Skip to content

Martabarmu | Babi Na Talatin Da Uku

5
(4)

<< Previous

Fitowa tayi daga wanka, idanuwan ta kan Nur suka fara sauka kafin ta saki salati,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Idanuwan shi Rayyan ya daga ya kalleta a kasalance, kamar bai san dalilin yin salatin nata ba, yana kallo ta karaso ta kama Nur tana karewa gashinta da yake tsaye birci-birci duk ya cakude waje daya kallo wani malolon bakin ciki ya taso ya tokare mata wuya. Ita kadai tasan wahalar da tasha daren jiya tayi mata kitson, da kuka da komai, har dukanta sai da tayi, saboda Rayyan din ya kwana asibiti wajen aiki, Aminu Kano bangaren masu matsalar kwakwalwa. Ta san indai ya dawo ba za’ayi ba tunda Nur ba son kitso takeyi ba, ko kibiya ta gani a hannun Layla sai ta saka kuka.

“Kwance mata kayi?”

Ta tambaya, gira Rayyan ya daga.

“Me yasa zakiyi mata kitso? Kin matse mata kai da kyar take motsa wuyanta, har gefen kan ya fara yin alamar kurji.”

Sakin Nur tayi kawai, idan tayi magana tsaf hawayen takaici zasu biyo baya. A shekaru uku da aurenta da Rayyan ba zata ce bata cikin kwanciyar hankali ba. Amman tunanin da tayi na cewar auren Rayyan shine zai gyara mata komai, idan tana tare da shi babu wani abu da zai dameta ne ya sha bamban. Mutane ne suka nuna mata damuwar ta babu inda zata je, kamar yanda suka koya mata rayuwa da damuwar a kasan zuciyar ta. Ko biki akeyi ko suna idanuwan mutane akan Nur suke fara sauka, Nur suke fara gani, kamar yanzun rayuwar ta gabaki daya ta tattara ne akan yarinyar.

“Ita ce wannan ko? Allah sarki.”

Sune kalaman da suka fi tsaya mata a kirji suna sakata jin wani irin ciwo na ban mamaki. Ba manta yanda aka sami Nur tayi ba, amman na rana daya tana so ta rufe idanuwan ta, ta bude su ta kalli yarta a matsayin ya, ta kalleta batare da taga tabon da tayi mata ba, tabon da shi kowa yake fara dubawa. Ba son kai zatayi ba, amman Nur tana da kyau, sosai tana da kyau saboda tana kama da Bilal, kamannin da yasa in ba sanin su kayi ba sam ba zaka gane ba daga jikin Rayyan ta fito ba, gashi tana da hasken fata kamar na Rayyan din. Sai dai kyawunta ya kasa dishe munin tabon da yake tare da ita.

Shekarar su daya da aure, Rayyan ya saka ta sake yin jamb ta nemi gurbin karatu a BUK.

“Kina da buri kafin faruwar komai, abubuwa da yawa sun canza miki, bana son ya zamana harda wannan…ki koma makaranta Layla, kiyi karatu, ki fita da sakamakon da kike burin fita, ki nemi aikin da kike fatan samu.”

Shine kalaman shi, kalaman da suka bude mata zuciyarta suna dawo mata da burin ta sabo. Ko ba komai makarantar ta rage mata damuwa, yanzun tana shekara ta biyu, ta sha wahala a farkon zango na biyun a shekarar saboda laulayin cikin da yake jikinta, ga kula da Nur, tunda Rayyan yaki yarda a sakata makaranta sai a sabon zangon da za’a shiga, dan ma bakomai take yiwa yarinyar ba saboda Rayyan in dai yana gida fiye da rabi da kwata na lokacin shi yana kan Nur dinne, in ba bacci tayi ba ita Layla bata samun kan shi sam. Duk da haka ta sha wahala, tunda in dai aikin safe yakeyi sai ta dafa mishi abinda zai tafi da shi. Wata ukku na farkon cikin ta wahala sosai, yanzun ne ma ta dan samu saukin laulayin.

Yau da ya kama asabar zasu je gida ne gabaki dayan su. Basu ma tashi da wuri ba, indomie da kwai ta dafa ma Rayyan din da Nur, ita tana da sauran doyar da sukaci da daddare, ita tayi warming taci. Yanzun ma mai ta shafa ta dauki kayanta tana ficewa daga dakin ta kyale su. Sanda ta dawo ta gama shiryawa tsaf.

“Ki gyara mata kan, ina takalman ta?”

Ya bukata, inda suke Layla bata kalla ba.

“Magana fa nake yi.”

Rayyan ya sake fadi da alamar dariya a muryar shi, sarai yasan ta kule, ranta a bace yake. Babu yanda zatayi da shine kawai tunda ya fita rikici, ya kuma fita iya fada. Baisan sau nawa zai gaya mata ta daina ma Nur kitso ba, duka yarinyar yaushe kanta yayi kwarin da za’a kama shi ana mai kitso, ko gashin kirki ma babu, keyar ba komai har yanzun. Kawai salon a saka mata ciwon kai. Ya ce ta dinga shafa mai sai tayi mata kalba ta saka mata hula, kan da za’a rufe in ba rigima ba meye nayi mishi kitso. Sanin Layla ba kula su zatayi ba yasa ya mike yana daukar Nur din, da kan shi ya karasa in da kayanta suke ya samo wata farar hula mai duwatsu a jiki ya saka mata, takalman ma shi ya dauko mata.

A shekarun natsuwar da bai taba sanin akwaita ba ita ya samu da auren Layla, rayuwar su bata cike da farin ciki ko da yaushe, suna da nasu matsalolin, amman babu rana daya da zaice baiyi dariya daga dukkan zuciyar shi ba, iya wannan yakan isa ya kori koma menene yayi ma farin cikin shi kutse a ranar, balle kuma Nur da yake jin ita din duka rayuwar shi ce. Akan ta yake jin damuwar da a fuskar Abbu kawai yakan ganta, damuwa ce da iyaye suke ji a lokuttan da yaran su basu da lafiya, a lokuttan da zasu ji kukan yaran nasu batare da sanin me yake damun su ba.

Ko faduwa tayi yaga jini duk wani abu da yake kwance a tare da shi saiya ta shi. Yana son Layla, daga baya yasan soyayyar su Ayya, amman son da yake yiwa Nur daban ne, bai san ko dan ita yake gani tana rage mishi kewar Bilal ba, ko rike ta yayi yakan ji wani kusanci da Bilal na ban mamaki. Bai san lokacin da ya daina duba hanyar dawowar Bilal ba, rana daya ya tashi yaji zuciyar shi tayi wani sanyi da yake tare da hakuri, sanyin da yazo mishi da daukar kaddara. Yayi kuka dai ranar, sosai yayi kuka a jikin Layla, kukan da bai bari zuciyar shi tayi mishi ba saboda yana saka ran dawowar Bilal din.

Abinda ya zame mishi jiki shine tura kudi a account din Bilal, duk da yana da wani bankin da yake ajiya, duk yanda yaso ya daina saiya kasa, daga safiyar da aka biya albashi zuwa yamma sai ya kasa samun natsuwa idan bai tura ba, a lokutta irin ranar yakan ji daman ace yaga gawar Bilal, da ya dibi kasa ya zuba a kabarin shi, da tuni ya aminta da rashin shi. Amman har abada akwai bangaren shi da ba zai taba daina jin kamar Bilal din yana da rai ba.

“Layla ki kira mun Bilya a wayata, ki saka mun a speaker…”

Rayyan ya fadi yana gyarawa Nur madaurin takalmin ta.

“Mota na mun wata kara tun jiya, mutuwa tayi jiya fa a hanya, da kyar ma ta tashi, in munje gida sai yazo ya dauka.”

Wayar tashi Layla ta dauko can karshen gado.

“Yaushe screen dinka ya kara fashewa?”

Ta bukata.

“Nur ta fado da ita shekaranjiya.”

Kai kawai Layla ta girgiza, idan tace ya daina bata wayar shi ba zaiji ba. Tunda yana da kudin sake screen. Tana jin dadin yanda bako da yaushe soyayyar yarinyar take rufe mishi ido ba. Kusan tama fi tsoron shi duk da baya dukanta, yana mata ihun da ba ita ba har Layla sai ta tsorata.

“Na ga karamar wayar ka, bayan gado ta fada…mantawa nayi tun jiya… Na saka ta caji tana falo…”

Layla ta fadi tana duba contacts din shi, amsa ta yayi hakan yasa ta daga kai ta kalle shi, da yake suna ne ta fara rubutawa ta saka “Bil…” bata karasa ba sai ta kira lambar farko data fito, ta amsa Rayyan ta mayar da hankalin ta kan screen din, zuciyarta na wata irin dokawa. Jikinta har rawa yake lokacin da ta kashe kiran ganin lambar Bilal, wajen kiran ta shiga ta goge kar Rayyan ma ya gani. Kafin ta kira mishi Bilya din, sai da ta fara ringing sannan ta karasa ta mikawa Rayyan din. Mayafin ta, jaka da sauran tarkacen da zasu bukata ta dauka suka fice daga gidan.

Sosai suka bata lokaci akan hanya saboda Rayyan yayi kwana ya tsaya siyawa Nur mangoron da tunda ta hango shi ta cikin motar take zillo tana dukan gilashin kamar zata fita ta dauka.

“Daada…ina so, ina so.”

Take fadi tana sake maimaitawa.

“Dan ubanki sai kin fasa mun kunne ne?”

Cewar Layla tana juyawa ta harari Nur din da take sake ziro kai tana kiran.

“Daada.”

Kamar yanda take cewa Rayyan, duk yanda Layla taso ta gyara mata ya koma “Daddy” taki. Harta hakura ta kyaleta.

“Da ni nace ka tsaya a siya mangoro babu surutun da ba zakayi mun ba.”

Layla ta fadi cikin sigar mitar da Rayyan bai ko kulata ba. Bayan motar ya ajiyewa Nur ledar yana fadin.

“Karki taba sai munje gidan Ayya sai a wanke a yanka.”

Kai ta daga mishi tana murmushin jin dadi. Da suka karasa ma, Rayyan bai shigar da motar ba tunda Bilya zai zo ya dauka. Anan kofar gida ya ajiye ta, shi ya fara fita ya bude bayan ya taimakawa Nur yana sauko da ita, ledar mangoron ya dauka, kiciniyar da zata fara yi da shi yasa ya sakar mata yana kallon ta, ganin zata fadi yasa shi karba ya zare guda daya a ciki ya bata ta rungume shi kamar ta rike jariri. Dariya yayi kawai yana rufe motar. Tare suka shiga gidan, Nur na rugawa da gudu ta nufi bangaren Ayya, shi baima karasa ba yaga Bilya na kiran shi, dagawa yayi yana sakawa a kunnen shi.

“Gani a kofar gida yallabai.”

Batare da Rayyan ya amsa ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana juyawa. A can gefe ya hango Bilya da yana ganin shi ya fara takowa, sake gaisawa sukayi Rayyan ya mika mishi mukullin motar, yana fada mishi abinda yaji tana yi,

“Dan Allah ka duba min kafin anjima in dai ba wata matsala bace babba.”

Rayyan ya fadi, saboda gabaki daya satin da zai kama aikin dare gare shi, yafi jin dadi ace da motar shi, gashi yasan halin Bilya, ya iya gyara ga ba ha’inci, amman akwai shiririta.

“In shaa Allah zan kiraka dana duba.”

Sallama suka yi, ya tsaya duba text din MTN da suka cire mishi har naira dari na wani caller tune da bai san lokacin da ya shiga tsarin ba. Karamin tsaki yaja kawai, yana tura musu sakon da zai bashi damar fita daga tsarin, matsalar shi da su kenan. Sai su fara cire maka kudin da babu dalili. Sakon Bappa ya amsa ta manhajar WhatsApp, shima Allah ya kama shi, addu’ar Baba taci, sosai yaso ya sake gudu yabar kasar, yanzun gashi nan da matar shi harda yaro daya. Sai dai yaki garin Kano sam, a Kaduna yayi zaman shi, in dai ya shigo sai dai ziyara, zumunci mai karfi ne a tsakanin su, duk da Rayyan ba zai kira matar Bappan da Layla kawaye ba.

Sukan gaisa dai idan sun shigo gari da Bappa din, da ta haihu kuma Layla taje ranar suna ta dawo washegari. Iya wannan din ya ishi su biyun, dan suna zumunci babu inda ya zamana dole matan su ma suyi. Juyawa Rayyan yayi bayan ya saka wayar a aljihun shi, ya kama kofar gidan zai tura kenan yaji kamar iska ta dibo mishi muryar da take cikin kan shi ta fito da ita waje tana dukan kunnuwan shi da muryar.

“Hamma…”

Sai da ya runtsa idanuwan shi kafin ya bude su yana tura kofar.

“Hamma…”

Aka sake kiran shi cikin muryar da wannan karin ba kunnuwan shi kawai ta daka ba, har da zuciyar shi. Idanuwan shi ya sake runtsawa a hankali ya furta,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Saboda ya bawa shekara wajen biyu baya rabon daya shiga cikin wannan yanayin, ba zai koma ba, ba zai koma lokuttan da yake jin kamar takun tafiyar Bilal da baisan yana da sauti ba sai bayan ya rasa shi, ba zai koma lokacin da yake neman fuskar Bilal a cikin duk wani taro da zai gani, a masallacin juma’a, har a wajen jana’iza idan ya samu halarta. Lokuttan da muryoyin mutane da yawa a cikin gidan su take mishi kama da ta Bilal, lokuttan da zai iya rantsewa ba’a cikin kan shi kawai yakan ji muryar Bilal ba. Yana da yarinya yanzun, yana da Nur, zaiyi duk wani kokarin ganin bai rabu da nutsuwar da yake tare da ita ba koya ne.

Saboda tana bukatar shi da duka wata natsuwa da yake da ita. Ba yanzun ba kawai, har lokuttan da zasu zo a gaba, lokuttan da ko tunanin su yayi sai kirjin shi ya dauki zafi, tana bukatar tsayayyen uba da zata rugo wajen shi da dukkan tambayoyin da mutane zasu saka tayi mishi, ba zai bari rashin Bilal ya raunana shi ba. Kafar shi ya daga ya saka guda daya a cikin gidan yaji an dafa mishi kafada.

“Hamma.”

Wannan karin da rauni muryar ta fito tana tsinka abubuwan da Rayyan bai san suna hade a jikin shi ba, kafin zuciyar shi ta fara dokawa cikin sautin da yake ji har cikin kunnuwan shi, a hankali ya juyo yana fara sauke idanuwan shi kan fuskar Bilal, yawu yake tattarawa yana so ya hadiye ko zai jika makoshin shi da yake ji a bushe, ya bude bakin shi yafi sau biyar yana mayar da shi ya rufe,

“Hamma ni ne.”

Bilal ya sake fadi, Rayyan bai yarda ba, ko yaushe zai iya farkawa, wani zai iya zuwa ya tashe shi abinda yake faruwa ya zamana mafarki. Hannun shi ya daga yana kaiwa fuskar Bilal ya taba, ba zai tuna ko ya yanayin Bilal yake a duk mafarkan shi ba, sake taba fuskar yayi, wannan karin samu yayi ya gyara tsayuwar shi ya saka duka hannuwan shi biyu yana taba fuskar Bilal din yana son tabbatar da cewa shine a tsaye a gaban shi ba mafarki yake yi ba.

“Ni ne, ni ne Hamma.”

Bilal ya sake fadi muryar shi na karyewa sosai, wani irin numfashi Rayyan yaja yana sauke shi hadi dayin dariya mai sauti, dariyar da ta saka yaji idanuwan shi sun cika taf da hawaye, dariya ce da babu wani nishadi a tare da ita, wani abu yake so ya fadi amman ya kasa,

“Kace wani abu Hamma… Dan Allah kayi Magana.”

Dariyar Rayyan ya sake yi, yana kai hannuwa ya share kwallar da yake ji a cikin idanuwan shi, juyawa kawai yayi ya tura kofar wannan karin yana shigewa cikin gidan, yana jin Bilal na bin bayan shi, juyawa yayi ya daga mishi hannu cikin alamar da take nuna ya daina bin shi, kafin ya sake juyawa yaci gaba da tafiya, ko hanya baya gani sosai saboda idanuwan shi da suke cike taf da hawaye. Sake juyowa yayi wannan karin duka hannayen shi biyu ya saka ya hankade Bilal din.

“Hamma.”

Bilal ya kira yana dafe kirjin shi inda Rayyan din ya hankade yana dorawa da.

“Kayi hakuri…”

Na shi idanuwan cike da hawaye shima, sai da Rayyan ya dan duga saboda yanda yake jin numfashin shi kamar baya kaiwa kirjin shi, kafin ya mike tsaye sosai yana kallon Bilal.

“Ba kwanaki ba, ba satika ba, Bilal ba wata daya ba. Shekaru, shekaru fa… Shekaru zaka dora akan kalmar hakuri?”

Bayan hannun shi Bilal ya saka yana murza idanuwan shi kafin ya dan daga kafadun shi cikin alamar helplessness, bai san me zai fada ba, baisan ya zaice ba. Abu daya ya sani, har cikin motar Lagos ya shiga, har zama yayi ya kasa, bai zaice ga dalili guda daya ba, amman nisan awannin da suke tsakanin Kano da Lagos ne sukayi mishi yawa, nisa yake so yayi da gida, nisa yake so yayi da kowa saboda laifn shi da yake ji yafi karfin yafuwa. Nisa yaso yayi musu ko zai rage musu zafin laifin da yayi, amman ba nisa mai yawan wannan ba.

Yana bukatar ya bude idanuwan shi a duk lokacin da bacci ya dauke shi da sanin cewa suna kusa da shi duk da yayi musu nisa, ko kudin shi bai tsaya an mayar mishi ba, tunda zasu iya siyarwa da wani kujerar, lokacin ana ta saka kaya, jakar shi kawai ya dauka, daman dayar tana goye a bayan shi. Hotel ya kama, wayar shi kasheta yayi, satin shi biyu a hotel din batare daya fito ko ina ba, jinya yayi ba karama ba ta rashin su, ta nisa da gida, ta tunanin halin da kowa zai shiga. Ranar daya fita kuwa sabon sim ya siya ya saka a wayar shi ya adana wancen.

Yasan kudi zasu kare mishi, dole yana bukatar neman wata hanya ta samun kudi, sana’ar karfi ce karshen abinda zaiyi, ba zai karya ba in ba dole ta kama mishi ba ba zai iya ba. Bai saba wahala ba, baima san wani abu wahala ba tun tashin shi. Su Abbu sun tabbatar da hakan, unguwannin da ko da wasa bai tabajin su Ayya na kaiwa ziyara ba nan ya fara nufa yana shiga duk wata private school da yaci karo da ita, bai boye musu cewa shi din bashi da takardu ba, amman yayi karatu har zuwa shekarar shi ta karshe, ya dai ce musu matsala ce ta saka shi ajiyewa dole, fiye da makarantu biyar sun so rike shi, musamman bayan sunyi mishi gwaji, amman sai suka so yin amfani da wannan damar ta cewa ba shi da takardu wajen biyan shi kudin da basu taka kara sun karya ba, haka yaci gaba da yawo wajen sati daya, kafin ya samu wata makaranta a cikin rijiyar lemo can wajen layin masallacin espa.

Da yake shugaban makarantar musulmi ne, mutum mai matukar kirki da sanin ya kamata. Har kara ma Bilal din kudi yayi daga baya ganin yana da sani ta bangaren addini, makarantar kuma boko ce hade da islamiyya, sai yake koyarwa a duka bangarorin biyu. Anan cikin rijiyar lemon ya samu karamin gida daki biyu ya kama. Watan daya duba account balance din shi yaje cire kudi yaga sun karu sosai, daga farko ya dauka ko wani yayi kuskuren tura mishi kudi, tunda layin da yake ganin alert yana kasa, amman yakan duba ta email din shi. Hakan yayi, yaga Rayyan ne.

“Hamma, nauyin zai mun yawa…dan Allah Hamma.”

Shine kalaman da ya dinga furtawa yana maimaitawa, yayi nisa da sune dan su sami sauki, ba dan ya kara dora musu wata wahala ba. Sai dai ba zaiyi karya ba, kudin suna taimaka mishi sosai da sosai. Ba zaice ya nemi wani abu ya rasa ba, iya cikin shi da abinda ba za’a rasa ba, kudin ya ishe shi har ma yayi mishi yawa. Watanni shidda ya dauka cir kafin mafarkan kowa na gidan ya fara damun shi, rana daya ya wayi gari yaji kewar su ta danne mishi kirji, numfashin kirki ma baya iyawa, shisa ya dauki sim din shi ya saka a wayar, hankalin shi rabi da rabine ko da yaje wajen aiki, ba zai manta uzurin rashin lafiya daya bayar ba ya kama hanyar gida, a hanya ya tsaya ya siyi kati ya saka a layin.

“Watakila ko dan babu kudi shisa sako ko daya bai shigo ba.”

Ya fadi a zuciyar shi, har wajen sha biyun dare yana kallon wayar.

“Kirana kawai zakuyi, zan dawo gida.”

Tunanin da yakeyi kenan a cikin kan shi har wayewar gari inda ya zare layin daga wayar shi, daga lokacin ne kuma ya sami karamar waya ya siya inda ya saka layin a ciki. Daga ranar kuma ya fara kunna wayar daga safiya zuwa karfe biyu na rana, wani lokacin ma yana kwana bai kashe ba, banda yan MTN babu wanda yake kiran shi, ko sako yaji ya shigo sai zuciyar shi ta doka, sai dai idan ya duba yaga ko bankin shi ko MTN din ne dai. Fushi sukeyi, ya san fushi sukeyi da shi shisa basu kira ba, laifin shi ya so wankewa da karin wani laifin na tafiya, amman bai taba cire rai ba, yasan zasu kira shi, komin dadewa zasu kira.

Ba zaice ga yanda yayi shekarun nan batare da su a kusa da shi ba, bai san me ya rike nutsuwar shi har haka ba. Yau din ma kamar kowacce ranar karshen mako, zaune yake bayan ya karya yana marking assignment din yara, sai wasu azuzuwan da test ne yayi musu kasancewar an kusan fara jarabawa yaji karamar wayar shi na ruri, karamin tsaki yaja kawai yana cigaba da abinda yake yi saboda yasan MTN ne, su kadai zasu fara kiran shi kamar suna bin shi bashi. Wutar da aka kawo yasa shi daukar babbar wayar shi da ba wani amfanin kirki yakeyi da ita ba, tunda ya koyi rayuwa babu kafar sada zumunta, abinda bai taba tunanin zai iya yakicewa ba.

Sai dai ya iya karfin halin barin su Rayyan ma, ballantana wani whatsapp, hannu ya mika ya dauki karamar wayar ya duba yaga ko akwai sauran caji tunda ya kwana wajen hudu bai sakata a caji ba, latsawa yayi kawai dan sabo yana shiga yaga missed call din da yasaka shi mikewa babu shiri ganin lambar Rayyan da ko a bacci ya ganta zai ganeta. Mukulli kawai ya dauka yana saka takalma a kafafuwan shi, zai iya tuna ya kulle gidan, amman ko mai mashin daya sauke shi a kofar gidan su, hannu kawai ya saka a aljihun shi yana lalubawa ya kuwa samu dari biyu ya mika mishi, zuciyar shi yake ji a tafukan kafafuwan shi a duk takun da yakeyi, shisa yake jin kafafuwan sun mishi wani irin nauyi na ban mamaki.

Basu kara nauyin ba sai da ya hango Rayyan, wannan karin tsallen da zuciyar shi tayi a ko ina na jikin shi yake jin dokawar ta, shi da kan shi bai gane muryar shi ba lokacin daya kira Rayyan din, yanzun ma da suke tsaye ji yake kamar mafarki, kamar bashi bane tsaye a gaban Rayyan da yaga kamar bai canza ba a shekarun nan, yana nan yanda ya san shi, sai dai akwai wata natsuwa da yake gani a fuskae Rayyan da bai taba sanin yana da ita ba haka.

“Me zance Hamma?”

Wannan karin rashin madafar a muryar Bilal ya fito.

“Baku kirani ba. Hamma kirana kawai zakuyi kamar yau…”

Da rashin fahimta Rayyan yake kallon shi, saboda baya gane abinda yake fadi, baya ma gane abinda yake ji balle kuma zantukan Bilal din, wayar shi Bilal ya daga duk da baya tunanin Rayyan yana ganin screen din saboda kankantar wayar.

“Baku kira ni ba, kai ma baka kira ni ba, ni din mai laifi ne, ban san ya zan nuna fuskata ba baku neme ni ba Hamma.”

Dariya Rayyan yayi mai sauti yana kallon Bilal din sosai, duk shekarun nan jira yake yi su kira shi kafin ya dawo, sau nawa yana daga wayar shi ya danna lambar Bilal din yayi ta kallon ta, saboda yasan koya kira a rufe zaiji ta, kiran ba zai mishi amfanin komai ba sai karin daga mishi burin cewa bai rasa Bilal din ba, daga baya ma daina dannawa yayi saboda yasan an siyarwa da wani daban lambar, balle harya gwada kira wani ya dauka ya tabbatar mishi da yanda ba Bilal kawai ya rasa ba har lambar wayar shi ma ta tafi.

“Ta ya zamu fara kiran ka idan duka muna tunanin ka rasu?”

Kallon shi Bilal yayi, saboda maganganun shi sun daki kunnuwan shi da wani yanayi mai wahalar misaltawa.

“Motar da ka shiga, babu wanda ya fita a motar, da alama kai ka dai ka fita.”

Kai Bilal yake girgizawa Rayyan.

“Ta ina zamu kira ka Bilal? Ta ya zaka jira kiran da bamu san kana jira ba? Kiran da banda karfin zuciyar yin shi in sake jin wayarka a kashe…”

Kan dai Bilal yake girgiza mishi.

“Na shiga motar da kuke tunani, amman ban zauna ba, na kasa yin nisa mai tsayin wannan… Ban zauna ba Hamma”

Bilal yake fadi cikin tashin hankali, yana jin zuciyar shi kamar zata tsaga kirjin shi ta fito da halin da yake hasaso sun shiga, sanin tafiya yayi daban, amman tunanin ya rasu? Tunanin sun rasa shi gabaki daya, baisan ta inda zai fara hasaso tashin hankalin su ba.

“Ayya fa?”

Ya tambaya, kallon “Sai yanzun tunanin ta yazo maka? Sai yanzun kake tunanin halin da ta shiga? Me yasa kafin ka tafi bakayi tunanin ta ba?” Rayyan yake yi wa Bilal din. Kafin ya dora wasu tambayoyin akan harshen shi yana jifan Bilal da su

“Me yasa zaka tafi? Nace ba zan yafe maka ba na sani, amman me yasa zaka tafi? Idan baka duba ni ba, me yasa zaka bar Ayya? Me yasa ka tafi Bilal?”

Ba tambayoyin Rayyan bane suka saka hawayen shi zuba, yanayin yanda yayi mishi sune, muryar shi, yanayin da yake kan fuskar shi da cikin idanuwan shi.

“Hamma…”

Kai kawai Rayyan ya girgiza mishi yana juyawa, komai ne yake dawo mishi sabo, duk wani ciwo da yake tunanin lokaci ya dishe mishi zafin shine yake budewa yana dawowa sabo fil, kiran duk da Bilal yake mishi baisa ya juya ba. Amman takun tafiyar Bilal din da yake bin shi a baya jinta yake har cikin zuciyar shi. Kan shi tsaye bangaren Ayya ya wuce, bata ma falon sai Huda da tana ganin shi tace,

“Hamma, yanzun naga Nur, nace tare kuka zo tayi banza ta kyaleni, ko kallona fa batayi ba ta wuce tana neman Ayya….har…”

Maganar da ta dauke mata ya tabbatar wa da Rayyan din cewa ta ga Bilal ne da yake bayan shi, da sauri ta karasa inda Rayyan yake ta kama hannun shi tana girgiza shi, idanuwanta yana kan Bilal, so take ya juya yaga abinda take gani, ya tabbatar mata da yana ganin Bilal din ba ita kadai bace take ganin fatalwa a cikin dakin su, tasan tsoro, amman bata san firgici ba sai yau, muryarta a wahalace ta fito.

“Hamma… Hamma.”

Ta ke fadi tana sake girgiza Rayyan daya kama hannuwan ta duka biyun ganin tana shirin shidewa.

“Na gan shi, ki kalle ni Huda, na gan shi… It’s okay…bake ka dai kike ganin shi ba.”

Rayyan yace yana so ta dauke idanuwan ta daga kan Bilal ta kalle shi, amman kai take girgiza mishi hawayen da yake cikin idanuwan ta yana zubowa.

“Ayya! Ayya!!”

Take kira cikin firgici tana kokarin kwacewa daga rikon da Rayyan yayi mata, amman yaki sakin ta saboda yanda jikinta yake bari zata iya samun matsala idan ya sake ta.

“Ayya!!!”

Huda ta sake kira tana neman taimako daga wajen Ayya.

“Huda!”

Rayyan ya kira, wani irin kuka take tana fitar da numfashi da kyar, lokacin da Ayya ta fito a gigice itama saboda bata taba jin Huda ta kirata cikin yanayin da ta kirata yanzun ba, sam bata kai hankalinta kan Bilal da ganin ta ya saka shi dafa bangon da yake kusa da shi saboda yanda yaji gabaki daya gwiwoyin shi sunyi mishi sanyi.

“Ayya”

Ya kira, amman labban shine kawai suka iya motsawa, sam sauti ko daya bai fito ba, Ayya kuwa Huda ta kama daga hannun Rayyan.

“Me ya faru? Lafiya? Me ya faru?”

Take tambayar Huda din, tana karasa tambayar hadi da kallon Rayyan daya sauke idanuwan shi daga cikin nata.

“Ayya…”

Huda ta kira cikin sabon tashin hankali tana juyawa, yanayin da yasa Ayya kallon inda ta kalla, tana ganin Bilal, runtsa idanuwan tayi tana sake bude su hadi da jin kamar wani ya watsa mata ruwan kankara saboda tsikar jikinta da ta mike gabaki daya, wani irin yanayi ne da babu kalaman da zasu misalta shi, dole Huda zata firgice, ta sha hasaso ganin Bilal, ba’a mafarki ba a ido biyu, amman da gaske ne, girman kusanci ba zai taba hanaka tsorata ba idan har zakaci karo da mutumin da kasan mutuwa ta rabaku, saboda wani irin tsoro ne kamar bargo ya nannade daga kafafuwanta har zuwa kanta kafin ya sami wajen zama a cikin zuciyar ta.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×