Sambo. Da yake Ahmadi ba ma’abocin zaman majalissa bane ba, tunda Alhaji Sambo ya dawo basu hadu ba sai yau, yakan tsaya a lokutta irin haka a gaggaisa dan karamcin mutanen unguwar ba karami bane ba. Haka Alhaji Sambo ya dinga nishadantar dasu da labarai kayatattu yana kwadaita musu zuwa aikin Hajji duk idan halin hakan ya samu.

Kiran sallar Isha’i ya tarwatsa taron nasu, inda ana idarwa kai tsaye Ahmadi gida ya wuce, yana shiga soron ya mayar da gidan ya rufe sanin ba bako zasu karayi ba, inma sunyin a kwankwasa yaje ya bude. Jin shirun gidan ya tabbatar mishi da yaran sunyi bacci, da ya shiga daki kuwa Maimuna kadai ya samu, yasan harta kaisu dakin da suke kwana ta kwantar, baisan kuka takeyi ba saida ya zauna gefenta

“Subhanallahi…. Maimuna? Lafiya? Me ya faru? Ko jikinne?”

Ahmadi yake tambaya hankali a tashe yana riko hannunta, kai take girgiza ma duk tambayoyin shi alamar a’a kafin tace

“Me yasa ba zaka rayu dani kadai ba? Me kakw tunanin Maryama zata iya baka wanda ni ba zan iya ba? Ka fadamun dan Allah kagani, Wallahi Ahmadi zan maka komai. Karka tonamun asiri ka hadani da wata….”

Kallonta yake yanda kwanaki basu wuce sittin ba suka rage a daura auren shi da Maryama, har a sujjadar shi addu’ar kwanciyar hankali da dangana yakewa Maimuna saboda kishinta ya fara bashi tsoro, sake rike hannunta yayi, cikin taushin murya ya fara magana

“Da wanne yare zan fahimtar dake ba zan kara aure bane dan in wulakantaki? Maimuna baki yarda da kalar kulawar da nake miki bane ba? Shin a duk rana bana nuna miki yanda kike da muhimmanci a wajena? Ba zai canza ba dan na kara aure”

Wasu hawayen ne suka kara zubo mata saboda yaki fahimtar tsoronta, yaki gane ba soyayyar shi bace bata yarda da ita ba, soyayyar ce batason rabawa da kowa, tsoro take kar auren nashi ya zama sanadin da za’a rabata dashi gabaki daya

“In dai ba wahayin auren nan akayi maka ba dan girman Allah, dan datajar Ma’aiki da iyayen mu kayi hakuri”

Hannunta ya saki, duk hakurin da yake a kanta ya fara gajiyawa, tanayi kamar bata taba ganin an kara aure ba, kiriri kiriri take nuna kamar haramci yake son aikatawa ba abinda musulunci ya yarje mishi ba

“Maimuna kinga gara ki kwantar da hankalinki ko zamu samu zaman lafiya tunda auren nan ba fasawa zanyi ba”

Hawayenta ta share tana saka idanuwanta cikin nashi

“Tunda an shanyeka daman ya zaka iya fasa aure?”

Rai a bace yake kallon ta shima

“Wacce irin maganace wannan? Ba zaki daina baiwa sh Gwaggo damar darsa miki wasu zantuka marassa kan gado a rai ba ko?”

Kada kai Maimuna tayi cikin zafin rai

“Babu wasu maganganu da ake darsa mun a rai sai gaskiya. Yanzun daga ina kake tunda ka fita? Adalcinne kake son gwadawa bayan tun safe ka fice daga gidan nan, dan lokacin naka da zan samu ma tun kafin ka aurota sai ka raba mana tare”

Kai Ahmadi ya dafe yana rasa ta inda zai fara shawo kan wannan al’amarin

“Idan nace miki ba wajen Maryama naje ba zaki yarda?”

Yanda take kallon shi ya sakashi dorawa da

“Tunda nai maganar kara aure kike neman laifina a duk wani abu da zanyi, karyatani kike ko gaskiyata na fada miki. Halayen nan babu inda zasu kaiki Maimuna, karki rage kimarki a idanuwana wallahi”

Yanda ya karasa maganar yasa wani abu tsinkewa a cikinta, da gaske an asirce mata Ahmadi, in har da bakin shi yake furta hango raguwar kimarta a idanuwan shi an asirce shi

“Ashe kimata zata iya raguwa a idanuwan ka? Kaga dalilina na gudun aurenka ko? Kaga abinsa suke sa kana fadamun tun kafin ta shigo, wanne irin wulakanci zan gani kenan nan gaba?”

Take maganar tana wani irin kuka da yakeji har ranshi shisa ya mike saboda bayason biye mata, bayason bata mata rai fiye da yanda yake a bace ko dan cikin jikinta. Kuma da a karo na farko ya zanta sirrin gidan shi da babban abokin shi Nasiru saboda tsoron kalar kishin Maimuna daya gani shawara ya bashi mai kyau, kalaman Nasiru sun zauna mishi sosai

“Su mata ba’a biye musu, hakuri ake da halin su saboda wasu lokuttan kamar yara haka suke da karancin tunani. Laifine kayi mata da kara aure dole kuma tayi kishi, na kula shi kishin nan ya bambanta a tsakanin mata, kowacce da kalar nata. Kayi hakuri da duk wannan tashin hankalin da takeyi, da anyi auren zata hakura. Gani take kamar intaci gaba da daga maka hankali zaka hakura ka fasa. Kai dai karka biyeta, in ranka ya baci kabar mata gidan saika huce ka koma gudun biyewa zugar shaidan”

Aikam shawarar Nasiru ta mishi amfani wajen kaucewa rikicin rashin dalili da Maimuna kan takale shi da shi. Yanzun ma dakin yaran yaje yana samun tabarma ya shimfida kusa da yar katifar su da suke bacci a kai ya kwanta. Yasan halin Maimunar shi, duk fadan da zasuyi bata iya bacci ba’a kusa dashi ba, da almatsutsan kishin nata sun sauka da kanta zata zo ta neme shi. Dan haka ya lumshe idanuwan shi yana musu addu’ar tabbatar alkhairi a wannan auren da zaiyi da kuma zaman lafiya bayan yin shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 12

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Martabarmu 2 >>

1 thought on “Martabarmu 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×