Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Marubuci by Umar bin Ally

Babban mafarkina a rayuwa shi ne na zama marubucin fina-finai amma kasancewa ta ba kowa ba kuma ban san kowa ba haka na bar wannan mafarkin nawa ya ci gaba da kasancewa mafarki ban yi yunkurin maida shi gaskiya ba domin kuwa ban ma san ta inda zan fara ba haka na cigaba da zama ina ta dakon tarin labarai a kwakwalwata har wata rana na samu wata babbar dama da zan iya amfani da ita dan ganin na cimma muradina.

Bakomai bane face hira da na gani da wani jarumin masana’antar shirya fina-finai, wanda ake masa tambaya akan me yasa ake samun yawan faduwar fina-finai awannan lokaci sai wannan jarumi ya bada amsa da cewa:

“Matsalar da take damun masana’antar film a yanzu shi ne akwai mutane masu mahimmamci da ba’a damawa dasu. Sanin kowane a harkar film abu na farko da ya fi komai muhimmanci shine labari wanda zamu iya cewa labari shine film.”

“Rashin labari domin kuwa akoda yaushe masana’antar tana kara yawa da jarumai masu daukar nauyi har da ma masu bada umarni amma kuma marubuta suna raguwa. Tabbas muna da hazikan marubuta acikin masana’antar amma kuma yanzu yawancinsu sune masu bada umarni sune screenplay sune rubuta dialogue da dai sauransu. Ka ga kuwa dole a samu karancin labarai domin kuwa babu lokacin ma da zasu tsaya su tsara labaran.”

“Gashi kuma aikin kullum kara yawa yake kullum ana ta kara shigowa harkar sannan mutane za suga kamar kullum kara maimaita labari daya akeyi saboda marubutan shekara ashirin baya sune har yanzu suke rubutun.”

Sannan hanyar da za a bi dan magance hakan shi ne abawa sababbin marubuta dama ba sai wane ko dan wane ba, a karbi labarin koma wanene a ga tasu basirar tunda kowa da irin baiwarsa. Su wadannan gogaggun marubutan namu su ajiye rubutun.”

“Aikinsu ya zama duba rubutun dayin gyare-gyare a cikinsa da rubutun dialogue da dai sauransu duk labarin da suka ga yayi a karbe shi. Ta wannan hanyar zamu samu abinda muke bukata da yardar Allah. Sannan ina mai albishir ga duk wani mai baiwar rubutu kowanene kuwa shi ya kawo mana labarinsa akamfanin da nake akarkashinsa zamu duba mu gani indai labrinsa yayi zamu karbeshi kuma zamu yi aiki dashi.”

Koda gama sauraron wannan bayani sai zuciyata ta cika da farin ciki domin kuwa na samu babbar dama ta maida mafarkina zuwa zahiri. Nan da nan kuwa na kama aikin rubutu ba dare ba rana cikin kankanin lokaci kuma na tara labaru kala-kala, sannan na dauka na kaisu wannan kamfanin na shirya fina-Finai domin tantancewa.

Amma da yake wannan jarumi ba shine zai yi wannan aikin ba na tantancewa sai abun yaz o da sabon salo domin kuwa dai sababbin marubuta ko takan labrinsu ba a bi ana zabar labrin sanannu ne da kuma wanda suka san wani ba maganar wani cancanta a gurin sai an gama zaba sai adauko labarin sabon marubuci guda daya a saka saboda kar a gane abinda ke faruwa.

Aikuwa a irin haka ne aka yi sa’a aka dauko labarina guda daya aka kaddamar dashi har takai ga an yi film dinsa. Na yi matukar farinciki sosai, sannan kuma cikin ikon Allah film din ya samu karbuwa ya yi gagarumar nasara hakan kuwa nima ya jawo min daukaka a gurin Jama’a su kai ta turomin sakonnin fatan alkairi da shawarwari kan na cigaba da rubutu ni kuwa hakan ya karamin karfin guiwa wajen rubuta labarai.

Sai dai tun daga nan ban sake ganin an biyo ta kan labarina ba. Haka na yi ta jira har tsawon wata biyar ko zan ga an sake kirana kan wani labarin amma shiru. Watarana kwatsam ina zaune sai na ga sako ta WhatsApp dina na dauka na duba ina tunanin ko acikin masu sakon fatan alkairi ne, bisa ga mamaki sai na ga wani fitaccen mai bada umarni ne a masana’anatar film na yi mayarda amsa cikin girmamawa bayan mun gaisa ya ce dani yaga film din da aka yi da labarina kuma ya yaba da basira ta dan haka idan ba damuwa zaimin register a kamfaninsu na zama marubucinsu sannan za su dau nauyina nakara karantar harkar rubutu amma sharadinsu su kadai zan ringa yiwa rubutu.

Dukda cewa wannan babbar dama ce agareni wacce kuma ba ni da yakinin samun irinta anan gaba amma sai na yi tunanin labaruna da suke awancan kamfanin wanda sune sanadiyar fara sani da da labari guda daya kawai idan na yi signing da wancan kamfanin su kuma suka fito da labaruna da yake hannunsu ya abun zai kasance.

Aikuwa sai na ce da mai bada umarnin nan gaskiya yanzu akwai magana tsakanina da wani kamfanin amma yayi hakuri yabani lokaci idan bamu daidaita ba zan masa magana. Ya amince amma yace koma dai ya ake ciki na neme shi da wuri dan suna bukatar marubuci. Idan nadau lokaci zasu nemi wani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

3 thoughts on “Marubuci 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×