Skip to content

Martabarmu | Babi Na Sha Biyar

3.7
(3)

<< Previous

Su Rayyan ne suke makaranta, sune da karatu amman Ayya ce take ramewa saboda tunani. Duk yanda Bilal yake jaddada mata cewa lafiyar su Rayyan din kalau hankalin ta ya kasa kwanciya. Asalin abinda take son ji Bilal ba zaj fada mata, balle kuma tunda suka tafin basu dawo ba sai yanzun da akayi hutun karshen zango. Da kanta ta nemi Hajiya Dije saboda ta samu a shiga tsakanin Rayyan da Layla, harma da Bilal din. Bata da natsuwar binta wani waje ma, tace taje mata ne, tashin farko dubu sittin Ayya ta tura ma Hajiya Dije. Abinda bata sani ba shine wajen shekaru hudu kenan komai ya kwance a gidan Hajiya Dije.

Tunda maigidanta ya dawo da uwargidan shi, ga yara da take dana sanin cusa musu bakin hali tun suna da kankantar su, mazan kusan duk suna da sana’ar su ta kasuwanci da sukeyi. Amman basa bata kudi, idan ta tambaya sai dai suji abinda zatayi da su, idan ta kama su siya mata ne su siya. Komai ta samu kamawa takeyi ta karyar wajen dillalai ta kai ma Malamai, to yanzun ma tunda ya kamata tana mishi barbade yai mata saki daya, da kyar aka samu aka maida auren, duk wani abu da zai fito daga bangarenta ya daina ci balle ta samo kan shi. Gani takeyi bokan uwargidan tane yafi wanda take bi.

Shisa take ganin Ayya rashin godiyar Allah ne ya ke damunta, sam matsalarta ba matsala bace ba, kukan dadi takeyi, ta ga Laylar da Ayya take ta daga hankali a kai, yarinya ce mai kyawun gaske, yarinyar da gari banza duk kyan Rayyan din shima sai yayi gaske ya samo me kyawun Layla. Mijinta abinda duk take so shi yakeyi, kaffa-kaffa yake da bacin ranta batare da wani aikin malami ko boka ba. Amman kullum bata rasa abin mita, shisa ta samu saniyar tatse, ranar da sukaje wajen wani Malamin tare kudi ake tsulawa Ayya idan sun tafi Hajiya Dije ta koma ta karbo. Rabonta da zuwa ma Ayya wajen wani Malami na kwarai tun wanda yai mata aiki akan Haris da tambayar duniya da tayiwa Ayya akan zancen aikin sai tasan dabarar da tayi suka fada wata hirar.

Watakila taji tsoro ne batayi amfani da maganij ba, duk kudin da ta kashe a kai. Tunda kwanaki ma da taje gidan ta ga Haris din ya shigo har bangaren Ayya yana gaishe da ita, harma da yar hira sukayi yana shiga Kitchen ya zuba tuwo da tayi, ba zata manta cewa Ayya,

“Haris dinne nan?”

Saboda ita bata ga alamar lalacewa a tare da shi ko daya ba, mikewa Ayya tayi yana amsa ta da,

“Shine, bari in dauko miki leshin da nake magana.”

Murmushi kawai Hajiya Dije tayi, tasan dan karta tayar mata da zancen Haris ne. Wannan kuma duk matsalar Ayya dinne a ganinta. Yanzun dai a sama ta sami saniyar tatse. Danma kudin a wajen bin ‘yan tsubbu suke tafiya itama. Duk kan mijinta da take tunanin an janye hankalin shi daga kaine. Ayya kuwa ranar wata zuciya aka kawo mata an yayyanka turbude da magani akace ta wanke ta zuba ruwan a bakin kofar dakin su Rayyan, sai ta ajiye zuciyar tayi mishi girki da ita duk idan yazo, daga shi har Bilal din a tabbata sun ci, to zai zama kamar ta kwato musu tasu zuciyar ce da Layla ta lashe.

Karba Ayya tayi, da fari maganin yayi mata kama da ararrabi saboda kalar shi, kamar ta dandana da ta wanke, sai tayi saurin kauda tunanin daga ranta. Duk irin wannan was-wasin kan bata aiki wani lokacin. Yanda akace tayi haka tayi, zuciyar ta kulle a leda ta saka a fridge, take ta ajiyarta tunda su Rayyan din sunki zuwa, sai a satin da tayi waya da Bilal ya tsayar mata ranar zuwan nasu. Cous-cous ta dafa musu da ya sha hanta da zuciyar da kuma kayan hadi. Aikam ranar tas suka cinye shi da Bilal, danma Bilal ya tsaya taince albasar da take ciki.

Duk da haka taki samun natsuwa, rabin rayuwar ta tun zuwan su jikin window take yinta, ko baccin rana ta daina samu tana runtsawa, dan ko ta kwanta sai taji kamar an gitta, da sauri take dirkowa daga kujera ta leqa ta ga ko Layla ce. Ga Rayyan din da ta dan fara gane kan shi kafin ya tafi ya kara hargitse mata. Ko sau daya bai tako dakin ba, itama da taje ta same su a bangaren su kan shi a kasa suka gaisa, surutun duniya da tayi baice mata uffan ba. Haka ta fita cikin kunar rai, Bilal ne ma yabi bayanta yana lallashinta.

“Ayya kinsan halin shi ai, kuma baya ma jin dadi kwana biyu tunda muka dawo, nima shiru-shirun ake tayi mun”

Ya karashe da murmushi, ranta na suya tace,

“Dan uban shi dan bayajin dadi sai inta magana yanaji na yaki dagowa balle inyi tunanin zai tanka? Har yaushe zai san ina da muhimmanci mai girma a rayuwar shi Bilal? Ace yafi karfin ya taso yazo ya gaishe dani ko da sau dayane a rana? Shikenan…”

Ta karashe muryarta na karyewa cikin yanayin da yasa Bilal fadin

“Dan Allah kiyi hakuri….zai gyara ai…”

Kai ta jinjina, da kyar ta iya cewa,

“Hmm…Allah ya shirya.”

Nan Bilal ya zauna yana ta mata labari har saida ya ga ta warware tukunna ya tafi. Shisa tayi kewar shi matuka a watannin nan da baizo ba. Duk wata hanya da zaibi ya rage mata damuwa ya sani. Yafi kowa fahimtarta, akwai halayenta da ko Abbu baisan yanda zaiyi da su ba amman Bilal ya sani. Zata iya cewa idan da na zama amini to Bilal ne amininta, duk wata damuwarta ko ta waya idan ta kira shi ta kai karar Abbu da Mami sai ya lallaba ya bata hakuri, saiya nuna mata yanda yake goyon bayanta, cikin dabarar shi. Neman Malamanta ne kawai abu daya da Bilal bai sani ba, abu daya da ba zata iya rabawa da shi ba saboda bata so yayi mata wani kallo na daban.

Mami kuwa tun da suka dawo sai ta tsinci kanta da bin Layla da ido a duk al’amurranta, tun kafin tafiyar su wayewar da yarinyar tayi ya wuce shekarunta, amman yanzun sai take ganin wata irin wayewa ta ban mamaki ta kara shigarta, kamar idanuwanta sun kara budewa. Bakinta bai daina bin Layla da addu’a ba ko a zaune take. Musamman da take makaranta, sai taita yawan tsintar kanta da faduwar gaba na rashin dalili, kuma tasan duk akan damuwar Layla ne da ta saka a ranta. Sai ta kirata sau nawa a rana, a duk karshen wayar tana jaddada mata.

“Dan Allah ki kula Layla, ke mace ce. Kiyi kokarin kare martabar ki a dukkan al’lamurran ki. Ba lallai sai a shigar ki ba, martabar ki na tare da abinda harshen ki zai furta, tana kuma tare da mu’amallar ki da mutane, musamman maza… Ki kula, ki rufamun asiri ki rufawa kanki asiri.”

Ta kan amsa da,

“In shaa Allah.”

Wani lokacin kuma ta kanyi shirun da yake karawa Mami damuwa, sai taji kamar ko Layla nayin wani abu da bai kamata ba shisa tayi shiru tana jinjina kalamanta na ranar, a lokutta irin wannan da ta sauke wayar take fadin.

“Allah ka taimakeni, Allah ka bani ikon sauke amanar da na dauka.”

Amman zuciyarta na rawa sosai. Jiya cikin dare ta farka, sabonta ne duk idan ta farka taji ba kishi bane ko wani matsi na fitsari da makamancin shi ya tasheta to fa sai tayi kokarin yin sallah ko da raka’a biyu ce tayi addu’a. Ta kanji kamar akwai dalilin da yasa Allah ya dawo mata da ruhinta a dai-dai lokacin. Watakila wani abune zai sameta, ko ahalinta shisa Allah ya bata damar sake kaddarar ta hanyar addu’a. Jiyan harta ninke dardumarta sai taji son ta duba Layla, wajen karfe biyu da rabi, tana kama kofarta da take kullewa a kwanakin nan sai tayi nasarar jinta a bude, turawa tayi taga Layla ta kife wayarta da saurin gaske.

Kwan fitilar dakin ta kunna, haske na gaurayewa da yake akwai wutar lantarki.

“Layla?”

Ta kira tana karewa Layla da take zare mata idanuwanta da ta ga sun sake launi da alamar baccin da yake cikin su da kuma wani abu daban da ba zata ce ko menene ba.

“Karfe nawa yanzun? Baki yi sallah ba bakiyi komai ba dan ubanki kin zauna danna waya?”

Mami ta karashe a fadace, wayar nan tana ci mata tuwo a kwarya, daman da rana sanda zasu ci abinci duk sai da ta amshe a hannunta da na Jabir tukunna suka maida hankali suna cinye abinci suka sake daukar wayoyin. Yau dai a tsorace Layla take kallonta, ko kadan bata san cewa bata kulle dakin ba. Kamar sanda ta dauko ruwane wajen karfe sha biyu, hankalinta nakan labarin da take karantawa, shaf ta manta da ta kulle dakin. Hankalinta a tashe yake da yanayin labarin, ta fita daga group din. Idan an aiko wani mai zafine sai Nanaa ta mata copy ta tura mata.

Makoshinta da kamar an zuba kasa saboda yanda take fitar da numfashi yasa ta tashi ta dauko ruwan, ashe bata kulle kofa ba, har zazzabi take ji na rashin dalili kafin Mami ta shigo mata daki babu tsammani, zuciyarta har cikin bakinta taji saboda yanda ta tsorata, idan Mami taga abinda take karantawa kashinta ya bushe, ita da waya har abada, a jikinta take jin haka.

“Bani wayar ki kwanta dan ubanki, marar hankali kawai.”

Wani irin bugawa zuciyar Layla tayi, muryarta na rawa tace,

“Dan Allah Mami kiyi hakuri, wallahi caji zan saka in kwanta yanzun daman…”

Layla ta karashe tana dauko wayar daga karkashin cinyarta, hannuwanta rawa suke sanda ta fita daga WhatsApp tsabar tashin hankali. Gabaki daya wayar ta kashe ta janyo cajar ta da take makale a bango ta saka wayar ta dora kan durowar gefen gadon. Tana jin idanuwan Mami akanta.

“Akan wannan raba daren na kusa haramta miki wayar nan gabaki daya. Taya ba zakiyi fama da ciwon kai ba? Kullum ba zaki samawa kanki hutu ba.”

Ita dai Layla kwanciya ta gyara tana jan bargo ta lullube har wuya, zuciyarta banda bugawa babu abinda takeyi, duk fadan Mami bakomai yake karasawa kunnuwanta ba, yanda ba zata sake kuskuren barin kofa a bude ba take tunani. Har Mami ta kashe mata kwan dakin tana ficewa hadi da ja mata kofa. Wucewa dakinta Mami tayi, amman har yau abin yayi mata tsaye a rai. Tana tunanin ko Layla ta fara kule-kulen samarine da suke riketa da hirarraki har cikin dare haka. Duk da tana tunanin akwai wani abu da yake wanzuwa a tsakanin Layla da Rayyan da su kan su basu fahimta ba har yanzun. Tsoro ne fal a ranta, saboda a lokaci irin wannan ba yara mata bane matsalar, su daman masu rauni ne, mazan ya kamata iyaye su tsawatarwa.

Allah ya sani saboda Layla take kokarin bin diddigi akan su Haris, tasan shi bashi da matsala, budurwar shi guda daya. Yar gidan Yaya Ayuba ce kuma, tasan baya kule-kule. Jabir ne damuwarta, kullum cikin mishi nasiha yake, idan wasu yake yaudara zai iya dawowa kan Layla.

“Dan Allah Jabir ka kula, kaga kana da kanwa, ka tayata kare martabar ta wajen mutunta yaran wasu, karka cutar da ‘yar kowa…”

Dariya yakan yi sosai.

“Malama Mami.”

Ya kan fadi yana dariya, har sai ta zage shi ko yaga tana shirin daukar wani abin dan ta kwada mishi tukunna yake tashi ya gudu daga dakin yana mata dariya. Tasan ba zata raba Layla da samari ba, ko dan yanda take da kyawu. Dan ta hanata raba dare tana hira abinda zasu fada din idan na banza ne har da rana ma sai su fade shi. Tana hana danna wayar daren ne dan ta kwanta ta samu wadataccen bacci, saboda yanda take yawan mitar ciwon kai. Sosai Mami na ganin wautar masu yankewa yaran da zasu gani tsakiyar dare suna chatting hukunci marar kyau.

Ba lallai maganganun banza sukeyi ba, maganar banza bata bukatar lokaci, zai iya yiwuwa hira suke ta yau da kullum da abokan su, kamar yanda kake zama kayi hira sosai da naka abokan, ko idan kayi baki hira tayi muku dadi sai a raba dare ana zantawa, zai iya zamana bacci ne ya kauracewa idanuwansu, zamani da yai musu sabo da waya yasa suka dauka suka shiga dan duba tsofin sakkoni su rage kewa, watakila, watakila dalilai ne mabanbanta. Akwai munafunci da son kai a yanke hukuncin cewa maganar banza yaran sukeyi da tsakar dare. Saboda kai me kakeyi kenan? Me ya kaika shiga manhajar da tsakar dare? Me ya kaika bincikowa kaga ko suna online ko basa nan? Gulma?

Addu’a Mami tayi sosai da ta dan sama mata natsuwa. Da yake tun dawowar Layla bata barinta yin wani aiki, ita take su girki da gyaran gidan tunda bata da kwiya. Magriba da aka kira yasa Mami kiran sunan Allah tana mikewa dan taje ta gabatar da sallah.

*****

Tsaye yake a bakin kofar dakin su ya dawo masallaci sallar isha’i. Wayar shi yake dubawa yana ganin sakonnin Mtn da suke ta cire mishi kudi na rashin dalili, harda su wani caller tune da baisan sanda yai subscribing ba. Karamin tsaki yaja, sakonnin ma duk sun taru sun cika mishi waya, ba dubawa ya cikayi ba. Ya goge duk na Mtn din. Ya shiga na bankin shi ma yana gogewa. Na Layla ya shiga, akwai wanda ma bai bude ba ashe, shifa waya sam bata dame shi ba. Balle kuma tunda suka dawo gida, in banda Layla babu wanda ya kira da wayar, sai fa Bilal da idan ya fita yana son gaya mishi wani abin ya kira shi.

Ya kara yawan kwayoyin da yake sha saboda ya daina samun bacci kwata-kwata, na ranar ma wahala yake mishi. Haushin komai da kowa yake ji, baison yin magana, ba kuma yaso ayi mishi. Surutun na kara mishi hayaniya cikin kan shi sosai da sosai. Yafi bukatar shiru akan komai yanzun. Sam baiji takun tafiyarta ba, sai hannuwanta da ta sakala cikin na shi tana fadin,

“Hamma…”

Ba dan bata gan shi ba duk yinin ranar, ta gan shi bai dai kulata ba, inda take ma bai kalla ba, tunda suka dawo ya kara zama shiru-shiru.

“Ka ki fadamun abinda ya ke damun ka ko?”

Ta furta da wani irin sanyin murya, saboda ta tabbatar akwai abinda yake damun shi. Rayyan na jinta a wajaje fiye da jikin shi, musamman da ta kara riko hannun shi tana dora kanta a damtsen hannun nashi, bai hanata ba, bai kuma daina duba sakonninta da yake dubawa ba, surutu takeyi amman tare da ita a jikin shi haka sai yake jin shirun da yake dan bukata a cikin kan shi, kamar karta raba jikin shi da nata, kamar ta zagaya duka hannuwanta ta bayan shi ta rike shi dam haka yake ji.

“Hamma…”

Layla ta kara kira tana jin kamar ta mayar da shi cikin ta saboda wani irin yanayi da taje ji. Da gaske tana son shi, tana kaunar shi da dukkan zuciyarta, a kwanakin nan tana hasaso rayuwa kala-kala a tare da shi. Wayar dai yake dannawa, yanda tayi luf a jikin shi da yanayin sunan shi da ta kira sun sa ya daina gane abinda yake karantawa. Su duka biyun suna wata duniya ne ta daban, har sai da suka ji muryar Mami da tace,

“Layla?”

Cikin wani irin tashin hankali, dai-dai lokacin da Layla ta tittida kafarta tana son sumbatar gefen fuskar Rayyan din saboda yanda wata irin soyayyar shi take nukurkusarta. Mami kuwa jikinta babu inda baya rawa, Layla din ta fito ta kira dan ta bata lambar Haris ta Etisalat din shi, wadda take ta kira taki shiga, ta tsammace ta wajen bangaren su Rayyan din daman, amman ba’a jikin shi makale ba, ba a cikin wannan mummunan yanayin da yasa numfashinta har tsaitsayawa yakeyi ba. Ga kafafuwan ta da taji suna barazanar kasa daukarta.

Tun da ta shiga aji biyu sakandire ta zaunar da ita tana kara jaddada mata yanda babu halaccin wannan rirrike rirriken a tsakaninta da duka mazan gidan. Har misali tayi mata da su Rukayya, da yanda ko su basa rike hannun Rayyan. Sosai ta tsawatar mata saboda ta ganta da ta Rayyan din yazo nemanta ta rike mishi hannu. Ta dauka tun a lokacin ta bari, tunda a gabanta Rayyan din ya fisge hannun shi har duka ya kai mata, sai Mamin taji sanyi. Idan ita Layla bata da hankali Rayyan yana da shi.

Amman ko da Layla tana tunanin Rayyan din Yayanta ne, wannan rikon da tayi mishi ya wuce na yan uwantaka, idan ba idanuwanta bane suka gane mata kamar sumba Layla take shirin mannawa Rayyan din.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Mami ta fadi tana nufar Layla da ta raba jikinta daga na Rayyan da bayanannen tsoro a cikin idanuwanta.

“Ma.. Mami”

Ta furta muryarta na fitowa a sarke, Mami na karasawa wani mari ta dauke Layla da shi tana kai mata dukan da Rayyan yaji har tsakiyar zuciyar shi. Lokaci daya kan shi ya sara yana daukar ciwo, bai dai motsa daga inda yake ba, idanuwan shi na kafe kan wayar da hankalin shi baya kai.

“Ashe baki da hankali? Ashe baku da hankali”

Cewar Mami da wani irin firgici marar misaltuwa, tana kara kaiwa Layla da take zubar da hawaye duka tana damko hannunta, Rayyan da yake tsaye Mami take kallo.

“Idan ita bata da hankali kai baka da shi? Baka san haramcin da yake cikin abinda kuke aikatawa ba ko? Wallahi da Abbun ku zan hada ku, ba zan iya ba, ba zaku ja mana magana ba.”

Mami ta karasa tana fisgar Layla zuwa bangaren Abbu, sai tirjewa takeyi saboda tsoron da yake cike da zuciyarta. Rayyan ba zaice ga abinda yake ji ba, amman jikin shi har bari yake daya kare Layla daga dukan Mami din, sosai zuciyar shi take jin ciwon dukan da tayi mata. Baice abinda tagani me kyau bane ba, har Bilal ya fada mishi ya daina baiji ba, ba laifin Layla bane ba, shine daya barta. Yaso ya bude baki yau ya gayawa Mami haka, amman baisan ta inda zai fara ba, shisa yayi shiru. Ya kasa barin wajen, yana nan tsaye har lokacin yaga Abbu yayo wajen, Mami na biye da shi, sai Layla da take biye da Mami din tana kukan da yake shigar mishi rai.

Yau yasan bayason hannun kowa ya taba jikin Laylar, bayason kowa ya zama dalilin kukanta idan bashi ba. Ita yake kallo har suka karaso wajen da Abbu yana kiran.

“Rayyan?”

Saboda shima zuciyar shi bugawa takeyi, ya zauna kenan Mami ta shiga rike da Layla tana fadin,

“Dan Allah kayi musu magana ko zasu jika, kayi musu magana kafin mu suja mana magana…”

Yanayin muryarta da yake cike da tsoro da karaya yasa Abbu tambayar.

‘Su wa? Lafiya? Me yake faruwa ne Maryama? Layla me ya faru?”

Ya karasa maganar yana mikewa, Layla da take kuka Abbu take kallo.

“Dan Allah Abbu kayi hakuri, ba zan kara ba, ba zamu kara ba.”

Saboda yaune karo na farko da tsoro matsananci ya cika mata zuciya haka. Kaunar da takewa Abbu mai girma ce, bataso yayi fushi da ita.

“Wai me ya faru?”

Abbu ya sake tambaya dan duk zuciyar shi dokawa takeyi, Mami da kyar ta iya fadin.

“Rungume na gansu ita da Rayyan.”

Maganganun na fito mata da wani irin nauyi na tashin hankali. Wani sarawa Abbu yaji kan shi yayi kafin maganganun Mami su zauna mishi, ma’anar su da tashin hankalin su ya zauna mishi yana wujijjiga duk wani zaman lafiya da yake tare da shi. Marainiya, amanar da suka dauka shi da Mami, ai baisan kafafuwan shi sun taka ba sai da yaji shi a waje, kan shi tsaye bangaren su Rayyan din ya nufa yana kuwa hango shi a tsaye, suna karasawa hannun shi Abbu ya daga yana saka Rayyan lumshe idanuwan shi, saboda a karo na farko yau yayi tunanin hannun Abbu zai sauka a jikin shi. Bai bude idanuwan ba sai da yaji ya kama hannun shi.

Lokacin da Ayya ta zo wajen, saboda Huda taje ta fada mata ga Mami can tana dukan Layla yanzun ta gansu wajen dakin Rayyan din, kuma ta ga Rayyan a tsaye a wajen. Shisa Ayya ta taso ta fito a bazame, ganin Abbu rike da hannun Rayyan ya sata fadin.

“Lafiya? Me ya faru?”

Tana sauke idanuwan ta akan Mami da Layla da ta kara boyewa bayan Mami tana tsiyayar hawaye saboda kallon da Ayya ta watsa mata.

“Me ya faru wai?”

Mami ce ta kalli Ayya tana amsawa da,

“Me yasa ba zaki tambayi dan ki ba?”

A fadace Ayya ta kalleta

“Da yai uwar me zan tambaye shi? Maryama kinga ki kiyayeni…”

Sun kwana biyu basu shiga harkar juna ba, tunda Mami ba biye mata takeyi ba, amman yau ranta a bace yake matuka, abinda duk Ayya taje ji itama tana dai-dai da ita.

“Idan ban kiyayeki ba me zai faru? Maimuna ki fadamun abinda zai faru yau idan ban kiyayeki ba, kuma wallahi kija ma danki kunne, ya kyalemun yarinya, domin amana ce a wajena”

Da tashin hankali Ayya take kallon Mami jin maganganun ta, ta bude baki Abbu ya kalli su biyun,

“Maryama ki wuce ki koma ciki.”

Akwai wani yanayi a muryar shi da yasa Mami juyawa, Layla zata bi bayanta Abbu yace.

“Ke ki tsaya…”

Sosai Ayya ta kalli Abbu

“Ahmadi ban…”

Wani irin kallo yai mata.

“Kema ki wuce Maimuna.”

Bata taba ganin shi a yanayin da take ganin shi ba yanzun shisa ta kama hanya tana wucewa cike da son sanin abinda ya faru. Sai da tabar wajen sannan Abbu ya kalli Layla da take ta tsiyayar da hawaye.

“Kar in sake ji, kar kuma in sake gani…”

Saboda yana ganin dana sanin da yake shimfide a fuskarta, ga kuma tsoro, ko da nasiha ko fada zai mata babu wanda zata fahimta a halin da take ciki. Kai kawai take daga mishi tana share hawayenta da bayan hannun, ganin yaja Rayyan zasu wuce ya sata fadin.

“Dan Allah Abbu karka dake shi, baiyi komai ba shi.”

Numfashi Abbu ya fitar da kalaman ta yana girgiza kai kawai saboda baisan inda zai dauke su ya ajiye ba, dakin su Rayyan din yaja shi saboda gani yake kafin su koma bangaren shi kalaman da yake ta hadawa sun bace mishi, gefen gado ya ja Rayyan da bai musa ba ya zauna. Tsugunnawar da yaga Abbu yayi yasa ka shi jin wani irin abu ya tsirga mishi cikin kai. Ga wajen da Abbu ya rike mishi hannu kamar an kona shi yake ji, radadi wajen yake mishi ba fitar hankali.

“Rayyan…”

Abbu ya kira zuciyar shi na wani irin ciwo, yau so yake yaji matsalar yaron na shi, amman yaki yarda su hada ido, gabaki daya iskar dakin tayiwa Rayyan kadan.

“Rayyan dan Allah yau ka kalli idanuwa ka fadamun matsalar ka, ina so in sani. Idan da yanda zan taimaka maka zanyi, wallahi zanyi komai in taimaka maka, amman hakan ba zai yiwu ba sai ka mun magana.”

Kan shi Rayyan ya kara sunkuyar wa kasa, kirjin shi kamar zai kama da wuta saboda iskar da bata kai mishi inda ya kamata. Baison magana da Abbu, baya son ganin shi, bayason jin muryar shi duk da yasan yana cikin jerin mutanen da ya kamata ace yana jin kusanci da su, ya kamata ace yana so.

“Kayi mun magana.”

Abbu ya sake fadi, ya kai mintina kusan goma a tsugunne yana so ko idanuwan Rayyan din ne ya saka cikin nashi amman hakan ya gagara. Numfashi Abbu ya sauke kirjin shi na mishi zafi.

“Idan son ta kakeyi ka fadamun, itama zan tambayeta sai in muku aure…”

Sai lokacin Rayyan din ya dago yana saka idanuwan shi cikin na Abbu.

“Kana son ta?”

Baisan dalilin shi na girgizawa Abbu kai ba, shi bai san me yasa kowa yake tsallen yanke mishi hukunci haka ba akan Layla. Baisan me yasa ba zasu barshi ya dora sunan akan alakar da take a tsakanin su ba, amman yanzun da Abbu ya tambaya sai yake ganin kamar a cikin idanuwan shi yana so amsar ta kasance eh, dalilin da yaji ya dauki Layla ya jefa can wani waje a bayan zuciyar shi, yanayin da baisan ya zai tsaida faruwar shi ba. Numfashi Abbu ya sake saukewa.

“Amana ce ita din a wajena, rokon ka nakeyi ka rufa mun asiri, idan baka tayani kare martabar ta ba, karka taba ta, dan Allah Rayyan a karo na farko kayi abinda nace, badan ina so ba, sai dan shine dai-dai.”

Shiru Rayyan yayi yana kara sadda kan shi kasa, da kyar Abbu ya iya mikewa, har jiri yakeji yana daukar shi sanda ya kai bakin kofa saboda kan shi da yake sarawa, har lokacin jin shi yake kamar yana yawo a duniyar mafarki.

“Abbu…”

Yaji Rayyan din ya kira, da babu taimakon kofar da Abbu ya dafa tabbas da kafafuwan shi sun kasa daukar shi, rabon da yaji sunan shi a bakin Rayyan tun yana dan karami. Na rana daya ya kira shi haka bai taba ba.

“Yaa Rabb.”

Abbu ya fadi a cikin zuciyar shi, yana jin ko addu’o’in shi akan Rayyan dinne suka fara karbuwa, juyawa yayi yana kallon Rayyan da yake yawata idanuwan shi akan fuskar Abbun, akwai tarin abubuwa da yake so ya fadama Abbu amman kamar an shake shi haka yake ji. Idan bai fadi sauran da baisan ta inda zai fara ba, yana so ya fada mishi yanda tunanin zai taba martabar Layla ya yi mishi ciwo sosai, yana kuma so ya tambaye shi ko shima a tsakanin shi da na shi mahaifin yana jin irin wannan abin da yake ji.

Yau yana so ya fadama Abbu abubuwa da yawa kamar yanda yake roke shi, ya fada mishi yanda yanzun haka yake ji kamar ana zare mishi rai kallon Abbun da yake, cikin tsokar jikin shi kamar an hura wuta. Amman ya kasa, babu kalma daya da zata iya fitowa daga makoshin shi da yake ji kamar an shake. Saiya sadda kan shi kasa kawai, numfashi Abbu ya sauke, ya dauki kiran da Rayyan din ya yi mishi a matsayin amincewa da rokon shi.

“Na gode…”

Abbu ya fadi da sanyin murya yana ficewa daga dakin. Yau sai yake jin kamar akwai wata matsala mai girma tattare da Rayyan, matsalar da baisan ta inda zai fara shawo kanta ba. Amman addu’a, yana da yakini a kan addu’ar shi ba zata taba tashi banza ba, zai magana ta fahimta da Ayya, zai gaya mata da ta kara tsananta addu’arta akan Rayyan din, zai kuma yi magana da Mami itama dole. Rayyan ya kalle shi yau ya girgiza mishi kai a tambayar ko yana son Layla. Amman ya rasa dalilin da yasa ya kasa yarda, haka kawai zuciyar shi na mishi rawa akan abubuwa da yawa yau din nan.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Shine abinda yake furtawa yana karawa har ya kai daki.

“Allah ka musanya mun kaddarar duk da zaka dora akan yarana, Allah ka fini sanin zuciyata, amman ni inaji kamar kowacce kaddara ba zata dauku a wajena ba in har ta hada da yarana…”

Shine kalaman shi a cikin sujjada, a tsorace yake da lamarin rayuwar gabaki daya. A tsorace yake da kaddarar da yake hangowa kamar tana kusanto yaran shi, kaddarar da yake son amfani da addu’a ya gina katanga a tsakaninta da yaran shi. Domin sune raunin shi, abinda zai taba su zai taba shi fiye da su.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×