Skip to content
Part 34 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

“Ayya…”

Bilal ya kira yana sa ta raba idanuwanta da inda yake tsaye tana kallon Rayyan daya daga mata kai yana tabbatar mata da yaji kiran, ba kunnuwanta bane kawai suka ji cewa Bilal ba tsaye kawai yake a cikin dakin ba, har magana yakeyi. Hankalinta ta sake mayarwa kan shi tana ganin yanda yake takawa yana karasawa inda take kamar wanda yake koyon tafiya, da duk takun da zaiyi da yanda zuciyarta take kara dokawa a cikin kirjinta da wani irin tsoro, sai dai kamar jira kawai yake ya karasa inda take kafafuwan shi su kasa daukar shi dan anan gabanta ya durkushe. Yayi kuka mai yawa bayan da ya tafi, amman baiji kalar kukan da yake tattarowa daga duk wani lungu na zuciyar shi daya taba yin ciwo ba irin yanzun.

Dan wani irin gunji ya saki mai tsuma zuciya yana rike kafafuwan Ayya da itama taji sunyi mata wani sanyi, Huda ta ture gefe, ba tsugunna tayi ba, zama tayi akan kafafuwan ta kamar mai zaman sallah tana kallon Bilal, ya sha bamban da fatalwin da take gani a fina-finai, jikin su baiyi kalar na shi ba, batajin kuma ana iya jiyo hucin numfashin su, a hankali ta daga hannunta da kafin ta kai shi fuskar Bilal ya kama shi da duka nashi biyun. Ko da fatalwa ne shi na danta ne, Bilal ne. Hannun shi na shine, hannu ne daya saba kama nata tun kafin yakai girman haka.

Duk da yanzun girman bai canza yanayin shi ba, zata gane hannun Bilal a cikin dubban hannaye, saboda zai rike nata hannun kamar yanda ya rike shi yanzun, cike da yarda da kaunar shi da batajin wani da bai san zafin da ba zai iya fahimta.

“Bilal”

Ayya ta kira yana daga mata kai kawai saboda kukan da yake yi, abu na farko da duk wata mahaifiya takeyi a lokacin da take ganin hawayen da na ita bace sanadin zubar su shi Ayya tayi, zame hannun daga cikin na Bilal ta kama shi zuwa jikinta duk kuwa da girman shi, kan shi ya dora a jikinta yana sake sakin wani sabon kukan, kukane na kewar ta, na kewar su gabaki daya, kukane na ban hakuri, kukane na abubuwa da yawa. Ba zaice ga lokacin daya dauka a haka ba, amman bai dago ba sai da yaji zuciyar shi ta daina nauyin da take mishi tukunna ya dago yana kallonta, ita yau ta nemi inda hawaye suke ta rasa, da kansu sun san cewa yanayin da take ciki sun girme su.

“Bana cikin motar Ayya, ban shiga ba, bana ciki.”

Sune kalaman da suka zo ma Bilal, kallon shi Ayya takeyi, kallon shi take saboda bata taba saka ran sake ganin shi ba, kallon shi takeyi kaunar shi da babu inda taje mata tana tasowa tana kuma shafe duk wani bangarori na zuciyar ta daya hakura da shi, bangarorin da sukayi jinyar rashin shi, hannuwan shi ta kama tana saka fuskarta a ciki hadi da sauke wata irin ajiyar zuciya da ta budewa hawayenta waje, wannan karin ita ta kwantar da kanta a jikin Bilal, kukan ta yana sake fito mishi da sababbin hawaye.

“Kaga me kayi ko Bilal? Kaga me tafiyar ka tayi mana?”

Rayyan yake fadi yana kifta idanuwa saboda baya son ya fara kuka, yanajin su duka ba kuka sukeyi ba, idan ya fara ba zaiji lallashi ba.

“Daada”

Nur da ta fito ta kira Rayyan din, da gudu take tahowa tana saka zuciyar shi mantawa da komai da yake faruwa saboda yanda take dokawa da tsoron karta fadi, bai sami natsuwa ba sai da yaga ta zagayo ta kama kafafuwan shi kamar ta dade bata gan shi ba, ko daki ya shiga tana wani dakin, idan ya fito haka take barin duk abinda takeyi ta tashi ta rugo ta rike shi kamar yayi wata tafiya mai nisa, sai yaji ta nutsar da shi, ta saka zuciyar shi wani irin sanyi. Ganin ta dago daga jikin shi tana kallon Bilal yasa shi kallon Bilal din shima. Sosai Nur take kallon Bilal kamar ta san shi. Abinda kafin psychology yayi mishi bayanin shi yake ganin tsakanin Ayya da Bilal, tsakaninta da sauran yan gidan shi yake gani tsakanin Nur da Bilal da har lokacin baima kula da ita ba.

Hankalin shi gabaki daya yana kan Ayya da ta dago tana saka hannunta ta goge fuskarta da shi. Shima Bilal tashi fuskar yake gogewa, hakuri yake so ya bata, amman kalaman sunki fitowa. Ko da Nur bata kai haka ba, sam yarinyar batayi qwiya ba, kowa ya dauketa zuwa takeyi, gashi bata tsoron mutane, kawai magana ce batayi sosai.

“Yarinyar nan ko dai kurma ce Hamma?”

Layla ta tambaye shi, yayi dariya sosai ranar, har yanzun ko shi kadai ya tuna sai yayi dariya.

“Allah da gaske nakeyi fa, ko irin wakar nan ta yara Nur batayi sam, in ba kuka take ba bakajin sautin komai.”

Kai kawai ya girgiza saboda dariya da ta hana shi magana, shi yanajin wakar da take magana, ba ko yaushe ba, haka ta dade bata fara magana ba, da ta fara din ma ba sosai ba, duk rashin surutun shi yana iya ba Nur labari har ya gama yanayin fuskarta ne kawai zai nuna tana jin shi, ko in abin amsawa ne ta daga mishi kai. Ko kayan wasa tafi son wanda suke kamar bulalluka tayi ta hadawa, sai kuma puzzle da zata zazzage ta yini tana shiryawa, shisa yanzun ma baya tarkato mata komai sai kalaluwan su. Yar tsana da teddy duk inda ka ajiye nan zaka dawo ka dauka, bata so, in ya tare mata hanya zata dauka tayi cilli da shi gefe.

Yanzun ma Rayyan ta kalla, kamar tana son ya bata izini ne bai fahimta ba, ya dai daga mata kai, sannan ta juya, hannunta daya rike da rigar Rayyan, dayan kuma mika shi tayi tana bubbuga bayan Bilal da yana juyowa ta kara matsawa tana shigewa jikin Rayyan, kallonta Bilal yakeyi, itama kallon shi takeyi. Zuciyar shi ta gama shan duk wani mamaki na duniya, watakila shisa yaji ta natsu waje daya yanzun. Rayyan ya kalla yana neman tabbaci, kai Rayyan ya daga mishi.

“Maimunatu… Nur”

Rayyan ya furta a hankali, yaso ya dora da.

“Bamu ka dai ka bari ba har da ita, ka rasa abubuwa da yawa Bilal.”

Amman sai ya kasa, yanayin da yake fuskar Bilal din ya saka shi ya kasa cewa komai. Nur ya rankwafa ya dauka yana sabata a kafadar shi ya raba su ya wuce, cikin dakin ya shiga sosai ya samu kujera ya zauna tare da Nur a jikin shi. Banda Huda data bar falon, daga Ayya har Bilal nan inda suke suka zauna, da alama babu wanda ya iya motsa. Rayyan bai musu magana ba, asalima Nur ya tashi yabi da taja hannun shi, mangwaronta ta dauko ya kamata zuwa kitchen ya wanke ya dauki wuka da filet, yayyanka mata yayi ya bata ta fita falo taje ta zauna.

Shikam jin ana kiran sallah yasa shi shiga dakin Ayya ya dauro alwala ya fito.

“Idan zakayi sallah ka tashi kayi alwala mu tafi masallaci…”

Juya kai Bilal yayi yana kallon Rayyan din.

“Zan taho yanzun…”

Sosai Rayyan ya kalle shi.

“Baka da hankali ne halan? Baka da ‘yancin fita kai kadai, idan na tafi sai dai kayi sallah a gida.”

Murmushi Bilal yayi cikin yanayin daya manta rabon da yayi shi.

“Babu inda zanje Hamma.”

Kai Rayyan ya girgiza

“Na manta yanda yarda da kai take, zai dauki lokaci kafin ta dawo, ka tashi.”

Bai musu ba ya samu ya mike, yanajin jikin shi a wani irin mace, alwalar yaje ya dauro shima yana fitowa.

“Daada…”

Nur ta kira cike da alamun tambaya.

“Masallaci zanje Nur, yanzun zan dawo kinji?”

Sai da ta daga mishi kai sannan ya kalli Bilal da idanuwan shi suke kan Nur din, kallonta yake yana rasa abinda yake ji akan ta, saboda kaunarta ko akwaita baisan inda ta labe ba, ciwon da samunta ya haifar mishi kawai yake ji, ciwon da bata da laifin shi, tabon da sukayi wa rayuwar ta yake gani a tare da yarinyar.

“Ki yafe mun, ki yafe mun kafin mu tsaya dake a gaban Allah, wallahi bani da hujja.”

Ya furta can kasan zuciyar shi, kafafuwan shi na daukar shi da kyar lokacin da suka fita masallaci, ga wani tsoro da yake ji har ran shi. Gidan bai sake rudewa ba sai bayan da suka dawo sallah, saboda lokacin duk yan gidan sun zo, da yake asabar ne, yawanci har masu auren idan basu zo da matan su ba suna zuwa su kadai, haka matan gidan ma, su Zubaida suna zuwa, kusan duk asabar din duniya da wahala kaga basu hadu a gidan ba, dan Rukayya sun dade akanta kafin ta dawo hayyacin ta, tana ganin Bilal din ta mike, sulalewa tayi gabaki daya, ga ciki da yake jikinta.

Gabaki daya Bilal a rude yake jin shi.

“Kuyi hakuri, dan Allah kuyi hakuri.”

Shine abinda yake furtawa yana sake maimaitawa yana wani irin kuka da daga baya su suka koma suna lallashin shi. Layla itama sai da Rayyan ya riketa, duk kuwa kunyar da daga ita har shi basu san suna da ita ba sai bayan auren su, dan kujera ma in suka zauna a cikin gidan ko babu kowa sai sun dan bada tazara a tsakanin su. Ranar kuwa da ya rike hannunta ta yana daura mata agogo sun zo gidan zasu tafi saboda tana rike da Nur, sai ta rike agogon a hannu, sai ga Abbu ya fito sakin agogon yayi har ya fashe, saboda kunyar da yaji, ita kanta Layla kasa hada idanuwa tayi da Abbun. Murmushi yayi kawai ya rabasu ya wuce.

Amman yau gaban kowa ya riketa har kitchen ya jata ya dibi ruwa ya bata.

“Ki rufa mun asiri Layla, babyna a jikin ki, dan Allah ki natsu.”

Yake fadi, amman bata san yanda zata fara natsuwa ba, sai da ya kamata yana riketa a jikin shi, tafi mintina goma kafin numfashin ta ya dai-daita, sannan ta iya raba jikinta dana Rayyan, suka samu suka baro kitchen din zuwa falo, kan kujera suka samu suka zauna. Banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, ganin Bilal din ya nutsar da wani shimfidadden kalubale da take hangowa a gaba, ko ba komai tambayoyin da Nur zatayi mata wata rana ba ita kadai zata yiwa ba, yanzun addu’a takeyi Allah ya bama Bilal aron tsayin kwanaki tare da su, saboda ganin shi ya tuna mata akwai tambayoyin da koya Rayyan zai rike hannunta ba zai isa ba.

Sam Bilal da Rayyan basu samu wani lokaci su kadai ba sai da dare, sai bayan isha’i, sannan, kallon shi Bilal yake yi, amman maganganun Abbu suke dawo mishi.

“Da yana nisa da iyayen shi haka Bilal?”

A idanuwan su yake ganin yanda bai kyauta ba, yayi tunanin su kafin ya tafi, amman tunanin kan shi yafi yawa, ba zai iya fuskantar su ba shisa ya zabi ya gudu. Amman gudun nashi bai canza komai ba, bai rage musu ciwo ba kamar yanda yayi tunani, asalima ya kara musu wani ciwon ne na daban.

“Hamma kace wani abu.”

Bilal ya bukata, saboda shirun yayi mishi yawa.

“Me zance? Bani da wasu kalamai.”

Numfasawa Bilal yayi.

“Kace ka yafe mun.”

Dan juyawa Rayyan yayi yana kallon shi, ba yafe mishi bane baiyi ba, ko da bai yafe mishi ba, dawowar da yayi ta wanke komai, amman ba zai fada mishi yaji ba dan yanzun, ya jira kamar yanda ya saka shi jiran shi duk tsayin shekarun nan.

“Da kana son ji da baka dade har haka ba.”

Kai Bilal ya jinjina, yana son ji, zai jira duk lokacin da hakan zai dauka, zai jira, zai kuma nunama Rayyan din da gaske yakeyi ya dawo. Babu inda zaije, yana kallo Rayyan ya mike, Nur da tayi bacci akan kujera ya dauka yana sabata a kafadar shi kafin ya kalli Bilal.

“Karka bar gidan nan, da gaske nakeyi Bilal, ko ina zakaje ka jira sai gobe idan Allah ya kaimu, ka jirani sai gobe mu tafi tare.”

Kai Bilal din ya jinjina mishi kawai, yana hada idanuwa da shi, dan baisan kome Rayyan din yake nema a cikin idanuwan shi ba.

“Ka rantse mun babu inda zakaje.”

Saboda a tsorace yake, ji yake kamar kar su koma su kwana a gidan yasa ido akan Bilal din karya sake tafiya.

“Ba inda zanje Hamma, babu inda zanje. Ka yarda dani, babu inda zani.”

Numfashi Rayyan ya sauke yana wucewa ba dan zuciyar shi ta so ba. Bangaren Mami yaje yana yiwa Layla magana ta fito su tafi gida. Da yake Bilya ya dawo mishi da motar shi, ko kudin shima bai tura mishi ba saboda bashi da wadatacciyar natsuwa, sai dai inya isa gida tukunna sai ya samu yayi mishi transfer, kafin su karasa kira biyu yayi wa Bilal duk idan ya daga amsa daya yake bashi.

“Ba inda zanje Hamma, ina nan.”

Har sai da Layla ta dafa shi sannan ya sauke numfashi.

“Ka yarda da shi ko yayane, babu inda zaije. Wannan karin ko da zaka rasa shi, rashin zaizo maka da tabbaci, ba zaka kwanta da rashin natsuwa ba saboda in shaa Allah.”

Kai kawai ya iya dagawa Layla, saboda a zantukan akwai tunatarwa, dawowar Bilal baya nufin mutuwa idan ta tashi zata tsallake shi, a yanzun din ma zai iya sake rasa shi, amman duk firgicin da kalaman ta suka sake jefa shi sun zo mishi da wata natsuwa da ba zata misaltu ba, addu’a yakeyi ko da zai sake rasa Bilal din ya samu damar da ko bashi zai suturta gawar shi ba ya halarci jana’iza, ya ga ya binne shi, yayi mishi bankwana, sai ya dawo yayi jira hakurin da yake saukarwa kowanne bawa a yayin rashi, ya kuma shiryawa tashi mutuwar, tunda babu wanda zai tsallake, babu wanda zata bari, kowa cikar lokaci yake jira.

******

Hutun da baisan yana bukata ba shi yayi, satika biyun da basu dai-dai ta mishi komai ba, amman sun nutsar da rayuwar shi, sun dawo mishi da abinda ya rasa, sun dawo mishi da yan uwan shi. Duk da har yanzun Ayya bata daina kallon shi kamar zai sake tafiya ba. Ko sun gaisa da asuba idan takwas tayi bai sake fitowa ba sai ta kira wayar shi taji ko lafiya. Da yake satin farko yaci gaba da zuwa aiki dan karamcin da mai makarantar ya nuna mishi, sai ya tsaya har sati daya ya bashi damar neman replacement kafin ya dawo, sai lokacin sukaje da Rayyan ya tattara duka yan kayan shi da suke gidan da yake haya. Daman saura wata daya kudin shekarar ya kare, mukulli kawai ya kaiwa mai gidan.

Yau kam tsaye yake kofar gidan su Aisha yana neman kwarin gwiwar shiga cikin gidan. Da kyar ya iya kwankwasa maigadi ya bude mishi, kallon Bilal yakeyi yana mamakin inda ya shiga a duk tsayin shekarun, gaishe da shi Bilal yayi yana wucewa harabar gidan, zufa har cikin tafukan hannayen shi yake jinta. Ba tunaninta bane baiyi, sosai take fado mishi. Ko bayan ya dawo dinma tana ran shi, yana tunanin inda rayuwa ta kaita, kasa hakuri yayi yace ma Rayyan.

“Aisha tayi aure na sani… Tayi aure yanzun.”

Tafiyar shi ta saka ya rasa abubuwa da dama, bayajin wata zata so shi yanda Aisha taso shi. Ya rasa shekaru uku a tare da su, baiga auren da yawa daga cikin yan uwan shi ba, baya cikin hotunan su da rayuwar da sukayi a shekarun, ya kuma rasa Aisha, kai Rayyan ya girgiza mishi.

“Bana so in maka magana baka shirya ba. In ba a watan nan tayi aure ba tana nan, naganta a gidan mai last month.”

Dan ba zai manta bayan sun gaisa ba, shi duk daburcewa yayi da yaji ta tace, yana zaune cikin mota, ya juyo ya ganta.

“Hamma”

Saukowa yayi, da suka gaisa saiya rasa abinda zaice mata, kamanninta suna nan, amman ba yarinyar da yasani bace, ba budurwar Bilal din shi da take yi musu girki bace a makaranta, wannan ta girma, ta zama cikakkiyar budurwa, idan sa’anni daya suke da Layla ba zata shige shekaru ashirin da biyar zuwa da shida ba yanzun. Ba kamar sanda ya santa tana sha wani abu ba. Haka kawai ya tsinci kan shi da son tambayar ko tayi aure, sai ya kasa, bakin shi yayi mishi nauyi, dan yana jiran Bilal ba shida tabbas din zai dawo, baiga dalilin da zaisa yayi mata tambayar ba, amman ga mamakin shi dariya tayi a nutse.

“Banyi aure ba Hamma, ban dade da gama bautar kasa ba…”

Kai ya jinjina mata, labarin yayi mishi dadin ji, sallama sukayi da sakon ta na ya gaishe da Layla.

“Ka dauki kafafuwan ka kaje kafin ka rasata gabaki daya.”

Shine abinda Rayyan ya fada mishi.

“Kana tunanin zata so ni har yanzun? Ni din bani da komai da zan bata, ga Nur kuma…”

Kallon shi Rayyan yayi.

“Kana da zuciyar ka, ni bansan me zance maka ba, ban iya kalamai kamar Abbu ba, idan kana tunanin makaranta ne na fada maka ina sake tsayar maka duk shekara, zaka iya cigaba sanda ka shirya. Zaka iya fara zuwa kasuwa kasani in ka fadama Abbu, zaka samu sana’ar da zaka iya rike mata…”

Sauraren Rayyan yakeyi

“Nur ba zata hana komai ba in dai tana son ka har yanzun, zata fahimce ka, kuskuren ka a wajen Allah ma mai yafuwa ne balle kuma mutum, rashin ta ne idan bata fahimta ba, sai ka hakura, sai ku hakura da juna. Amman kaje, ko ba komai ta cancanci kayi mata bayani.”

Numfashi ya sauke yana sake kallon Rayyan daya da kuna mishi fuska.

“Na gaji da magana Bilal, bansan me zan kara ce maka ba.”

Dariya yayi, kamar yanda yayi murmushi yanzun duk kuwa da yanda yake jin zuciyar shi na mishi rawa. Wayar shi ya zaro daga aljihun shi yana kiran lambarta, sai da ta kusa yankewa sannan aka daga.

“Aisha”

Ya fadi yana jin yanda take fitar da numfashi daga dayan bangaren ,

“Nawan?”

Ta kira cike da shakku da tsoron da yake karanta a yanda muryarta take rawa.

“Ni ne Aisha, ina cikin gidan ku…”

Jin yanda take fitar da numfashi yasa shi dorawa da

“Ban rasu ba, bana cikin motar da ake tunani, bana ciki Aisha.”

Daina jin ko motsinta ta dayan bangaren da yayine ya saka shi sauke wayar daga kunnen shi, mintina ya bata ta tattara nutsuwar kafin ya sake kira har sau biyu, amman ba’a daga ba.

“Ki daga dan Allah, Aisha ki daga”

Yake fadi yana sake kiranta, da yake kan shi na duke yana kallon wayar baisan ta karaso ba.

“Nawan”

Ta fadi tana saka shi dagowa yana kallon ta, tunda yake da ita yaune karo na biyu da take tsaye a gaban shi babu hijabi, na farkon kuma a asibiti ne. Ko takalma babu a kafafunta, shisa baiji takun tafiyarta ba.

“Nawan…”

Ta kira wannan karin muryarta na karyewa, kai yake iya daga mata, kafin yayi wani motsin kirki ta hade space din da yake tsakanin su, a jikin shi ya jita, ba haramcin hakan bane tashin hankalin shi, asalima so yake ya zagaya hannuwan shi ya riketa a karo na farko a jikin shi ko dan kewarta da yake ji a ko ina na jikin shi. Amman a cikin gidan su yake, baida idon da zai kalli wani na gidan su idan ya fito ya gansu a haka. Shisa ya kamata yana dago ta daga jikin shi.

“Ki rufamun asiri Aisha, laifina mai yawane har a idanuwan yan gidan ku, kar ki mu kara musu dalilin da zasu hana mun ke”

Hannu tasa tana goge hawayen da ta rasa ta inda zata fara tsayar da su. Duk yanda Bilal yaso ta koma gida ta dauko takalma da hijabi kiya tayi, haka ya hakura ya kyaleta, anan suka tsaya yana rasa ta inda zai fara yi mata bayani. Sai ya zabi yaji yanda take a maimakon bayani

“Ban sani ba Nawan, ban san ya nake ba, amman na san komai zai dai-daita tunda ka dawo kafin a hadani aure da wanda bana jin soyayyar shi ko kadan a cikin zuciyata”

Hira sukayi, hirar duk da tazo musu ita sukeyi, dakyar ya iya barinta da tarin alkawurran da yake fatan cikawa. Bai mata bayanin komai ba sai da yaje gida, har aka kira asuba suna manne da juna a waya. A washegarin ranar ya samu Abbu da maganar aje gidan su Aisha, bai musa mishi ba kuwa, da yake itama Aisha ta samu Baban nata da cewar za’a zo a gan shi. Ana isha’i su Abbu sukaje gidan. Bilal da yake gida ya kasa zaune ya kasa tsaye yana jiran dawowar su, sai kiran Aisha yakeyi sai tace mishi.

“Ba su tafi ba har yanzun, ban san me suke cewa ba, bana jiyo su daga inda nake. Nawan ba zan iya sake rasaka ba, bana jin zan dawo dai-dai wannan Karin.”

Bashi da kalaman bata tabbaci idan ba dawowar su Abbu ya gani ba, shisa yake fada mata na shi tsoron. Saboda da gaske ne, babu macen da zata so shi kamar ita. Su Abbu kam da albishir din an bashi Aisha din suka dawo mishi.

“Kaddarar su mai girma ce, ni ba zan hana Bilal ita ba, ba zan hana shi Aisha ba. Allah ya san dalilin da ya sake hada su.”

Sune kalaman Baban Aisha, shisa Abbu bai boye mishi komai ba har da kaddarar rabon Nur, da yake mutane ne masu dattako da wadataccen ilimin addini daya fadada fahimtar su, hakan bai zame musu matsala ba. Baban Aisha ya jima yana juyayin kaddara irin ta yaran. Bilal kasa hakuri yayi, motar Ayya ya ara yana zuwa gidan Rayyan dan bayason ya fada mishi a waya, ya fi so ya gan shi ido da ido

“Hamma an bani Aisha, an bani ita.”

Shine kalaman shi na farko bayan ya shiga gidan Rayyan din.

“Shine ba zaka yi sallama ba.”

Dariya kawai yayi yana yin sallamar ya karasa cikin falon ya zauna.

“Zan fara zuwa kasuwa, ina son samun abinda zan rike Aisha da shi, makaranta ta jirani na tsayin lokacin nan, zata kara jira shekara daya idan Allah ya aramun lokacin.”

Kai Rayyan ya jinjina mishi yana murmushi, dadi yake ji ganin farin cikin da yake shimfide akan fuskar Bilal din, muryar shi can kasan makoshi lokacin daya kalli Bilal yace,

“Ba zan baka Nur ba, ba zan baka ita ba Bilal… Yarinyata ce.”

Da bayanannen mamaki Bilal yake kallon Rayyan din, ko na rana daya tunanin yarinyar a matsayin tashi duk da daga jikin shi ta fita bai taba je mishi ba. Ya dauke ta sau daya, ya riketa a jikin shi, yanda yaji kaunarta sai da ya tsorata, bai kuma sake daukarta ba. Duka gani nawa ma yayi mata tun dawowar shi, baisan me yasa Rayyan zaiyi wannan tunanij ba, baya nan shekaru uku da suka wuce, ko yana nan ma bashi da zuciyar kiranta tashi.

“Hamma…”

Ya iya kira kawai, yana ganin Rayyan yaja wani numfashi yana fitarwa a hankali, ya fadane saboda ya tabbatar, saboda a tsorace yake, tsoron shi ya karu da yaji Bilal din yana maganar yanda rayuwar zata karasa nutsar mishi, kamar Nur tasan maganarta sukeyi ta fito, tana ganin Bilal ta tsaya tana kallon shi.

“Kawu”

Ta fadi, murmushi Bilal yayi mata, Rayyan ya mika mata hannun shi ta karaso ta kama, daukar ta yayi ya dora akan kujera a gefen shi, sai da ya sumbaci hannunta sannan ya sake shi, yana lumshe idanuwan shi da taja kafafuwanta ta dora akan kujera tana kwanciya a jikin shi, kafin ya bude su akan Bilal da yake kallon su da murmushi a fuskar shi.

“Kawu…”

Rayyan ya maimaita sunayin dariya gabaki dayan su. Duka sauran Uncle take kiran su da shi, da gangan Rayyan din yake nuna mata hotunan Jabir yana kiran shi da Kawu.

“Kasan Jabir kawai take kira da Kawu”

Ware idanuwa Bilal yayi, Rayyan ya jinjina mishi kai yana dariya. Ranar farko da ta kalli Jabir tace,

“Kawu”

Sai da ya matsa ya fara kalle-kalle yana neman wanda ta kira da Kawu.

“Da kai take.”

Haris yace mishi, cikin tashin hankali Jabir din yake kallon su.

“Nur ya sunana?”

Ya tambaya.

“Kawu”

Ta maimaita tana saka Jabir fadin.

“La hawla wala quwwata ila billah, wai me yasa? Wa taji ya fada? Me yasa take cemun Kawu saboda Allah?”

Dariya suka dinga mishi, har Abbu saida yayi, dan wani lokaci yakan tsokane shi yace,

“Kawu Jabir”

Sai dai yace

“Haba Abbu…idan kuna fada ba zata daina ba wallahi.”

Hira suke a nutse suna dariya, wanda duk zai gan su zaiyi tunanin basu da wata damuwa a fadin duniya gabaki daya, zai tunanin basu taba sanin matsala ba, kuma ba haka bane ba, matsala kan tsaida komai, amman zabin kane kayi farin ciki koya yake da yakinin cewa babu wata damuwa da take dawamammiya, da kuma sanin cewa ikon komai ba a hannun ka yake ba, addu’a ce kawai kake da ita, addu’a fa take da karfin sauya kaddarar da take a rubuce tun kafin samuwar ka, shisa suke dariya duk da sanin ko da sun kwanta yau ba lallai su tashi gobe ba, idan sun tashi babu wani tabbaci na ranar zata zo musu da daidaito, amman suna da junan su, komai zai zo da sauki.

*****

ALHAMDULILLAH!!!

Ina godiya ga tarin mutanen da basa gajiya da nuna mun kaunar su ta hanyar siyan littafina, bina da fatan alkhairi da addu’o’i. Allah ya saka da alkhairi ya biya muku dukkan bukatun. Allah kuma ya yafe kuskuren mu yayi mana Rahma. Amin thumma amin

Ma’assalam

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 33

1 thought on “Martabarmu 34”

  1. Ummulkhair Abdullah

    Ban taba karanta littafi mai storyline Irin wannan ba, I don’t even know how to express how I felt reading this book, it was all sort of emotion. Masha Allah it ended well, jazakillah khairan

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×