Skip to content

Mijin Mahaifiyata | Babi Na Biyu

4
(8)

<< Previous

Daga ranar da bakin Khadija ya tona sirrin dake cikin zuciyarta, Mahmuda bai ƙara samun murmushi koda na yaƙe ba. Azabtarwar da take yiwa rayuwarsa sai ta fi haka ninkuwa. Girki sai Khadija ta ga dama za ta dora, ta fake da laulayin ciki, Mahmuda bai takura mata ba. Banda tausayinta babu abinda yake ji, watarana haka zai zubamata ido ya yi shiru yana kallon zubar hawaye a fuskarta, yasan dalilin kukanta, sai dai yana da tabbacin zai yi fin nata matuƙar ya saketa ta auri wanda take so. Daga shi har ita ba su taɓa bari iyayensu sun gane komai ba, su kansu iyayen hankalinsu bai kai ga hakan ba. Ramar da Khadija ta yi sai suka danganta shi da ciki.

*****

“Kalli yarinyar nan, fara ƙal da ita ma sha Allah, ke kam dai Mahmuda ya maki wayo don ban ga inda ta bar shi ba.”

Gwaggo Hansai ke wannan zancen sa’ilin da ta karɓi ɗiyar Khadija a hannun Nos Shema’u, yarinyar da ba ta fi awa ɗaya da zuwa duniya ba. Khadija idanunta a runtse sai hawaye kawai ke kwaranya daga idanunta, ta ƙi kallon yarinyar, tana jin ƙarar tsotson hannun ƴar wacce ta ci kuka har ta ƙoshi ta haƙura ta koma tsotsar yatsunta. Kwakwalwarta ta shiga tuna kalaman Mansur a baya.

“Duk radda Allah ya nufa kika haifarmin ɗa namiji, Muhammad zan kirashi, yana daga cikin sunayen da na fi so. Duk kuma ranar da Allah ya ba ki ɗiya mace, in sha Allahu sunanki za ta ci, Khadijatul Kubra.”

Ba ta mance sadda ta yi fari da kwayoyin idanunta ba ta watsomishi tambaya.
“Me yasa za ka sanya sunana?”

Idanunta suka hasko mata sadda ya yi kyakkyawan murmushi gami da ba ta amsa.

“So ne Khadija, so ne sila. Kina mamaki ko? To ki daina.”

Ba ta san ta ƙara ƙarfin kukanta ba sai da ta ji hannun Gwaggo Hansai ƙanwar mahaifiyarta tana jijjiga kafaɗarta.

“Ke Hadizatu, meke damunki ne? Akwai inda ke ciwo?”

Sai a sannan ta fahimci kukan take yi a fili ba na zuci ba. Ta share hawayenta sadda Nos Shema’u ta matso sosai tana maimaita tambayar Gwaggo Hansai cikin muryar rarrashi. Dakyar ta ba su amsar lafiyarta kalau sannan ta kawar da kai. Jinta take ta tsani komai da kowa, ta ƙara tsanar Mahmuda fiye da baya, sai dai ba ta ji tsanar abinda ta haifa ba, amma ta ji har ranta ba za ta taɓa iya nuna kauna a gareta ba. Ba diyar Mansur ba ce, ba kuma jininsa ba ce. Za ta taya shi kishi.

Shekaru Uku Bayan Haka

Bahijja Mahmud Labaran

“Bahijja haske ce a rayuwata, kallonta, dariyarta har ma da murmushinta yana warkar min da zuciya.”

Mahmuda kan yawan faɗar haka a wurare da dama. A yau ma da yake zaune a falon ƙanwarsa Naja’atu da ya kai wa ziyara tare da diyarsa, yana kallon Bahijja dake ta tsalle tsallenta cikin sa’anninta, ya maimaita faɗi.

Naja’atu ta yi murmushi. Ta jima da ɗago Khadija, ta jima da sanin cewa ba ta so da kaunar yayannata, amma ta saduda ta kasa aiwatar da komai dalilin taka mata burki da Yayan ya yi. Ta jima da karantar zurfin da ya yi a soyayyar Khadija.

“Yayana ka ƙara aure, don Allah ka yarda da wannan shawarar tawa.”

Ya dauke kai daga kan Bahijja ya maido ga Naja’atu. Duk da cewa ya ba ta shekaru har hudu cif, amma yana yaba nutsuwa da hankalinta. Kowa a gidansu ya sani, sun shaƙu iyakar shaƙuwa da ita duk cikin ƙannensa kuwa, hatta a yayyunsa babu wanda ya shaƙu da shi sama da ita. Zumuntarsu mai ƙarfi ne, sukan kashe su binne ba tare da wani ko wata ya ji ya gani ba. Sai dai duk da wannan shaƙuwar tasu bai taɓa furta mata irin zaman haƙurin da yake yi da Khadija ba, don kanta ta soma ɗagowa har dai magiya da nacinta ya sanya shi fede mata daga biri har wutsiya. Ya tabbata tausayi ne da kauna ya sa ta furta hakan, sai dai ba ya jin mai yiwuwa ne har abada.

“Ba zan iya ba, da ace zan iya da tun a baya na aiwatar. Wallahi Naja’atu, ban taɓa fuskantar jarrabawa irin wannan ba, ki tayani addu’a, Allah ya bani ikon cinyewa, ya sanya wataran Mamin Bahijja ta bani matsayi fiye da wanda ta ba abin kaunarta.”

Naja’atu tsabar tausayi kawai sai ta fashe da kuka, wannan wane irin so ne? Inama Yayanta zai karɓi shawararta ya ƙara aure, ta sani don kyau Khadija Allah ya tsara halittarta. Son kowa ce, hakazalika tana kyawun ɗabi’a sai dai duk wannan ba sa tasiri a kan mijinta, ba ta yi amfani da iliminta ta danne ta hakura da abinda alƙalami bai hukunta za ta samu ba. Ta kama wanda ta ke da shi hannu bibbiyu, don ba ta ga abinda Yayanta ya rasa ba, asalima mata har gobe su na kwadayin aurensa. Ga kyau ga ilimi, uwa uba ga kasuwanci da ya fara tun bayan kammala sabis dinsa, komai dai sai hamdala. Amma ya ke kwasar kashi a wajen matarsa. Inama zai yi auren kamar yanda ta ke so, ai zama da mai turare ya fi zama da maƙeri, ko bai ba ka turare ka shafa ba, za ka ji ƙamshi. Ko ba komai Bahijja za ta samu so da kauna da kulawa don tsabar rashin kauna da kulawar Khadija a kan diyarta, tun ba ta isa yaye ba ta cireta daga shayarwa.

*****

Ta taso cike da gata daga ɓangare ɗaya, idan kuwa a cikin dangi ne, tana samun gata da kulawar da ta dace da kowane ɗa tun daga ɓangaren kakanninta na wurin uwa har na uban. Soyayya, gata da farin ciki daya ne babu a duniyar Bahijja, shi ne na ɓangaren Mahaifiyarta. Tun Bahijja na yarinya take masifar shakkar uwarta, ko raɓarta ta yi ban da kyara da hantara ba ta tsintar komai. Mahaifinta shi ne jigon rayuwarta, a wurinsa ta ke samun dukkan gata da kulawa, sau miliyan ta fi kaunarsa akan mahaifiyarta. Ta rasa me ta yiwa Maminta ta tsane ta. Ko kashi da fitsari idan Bahijja ta yi, matukar Abbanta ba ya nan sai dai ta wanke abinta da kanta. Duka kam za ta ci a wurin Khadija har sai da wataran ta yi akan idanun Mahmuda, anan ne ransa ya yi mugun baci, ya yi mata gargadi da kakkausar murya akan taɓa lafiyar Bahijja. Har sai da ya kasa hakuri ya dauke Bahijja ya kai gidan Naja’atu, sai da ta yi sati uku cif kafin ya maido ta ba kuma a son ranta ba don ita kam a duniyarta ta gwammace rayuwar gidan Naja’atu, ta na jin ta a sabuwar duniya. Da wannan Bahijja ta riƙi mahaifiyarta, tana ganin irin cin kashin da take yiwa Abbanta, tana ji tana gani za ta dafa abinci ta cinye abinta tas, ta hana Abban, ita ma ganin haka ko ta zuba mata sai ta ƙi ci. Ta sha ganin Abbanta na hawaye.

*****

Mutuwa rigar kowa, wannan hakayake, fadin tashin hankalin da jama’a suka shiga sanadiyyar mutuwar Hajiya Saratu ba zai fassaru ba. Khadija ta girgiza sosai da wannan mutuwa, dalilinsa ne kuma ta dan yi sanyi. Irin sanyin da Mahmuda bai taɓa kawowa ba, a sanadiyyar mutuwar Umma ne ya ƙara samun damar ganin Khadija wanda rabonsa da hakan har ya mance. Kwatsam kuma sai Allah Ya nufeta da ƙara samun juna biyu.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “Mijin Mahaifiyata | Babi Na Biyu”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×