Skip to content
Part 18 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Da wani irin ciwon kai ya sauka, ga alamun zazzabi yanaji. Ya kira wayar Layla yafi sau goma bata daga ba. A ranaku da ba irin na yau ba, kira daya idan yai mata bata daga ba shikenan. Ya san in tazo zata kira shi. Amman yau din wani irin tsoro yake ji da bai san dalilin shi ba, tsoron ma bai kara yawa ba sai da ya kira Bilal shima bai daga ba. Bilal da ko karatu yake sai ya mishi magana zai ajiye waya ya natsar da hankalin shi waje daya. Idan jarabawa akeyi ma, kamar yaro haka zai ce,

“Ban wayar nan Bilal…”

Zai saka a key ya ajiye yana fadin,

“Na ajiye Allah kuwa Hamma.”

Sanin halin shi yake saka Rayyan din kin yarda, sako na shigowa zai sake dauka, shisa yakan mike ya dauki wayar ya ajiye a gefen shi.

“Kayi abinda yafi danna wayar muhimmanci.”

Yakan fada mishi, ya rasa dadin me suke ji shi da Layla kan danne-dannen wayar nan. Ji yake kamar ya tsaya a hanya ya samu wata motar da zata juya da shi Zaria saboda rashin natsuwar da yake tare da ita.

“Allah Ka san halin da nake ciki, Ka san damuwa ta, Ka san zuciyata ba zata iya daukar wani abin ba. Allah Ka sa lafiyar su.”

Shine abinda yake fadi yana maimaitawa, duk inda network zai dawo mishi sai ya gwada lambar Bilal da ta Layla, amman duka tana shiga basa dauka ne. Yana sauka a tashar ya tsaya ya kira Bappa da bugu daya ya daga yana sallamar da bai jira Rayyan din ya amsa ba ya dora da.

“Har ka karaso ne? Ka jirani a tashar in zo yanzun.”

Rayyan din dan da kuna fuska yayi, saboda Bappa nayi kamar sun san juna, kamar sun saba ba yau bane farkon maganar su.

“Eh, ok tam.”

Rayyan ya iya cewa yana sauke wayar daga kunnen shi, fita yayi daga tashar zuwa bakin titi. Anan yayi tsaye, masu mashin da napep na ta mishi magana, harya kawo iya wuya, ga shi gari yayi duhu tunda sai bayan Magriba suka sauka.

“Alhaji tafiya ne?”

Wani mai mashin ya fadi a karo na biyu, kamar bai ga ya girgizawa mutane wajen hudu kai cikin alamar a’a ba.

“Sai ka daukeni ka dorani, me yasa dole sai kun sa mutane magana ne?”

Jinjina kai mai mashin din yayi.

“Allah ya baka hakuri, daga tambaya.”

Wani irin kallo Rayyan ya watsa mishi, dai-dai lokacin da wata mota baqa, kirar Honda Accord DC V6 ta tsaya a gaban shi. Gilashin aka sauke daga bangaren da yake, kafin aka kunna fitilar cikin motar haske na gaurayewa.

“Rayyan?”

Bappa ya fadi daga cikin motar, Rayyan din na jinjina mishi kai.

“Muje…”

Cewar Bappa, hannu Rayyan yasa yana bude murfin motar ya shiga, batare da yace komai ba ya rufe. Bappa ma baice mishi komai ba yaja motar, hankalin shi sam ba’a kan titi yake ba, shi dai yana garin Bauchi, zaune a cikin motar Bappa da sai kamshi takeyi. Amman hankali da natsuwar shi suna garin Zaria. Baisan anyi parking ba sai da Bappa yace mishi

“Mun zo.”

Budewa ya yi yana fita, in da duk Bappa ya sa kafar shi nan Rayyan yake mayarwa, ko sunan Hotel din bai duba ba, daga yanayin shi bayan sun shiga ya dan gane ko ina ne, ciki suke shiga sosai har suka karasa daki mai lamba 19, inda Bappa ya zaro mukulli daga aljihun shi yana bude dakin. Da sallama ya shiga, Rayyan na biye da shi, ya mayar da dakin ya rufe, akwai haske gauraye da dakin, babba ne da tanqamemen gado sai TV da take ta aiki, amman babu magana, anyi kasa da ita. Har da kujera doguwa a cikin dakin. Yayi kyau sosai da sosai. Ko ina a gyare tsaf, da alama zaiyi tsada.

“Na san ka kwaso gajiya, ga sallah kuma da wahala kun tsaya…”

Bappa ya fadi yana saka Rayyan kallon shi, dogo ne dan da wahala idan bai mafi Rayyan din tsayi ba, sai dai shi siriri ne, da kasumba a fuskar shi, akwai abin sallah a goshin shi, wata natsuwa Rayyan yake gani a tattare da Bappa, duk da kananun kaya ne a jikin shi yayiwa Rayyan din kwarjini. Mutanen da suke mishi kwarjini basu da yawa, duk izzar da kake tare da ita kuwa. Da hannu Bappa ya nuna mishi bandaki.

“Ga toilet din nan.”

Jakar da take rataye a kafadar shi Rayyan ya sauke akan kujera, bandakin ya karasa yana zira takalman da suke ajiye a bakin kofa ya shiga sosai yana rufewa. Har ruwa ya watsa, sannan ya daura alwala. Sanda ya fito sai yake jin shi ya samu yar natsuwa. Sai kan shi da yake ciwo kamar ganga ake bugawa a ciki. Baiga Bappa ba a dakin ya dai shimfida mishi darduma, sun tsaya suka yi azahar inda akaci abinci, shi banda nutri-milk da biscuit babu abinda ya sakawa cikin shi, shima dan yana bukatar wani dan karfi ko ya yake kafin zullumi ya saka shi faduwa.

Sallolin shi yayi a nutse yana zaro wayar shi ya duba, ganin lokacin isha’i yayi ya saka shi gabatar da ita. Zaune yake akan kafet din yau ya rasa kalar addu’ar daya kamata yayi bayan rokon Allah da yasa daga Bilal har Layla lafiyar su kalau. Lambar Layla ya sake kira.

“Dan Allah ki daga.”

Ya fadi a hankali, amman bata daga din ba, haka Bilal. Rasa abinda yake mishi dadi yayi a duniya, saboda zuwa yanzun ya aminta da zuciyar shi, tabbas wani abu ya faru, babu yanda za’ayi yayi tafiya haka ace ko sau daya Bilal bai neme shi ba. Lakca zai tafi yayi yamma, in har bai fada mishi zai yi yamma ba ya dinga kira kenan har sai ya mishi text cewar yana aji.

“Wai ni karamin yaro ne Bilal?”

Ya taba tambayar shi wani lokaci da ya yi mishi kira goma akan shidda tayi ina ya tsaya bai koma gida ba.

“Ni dai ka dinga fadamun in ka san zaka biya wani waje.”

Bilal din ya amsa cike da damuwa a muryar shi, amman yau ya tafi wani waje mai nisa haka ace ko sau daya Bilal bai neme shi ba, da gaske ba lafiya ba, wani abu ya faru, ko da shi ko Layla. Saboda tunanin Rayyan din sam bai kai gida ba, kallon wayar shi yake kamar yana so ta taimaka mishi da wata maslaha. Amman shiru

“Ayya…”

Zuciyar shi ta ambata, a karo na farko a tsayin rayuwar shi da yaji yana son ya kirata da kan shi, yana kuma bukatar taimakonta, watakila ita tayi magana da Bilal a tsayin ranar. Ko Bilal bai yi magana da kowa ba, tabbas zai yi da Ayya, lambarta ya lalubo ya kira, zuciyar shi banda dokawa babu abinda take yi mishi, tana dagawa bai jira ta gama sallamar ba yace,

“Ayya kinyi magana da Bilal?”

Dan jim da tayi ya sa Rayyan din kiran,

“Ayya.”

Yana jin numfashin da ta sauke.

“Rayyan?”

Ta kira sunan shi kamar tana shakkun cewa da gaske ya kirata, da gaske tana magana da shi.

“Kunyi magana? Bilal…”

Ya sake maimaitawa.

“Ina ta kira bai dauka ba, tun da safe da yace mun ya kaika ta sha, yace yana da lakca da safen da, amman ba za’ayi ba zaije gida ya kwanta yayi bacci, har yanzun bai kirani ba, na kira shi yafi sau hamsin bai daga ba. Na kasa samun natsuwa.”

Runtsa idanuwan shi Rayyan yayi yanajin kamar bangwayen dakin na hadewa da shi a ciki saboda wani irin tsoro daya taso mishi.

“Kai ma bai neme ka ba?”

Ayya ta tambaya da wani irin yanayi a muryarta, kai Rayyan yake girgiza mata, tashin hankali bakon abune a wajen shi, ya san kunci, ya san rashin natsuwa, yasan bacin rai, har tsoro ya sani saboda yana jin shi idan ya ga mage, yana kuma jin shi duk idan ya sauke idanuwan shi akan Layla, ya san abubuwa da dama, tashin hankali bakon shine, musamman mai hade da firgici irin wannan. Kafin wasu dakika ya fara kokawa da numfashin shi.

“Rayyan!”

Yaji muryar Ayya kamar a wata duniya kafin wani haske ya gilma ta cikin idanuwan shi yana saka shi runtsa su ya sake budewa, ji yake kamar an kama kafafuwan shi an sadda kan shi kasa ana jijjiga shi, idan wani abu ya sami Layla, baisan ya zaiyi ba, amman bai kara sanin asalin firgici ba sai da yai tunanin wani abu ya sami Bilal.

“Gabana sai faduwa yake tun safe.”

Ya tuna maganar Bilal jiya da daddare.

“Kayi addu’a.”

Ya amsa shi, yana kallon yanda ya danyi jim kamar mai nazarin wani abu sai kuma yaci gaba da danna wayar da yake yi, sai yau din yaga kamar akwai rama a cikin idanuwan Bilal din da baigani ba sai yanzun yake tunawa.

“Ka kwantar da hankalin ka, watakila ko ya ajiye wayar wani waje bai ganta ba, ka san Bilal.”

Wani irin numfashi Rayyan ya sauke.

“Ni da ke mun san Bilal baya ajiye abu ya rasa in da ya ajiye Ayya.”

Cewar Rayyan yana sauke wayar daga kunnen shi ya kashe kiran, a gefe ya ajiyeta yana dafe kan shi da hannuwa biyu, tabbas da ace zai sami motar da zata juya Zaria ba zai kwana a garin nan ba yau, bashi da wata natsuwa idan bai sami Bilal ba. Bappa ne ya shigo da leda a hannun shi yanayin sallamar da Rayyan ya amsa ya dora da,

“Zan iya samun motar da zata koma Zaria yau?”

Da mamaki Bappa ya kalle shi.

“Da daren nan? Amman ka san hanyar ba aminci gareta ba ko? Kuma me yasa kake tambayar motar Zaria.”

Cike da damuwa Rayyan yace,

“Zan koma ne.”

Sai da Bappa ya karasa ya ajiye ledar hannun shi ya zauna sannan ya fuskanci Rayyan sosai.

“Lafiya dai ko?”

Bai san me yasa yaji kamar zai iya yadda da Bappa ba, bayan shi din baya yarda da mutane.  Amman yana cikin damuwa kalar da bai taba sani ba, taimako yake bukata ko daga wajen waye.

“Ina ta kiran kanina baya dagawa.”

Kai Bappa ya jinjina.

“Watakila baya kusa da wayar, ko kuma ya yarda ba’a kai da tsinta an kashe ba. Ko wani ya dauke, akwai dalilai irin haka.”

Kai Rayyan ya girgiza mishi, yau kalamai yake nema da zai misalta abinda yake ji Bappa ya fahimta.

“Banda kanina, Bilal ba haka yake ba. Zai kirani ko da wayar wani ne ya fadamun. Yaune na farko da muka yini bamuyi magana da juna ba.”

Numfashi Bappa ya sauke.

“In shaa Allah komai lafiya. Ka kwantar da hankalin ka, ba kada lambar ko abokin shi haka? Sai ka kira a duba shi?”

Kai Rayyan ya girgiza, a karo na farko yana dana sanin halayen shi, da ace ko lambar mutum daya a cikin gidan nasu yana da ita yau zata yi mishi rana.

“Mutum yana da ranar shi Hamma, duk yanda kake tunanin baka bukatar wani bayan ni da Layla ba fata nai maka ba, Allah kar ya nuna maka ranar da zata karyata tunanin ka…”

Ga ranar ta zo yau, ranar da Bilal ya yi mishi addu’a karya gani.

“Allah bai amshi addu’ar ka ba Bilal.”

Rayyan ya fadi a zuciyar shi.

“In shaa Allah komai lafiya. Na san zai kira.”

Numfashi kawai Rayyan ya ja yana mikewa da kyar, kamar abinda ake kira “anxiety attack” ne yake shirin kamashi saboda tashin hankalin da yake ciki. Inda jakar shi take ya karasa ya dauka yana budewa, jikin shi babu inda baya bari sanda ya dauko kwalin sigarin shi, ya dauki kara daya ya saka a baki ya lalubo lighter din saiya tsinci kan shi da juyawa, yau abubuwan da suke baKi a wajen shi yake tayi.

“In ba zaka damu ba.”

Ya cewa Bappa da yayi dan murmushi yana girgiza mishi kai. Kunna sigarin ya yi yana shanyeta cikin yan dakika ya sake kunna wata, sai da ya sha kara biyar, amman jikin shi bai daina kyarmar da yake yi ba. Karshen daya rage ya karasa bakin kofa inda ya hango kwandon shara ya zuba, harda kwalin daya tara toka a ciki. Dawowa ya yi yana kara saka hannun shi cikin jakar shi ya laluba, kafin zuciyar shi tayi wata irin dokawa da bata da alaka da su Bilal, ya manta magungunan shi, jiya bai saka a jakar shi ba.

“No.. No… Please no.”

Yake fadi cikin tashin hankali yana kara dubawa ko watakila bai manta din ba, amman babu su, har kayan ya fito da su yana duddubawa, kafin ya sake mayarwa yana runtsa idanuwan shi, ji yake kamar wani abu ne a cikin kan shi yau da yake jiran cikar lokaci kafin ya tarwatse. Juyawa ya yi ya nufi kan gadon, bai karasa ba yaji muryar Bappa da shaf ya manta yana dakin ta daki kunnuwan shi.

“Ka ci abinci sai ka kwanta.”

Kai Rayyan yake girgiza mishi yana zama a gefen gadon saboda yanda jikin shi yake bari, sosai yanzun yake bukatar magungunan shi, badan bacci ba, sai dan mugun sabon da jikin shi ya yi, jiya bai sha ba in zai tuna, yini biyu kenan bai sha ba, shisa jikin shi yake sanar da shi babu lafiya.

“Kana bukatar ka sa wani abu a cikin ka.”

Cewar Bappa da ya bude ledar take away din da yayo musu a cikin hotel din, shinkafa ce dafaduka ta sha nama da kayan hadi, harda hadin salad a gefe. Yana kallon Rayyan din ya sake girgiza mishi kai.

“Yunwa da withdrawal effect ba hadi bane me kyau.”

Bappa ya karasa maganar yana saukowa kasa kan kafet din dakin ya ja abincin shi daya saka cokali a ciki ya fara ci. Shi din ya karanci Psychology ne a kasar Amurka, zai koma yaci gaba, saboda yana son zama abinda ake kira Profiler, akwai graduate degree da zaiyi akan forensic psychology kafin ya fara aiki da hukumar tsaro ta yan sanda da yake a can kasar, yana da kokarin da yasan da wahala idan bai samu ba.

Shi din dan gidan Sheikh Abdullah Bappa ne, sunan kakan shi yaci wato Muhammad sai suke kiran shi da Bappa kamar yanda ake kiran kakan na shi, baban shi sanannen Malami ne, duk kuwa da tarin arziqin da suke da shi. Suna da dattako, ana kuma ganin girman su a garin Kano, da wahala ka kira sunan Baban shi ace an samu mutane biyar a waje babu wanda ya san shi ko yaji labarin shi. Tun da ya dauko Rayyan yaga alamun damuwa a tare da shi, karantar shi yake tayi har zuwa yanzun.

Yanayin dabi’un shi, yanda jikin shi yake kyarma da idanuwan shi da sukayi wani irin haske duk kuwa da doguwar hanyar daya sha yasa Bappa gane cewa yana ta’ammali da miyagun kwayoyi. Watakila shima Rayyan kamar sauran mutane ne masu fama da depression, daga shan magungunan da zasu taimaka sai su dinga kara daya akan ka’idar da likita ya rubuta, a hankali a haka sai abin ya zame maka shaye-shaye batare da ka kula ba. Ka kara wa kanka matsala da kanka. Rayyan kuwa shiru yayi yana tauna maganganun da Bappa yayi kafin ya kwanta yana juyawa, Bappa bai san shi ba, dan ya gane daya daga cikin matsalar shi baya nufin ya gane gabaki daya.

Amman jikin shi kyarma yake, makoshin shi yake ji kamar an zuba yashi saboda bushewar da yayi, harshen shi babu miyau ko daya a ciki. Numfashi Bappa ya sauke yana mikewa, Rayyan baiga me yake yi ba saboda ya rufe idanuwan shi har sai da ya karaso in da yake kwance yana fadin.

“Ungo.”

Bude idanuwa ya yi, yaga robar ruwa sai irin maganin shi guda biyu a dayan hannun Bappa, jikin shi na kara sabon bari ya mike yana karbar maganin ya watsa a cikin bakin shi hadi da lumshe idanuwan shi, kafin ya sake bude su yana karbar robar ruwan ya kora.

“Ka kara mun guda biyu.”

Kai Bappa ya girgiza mishi.

“Zai rikeka zuwa safe.”

Ya fadi yana wucewa ya koma inda ya tashi, abincin shi yaci gaba daci, Rayyan kuwa ya kai mintina talatin kafin maganin ya fara nutsar da shi, rawar jikin da yake ya bari, ya sake gwada kiran su Bilal amman shiru. Wannan karin Bappa da yake kwance akan kujerar cikin dakin yana danna waya ya kalla, a saman damuwar shi tunanin waye Bappa ya darsar mishi, haka kawai ya tsinci kan shi da son sanin waye Bappa?

*****

Sama-sama yake jin shi, iskar da yake shaka da fitarwa ma kamar an daureta da zaruruwa haka take shiga kofofin hancin shi. Jin shi yake kamar a cikin wani mugun mafarki da zai farka daga shi ko yaushe. Sai dai kamar ya farka kusan awa daya da ta wuce ko fiye da haka, babu agogo a hannun shi balle ya duba lokaci, ba shi da natsuwar kiyastawa kuma. Amman tabbas ya farka daga abinda ya tabbata ba mafarki bane ba, dumin jikinta ya fara tabbatar mishi da ba mafarki yake ba, kafin ya kara ware idanuwan shi akan fuskarta, wani irin mikewa yayi yana hankadeta gefe tare da fadin,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

A matukar razane, kan shi ya kalla da yanayinta itama kafin komai ya dawo mishi, ba Aisha bace ba, Layla ce, Layla ce. Wata murya a cikin kan shi take fadi tana maimaitawa. A matuKar gigice ya suturta kan shi, baisan abinda ya kamata yayi ba banda kokarin ganin ta tashi, dabarar ya shafa mata ruwa bata zo mishi ba, haka yaci gaba da jijjigata a gigice har Allah ya dawo mata da hankalinta ta bude idanuwanta akan shi.

“Layla ki tashi, dan Allah ki tashi ki karyata mun abin nan, ki ce mun karya ne, ki ce mun ko a mummunan mafarki ba zai faru ba…”

Bilal din yake fadi a gigice, yana girgiza ta, sai da ta kama hannun shi ta ture, jinta take kamar tana yawo a saman gajimare, da kyar taja jikinta tana mikewa, numfashi da kyar take fitarwa lokacin da ta kama skirt dinta tana saukewa, idan tace ga abinda take ji karya ne, a fadin duniya babu wasu kalamai a cikin kowanne yare da zasu taba yiwa halin da take cikin adalci wajen fassara shi. Kafafuwanta ta sauko daga kan gadon, tana mikewa taji wani irin abu ya tsirga mata, amman bata da lokacin ririta kowanne ciwone yake taso mata, dakin kawai take son bari

“Layla…”

Bilal ya kira, amman bata kula shi ba, dankwalinta ta dauka tana daurawa. Ta dauki jakarta da mayafi.

“Layla…”

Ya sake kira ganin tana shirin nufar kofa a halin da take ciki. Shirun tashin hankalinta yake karanta da yake kara bugun zuciyar shi. Bashi da karfin motsawa balle ya hanata ficewa daga dakin. Tun fitarta bai motsa daga inda yake ba, sai yanzun daya samu yaja jikin shi yana dora kan shi a jikin katifar, idanuwan shi ya lumshe kamar hakan komai daya faru yake jira ya dawo mishi.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Ya furta daga wani lungu na zuciyar shi jikin shi na wani irin bari.

“Me zan cewa Abbu? Me zan cewa Abbu…”

Yake fadi kamar wanda ya sami tabin hankali, har lokacin so yake ya tuna lokacin da Layla ta shigo dakin, so yake ya tuna yanda akayi ta hau kan gadon shi, yanda akayi wannan kaddarar ta same su, ko tabin hankali ya fara bai sani ba, tunda ance in kana hauka baka sanin abinda yake faruwa. Saboda in ba hauka yake ba babu yanda za ayi ace wani abu ya faru a tsakanin shi da wata mace daban da igiyar aure bata kulla su ba, balle kuma Layla. Yana da yakinin ko mazinaci ne shi ba zai bi Layla ba, yana mata son da ba zai yarda su kasance a irin wannan yanayin ba.

Hannun shi daya dora kan katifa yaji kamar ya taba wata lema-lema, ba shiri ya dago kan shi yana kallon wajen da hannun shi, abinda yagani na kara gudun zuciyar shi, baisan yanda ciwon bugun zuciya yake ba, amman tabbas yana gab da kama shi, saboda abinda yake gani na kara tabbatar da ko ciwon hauka yake, to tabbas a cikin wannan ciwon ya kasance tare da Layla. Wannan gaskiya ne ko da hankalin shi yabar jikin shi. Wata irin mikewa yayi yana kama zanin gadon ya yaye shi daga kai, fita yayi daga dakin kamar sabon mahaukaci.

Bokitin daya fara cin karo da shi ya saka zanin fadon a ciki ya koma daki ya dauko omo, ya nufi bokitin da sukan tara ruwa ya bude ya diba, kallo daya zakayi mishi da yanda yake wanke zanin gadon kasan ba a cikin hayyacin shi yake ba, yayi mishi wanki yafi biyar kafin ya shanya. Ruwan ya kara diba ya shiga wanka, sai dai ya kai awa daya tsaye a cikin bandakin ko kayan shi bai cire ba, kalar wankan da zaiyi yake tunani, idan ya saka sabulu ya fito tabbas zai fito da daudar da yake ji har cikin ruhin shi.

Idan kuma yayi wankan da zai tsarkake daudar wajen shi baisan yanda zaiyi da ta ciki ba, kuma wankan zai tabbatar mishi da abinda yake so ko yayane tunanin shi ya karyata mishi. Bashi da wani zabi daya wuce yin wankan tsarki ya daura alwala ya fito zuwa daki, kaya ya sake yana fita da wanda ya cire kamar suna tare da wata dauda da ta girmi idanuwa ya saka su a bokiti, dakin dai ya sake komawa ya dauki darduma ya shimfida, har ya kabbara sallar azahar da yake tunanin ta wuce shi, saboda sanda ya fita yaga kamar yamma tayi sosai, komai bai kwance mishi ba sai da yayi sujjada, sai da ya dora goshin shi a kasa ya kara jin yanda bashida wata hijabi tsakanin shi da Ubangiji sannan sauran nutsuwar da yake tare da ita ta kwance.

Maimakon karatun sujjada sai.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Da yake fadi muryar shi can kasan makoshi yana maimaitawa ko Allah zai tausaya mishi ya sake mishi wata kaddara da zai iya dauka ba wannan da ta faru ba, tun yana yi muryar shi na fitowa harta daina ya koma yi a zuciya, tun kafafuwan shi na da sauran karfin durkuson sujjadar harya kife gabaki dayan shi, Ayya kance

“Ko rigimar yarinya bakayi ba Bilal, zan iya kirga lokuttan da naga hawaye a fuskar ka.”

Amman yanzun kuka ne mai gunji ya kwace mishi, kuka yake daga zuciyar shi, rurin shi na fitowa da sauti kafin wasu irin hawaye masu zafi su zubo mishi, hade jikin shi yayi yana wani irin kuka yau da yake neman mai lallashin shi, saboda a labarai ma bai taba cin karo da kalar kaddarar su ba, bai taba jin labarin tashin hankali makamancin wannan da yake ciki ba, bayani yake nema yayiwa kan shi ya kasa, idan ya kasa gane abinda ya faru ko ya akayi ya faru taya zai ma wani bayani ya gane, wanne irin uzuri zai bayar.

“Abbu…”

Ya kira sunan na fitowa da gunjin kuka, ta ina zai fara yiwa Abbu bayani, me zaice mishi, me zai cewa Abbu, ya dade yana jin bai cika mishi alkawarin daya rike ba, ya dade nauyin amana na bibiyar shi, amman yau yake jin duniyar shi ta tsaya cak, kuka yake na yanda lokaci daya kaddara ta bude mishi shafin da baisan ya zai karanta shi ba balle yayi tunanin wucewa, saboda an kashe fitilar da take haske da rayuwar shi, duhu ya baibaye ko ina. Yau kuka yake da dukkan zuciyar shi, kukan maraicin da bai taba shi ba shekarun da suka wuce sai yanzun.

Ji yake kamar wani abu na ruri banda zuciyar shi, kafin kwakwalwar shi ta sanar da shi wayace, wayar shi ce take ihu, da kyar ya iya daga jikin shi ya rarrafa inda wayar take kan tebir ya mika hannu ya dauka, zuciyar shi nayo tsalle zuwa cikin makoshin shi ganin.

“Hamma.”

Rubuce a jikin screen din wayar da ta subuce daga hannun shi tana faduwa kasa, baiko matsawa ya yi kamar wayar na dauke da wani abu da zai iya cutar da shi, sam a lissafin da yake yi na mutanen da zasu tuhume shi Rayyan ya bace mishi, komai ya bace mishi banda Abbu har wayar ta yanke bai iya motsawa ba, tana sake daukar ruri wasu hawayen na kara zubo mishi.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Yake fadi yana maimaitawa, yanzun kam ya tabbatar da wannan shafin da kaddara ta bude mishi shine shafin karshe, babu yanda zai ayi yai tsahon ran ganin wucewar shi, zuciyar shi bata da karfin daukar wannan tashin hankalin.

“Ka kula da Layla, ka kula mun da Layla kaji Bilal, zuciyata na mun wani iri.”

Maganganun Rayyan suka dawo mishi, sake durkushewa ya yi, da yawan mutane in suka shigo su kaga Bilal din zasu yi mamakin ganin namiji kamar shi yana kuka haka, abin zai zame musu bako, saboda an san namiji da juriya, shi da kan shi in da wani yace zai kuka kamar dan shekara biyu zai karyata, saboda bai taba hango rayuwa zata bashi wannan dalilin ba, amman yau kuka yake.

“Me zan ce musu?”

Ya furta a zuciyar shi, ashe akwai wani abu da ba zai fassaru ba, ashe akwai kalar kaddarar da babu kalaman da zasu misaltata, ya akayi Layla ta zo dakin su? Yaushe Layla ta shigo dakin su?

“Sai kayita bacci kamar ba namiji ba, ka dinga rufe daki idan ba kowa a gida…”

Rayyan kan ce mishi, saboda kar a shigo a illata shi yana bacci, amman bai taba bacci irin wannan ba, bai taba baccin da za’ace Layla ta shigo har tahau kan gadon shi bai sani ba, har wani abu ya shiga tsakanin su haka.

“Ko mafarki nake? Ko da gaske mafarki ne?”

Ya furta yana tashi zaune, fuskar shi harta kumbura saboda kukan da yakeyi, wayar shi ce take ci gaba da ruri, da kyar ya iya mika hannu ya dauka.

“Layla”

Ya gani, cikin sauri ya daga yana karawa a kunnen shi, watakila da gaske mafarki yake, muryar shi a dakushe yace.

“Layla…”

Sai dai yanayin tata muryar ya tarwatsa wani abu a cikin tashi zuciyar da ba yajin zai taba komawa dai-dai.

“Hamma ba mafarki bane ba, ba mafarki bane Hamma…”

Wayar ce ta sake subucewa daga hannun shi a karo na biyu, sosai yake kokawa da numfashin shi, sai dai wannan karin a juye ta fadi, yana ganin screen din, baisan iya mintinan da ya dauka ba kafin ya ga kiran Aisha ya shigo, dariya yayi wannan karin, saboda abin ya fara fin karfin shi, nata kiran na yankewa na Ayya ya shigo

“Ayya…”

Ya kira wata dariya da ta fito da sautin kuka na kwace mishi, da gaske karshen duniyar shine yazo, sosai yake tabbatar da hakan lokacin da idanuwan shi da suke wani irin radadi suke kafe akan screen din wayar da kararta ta daina zuwa kunnen shi, yana kallonta in wani kiran ya yanke sai wani ya sake shigowa, kiran mutanen da kamar sun san abinda ya faru, kamar suna jira ya daga ne su fara jeho mishi tambayoyin da yasan bashi da amsar su!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 11

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 17Martabarmu 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×