Skip to content
Part 25 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

Masoyiyata

Ke ce a zuciyata

Na baki rayuwata

Kin fi su dukkan mata

*****

Saboda ƙauna

Har an sa mini suna

Wai ni na zama sauna

Akan ki na zama sauna

*****

Ko da bani da kowa

Ni kin fi mini kowa

Ko babu komai

Ai ni kin fi mini komai

*****

Zuciyata dai kin sace

Akan ki duk na zauce

Na bi na susuce

Gani nan ƙasa kwance

*****

Na bani lalace

Masoyiya ta fece

Ta barni sai yin zance

Ni kaɗai kamar na zauce

*****

A taimaka a ɗan nemota

Idaniya su ganota

Wallahi ko ba mota

Zan ce in biɗota

*****

Ke ce ɗai a cikin rai

Aure tuni na sa rai

Duk da wuya ag garai

Na sani sarai

*****

Amma akan ki bani da haufi

Ko da za ki koma kifi

Ni zan koma kogi

Ki zamo kifi a kogi

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 24Fasaha Haimaniyya 26 >>

1 thought on “Fasaha Haimaniyya 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×