Skip to content

Matar Bahaushe | Babi Na Daya

2.3
(3)

5th October 2015

National Assembly Asokoro, Abuja

A cikin turancinta mai yanayin na sauraniyar Ingila take jera jawabinta. Hanyar da ta dauka daga karamar hukumar Sandamu da ke Jihar Katsina, zuwa karamar hukumar Baure da abunda ya kewaye ta ce ke bukatar titi har izuwa tushenta, mahaifarta, garin Zangon-Daura.

Shekaru kusan ashirin kenan, ko kuma ta ce a iya tsayin shekarun da ta samu a duniyarta, ta san yadda yankinsu ke da bukatar ingantacciyar hanyar da zata taimaka wurin raguwar yawan hatsarin motar da ke yin asarar rayuka, da dukiyoyin mutane. Tun ba ta da wayau take jin labarin yadda yan siyasa ke ansar kudin gyaran hanyar, amma a karshe ba za su kara jin labarin yadda aka yi da kudin ba. Haka suke rayuwa a wahalce, tamkar garuruwan da suka saka kwarmatsatstsen titin a tsakiya ba kananan hukumomi ba ne ba.

Zaman gilashin da ya like a idanunta ta gyara tana ci gaba da kora jawabinta. Domin kuwa bayan inganta ilimin yara mata da ya kasance na farko a kundin ajendarta, gyaran hanyar shine abu na biyu da take mafarkin kaddamarwa ko dan ta sanya murmushi a fuskokin mutanen da suka turo ta wakilcinsu.

Har sai da ta kai karshe, kafun ta ajje kallonta a kan tarin yan majalissun da suka kewaye kujerun na National Assembly. Ta koma kujerarta ta zauna tana ba mai jawabi na gaba damar zayyana nashi korafin da abun da ya tara su a babban dakin taron.

Awanni kusan ukku suka shude suna zaune tare da bayyana manufofin wakilcinsu, haka kiran Capt. Anwaar Sarari ya dinga dagula lissafinta, ya dinga shigo mata a kai a kai, a karshe ya sanya ta kashe wayar gaba daya tana mika dukkan hankalinta a abubuwan da suka sa gaba.

Hon. Bamanga Jafaru ne mai jawabi na karshe da ya sanya ta kara nutsewa a cikin kujerar da take zaune, ta lullube idanunta tana tunanin dalilin kiran da Capt. Sarari ke mata bayan duk bayanan da ta gama jera mishi jiya da yamma. A hankali ta bude idanuwan, tana kallon jama’ar wurin da ke tattara takardunsu suna dosar hanyar fita. Mikewa ta yi itama, tana daukar jakarta kirar Aldo mahadin takalmanta, a lokaci guda doguwar jilbaab dinta mai kalar makuba tana zarcewa domin lullube kyakkyawar surar da ta kan zamo barazana a gare ta da duk namijin da ya sauke kallonshi a kanta.

“Hon. DanGambo.”

Ta ji sautin maganar a setinta. Ba wai bata san mai muryar ba ne, sai dai yadda ya kasa fahimtar babu wani abu da take bukatar ya hada su shine abun da ya hana ta juyawa. Bai yi kasa a gwiwa ba, domin kuwa zira’in tafiyarshi ya kara har sai da ya kai kafada da kafada shi da Ruqayya Manaaf DanGambo. Ya kalle ta, irin kallon da a ko da yaushe bai taba barin idanunshi ba, a hankali ya ce

“Idan ba fada me ya kawo gaba?”

A saman kafafunta ta dakata, kafun ta juyo da fuskarta tana kallon Hon. Bamanga Jafaru da ya kafe ta da nashi idanun. Abun da ta kasa fahimta a lokacin shine yadda tun bayan rantsar da su a matsayin yan majalissu watanni ukku da suka wuce mutumen ke bibiyar lamurranta. Ya kasa gane yadda ba wannan ba ne abun da ya sanya ta neman kujerar House of Reps. Kamar duka sauran mutane, shima ya kasa fahimtar yadda ba ta da lokacin batawa wurin sauraren maganganun sauran yan siyasar da bai shafi aikinta ba. Wasu daga cikinsu sun gane hakan har sun hakura sun daina kula ta, sai dai Bamanga Jafaru ne ba ta san ranar da zai bude kwanyarshi ya zuba manufarta a cikinta ba. Bata san har sai zuwa wane lokaci ba ne zai gane babu wata alaka da zata iya shiga tsakaninta da sauran mazajen duniya da ta dade da yiwa kudin goro a kasan ruhinta. Hakan ya sa a duk wasu harkokinta babu namiji ko guda daya a jerinsu. Direbarta mace ce, haka yan sanda biyun da suke tsare lafiyarta, ma’aikatan gidanta, da hatta mai gadin kofar gidan tsohuwar kurtun soja ce.

Ajiyar zuciya ta sauke, ta kalle shi sosai tana ganin yadda yake fadada murmushin fuskarshi kafun ta ce

“Ban san ta ya zan fara gaba da mutumen da ban taba sani ba, mutumen da fuskarshi kadai na sani sai kuwa sunanshi da nike ji a bakin mutane.”

A hankali murmushin shi ya fara disashewa, ba wai dan bai yi tunanin maganar da zata jefa mishi kenan ba, sai dan yadda ta fito kiri-kiri ta gwada mishi rashin muhimmancinshi a duniyarta.

Ci gaba suka yi da takawa, a hankali yana fadin

“Wannan ba wata matsala ba ce ai, ki ba kanki damar sanina, na tabbata ba za ki taba da na sani ba.”

Siririyar dariya ta sufce a lebenta,

“Bamanga Jafaru, ba haka nike ba. Ba za ka fahimci komai ba, shi yasa ba zan bata lokacina wurin fahimtar da kai ba. Amma ka yi hakuri, duk wata gaisuwa da ta dace mun riga mun yi ta a cikin dakin taro.”

Ta mika jaka da takardun hannunta zuwa ga Grace direbarta, bata jira komai ba ta bude bayan motar ta zauna tana gyara zaman jilbaabinta, ta sanya hannunta ta kulle kofar tamkar babu halittar Bamanga Jafaru a tsaye. Ta gefen idanunta take hangen rashin natsuwarshi da yadda yake yawo da hannunshi na dama a cikin sumar kanshi. Wannan ne kadai abun da za ta iya mishi ko da hakan zai bata ranshi. Wannan ce iya gaskiyar da zata fada mishi domin kuwa ba wai shi ba, ko Capt. Anwar Sarari ba ta taba haskowa a cikin rayuwarta mai zuwa ba. Maza ukku ne kawai suka mata saura a duniya wanda ba za ta iya wurgi da al’amarinsu ba. Hakan ya sanya har lokacin ba ta cire rai da sake ganin fuskar Usman ba. Ta kuma dage da dukkan karfinta dan ganin ta fitar da Farouq daga taskun rayuwar da ya samu kanshi. Sannan ta jajirce wurin inganta tarbiyyar Hammad dan ya san daraja da mutuncin ‘ya mace. Ya san rauni da bukatar kulawa da mata ke dashi. Ya kuma gane babbar illar da wulakanta mace ke haifarwa a duniyar hausawa inda ake ganin MATAR BAHAUSHE ba ta da wani amfani.

Tunanin rayuwa ya sa ba ta san lokacin da suka karaso cikin Maitama Ministers Hill ba, sai jin tsayuwar motar da ta yi a harabar wangamemen gidan da ko a mafarki bata taba tunanin mallakar makamancinshi ba. Bata damu da wahaltar da Grace da son ta bude mata kofa ko ta rufe mata ba, hakan ya sa ta bude ta ziro da zaratan kafafuwanta, suka gaisa da Magret mai gadi cikin mutuntawa, kafun ta doshi hanyar da zata sada ta da babban falon gidan inda ta samu Hammad a tsaye kamar ko da yaushe yana jiranta.

“Sannu da zuwa Ammi. Yau na ga baki dade ba.”

Suna jerawa zuwa sashen Hajiya Maryama suke maganar da hannayenta dore a saman kafadarshi.

“Na gode Hammad. Yau ba ni da wasu aiyuka masu yawa ne. Ina Ummi? Ko bata nan?”

Tsayuwa yayi a saman kafafunshi kafun ya sauke kallonshi a fuskarta. Kallonshi itama take yi tana ganin komai na mahaifinshi lullube da dukkan halittarshi. Tsawonshi, wanda ya kusan zarce kafadarta, budewar halittunshi duk da kananun shekarunshi goma sha biyar, manyan idanunshi da kalar murjajjiyar bakar fatarshi, doguwar fuskarshi, har ma da jajayen labbanshi dukkansu irin na Marzouq Zannah ne. Ta dan cije cikin bakinta tana kauda tunaninta tare da fadin

“Me ya ke faruwa ne Hammad?”

“Uncle Anwaar, Ammi. Yana falon Ummi tun dazu. Na san kuma ba ko da yaushe kike son ganinshi ba.”

Ya fada cike da damuwa, kulawa, da kuma tausayin mahaifiyar tashi a saman fuskarshi.

Idanunta ta lullube tana tunanin mutane irinsu Capt. Anwar. A fuskar Hammad ta bude idanun kafun ta kirkira murmushi tana fadin

“Kar ka damu. Ka je ka jira ni akwai magana da za mu yi da shi.”

Tana kallon yadda ya juya kamar ba abun da zuciyarshi ke so ba kenan, ta zuki numfashi mai nisa kafun ta fesar da shi. Zuciyarta dokawa take yi, amma abun da za ta yi shine salama a gare su har kuwa Capt. Anwar. Cikin tsanaki ta ci gaba da takawa ta murda kofar falon na Ummi tare da sallama kafun ta bayyana kanta.

Idanunshi da suke sauke a saman allon talabijin ya dago ya sauke su a fuskar Ruqayya da take takowa.

Doguwa ce sosai, mai murjajjen jikin da babu rama ko kadan. Yanayin bakar fatarta, ta asalin matan hausawa ce wadda hutu ya taimaka mata wurin kara salki da gogewa. Madaidaitan idanunta dauke suke da zaratan gashin ido wanda idan ta kulle idanun suke kara kawata fuskarta, gassan girarta zirara ne masu kamar an zana su. Gashin da ya kwanta a gaban goshinta, shi kadai ke tabbatarwa mai kallonta da tarin yawan gashin da kanta ya adana. Duka ba wadannan ba ne ababen da suke jan hankalin Capt. Sarari zuwa a gare ta ba. Kyawawan dabi’unta na taimako da tsantsan tausayi, irin tarbiyyar da take wadata Hammad da shi duk da rashin lokacinta wadda irinta ce ya ke kwadaitawa Fatima da Aysha, da kalar kulawar da take bai wa Hajiya Maryama, sune ababen da suka taru suka yi mishi ginin kaunarta mai zurfi wadda bai san ranar da zai daina ba.

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.