Skip to content
Part 18 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Me Yasa?

01.

Da sunan Rabbi Sarki mai kowa, 

Al-Ƙaliƙu Allah Kai ka yi kowa, 

Salati gun manzo na ninkawa, 

Sahabu ba zan bari ba ko yaya. 

02.

Me yasa ne ya jama’a, me yasa ne? 

Me yasa yau muke yin yaudara ne? 

Me yasa wai muke cin amana ne? 

Me yasa ne, ya jama’a me yasa ne? 

03.

Me yasa yau soyayya ba ta gaske? 

Me yasa gaskiya duk muka take? 

Me yasa an bar ƙaunar ga ta gaske? 

Me yasa ne, ya jama’a me yasa ne?

04.

Cin hanci ya gawurta me yasa ne? 

Ga rashawa ana yi me yasa ne? 

Maɗigo har da Luwaɗi me yasa ne? 

‘Yan uwa nai tambaya me yasa ne? 

05.

A sanina maƙwafci ɗan uwa ne, 

A sanina malami fa uba ne, 

A ganina Shuguba jagora ne, 

Amma yau na rasa wai ya akai ne? 

06.

Maƙwafci na kishi da maƙwafci, 

Malami na hassada da malami, 

Shugaba bashi shiri da shugaba, 

Me yasa ne, ya jama’a me yasa ne? 

07.

Matsalarmu mu tuna ta juna ce, 

Aibunmu mu tuna na juna ne, 

Sirrin mu tabbas na juna ne,

Nasarar mu tabbas ta juna ce. 

08.

Muna ina hassada ke kashe mu? 

Muna ina ƙyashi na kashe mu? 

Me yasa wai ba mai kishinmu? 

Sai yaushe, zamu gyara sai yaushe? 

09.

Allahnmu Wahidu ka haɗe mu, 

Ka sa zukata su zamo ɗaya ɗungum, 

Mu kasance tsintsiya dukkanmu, 

Masu sharar dauɗar nan dukkanmu. 

10.

Haiman ne yake kira ku ji yanzu, 

Wasu sun faɗi jiya har ma ɗazu, 

Gashi ayau ina kira har yanzu, 

Haɗa kai dai muke jira har yanzu. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tambaya 17Tambaya 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×