Skip to content
Part 19 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Har ta sauka daga cikin napep din jinta take kamar a wata duniya ta daban. Tayi gaba yayi mata Magana.

“Hajiya kudin”

Jakarta ta bude, bata san nawa bace ta dauko ta miqa mishi, tayi juya ya sake cewa,

“Ga canjin, ko kin barmun?”

Hannu tasa ta karba tana zuba su cikin jakar da ko zageta batayi ba. Ta sha jin kalmar tsiraici, ta dauka tasan ma’anar kalmar, a da ta dauka tsiraici shine ka rabu da tufafin jikin ka, sai yau ta fahimci akwai tsiraicin daya girmi rabuwa da tufafi.  Akwai suttura da ba kaya bane kawai yake saka jinta a ranka, haduwa take da mutane a hanyar hostel din, musamman da ta shiga, sai ta tsinci kanta da jan mayafinta tana kara gyara shi, babu inda yake bude a jikinta, amman jinta take kamar bata saka komai ba, kamar kowa na ganin duk wani tsiraici da yake tare da ita.

A daddafe ta karasa dakin su, babu kowa sai Anisa da take zaune akan gadon Layla din, da yake nata saman na Layla ne, in ba lokacin baccinta yayi ba anan suke zaman su, wasu ranakun ma in tayi bacci Layla bata tashin ta. Yau ita batayi lakca ba sai karfe sha biyu na rana. Tana dawowa ruwa ta kara watsawa ta samu waje ta kame ta dauki waya tana dannawa, da yake taci abinci a restaurant, yayarta ta turo mata banner din Zahra Tabiu. Su kan siyi Donut dinta sosai, matar karshe ce, taje gidan Yayar tata ne ta samu Donut, duk a tunaninta na Zahra Tabiu ne, ko da ta fada mata ita tayi sam bata yarda ba, sai da ta kwana taga tayi a gabanta

“Inalillahi… Anty yaushe kika koya? Ina kika koya?”

Murmushi Antyn tayi.

“Zahra Tabiu dince fa ta koya kwanaki, kin san nayi saving lambarta saboda siyen Donut, to shine naga tana talla zata koya yanda akeyi online, dubu biyar.”

Ware idanuwa Anisa tayi, zatayi abubuwa da yawa da dubu biyar.

“Kuma har kika iya haka?”

Tayi maganar cikin rashin yarda, dariya Antyn tayi mata.

“Akwai videos haka, sosai ake ganewa, dan su Ammar sun fasa mun screen din waccen wayar dana nuna miki, kiyi joining in zata sakeyi.”

Batayin ba ko da Anty ta turo mata, amman duk wani Donut da zata siya sai taji kamar bai kai na Zahra Tabiu ba, shine da safe da ta tashi taga Anty ta turo mata banner din, ta zabtare rabin kudin koyarwar daga dubu biyar zuwa dubu biyu da dari biyar. Gara dai ta koya ta huta, in ta koma gida ta dinga cin kudin Yayyenta, tana da kwalayen Donut Fairy data siya, in sun ce tayi musu order sai ta karbe kudin tayi a gida ta saka a kwalin, in sun cinye tabi ta kwashe. Lambar wayar take dubawa ko iri daya ce da wadda take da ita +234 806 515 6303. Ta gama dubawa kenan ta ga ita din dai ce, sai ga Layla ta shigo dakin kamar an korota. Kallo daya Anisa tayi mata tace,

“Layla?”

Tana sauko da kafafuwanta daga kan gadon, tsaye Layla tayi bakin kofar, so take wani abu da zai nuna mata mafarki takeyi ya faru, kamar ace Anisa ta girgizata tana tashinta yanda ta saba da fadin,

“Ke banza takwas saura.”

A ranakun da suke komawa sallar asuba bayan sun makara. Amman kallon da Anisa takeyi mata ya tabbatar mata da cewa ba mafarki takeyi ba, idonta biyu. Ta dai kasa karasawa cikin dakin ne, kafafuwanta take ji sunyi wani irin sanyi. Ganin haka yasa Anisa ajiye wayar tana saukowa daga kan gadon tazo ta kamata.

“Layla? Lafiya?”

Kai ta girgiza ma Anisa da ta kamata tana janta zuwa kan gadon, sai da ta zauna sannan jikinta ya fara bari.

“Dan Allah mene ne? Me ya faru? Ko wani ne ya rasu?”

Anisa ta karasa muryarta na karyewa. Gabaki daya yanayin Layla ya gama daga mata hankali, ta san yanda mutuwa take, Yayanta ya taba rasuwa, ta kuma ga kalar hargitsin da kowa ya shiga, yanayin Layla ya nuna cewa tana cikin matsananci shock da ba labari bane me kyau yake haifarwa. Shisa gabaki daya hankalinta ya tashi.

“Ki saka mun ruwa inyi wanka.”

Layla ta fadi daga kasan makoshinta, watakila ruwa da sabulu su fitar mata da daudar da takeji, kila kuma idan ta saka ruwa a fuskarta zata farka. Babu musu Anisa ta tashi, sukan ajiye ruwan zafi a flask ko dan shan shayi, shi ta juye mata a bokiti tana sirkawa, da kanta ta kai mata komai bandaki ta dawo tana fadin,

“Ki tashi ga ruwan can.”

Mayafi kawai Layla ta cire, ko towel bata dauka ba ta fice daga dakin. Da yake sukan dibo ruwa da bokatan wankan nasu, da sun fito bandaki sukan saka omo su wanke shi har bayan. Shisa tasan ruwan ciki mai tsarkine, karkatawa tayi ta fara wanke hannayenta, a karo na farko da takejin sauqi irin na addinin musulunci, niyyarka a zuciya idan ka daurata tayi, ba saika fadeta a fili ba, bata da kwarin gwiwar motsa labbanta da daura niyyar wannan wankan da take tunanin ya zame mata dole. Tashin hankalinta bai fara ba sai da ta wanke fuskarta tana sake bude idanuwanta a cikin bandakin.

A daddafe ta karasa wankan, kayanta ta mayar tana fitowa, can ta baro bokitin, sai Anisa ce ta koma ta dauko. Doguwar riga ta dauka ta sake kayan jikinta da take da tabbacin ta gama saka su har abada. Wayarta ta bude jaka tana dauka, tana kallon yanda hannunta yake bari, a kasa ta zauna. Tambayoyin Bilal ne suke dawo mata, amman yanda ta kula ya kasa gane yanda akayi abinda ya faru ya faru, haka itama take cikin wannan rudanin. Ta san sanda ta shiga dakin su, ta tuna sanda ta zauna harta sha ruwa, amman daga nan babu abinda zata iya tunawa banda tashin hankali da wani irin firgici marar misaltuwa.

Da kyar ta iya lalubo lambar Bilal tana kiran shi, bugu biyu ya daga.

“Hamma ba mafarki bane ba, ba mafarki bane Hamma…”

Ta furta da wata irin nisantacciyar murya, girman kalaman na zauna mata da wani yanayi daya birkita mata komai, wayar ta sauke daga kunnenta tana ajiyewa a gefe, kafin ta janyo kafafuwanta ta hade su da jikinta. Har lokacin jinta take yi kamar bata da kaya.

“Martabar ki darajar ki Layla, martabar ki sutturar ki…”

Kalaman Mami suka dawo mata. Kalaman na tuna mata da Mami.

“Mami… Mami.”

Ta ke kira cikin wani irin tashin hankali, duk wata nasiha da ta tabayi mata tana dawo mata. Da gaske martabarta suttura ce a wajenta, sutturar da bata gane muhimmanci ta ba sai yanzun da take jin bata tare da ita. Kuka take nema amman sam yaki zuwa, banda wani irin numfashi da take ja tana fitarwa kamar mai ciwon asma babu abinda take iyayi, batsan shigowar Anisa dakin ba sai da taji ta kamota

“Dan Allah kiyi mun magana Layla.”

Cewar Anisa da hawaye cike taf a idanuwanta, dan ita bata son tashin hankali sam, sai lokacin wani irin kuka ya fito tun daga kasan zuciyarta tana sakin shi cikin shesheka, ko ina na jikinta bari yake yi.

“Kiyi hakuri, banma san me ya sameki ba, ko me ya faru, dan Allah kiyi hakuri…”

Anisa tace tana kara rike Layla a jikinta, yanayin yanda take kuka ne yake ba Anisa tsoro, saboda bata taba ganinta cikin yanayi irin wannan ba, wayarta da ta fara ringing Anisa ta dauka tana dubawa, an rubuta

“Mami”

A jiki, gyarama Layla kwanciya tayi a jikinta.

“Dan Allah kiyi shiru, kinga ga Mami tana kiran ki.”

Wata irin mikewa Layla tayi tana jin kamar an watsa mata ruwan zafi, fisge wayar tayi daga hannun Anisa, tana kifeta akan cinyarta, kamar hakan zai hanata rurin da takeyi, jikinta kara bari yake yi cike da sabon tashin hankali, ji takeyi kamar Mami ta gane, kamar tasan me ya faru shisa take kiranta, tana yankewa wani kiran na sake shigowa, amman ta kasa dubawa, sau biyar ana kira tana yankewa, kukanta ke kara tsananta saboda tashin hankalin da take ciki, saboda tasan duniyarta ce gabaki daya tazo karshe shisa Mami ta gane, shisa take kiranta. Bata da abinda zata fada mata.

“Fyade”

Shine kalmar farko da ta dace a yanayi irin wannan, ita kuma ce kalma guda daya da zata iya labewa bayanta dan samun sauki. Amman zuwan kalmar tunanin ta, alakanta Bilal da wannan kalmar kawai barazana take karawa shige da ficen iskarta. Ko kwaya Bilal yasha ba zai taba mata fyade ba ita tasani, ita zata bada shaidar waye Bilal. Shisa bata da kalmar da zata fassara abinda ya faru din, bata da shi, da duk dakika da yanda rudani da tashin hankalinta suke karuwa. Wanne irin mugun abune wannan yake faruwa dasu? Kamar wanda akayiwa asiri, asiri ne kawai abu daya da take da shi da zai fassara mata abin nan ta yarda, sai kuma iskokai, amman a iya saninta bata da iska, haka ma Bilal.

Sai dai akwai iskar da bata bayyana sai daga baya, watakila abinda ya faru da su kenan. Amman wa zatayiwa wannan bayanin ya gane?

“Ke yanzun kina tunanin shi Rayyan din da kike biyewa idan tsautsayi ya gifta a tsakanin ku zai aure ki?”

Kalaman Mami suka dawo mata, suna kuma tuna mata da Rayyan daya fice daga kanta na wucin gadi.

“Na shiga uku, Anisa na shiga uku na.”

Ta ce cikin firgici.

“Ki daina Layla, babu kyau fadar haka, ki daina dan Allah. Kiyi addu’a koma mene ne zai zo da sauki.”

Kai Layla take girgiza mata wasu irin hawaye masu dumi na zubo mata, jiya ta ga yanayin da bata taba gani ba a cikin idanuwan Rayyan, a karo na farko jiya yayi mata kalar murmushin da bata taba gani ba, zata rantse daga zuciyar shi yayi mata murmushin bayan ta fada mishi tana son shi, kamar yana son gaya mata ita da shi din zasu iya faru, a cikin murmushin shi ta ga possibility din zamansu a karkashin inuwa daya a matsayin masoya da zai iya kaisu da aure wata rana, ta hangi cikar burinta a kwayar idanuwan shi. Da yace ta tafi sai taga kamar akwai rokon da yake mata, kamar yana bata amanar kanta ne kafin ya dawo.

“Bana son kowa a kusa da ke Layla.”

Ya sha fada mata, a wasu lokuttan takan gane zai fadi kalaman tun kafin ya furta su. Da wanne ido zata kalle shi? Ya zatayi mishi bayani ya gane? Zai fahimceta? Zai fahimce su ita da Bilal idan suka yi mishi rantsuwa da su kan su har yanzun basu san ya akayi abinda ya faru din ya faru ba. Wayarta da ta sake daukar ruri ta katse mata tunanin da takeyi, wannan karin da wani irin bugun zuciya tasa hannu ta birkita wayar tana ganin

“Hamma Na”

A rubuce, bakinta da matuqar nauyi ta iya furta.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Wani irin yanayi take ji da batasan ya zata fassara shi ba, ashe haka tashin hankali yake bata sani ba? Ashe haka asalin firgici yake, ko ranar da ta fita bandaki cikin dare taga gicci tayi tunanin aljani ne bata firgita irin wannan da take ciki yanzun ba. Tashin hankaline da babu wanda zai taba fahimtarta sai wanda ya taba shiga cikin irin yanayin da take yanzun. Wayarta da ke ruri ta ga Anisa ta mika hannu ta dauka, da sauri ta rike hannunta.

“Ba dagawa zanyi ba, zan saka a silent ne.”

Tayi maganar cikin wani irin yanayi, a silent din ta saka mata wayar tana mikewa ta ajiyeta gefe. Fita tayi daga dakin, ruwan sanyi ta siyo ta dawo. Guda daya ta dauka ta tsiyaye a kofi ta zo tana ba Layla din da ta girgiza mata kai

“Ki sha dan Allah, watakila kidan ji dama-dama.”

Hannu biyu ta saka ta karbi kofin saboda yanda jikinta yake bari, shan ruwan tayi sosai, Anisa ta karbi kofin tana ajiyewa a gefe. Mikewa tayi ta fita ta daura alwalar la’asar tana tunawa Layla yanda itama batayi sallar ba. Da  kyar ta iya mikewa tana dauro alwala, a karo na farko ta tsinci kanta da kunyar tsayawa a gaban Ubangiji, sai take jin kamar ita din bata cancanci tsayawar ba, kamar tana da tarin laifukan da batasan yanda zata fassarasu ba, har Anisa ta idar ita tana ta rakubewa a gefen gado.

“Kinsan la’asar da saurin wucewa, ki samu kiyi sallah sai ki sha panadol ki dan kwanta. Sannu.”

Kai ta jinjina, ko da ta gabatar da azahar ta sake mikewa ta gabatar da la’asar ta idar Anisa bata ce mata komai ba. Hannuwanta ta daga tana rasa abinda ya kamata ta roka, gabaki daya addu’o’inta basayin tsayi ko da can, idan tayiwa iyayenta da suka rasu, sai Mami da Abbu, sauran ta fatan samun Rayyan ce, sai kuma Bilal, shima bata taba mantawa da shi a cikin addu’o’inta, in tayi tama sauran yan uwanta shikenan. Lokutta da dama sai tayi niyyar mikewa sai taji kamar bata kyauta ba, kamar saboda Rayyan da Bilal ya kamata tayiwa Ayya itama, a ranakun da abin yake ci mata rai, takan koma tace.

“Allah ya raya miki duka yaranki cikin aminci Ayya, Allah ya yafe miki, nima na yafe miki duk ce mun mayya da ki kayi.”

Wasu ranakun kuma turo labba takeyi ta mike abinta, yanda Ayya bata sonta, itama hakan take ji. Amman yau ta rasa abinda zata roka, a karo na farko ta rasa. Tana tsakanin rokon sauki, ko kasancewar abin da yake faruwa mafarkin da tasan ba haka bane ba.

“Mami.. Mamina… Allah ka dauke duka saukin a kaina ka bata…Allah Mami…Mamina.”

Shi take fada hawaye masu zafin gaske na zubar mata. Nan take zaune kan dardumar, tun tana iya fadar kalamai har suka bace mata, banda Mami da take kira tana wani irin kuka babu abinda take iyawa. Anan Magriba ta sameta ta tashi tayi, isha’i ma haka. Duk yanda Anisa taso ko ruwan shayi ne ta kurba kiyawa tayi. Zuwa goman dare sanda ta kwanta zazzabi ya rufeta kuwa. Tun Anisa na mata sannu, har ta daina amsawa, tana jinta ta tabata, tayi luf dan Anisa ta samu bacci, sannan kuwa ta hau sama tana kwanciya. Bude idanuwanta takeyi, dan duk idan ta rufe bata ganin komai sai ita da Bila a abinda take tunanin mafarki ne, tambayoyin da take da su idan ta fito dasu fili zai iya barazana da imaninta, shisa ta zabi taci gaba da fadin.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Ko zata samin saukin da kalmomin sukan samar a yayin tashin hankali.

*****

Tun da ta sauke wayar daga kunnenta take cikin tashin hankali, har ciwon kai ya taso mata. Tunda akayi wayar hannu, ko tace tunda Bilal ya mallaki tashi wayar, ko suna gari daya sai yayi mata kira fiye da hudu a rana. Duk a cikin yaranta Bilal ne zai fita fiye da awa biyu ya kirata ya tabbatar mata da cewa yana lafiya, ko da kuwa ya sanar da ita cewa zai wuce awa biyun. Shakuwar da take tsakaninta da yaranta, gabaki dayan su Rayyan ne kawai bata kira a waya, sai ta jima bata kira shi ba saboda ranta kan baci idan bai daga ba, gara ta kira Bilal taki ya yake.

Amman ita ko su Rukayya sukaje makaranta tana iya musu kira goma-goma kafin su dawo. Ko muryoyin su taji sun sauya sai ta gane. Shisa tun da safe da bataji Bilal ba ta kasa samun natsuwa, ko da yana lakca zai mata text ya fada mata, yana kuma fitowa zai kirata. Ko Abbu bata waya dashi yanda takeyi da Bilal, wani sim Bilal din ya siyo musu ya bata guda daya, duk wata yake tura mata kudi sai su dauke, haka zasuyita labari ba kama hannun yaro. Kwanaki Khalifa daya sameta sunata waya bayan sun gama yake cewa,

“Hajiya Ayya da danta.”

Dariya ta yi.

“Ko katin ku ma bakwaji, ni da nake saka katin ma ba’a kirana haka.”

Dariyar ta sakeyi sosai.

“To dan ubanka kafin ka samun kati sau daya mijina ya sakamun sau hamsin… Kuma wannan layin Bilal ne ya siyo mana shi, ba’a daukar kudi, duk wata ake saka ko dari shida ne.”

Khalifa yayi dariyar, takan ga mamaki a fuskar yaran nata kan kalar shakuwar da take tsakanin ta da Bilal, har tsoro takan ji wata rana kar abin ya darsa kishin Bilal a ransu. Amman ko na rana daya bata taba gani ba, suna kaunar shi kamar daga cikinta ya fito, ko dan Bilal dinta haka yake. Da wahala ka zauna da shi baka kaunace shi ba, ko dan yanda zai dinga kaffa-kaffa da bacin ranka, a duk gidan daga shi sai Haris zata yiwa wannan shaidar, dan ko yanzun duk a cikin yaran Maryama babu wanda take ji a ranta kamar Haris.

Shi ka daine yake kiranta kullum su gaisa harma suyi labari, ko yanzun da akayi maganar auren shi da yar wajen Yaya Ayuba, kudi na nan tana warewa da zata bashi gudummuwar ta, so take tayi hidimar auren yaron kamar yanda zatayi ta su Bilal. Yanzun wayarta tabi da kallo da ta sake kiran Bilal amman wannan karin a kashe ma taji wayar tashi, abinda ya kara daga mata hankali matuka. Ta kara kiran Rayyan har sau hudu bai daga ba, tasan yana Bauchi. Yanzun take tunanin yanda in har Bilal ya daga waya zata saka ya tura mata lambar abokan shi guda uku ko fiye da haka yanda zata kira su duk idan bata same shi ba a duba mata a gani ko lafiya.

Tayi tunanin kiran Abbu, amman bata son daga mishi hankali, gara ta bari ya dawo, tunda ya kai wannan lokacin bai dawo ba tasan wani abin mai muhimmanci ne ya tsayar da shi. Nata hankalin dai yaki kwanciya, ga yaran duk suna gidan Yaya Ayuba, shiru sai ita kadai a falonta. Ta saka wannan ta kwance, sallama taji, sallamar da sai bayan ta amsa sannan muryar ta karasa kwakwalwar ta da wani yanayi da ya sata daga kai ta kalli kofar inda Mami take tsaye a tsorace. A nata bangaren ita tun cikin daren jiya ta farka da faduwar gaba, haka ta karasa daren cikin salloli, to tunda gari ya waye kuma jikinta yake a sanyaye, rabonta da yanayi irin wannan tun rasuwar mahaifiyarta.

Addu’a ta dingayi, sam hankalinta bai kai kan Layla ba sai da tayi mata kira ya kai goma da safe bata daga ba. A yinin ranar in ba wayarta aka duba ba, ko ta Layla babu yanda za’ayi a gane yawan kiran da tayi mata. Har dubawa tayi ko ta ajiye lambar Anisa da Layla ta taba kiranta da ita, tana fada mata dakin su daya da Anisar, amman bata ajiye ba. Kusan duk wata baquwar lamba da ta iya gani a wayar saida tabi ta kira cikin son gano lambar Anisa, amman bata samu nasara ba. Idan ta kira wani cikin yaran tabbas hankalin su zai tashi, shisa ta kira Bilal, shima sau hudu bai daga ba, kuma tasan in dai yagani to zai kirata, haka kawai ta kasa samun natsuwa.

Musamman ba jimawar nan da ta kira Bilal din taji wayar shi a kashe, haka ta Layla. Sosai zargin ko lafiya da takeyi ya tabbata, tasan ba shiri suke yi da Ayya ba. Na rana daya basu taba shiri ba, duk kuwa yanda taso hakan ya faru, amman akwai lokutta da dama da suka ajiye rashin jituwar da yake tsakanin su sukayi maganar fahimta, musamman lokuttan daya kasance ya shafi wani a cikin yaran su. Ko kwanakin baya da Haris ya sami hatsari, Ayya ce kiran shi na karshe, dan haka ita aka kira da wayar shi, bata ma kira Mami ba sai da taje asibitin wajen Haris, sannan tunanin yazo mata, shima Haris ya bata lambar Mami, dan bata taba sanin yanda lambar take ba.

Kuma sai Mamin bataje ba, tabar Ayya da Haris din da yake tace mata ba wasu ciwuka yaji ba, ya bugune harya suma, kuma ya dawo hayyacin shi ana mai dinkine, ana gamawa aka basu magunguna suka tafi gida. Shine karo na farko da Ayya ta dinga jera kwanaki tana shiga bangaren ta tunda can Haris yake wuni, ba kulata takeyi ba, zata duba jikin shine, ta dan zauna suyi hira, da aka kwana hudu ma sai Haris din ya dinga wuni a falon Ayya din. Shisa yau take da yaqinin Ayya zata kulata indai zancen yarane, duk kuwa yanda tasan bata kaunar Layla, duk a cikin gidan ita da Layla ta dauki tsanar duniya ta dora musu.

“Maryama?”

Ayya ta kira cike da alamar tambaya, saboda sai da taji kanta ya kara sarawa, tasan akwai dalili babba da zai shigo da Mami bangaren ta, cikin rawar murya Mami tace.

“Bansan ko kinyi magana da su Bilal ba, dan Allah zanji ko Layla tana lafiya ne, tun safe nake kiran wayarta ba’a dagawa, yanzun kuma a rufe, Bilal ma na kira shi bai dauka ba, yanzun da na sake gwadawa shima tashi wayar a kashe…”

Mami ta karashe maganar muryarta na karyewa, cikin tashin hankali Ayya tace

“Nima inata kira ba’a daga din ba, yanzun nake so Abbun su ya shigo… Bana so in kira in daga mishi hankali.”

Kai Mami ta jinjina.

“Allah ya sa dai lafiya. Na kasa samun natsuwa wallahi…”

Numfashi Ayya ta sauke, sam Mami ba zata gane yanda take ji ba, saboda watakila ita Layla kan yini basuyi magana ba, saboda haka rashin wayar su yau ba abin da zai daga hankali bane ba. Amman tasan ko a cikin yaranta ta fadawa wani duk yau tun safe batayi magana da Bilal ba hankalin su zai tashi, zasu san ba lafiya ba. Suna nan tsaye Rukayya ta karaso ita kanta mamakin ganin Mami tsaye a bakin kofar su tayi.

“Mami… Lafiya dai ko?”

Cewar Rukayya, Mami din na matsa mata ta shiga cikin dakin, Ayya ta kalla.

“Me yake faruwa?”

Ta sake tambaya gabanta na faduwa.

“Babu komai.”

Mami da Ayya suka amsa a tare, suna saka Rukayya kallon su cike da rashin yarda.

“Me yasa zaku amsani a tare idan babu komai? Me ya faru? Ina Abbu? Abbu bai dawo ba?”

Rukayya tayi maganar da wani irin tashin hankali da yasa Ayya fadin.

“Dan ubanki karya zamuyi miki to?”

Idanuwan Rukayya har sun fara tara hawaye, saboda tasan abinda duk zai hada Ayya da Mami waje daya haka, suna tsaye hayaniya bata tashi to mai girmane, kuma tafi kawowa ranta cewa Abbu ne, ganin yanda hankalinta ya tashi shisa Mami tace,

“Ke ba wani abu bane bafa, Layla ce ban samu a waya ba tun safe, shine nazo amsar dayar lambar Bilal in kira dan ya duba ta.”

Numfashi Rukayya ta sauke wani abu yana natsawa a zuciyarta jin ba Abbu bane ba.

“Nima na kira bata daga ba, ta saka hoton wasu takalma jiya sai nayi mata magana tace kawarta take siyarwa, to ina so in tura kudin, na dauka ko tana lakca shisa… Nasan lafiya in shaa Allah… Watakila wayar ta fadi ko ta ajiye wani waje.”

Kai Mami ta jinjina, ita sam batayi wannan tunanin na cewa zai iya zamana wayar Layla bace ta fadi, ko aka sace, sai taji ta dan samu natsuwa.

“Allah yasa lafiya dai… Sai anjiman ku, zanci gaba da kara gwadawa.”

Cewar Mami tana juyawa, har tayi taku biyu Ayya tace,

“Maryama…”

Juyowa Mami tayi.

“Idan na same su zan aiko Rukayya ta fada miki.”

Kai Mami ta jinjina, haka kawai kwalla na cika idanuwanta. Shisa ta kasa cewa komai ta tafi kawai, akwai wani abu a cikin idanuwanta da yasa taba zuciyar Ayya din, tasan yanda tashin hankalin tararrabi akan ko yaronka yana lafiya yake. Shisa ma ta ajiye kishi da tsanar da tayiwa Mami din a gefe yau. Suna nan zaune tana dan amsa Rukayya dai-dai cikin tsegumin malaman makarantar su da kuma rashin mutuncin su da takeyi mata dan ta dan rage damuwa Abbu ya shigo, suna gaisawa da Rukayya ta tashi tana barin dakin, da yake girkin Mami dinne. Ta so yaci abinci tukunna ta fada mishi, amman yasan ta, ya karanci damuwa a fuskarta.

“Lafiya dai Maimuna?”

Kai ta girgiza a hankali.

“Duk yau tun da safe banyi magana da Bilal ba, inata kiran wayar shi ba’a dauka, sai babu jimawa kuma Rayyan ya kirani yana tambayar ko nayi magana da Bilal din, kaga kenan shima basuyi magana ba…”

Cikin tashin hankali Abbu yake kallonta tunda ta fara maganar, shima yau aiki kawai yakeyi, amman tunanin yaran nashi ya addabe shi, musamman da Bilal din bai kira shi ba, ko da suna wani meeting da yammaci, lokaci zuwa lokaci ya dinga duba wayar shi ko, dan yasan zai kira shi, cikin hira zai fada mishi Rayyan ya sauka Bauchi lafiya tunda yasan shi Rayyan din ba zai taba kira ba. Ta hanyar Bilal yakan san Rayyan yana lafiya. To kuma hidimar da yayi yau tana da yawa, amman yanata tunanin su, har Layla ba suyi magana ba, garama ita Layla ya kira bayan azahar bata daga ba.

“Kuma yanzun Maryama tabar nan, tace bata samu Layla a waya ba.”

Wannan karin da kallon da yake mata hade yake da mamaki, duk da batun yanzun yasan akan yaran su Ayya zata iya ajiye duk wani tashin hankali a gefe ba, yaji dadi, sosai yaji dadi har cikin ran shi.

“Ki kwantar da hankali, in shaa Allah nasan lafiya. Yanzun haka wayoyin suka kai wani waje… Idan har zuwa anjima ba’a samu ba, gobe da safe sai in kira aje a duba su, kinga yanzun ba zaka kure mutane cikin daren nan ba dan suna jin kunyar ka.”

Kai Ayya ta jinjina mishi, duk da haka sai da ya kara zama a wajen nata ya tabbata ya ga murmushi a fuskarta sannan. Yana fita daga dakin nata wayar shi ya zaro yana kiran abokin shi da yake Zaria, amman bai daga ba, baya son ya karasa rikita Ayya, amman akan yaran shi ya fisu rauni, sosai zuciyar shi take bugawa, yunwar da ya yini da ita ta dauke daf, dakin shi ya nufa inda ya sami Mami ta shirya mishi abinci, shigowar da tayi yasa shi daukar plate, da kanta ta karasa ta zuba mishi abincin, yasan bataci ba shisa ya saka cokulla biyu, batayi mishi gardama ba, haka suka dinga tura abincin ba dan yana musu dadi ba.

“In shaa Allah babu wani abu, da yardar Allah lafiyar su kalua.”

Kai kawai Mami ta iya daga mishi, amman yanayin jikinta yana kara tabbatar mata da babu lafiya, kawai addu’a takeyi a zuciyarta. Abbu ma haka, daren duka ukkun cikin wani irin yanayi sukayi shi, kowa da abinda yake tunani.

*****

Tabbas yara raunin iyaye. Yara karfin gwiwar iyaye. Yara kwanciyar hankali da natsuwar iyaye. Yara tashin hankali da firgicin iyaye.

Allah ya bawa dukkan iyaye karfin zuciyar kaddarar da zata gifta ta kan yaran su.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 18Martabarmu 20 >>

1 thought on “Martabarmu 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×