Skip to content
Part 11 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Kallon Abbu takeyi, bakin shi motsi yakeyi, da alama magana yakeyi, sautin maganar tashi ce bata karasawa kunnuwanta. Sosai take kallon shi tana kokarin fahimtar sauran zantukan da yake yi tunda ta daina ganewa daga,

“Tare da Layla zasu koma Zaria, itama ta sami gurbin karatu acan…”

Duk abinda ya fada kafin wannan kalaman batajin suna da wani muhimmanci a wajenta, abinda yake fada bayansu kuwa bata ma ji ba sam-sam. Ko bayan nashi bakin ya daina motsi, ta bude nata yafi sau biyar tana rufewa cikin rashin sanin abinda ya kamata ta fadi. Tashin hankali take ciki, irin wanda bata taba hangowa ba, a gaban idanuwanta abinda take tunani ba matsala bane yake zame mata katuwar matsala.

Wanne irin Malami ne wannan mai zafi Mami take da shi, zuwa yanzun Ayya zata iya rantsewa duk wani sirri nata a hannun Mami yake. In ba haka ba, babu yanda za’ayi data like wata kofar sai Mami ta sake huda mata wata. Duka yaushe ta samu kan Rayyan din haka, yaushe ta samu harya dauki waya ya kirata. Wannan zuwan ne har sau biyu da kan shi ya sameta yana gaisheta. Kuma ita da idanuwanta bata ganshi tare da Layla ba, har wani bacci takeyi mai cike da natsuwa a tsayin hutun nan da su Rayyan din sukayi.

Saboda tana ganin duk kudadenta da ta bawa Malam basu tashi a banza ba, aiki yaci. Ashe tana bacci Mami nacan tana wargaza mata abinda ta kashe maqudan kudi wajen ganin ta kulla. Ta rasa kalar bala’in nan, ta kuma rasa yanda zatayi da karan tsaye da Mami tayi mata a makoshi.

“Layla naji kace zataje Zaria… Ahmadi Layla…”

Cewar Ayya tana kallon shi kamar wadda bata cikin hayyacinta, wannan rikicin da yake gani cikin idanuwanta shi yake gudu yasa bai fada mata maganar tafiyar Layla Zaria ba. Wani zaiyi tunanin yana tsoron rikicin Ayya ne, kuma ba haka bane ba, yana gudun abinda zai bata mata rai sosai da sosai. Saboda yasan matar shi, kusan tare da juna suka mallaki hankalin su, babu kalar rikici da shirmen ta da baigani ba tun kuruciya. Ta rigada ta sakama kanta tunanin cewa Mami na bibiyarta, abinda duk zai fada mata kuwa ba sauraren shi zatayi ba, ya sani.

In ba ranar da Allah ya nuna mata tagani da idanuwanta cewa Mami bata bibiyarta ba, ba zata taba cire wannan tunanin daga ranta ba. Shisa ya kasa samun kwarin gwiwar fada mata Layla zataje Zaria. Yasan tunanin farko da zata fara bana cewa Layla da kanta ta zabi Zaria bane, sam Ayya ba zatayi wannan tunanin ba, idan yace mata bada son ran Mami za’ayi tafiyar ba zai ja musu wata matsalar, kishin shi zaisa ta dauka yana kokarin goyon bayan Mami ne, yanzun dole ya nuna mata yana tare da ita dari bisa dari ko dan a samu zaman lafiya.

“Eh, ta samu gurbin karatu a can, tana son karantar bangaren yaren turanci.”

Abbu yai maganar cikin taushin murya, kallon shin dai Ayya takeyi, kafin wata dariyar ta kwace mata.

“Idan dole ya zame mata sai tabar gari zatayi karatu, duk garuruwan da suke cikin Najeriya sai Zaria? Kuma kana kallo kabarta? Me yasa sai Zaria idan ba Rayyan take son tabi can din ba. Na rokeka, Ahmadi na rokeka daka raba Maryama da yarana, na kara rokon ka daka ja nata kunne ta kyalemun ahalina amman kayi biris dani.”

Ayya take fadi tana haki saboda bacin rai.

“Dan Allah ki kwantar da hankalin ki Maimuna.”

Wani irin kallo ta watsa mishi.

“Gayamun kake in kwantar da hankalina? Ka damu da kwanciyar hankalin nawa ne? Ka damu dashi? Da ka damu da kwanciyar hankalina da baka bar Layla ta bimun yaro har Zaria ba… Wallahi sam abin nan ba zai yiwu ba…”

Ayya ta karasa muryarta ba karyewa saboda wasu hawayen bakin ciki da taji sun cika mata idanuwa, hannunta Abbu ya kamo cikin sigar lallashi, ta fisge tana mikewa.

“Na gaya maka ka ja mata kunne bakayi ba, na fada maka… Karka ga laifina idan zaman lafiya yayi karanci a cikin gidan nan.”

Cewar Ayya tana wucewa ta fita daga dakin, yanda ta doko kofar saida Abbu ya runtsa idanuwan shi. Wannan abin shi yake gudu shisa ya zabi yau daren tafiyarsu Rayyan din tukunna ya fada mata. Ko rikici zatayi bayaso tayi a gaban yaran, duk da in dai ana sabawa da rigimar Ayya, to zai iya cewa duk wanda ya ke kwana yana tashi a cikin gidan ya saba. Amman wani lokaci sai tasan yanda tayi ta fada maka maganar da zata zo wuyanka tayi tsaye. Shi jiya ma da yaje wajen Yaya Ayuba yake bashi shawara tunda dai yana da rufin asiri, kuma yana da hali ya kamata ace ya sami yar karamar mota an ba su Bilal, saboda zirga-zirga.

Tunda Yaya Ayuba ya kula da yanda yake yawan ganin sun zo gida daga makaranta, shima nashi yaran biyu da suke karatu a Bauchi motar ya hadasu da ita. Kuma ya dauki shawarar Yaya Ayuba. Akwai ‘yar karamar mota a gidan da yakan dauka wani lokaci, ko in za’a kai Mami unguwa. Tunda ita Ayya tana da abin hawa. Ya kuma rigada ya kira Bilal tun dazun yace su taho da Rayyan, shigar da sukayi kuwa a fuskar Rayyan zaka fahimci yanda yake a takure, dan ko zama cikin kujera sosai yakiyi, a gefen hannun kujerar da Bilal ya zauna shima nan ya samu ya zauna.

Yana saka Abbu jinjina wannan lamari. Ace ka haifi yaro, kiri-kiri yana gudunka, shekaranjiya Rayyan na hango shi yayi baya yana komawa inda ya fito, abin yayiwa Abbu ciwo ba kadan ba. Ya kasa sabawa da yanda Rayyan yake baya-baya da shi. Ko lambar wayar Rayyan din bashida ita, baya kuma zaton Rayyan yana da lambar shi a waya shima. Inda ace ya yarda da sihirine, yana kuma da abokin gaba, tabbas zaice an saka mishi hannu ne, an shiga tsakanin shi da danshi. Amman yasan bashida abokin fada, babu wanda zai kuma zarga da lokacin batawa wajen bibiyar rayuwar shi.

Dauke idanuwa yayi daga kan Rayyan yana mayarwa kan Bilal bayan sun gaisa.

“Daman naga zirga-zirgar da kuke tsakanin Kano da Zaria tayi yawa, ga Layla kuma yanzun. Shisa nace wannan karin ku koma da mota, kunga duk idan zaku zo ba sai kunyi ta jigilar zuwa tasha ba.”

Murmushi Bilal yayi yana tashi ya karbi mukullin motar da Abbu ya dago hadi da cewa,

“Allah ya kara arziqi da lafiya Abbu…mungode…”

Ya koma ya zauna yana kallon Rayyan.

“Hamma ga mota Abbu ya bamu.”

Kamar Rayyan din baya dakin, sai lokacin ya dago da idanuwan shi yana kallon Bilal.

“Kai kasan ban iya tuqi ba, me yasa kake fadamun?”

Rayyan ya karasa maganar yana dan kankance idanuwan shi saboda yanda kanshi yake bala’in sarawa tun da Bilal yace mishi Abbu yana kiran su. Sanda yake dosar dakin Abbu din ji yake kamar ana zare mishi rai. Kafafuwan shi ma rawa suka dingayi kamar ba zai iya karasawa ba, shisa kallo daya yayiwa Abbu ya mayar da kanshi ya sauke. Muryar Abbu dinma cikin kunnuwan shi kara mishi abinda yake ji takeyi. Jikin shi yayi wani irin dumi kamar gidan biredi. Duk akan za’a bada wata mota ne aka kira shi ya shiga wannan halin.

Duk ranar bayajin dadin jikin shi, shisa ko da Bilal yayi mishi magana baiyi gardama ba ya mike, yasan halin Abbu, in har magana yake sonyi dasu da gaske, idan ma baije ba shi zaizo ya same su har daki, da kuma yasan yanda Rayyan din yake ji duk idan sukayi kusanci taku goma a tsakanin su da bai fara zuwa kusa da shi ba, balle harya shigo dakin da yake yana saka iskar duk da take dakin tayi mishi kadan, zai rantse ko meye a tsakanin su da Abbu, yana girma ne abin ma yana kara girma. Ga mugaye mafarkan da yake fama dasu daya runtse idanuwan shi.

Rabon shi da bacci da daddare batare da taimakon wasu kwayoyi ba harya manta, zuwa yanzun saboda karatun shi yana fahimtar abubuwa da yawa da suka shafi kwakwalwar shi, yana kokarin ganin ya fassara matsalolin shi scientifically batare da zargin iskokai da yakan ji ana hada shi dasu ba. Yasan yana da matsaloli kala-kala, ciki harda abinda ake kira depression a turance, yanayin da kwararrun likitocin daya gani a fannin kwakwalwa sun kasa taimaka mishi wajen gano abinda ya haddasa mishi depression din. Kuma shine ma a fadar su ya jaza mishi insomnia. Shisa baya iya bacci da dare, babu wanda yasan baya iya bacci da dare tun tasowar shi.

Har Bilal da suke kwana waje daya su tashi baisan baya iya bacci da dare ba, tunda zai kwanta ya huta, zai saka hakarkarin shi a kasa, lokacin kuma duk da zaiji baccin to yana runtsa idanuwan shi ya fara wasu irin hargitsatstsun mafarkai da baya iya tuna farkon su balle karshen sune suke tashin shi. Da farko-farko magungunan da aka bashi kala biyu wato Anti-depressant sun dan fara mishi aiki, tunda yana bacci, amman magungunan suna saka mishi wani irin qunci na daban, sun kara mishi rashin hakuri da mutane.

Abu kadan ne yake harzuqa shi fiye da yanda yakeyi da. Daga baya ma guda biyu sun mishi kadan, bayajin komai idan ya sha. Yanzun a halin da yake ciki guda hudu asibiti sukace ya dinga sha. Kuma ba’a bayarwa da yawa, na sati biyu suke bashi, idan ma ya shanye kafin lokacin yasan ba zasu sake siyar mishi ba. Sai dai cikin gidan da yake haya akwai yaro daya daya kula yana siyar da kwayoyi, a wajen shi Rayyan yake siya, akwai wanda suka fi na asibitin karfi, kuma suna taimaka mishi ba kadan ba. Yanzun ma so yake ya tashi yaje yayi wani hadin da zai batar mishi da ciwon kan da yake ji. Inda yasan maganar wata mota ce Abbu zai mishi sam bazai zo ba.

Idan waje baya kama dole ya hau mota ba, bata dame shi ba. Ko makaranta yana rigan Bilal fita, daya saka earpiece da wayar shi zai taka da kafafuwan shi, yafi zabar yayi tafiya akan ya hau mashin. Saboda ita kadaice abinda yakan taimaka mishi ya samu natsuwa wasu lokuttan.

“Jikin ka baya maka ciwo?”

Bilal kan tambaye shi wani lokaci, kafadu yakan dagawa Bilal din kawai tunda baisan yanda zai fara mishi bayani cewar wannan doguwar tafiyar da yakeyi wani lokaci ita kadaice katangar da yakeji a tsakanin shi da tabin hankali, lokutta da dama yanajin kamar zai ta kurma ihu saboda duhun da yakeji cikin kan shi. Wasu lokuttan har sallah ma bai samun nutsuwa idan yayita, kullum cikin neman wani abu da zai saka mishi natsuwar zuciya yake amman ya rasa. Haka yake rayuwa badan yanajin dadinta ba, amman babu wanda yake fahimtar haka.

Wani lokacin yakan ji dariya daga dukkan zuciyar shi idan ya addabi Layla. Ko yana ganin yanda take son kwala mishi wani abu a cikin idanuwan nan nata da suke fadar mishi da gaba amman babu yanda zatayi. Shisa idan bai ganta ba bayajin dadi, Layla kan samar mishi da natsuwa wasu lokuttan. Mikewa yayi, daga Abbu har Bilal binshi sukeyi da kallo harya fice daga dakin, kafin Bilal ya mayar da idanuwan shi kan Abbu da yake kallon kofa har lokacin da wani yanayi a fuskar Abbun da Bilal yakeji har cikin zuciyar shi. Shima mikewa yayi.

“Abbu sai da safe.”

Wani numfashi mai nauyi Abbu ya sauke yana fadin.

“Sai da safe Bilal, Allah ya tashemu lafiya. Allah kuma ya saukeku lafiya idan bamu kara haduwa da safe kafin ku wuce ba.”

Kai Bilal ya jinjina.

“Amin. Zamu shigo ma ai in shaa Allah…”

Sallama yayiwa Abbu yana fita, dakin su ya nufa inda ya sami Rayyan a zaune da kofin ruwa a hannun shi. Da alama hankalin shi na wani wajen dan ko sallamar da Bilal yayi bai amsa ba. Shikuma yayi shirune saboda yanda kan shi yake sarawa har lokacin, yaki jin numfashin shi ya koma dai-dai. Iska bata kai mishi inda ya kamata, kwayoyin da ya sha yake jira su narke su fara mishi aiki ko zai dawo dai-dai. Shisa yake zaune shiru yana sauraren ikon Allah. Bilal gado ya hau ya matsa can yana kwanciya saboda baccin da yake idanuwan shi, kuma ya kasance cikin jerin mutanen da baccin su yake da muhimmanci a wajen su, sam abinda yake shiga tsakanin shi da bacci to gagarumine.

*****

Idan tace yanda taga dare haka taga rana batajin zatayi karya. Bacci ko da ya saceta to barawo ne tabbas, haka ta kwana tana juyi, ta kwana tana tunanin a duniya abinda tayiwa Mami mai zafi haka da take son taga bayanta. Kamar ba ita ta aure mata miji ba, kamar ba ita tayi mata babban laifi ba, kamar ba ita ta sakata raba soyayyar Ahmadi da take ji har kasan ruhinta ba. Duk ta hakura, duk ta kauda kai, badan kishinta ya ragu ko kadan ba, ko giccin Abbu tagani ta bangaren Mami sai taji kamar zuciyarta zata fado.

Ranar karshe da taga Abbu yana dariya da Mami numfashinta barazana ya dinga yi mata. Dariyar Abbu ita kadai take son jin sautinta, a yanzun inda zata baiwa Mami duk wani abu data mallaka ciki harda dukiyar Abbu din ta fice tabarta daga ita sai shi zata mika mata da gudu. Amman Mami tabbas mayya ce, bata hada jini da nupawa ba kamar Layla, amman watakila kafin Allah ya dauki ran Mannira ta baiwa Layla kankarun maitar, ta kuma zo dasu cikin gidan nan ta raba su da Mami.

Duk abinda tayi mata bai isheta ba, tana hango tauraron Rayyan da Malam ya fada musu mai haskene sosai, shisa take son dishe shi. Saboda bata tsoron Allah, bata tunanin ya kamata ta kyaleta ta huta haka.

“Allah ya isa tsakanina dake Maryama, wallahi ba zan yafe miki ba. Kin hanamun natsuwa, kudin dana tara ma kina neman sakani asarar su wajen malamai, me nayi miki haka?”

Ayya ta dinga fadi tana juyi har wayewar gari, kan kunnenta aka kira sallar asuba. Dakyar ta mike tana gabatar da sallah, addu’ar nemarwa yaranta tsari tayi tana mikewa ta wuce kitchen tunda tasan Rukayya ko da zata fito sai ta gama karatun Qur’ani da azkar dinta na safe. Kuma tana son su Bilal suci wani abu kafin su fita, akan ce.

“Mayu sunfi samun damar kama mutum idan ya fita baiyi karin safe ba.”

To su da Mayya zasuyi tafiyar tasu kacokan, gara ta basu duk wata kariya da zata iya, kafin ta samu ta kira Hajiya Dije dan samun mafitar wannan bala’in, farraku take so ayi ma Layla tsakaninta da Bilal da Rayyan. Gara ayi musu katanga ta bakin karfe yanda zata sama musu lafiya duk kowa ya huta. Ko nawane kuwa zata kashe dan ganin an rabasu, da ita Mami take magana.

“Mu zuba mugani Maryama. Ke din banza.”

Ta fadi tana kara cigaba da fere doya. Saboda tana tunani sai taga aikin yayi mata sauri sosai, dan harta soya doya da kwai kafin wani lokaci. Aikam kamar daga sama taga Rayyan ya fado kitchen din.

“Ayya yunwa nake ji.”

Ya furta da wani yanayi na rauni a muryar shi. Magungunan da yasha ne yasan suka wawake mishi ciki haka, kuma rabon shi da abinci tun jiya da rana, baici na dare ba saboda bayajin dadi. Yau dakyar ya fita masallaci, a hanyar dawowa kuwa har wani haske yake gani yana gilma mishi ta cikin idanuwan shi, a daddafe yayi wanka ya sake kaya yana yanke shawarar zuwa wajen Ayya din ta bashi koma meye yaci kafin yunwa ta kashe shi.

“Ga doya na soya muku daman, in hada maka shayi?”

Ayya ta bukata tana kallon fuskar Rayyan din, dan gani takeyi kamar zai iya juyawa kowanne lokaci yace tafiya zaiyi. Yaushe rabon da tagan shi da sassafe haka. Kai kawai ya daga mata yana bude kular ya dauki doya daya yana sakawa a bakin shi. Yunwa yake ji sosai, shayin Ayya take hada mishi, batare daya kalleta ba yace,

“Kar ki saka mun sikari da yawa Ayya.”

Bata saka mishi din ba, tana gama hadawa ta sami faranti ta zuba mishi doyar a ciki, da kanta ta dauko mishi zuwa falo yana biye da ita da kofin shayin shi a hannu. Ajiye mishi tayi, dai-dai lokacin da Rukayya ta fito daga dakin.

“Hamma…”

Ta furta cike da mamaki tana dorawa da.

“Ina kwana.”

Kallonta Rayyan yayi.

“Rukayya. Lafiya…ya kika tashi?”

Wani murmushi da tayi mishi sai tasa yanajin wani iri, saboda tanayi kamar ya bata wani abu. Taji dadi har ranta, rabon dayayi magana mai tsayi da ita harta manta, yaushe ma tagan shi balle yayi mata magana.

“Alhamdulillah, yau zaku koma makaranta ko?”

Zama Rayyan yayi yana jin kurbar shayin hadi da kallonta, idan tasan yau zai koma meyasa take kara tambayar shi, shisa bai son a fara wasu kananun gaishe-gaishe, suna jan surutun da bai kamata ba. Kai kawai ya daga mata yanaci gaba da karyawa abin shi.

“Allah ya tsare muku hanya ya kaiku lafiya.”

Kallonta ya karayi dan shine kawai amsar da zata samu yana cigaba da abinda yakeyi, itama kitchen ta wuce abinta. A hakan ma itace da godiya yau tunda har an kulata anyi magana da ita. Yana karasa cinye doyar ya tashi da kofin da plate din a hannun shi, daya shiga kitchen saida ya wanke su yana mayarwa inda yaga Ayya ta dauko su tukunna ya fito, ita kuma tana bakin kofa tana kallon shi, zuciyarta cike taf da kaunar yaron nata, yanzun take kara tabbatar da duk a yaranta babu mai sanyin hali irin na Rayyan, tun yana dan karamin shi yake da sanyin hali, lokaci daya ya canza, tayi sakaci da ta dauka abinda yasha ne, sam bashi bane ba. Mami ce ta shiga tsakaninta da yaronta ta juyar dashi ya koma haka.

Amman Allah yana nan.

“In zuba maka ka tafi da itane? Ko zakuci a hanya?”

Dan jim Rayyan yayi, doyar tayi mishi dadi, yasan kuma inba gida ya dawo ba, babu wani abu da zaici mai dadi. Girkin Bilal hadiyewa kawai yake batare daya tsaya yaji dandanon a bakin shi ba saboda yanda yake a hargitse. Amman gara rashin dadin girkin tunda a gaban shi akayi, ya kuma daina cin abinci a waje yanzun tunda Bilal din yana girka musu. Kwanaki yace,

“Bansan zan kewar Hamma Haris ba sai yanzun. Bilal kasheni zakayi? Meye wannan ka dafa?”

Harara Bilal din ya watsa mishi, duk da shima a lokacin kawai yana tura taliyar ne badan yana gane kanta ba.

“Surutun duk da ba’a so kayi shi kakeyi, wallahi zan daina dafawa in dinga siya a waje.”

Hakan da Bilal ya fadi ne yasa Rayyan din yin shiru, amman da gaske yake yayi kewar Haris a makarantar. Tunda abincin shi da dadi, kuma ranaku dai-daine baya dafawa ya kawo musu, wani lokacin ma har miyar da zasu kwana biyu idan yazo yana musu. Amman abinda Bilal yake dafawa yana da tabbacin ba abincin mutane bane ba.

“Akwai ne?”

Ya bukata yana kallon fuskar Ayya, saboda bayason su wanda zasuci a juye musu, kuma suzo sai sun sake dafawa.

“Saboda ku na dafa daman ai…”

Ayya tayi maganar tana murmushi, shiru Rayyan yayi yana tsayawa. Hakan ya bata amsar da take bukata. Manyan robobin da takan zuba kayan miya ko saura abincin inta rage ta saka a firij ta dauko tana juye musu doyar ta fito ta bawa Rayyan din. Yana karba ya fice daga dakin, sosai zuwan shi ya ragewa Ayya damuwar data kwana da ita, gaskiya wannan Malamin ya cancanci duk tarin kudin daya amsa a hannunta, aikin shi mai karfine, ta dauka Mami tayi nasara. Dole ta kara komawa wajen shi yayi mata wannan aikin, tunda da tana tunanin tayiwa Hajiya Dije magana ne su sake wani Malamin da yafi shi zafi.

Rayyan kam dakin su ya wuce yana ajiye doyar da fadin.

“Ayya ce ta zuba mana. Ni naci amman…”

Kai Bilal ya jinjina mishi, shi ba iya cin abinci yakeyi da sassafe haka ba. Jakun kunan su ya dauka ya kai mota, daman duk ya saka na Hindu a ciki. Ya dawo ya dauki robar da Rayyan din ya ajiye. Tun jiya da rana ya siyo ruwan roba tunda yasan Rayyan da shan ruwa kuma ba siya zai ya tafi da shi ba. To yanzun tunda motar su ce, duka ledar ya saka musu a ciki, ya dawo yana fadin.

“Duka abinda zaka dauka ne ka fito da shi?”

Kai Rayyan din ya daga mishi.

“Yayi kyau.”

Bilal ya furta yana ficewa, tunda suka tashi Rayyan din yaga Bilal na sha mishi kamshi, yayi tunanin duniya ko yayi mishi wani abu ya kasa tunawa, shi bayason Bilal na mishi haka babu wani dalili. Sai yana saka shi jin babu dadi sam-sam. Mikewa yayi tunda yasan Bilal din zaije yayi sallama da Ayya ne, dakin ya kulle yana saka mukullin a aljihun shi. Wajen motar ya karasa, gajiya da yayi da tsayuwa ya saka shi taba murfin bayan motar yana samu Bilal bai rufe ba, nan ya shiga. Ba zai zauna a gaba Bilal din na mishi wannan kumbure-kumburen ba.

Bilal kuwa wajen Ayya yaje sunayin sallama, da nauyin jiki ya fito saboda tana kara fada mishi ya kula da kan shi, ya kula da Rayyan. Tana kara mishi nauyi akan wanda Abbu ya dora mishi. A hanya ya hadu da Layla da ta saka hijab, sai yaga tayi mishi kyau sosai, fuskarta fayau babu kwalliya yau.

“Hamma ina kwana.”

Ta fadi da bacci cike da muryarta, bata ma jira ya amsa ba ta wuce. Zumudi ya hanata bacci daren jiya. Sai wajen karfe uku da rabi na dare, sai taga kamar tana rufe idanuwanta Mami tazo ta tasheta, ta samu tayi sallah. Nasiha tun da Abbu ya amince da tafiyarta Mami takeyi mata, yau dinma tana gama shiryawa taga Mami a ranta tace,

“Ni kam naga ta kaina… Wa’azi da asubar nan.”

A fili kuwa murmushi tayiwa Mami har hakoranta suka bayyana. Mamin ma murmushin tayi.

“Yar nema, yau ni akeyiwa wannan murmushin da bai kai zuci ba ko?”

Dariya Layla tayi sosai, wani lokacin yanayin kular Mami har mamaki yake bata

“Dan Allah ki rufamun asiri Layla, ki kula da kanki, karki ji tsorona, karkiji tsoron me zance, kiji tsoron Allah dan Shi yana ganin ki a inda ni bana ganin ki. Ki kula da kanki, idan duk kina da matsala kinsan kirana kawai zakiyi ko?”

Kai Layla ta daga mata, yanayin muryar Mamin na sanyaya mata jiki.

“Allah ya tsare mun ke a duk inda zaki shiga. Allah ya taimake ki ya baki sa’a, Allah ya banj aron rayuwa inji ki a gidan Radio din da kike buri.”

Da sauri ta matsa tana fadawa jikin Mami din.

“Karyani Layla.”

Mami ta fadi muryarta na rawa, kwalla cike da idanuwanta, a kasan kewar Layla akwai tarin shakku da tsoro da ta kasa kawarwa daga zuciyarta. Babu yanda zatayine, Layla da Abbu sun rinjaye ta, sunki fahimtar tsoronta. Shisa ta zabi ta bi Layla da addu’a kamar yanda Abbu ya fadi.

“Allah Shi ne yake tsarewa, Shi ya tsare mana su har zuwa wannan lokacin…ba tsoron mu ko dabara ba.”

Numfashi ta sauke a fili tana zagaya hannuwanta ta rike Layla a jikinta sosai.

“Ina son ki Mami, da yawa fa.”

Dariya kawai tayi, da Layla da Jabir basa gajiya da fada mata suna sonta, ko a gaban waye Jabir zaice yana son ta, musamman idan tayi mishi abinda yaji dadi. Kalaman na sanyaya mata zuciya ko da bata mayar musu ba, abune da bai yawaita a al’adar mu ba. Su kam sun mayar da shi kamar tun tasowar su sun sabajin ana fadin kalaman a tsakanin iyaye da yaran su. Tana son yaran, tana jin su a ranta, kawai batason dabi’ar nasaran da suka daukarwa kan su.

Musamman Jabir ma yanzun da yake ganin sai ta daga kai take hango shi, kuma kai tsaye zasuyi magana batare da sun tauna ba, suna ganin sun kai matsayin da zasu fadi duk abinda yake ransu, ga taurin kai, idan har suka kafe akan abu dai-dai ne to babu wanda ya isa yace musu ba haka bane ba. Halayen turawa shi suka daukarwa rayuwar su, kamar da suka shiga islamiyya haka suka fito batare da islamiyyar ta ratsa su ba. Addu’a ita take bin yaranta dasu har na Ayya ma, Allah ne shaida bata tashi daga wajen sallah bata hadasu duka a addu’o’inta ba.

Haka sukayi sallama da Mamin, bacci take ji idanuwanta har wani yaji-yaji yakeyi. Shisa sanda Bilal yazo daukar kayanta bata samu ta gaishe dashi ba sai yanzun. Abbu ya gaya mata ya basu mota, kuma tasan motar, tana zuwa ta bude bayan motar ta shiga. Ko kadan batayi tunanin Rayyan yana ciki ba harta ja murfin ta zauna. Numfashi ta sauke, Rayyan kuma idanuwan shi a lumshe suke, dan yasan yau zai samu yayi baccin safe tunda motar gida ce bata haya ba. Kawai yaji ana shigowa, hakan yasaka shi bude idanuwan shi, gyara kwanciya yayi yana juya kan shi ya kafa ma Layla ido.

Itama zama ta gyara tana dan juyawa taga an mata kuri.

“Wayyoo Allah…”

Ta furta da karfi saboda gabanta ya fadi sosai.

“Hamma”

Ta furta har lokacin da tsoro a muryarta .

“Baki da hankali? Da safe zaki zo kina mun ihu a kunne?”

Ita bata neman tashin hankali, tasan ko tafiya zasuyi zai zauna a gaban mota ne. Shisa ma ta bude bayan motar ta shiga abinta. Baccine a idanuwanta har sun mata nauyi.

“Kayi hakuri, dan girman Allah Hamma, wallahi bansan kana nan ba sam sam, ina kwana.”

Ta karashe a gajiye, hararta yayi yana jan wani tsaki dai-dai lokacin da Bilal ya shigo motar ya zauna. Juyawa yayi yana kallon su hadi da sauke numfashi .

“Me kuke nufi?”

Ya bukata, tunda shi yasan su duka Abbu ya baiwa mota, baice ya zama direban su ba balle su kame a bayan mota gabaki daya.

“Wani ya dawo gaba.”

Ya fadi yana kallon Rayyan daya kauda kai.

“Magana fa nakeyi.”

Cikin ido Rayyan ya kalle shi.

“Kana shamun kamshi tun da safe.”

Ya fadi kamar wani dan karamin yaron da kaiwa dukan tsiya kazo kuma kana yiwa dariya. Layla Bilal ya kalla, ita kuma ta kalli Rayyan din kamar tana neman izinin shine kafin ta koma, shikuma ya rigada ya lumshe idanuwan shi. Numfashi Bilal ya sauke yana runtsa idanuwan shi ya bude su a lokaci daya. Tuqi zaiyi, yana bukatar gabaki daya natsuwar shi, idan ya biye musu zasu birkita mishi lissafi, hakan yasa shi gyara zama, addu’a yayi yana jan motar suka fice daga gidan, sun kama hanyar da zata fitar dasu daga Kano kenan Rayyan ya bude idanuwan shi yana ganin Layla a zaune a kusa da shi.

“Mayya ce ke? Dole sai inda nake zaki zauna?”

Wani abu taji ya tokare mata zuciya yanayin yanda Rayyan din yayi magana. Inda ta tashi ta koma gaba ya bude ido kamar yanda yayi tana da tabbas zaice wani abu, dole saiya nemi dalilin da zai sata dana sanin tafiyar nan, bayan tun da satin ya kama take tunanin yanda zata zauna mota daya da shi, nishadin duk da takeyi ya dishe mata shi.

“Hamma ka tsaya in dawo gaba.”

Layla ta fadi da wani yanayi a muryarta, ta mudubin gaban motar Bilal ya kalle su.

“Na dora wayata a kujerar, kuyi zaman ku.”

Kafin ta karayin magana ya kunna radio din motar yana kure maganar.

“Ka fasa mana kunne Bilal!”

Rayyan ya fadi a masife, ko kallon su Bilal baiyi ba, balle kuma suyi tunanin zai saurare su, ba yanda za’ayi su rabashi da nutsuwar shi yana tuqi. Matsawa Layla tayi tana kara bada tazara tsakaninta da Rayyan din, jingina kanta tayi da jikin motar tana rufe idanuwan ta, duk yanda take jin ranta na mata susa bai hana bacci dauketa ba, Rayyan kallonta yakeyi duk da yasan bacci ya kamata yayi. Yanajin inama ace haka zata zauna, yanda zuciyar shi tayi wani luf a kirjin shi abin ya mishi dadi, amman yasan tashi zatayi, bude idanuwanta zatayi ta hargitsa mishi komai kamar yanda ta saba. Baisan me yasa zata zo da idanuwan mage ba.

Idanuwan shi na kafe a kanta, tana ta baccin ta, a cikin baccin ta juyo kwanciya, ganin da yayi kamar wuyanta zaiyi ciwo yasa shi girgiza kai kawai, babu wani abu da zatayi dai-dai, baccin ma ba zatayi shi dai-dai ba. Yana wannan mitar a zuciyar shi ya mika hannu ta baya dan ya dauko ruwan da Bilal ya ajiye, sai jin kan Layla yayi saman hannun shi, kamar ya mika ne dan ta kwanto, da dayan hannun shi ya tallabe wannan, yana zare shi a hankali, ruwan ya dauka sai ya dan janyo jikin shi yana gyara zama yanda kanta zai kwanta a kafadar shi da kyau.

Robar ruwan ya bude yana sha sosai, ya mayar ya kulle, yanajin Layla ta kara gyara kwanciyar ta a jikin shi, tana kwantowa sosai. Wani irin dokawa zuciyar shi takeyi kamar zata fito daga kirjin shi.

“Mayya…”

Ya furta a hankali yana sauke numfashi, sosai ya jingina kan shi da motar yana lumshe idanuwan shi, bugun zuciyar shi yake saurare da yake ji har cikin kunnuwan shi, kafin wata natsuwa daya kwana biyu baiji ba ta saukar mishi, bacci mai sanyi na dauke shi, baisan sanda ya jingina nashi kan dana Layla da yake kafadar shi ba. Kawai abinda ya sani wannan karin baccin nashi babu mugayen mafarkai ko daya. Ta gaban mudubi Bilal ya hango su, yanajin kamar an soka mishi wani abu a kirjin shi, sosai zuciyar shi ke dokawa kamar mai shirin samun matsalar bugun zuciya.

Shi yake bukatar kulawa.

Shi yake cikin matsala.

Shi yake bukatar Abbu da Mami su fadawa Rayyan daya kula da shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 10Martabarmu 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×