Skip to content

Mijin Mahaifiyata | Babi Na Daya

2.5
(32)

Gidan Alhaji Laminu Mai Goro, sanannan gida ne a unguwar ƙofar Na’isa ba don komai ba sai don dattako da halayyar kirki da aka shaidi Maigidan da kuma iyalinsa da shi. Mutum kan zaman mutum a idon jama’ar wancan zamanin, ba don yana da kudi ba, sai idan ya kasance nagari mai kuma kokarin sauke hakkin makwaftansa da ya rataya a wuyansa hakazalika da kokarin taimakawa talakawan da ke nema a wurinsa daidai gwargwado. Gashinan dai ba wani mai kudi ba ne na kwatance a faɗin garin Kano ba, amma kyawawan ɗabi’unsa da faran-faran da jama’a ya jawomasa daukaka. Sana’arsa siye da siyar da goro, sai Allah Ya sanya ta zame masa sanadiyyar daukakarsa. Sanadin goro, ya je Umarah kuma ya je Hajji tare da  matarsa daya, wato Hajiya Saratu, uwar gida kuma amarya a wurinsa. Zamansu suke yi lafiya kalau duk kuwa da cewa auren zumunci ne, ita din diya ce ga kanwar mahaifinsa, hakan bai sa zumunci ya lalace ba don kuwa zamansu akwai kauna, shakuwa da kuma fahimtar juna sosai. Hakurinta da kuma tsananin biyayyarta gareshi, ya siyamata wuri mai girma a zuciyarsa. Ta haifa masa yara goma cif a duniya.

Ɗansu na farko, Lawwali, wanda ya ci sunan kakansa, Marigayi Malam Lawwali, yana da mata da yara biyu, sai Hauwa’u wacce itama aka yi mata auren zumunci. Sadiya, Aisha, Fatima, Jamila, wadanda duk suke bin Hauwa’u, su ma babu wanda Alh Laminu bai aurar ba. Sunusi, Khadija da auta Sa’ad. Su ne kadai suka yi saura a gaban Alh Laminu da Hajiya Saratu wacce su ke kira da Umma.

Sunusi yana karatunsa a lokacin yana aji daya a jami’a inda yake karantar kasuwanci, ita kuwa Khadija  tana ajin karshe a sakandire wanda daga nan tana da tabbacin babu yanda za’a yi mahaifinta ya bari ta shiga jami’a don wannan dokar gidansu ce, mata iyakacin karatunsu Sakandire, idan kina sakandiren ma miji ya fito, za’a cireki ne a aurar. Kamar yanda aka yiwa yayyinta, Fatima da Jamila su kadai suka yi nasarar kammala sakandiren kafin aure, sai kuwa ita a yanzu. Kaninta Sa’ad yana firamare ajin karshe a sannan.

Karatu yana daya daga cikin burin Khadija sai kuwa burinta na karshe wanda duk duniya babu wanda ya san da zamansa idan ka cire yayarta Fatima. Ita kadai ta san da zaman MANSUR a duniyar Khadija, gidanta nan ne mahaɗarsu, nan zasu zauna a zauren gidanta su yi hirarsu irin ta masoya su tashi. Soyayyarsu ta fara ne tun tana aji daya a babban sakandire, sanadin wata kawarta Zainab da ta taɓa kaiwa ziyara, ta hadu da Mansur.

Mansur Ibrahim, ɗa ga shahararren ɗan kasuwa Alh Ibrahim Maifata da Haj Kareemah Hayatu, wanda iyayen ke ji da shi, kasancewarsa ɗa namiji tilo a cikin mata. Yayarsa Zulai, tana auren wani Alkali suna zamansu lafiya, ma’aikaciyar banki ba ce. Sai mai bin ta Saudah, ita kuwa tana auren wani babban Likita, ita dinma karatun likitan ta yi har kuma ta kammala tana aiki a karkashin asibitin mijinta. Sai Maimuna, ita kuwa yanzun take shirin haɗa Master Degree dinta a fannin ilimin Kasuwanci. Shi ne ɗa na huɗu a wurin iyayensa sai kanwarsa kuma autarsu Rukayya wacce sa’ar Khadija ce, ko a fannin karatu tare suke tafiya sai da kowanne da makarantarsa.Mansur matashin saurayi a zamaninsa, ga kudi ga kuma kyau daidai misali, baƙi ne amma hutu da jin dadi ya sanya fatarsa murjewa. Tsananin so da kaunar da iyayensa har ma da yan uwansa ke mishi, bai hana sun sangarta shi ya lalace ba. Bayan kammala Sakandire, mahaifinsa sam bai yi sha’awar tura shi waje karatu ba don a lokacin makarantunmu na Nijeriya ba su lalace kamar yanzu ba, ana karatu sosai  hakanan yara na iyakar kokarinsu wurin mayar da hankali ga abinda ya kai su.

Ya na matakin karshe na Degree dinsa na farko a fannin Kasuwanci, shi da yar uwarsa Maimuna abinda suka fi so da buri kenan. Har ta kai Mahaifinsu kan yi shawara da su idan wani abin na harkokinsa ya sha mishi kai.

Haɗuwar Mansur da Khadija, kaddara ce ta Ubangiji. Unguwar Yakasai, nan ne unguwar su Mansur, zuwan Khadija ziyara wurin Zainab shi ya kawo haduwarsu. Bayan sun fito daga gidansu Zainab, sun biyo za su wuce ta gaban gidan su Mansur ya kyalla ido a kanta. Kamar wasa ya tunkareta, kunya da kuma rashin sabo ga wani tsoro da ya shige ta lokaci guda na kar wani dan gidansu ya yi katarin zuwa nan ya ganta da shi, wannan ya hana Khadija nutsuwa. Ta ƙi ba shi kowace dama har ta wuce, bai yi yunkuri bin bayanta ba, ya riga ya san Zainab, don kanwar abokinsa ce,  sai bayan dawowar Zainab daga rakiya, ya roki alfarmar kwatancen gidansu, nan ta nunamasa Khadija ba ta fita zance. Dakyar dai ya amince da iyakar kwatancen makarantarsu da zummar idan sun je an tashi zai zo, ita kuma ta kiramasa ita.

Khadija a ɓangarenta kuwa, ranar kasa runtsawa ta yi, da zarar ta rufe ido, hoton fuskar Mansur  kawai ta ke gani, kallo ɗaya ta yi mishi, cikar haibarsa da tsawonsa ya tafi da ita. Da zarar ta tunashi sai gabanta ya fadi. Haka ta kwana ta tashi sukuku da ita, ganin lamarin take kamar a mafarki, wai ita ce yau ke tunanin wani ɗa namiji.

Ko a makaranta ba ta ba Zainab fuskar kawo zancensa ba, itama Zainab ba ta matsa mata ba kuma ba ta faɗamata batun zuwansa ba. Sai dai ana tashi kawai ta ja hannunta suka zagaya bayan makarantar da zummar za ta yi mata rakiya wurin wata ƴar ajinsu. Wanda ta gani ya sa ta daskarewa a wurin, sai dai ko kusa ba ta yi yunkurin gudu ba, kewarsa daga ranar da suka haɗu, yau kwana uku kenan, ta yi har ta gaji. Ta ji inama ta tsaya ta saurareshi, ko ba komai ajin karshe za ta shiga, idan har dagaske zai aureta to ita fa ba ta da miji sai shi. Za ta saurareshi, za kuma ta sanarmasa dokar gidansu, idan har yana sonta, tana da tabbacin zai yi jiranta har ta kammala aji ɗayan da ya yi mata saura ba tare da kowace matsala ba su yi aure.

Ta sunkuyar da kai ganin ya nufo ta, duk zantukan da ya dinga yi ba ta ce masa komai ba bayan gaishe shi da ta yi. Murmushi kawai ta ke yi, wannan kadai ya tabbatarwa Mansur cewa ya samu karɓuwa a zuciyar Khadija. Dakyar ta iya buɗe baki ta yi mishi kwatancen gidan Yayarta Fatima, ita kadai ta ke da yaƙinin za ta goyamasu baya. A gurguje ta fadamasa dalilin rashin ba sa kwatancen gidansu, ya kuma gamsu. Nan suka tsaida ranar da zasu hadu a gidan Fatima.

“Karatu nake yi nima Khadija, yanzu haka ina shirye-shiryen haɗa Degree dina na farko kafin daga bisani na wuce Masters. Ina da yaƙinin lamarinmu zai tafi a daidai. Kinga kema kin kammala karatunnaki sannan, bayan mun yi aure na cikamaki burinki na ci gaba da karatu.”

Wannan magana ta fi komai a wurin Khadija, shiyasa karatu da kuma auren Mansur kadai su ne mafarkinta koyaushe. Fatima sosai ta yaba da hankalin Mansur, hakanan mijinta shima. Tare da shi ake ɓoyon sirrin Khadija da Mansur har zuwa sadda komai zai bayyana. Mijin Fatima yana son karatu sai dai shi din ba mai hali ba ne sosai, amma ko gobe yana da burin idan ya samu, ta ci gaba da karatunta.

Kafin su ci wata daya, babu wani a yan uwan Mansur ba su san da zaman Khadija ba, ba su taɓa ganinta ba sai dai sun santa a hotunan da ta dauka ta ba Mansur. Hatta da iyayensa sun sa da zaman Khadija. Mahaifinsa sosai ya so ya  tunkari mahaifinta a lokacin da zancensu don ya san shi sosai a bakin jama’a, ba kasuwarsu daya ba, hakanan unguwa kowanne da nashi, amma yana da labarinsa sakamakon abokinsa yana Kofar Na’isa, yana yawan ba shi labarin irin alherinsa duk kuwa da cewar a ƙarfi na aljihu dukkansu sun fi shi, wannan bajintar da yake yi na aikin alheri ya sa ya shiga ransa ba kadan ba. Sai kuma ga shi kwatsam Mansur ya zo da batun soyayyar da yake yiwa ƴar wajen wannan bawan Allahn. Ya taɓa ganinsa sau daya wurin wani daurin aure, sun yi gaisuwar mutunci. Ba ya jin akwai matsala a auren ƴar da ta fito daga wannan tsatson.  Bayanin Mansur ya sanya shi janye kudurin tunkararsa, ya kuma kara sanyawa lamarin albarka da fatan Allah Ya nunamusu lokacin.

*****

“Hadizatu ba ta dace da kowane ɗa namiji ba sai Mahmuda. Yaron kirki, , babu yaro mai hakuri da kuma kau da kai irinsa. Ina faɗa ba don ɗa yake ga Aminina ba.”

Murmushi Umma ta yi jin bayanin mijinta, ita kuwa ta san Mahmuda, yaro mai nutsuwa ga hankali da kunya. Kunyarsa ke hanashi zuwa gidan a kai- a kai saboda tun yana yaro take kiransa da surukinta. Tana kaunarsa kamar yanda ƴaƴanta ma suka san shi suka kuma saba da shi idan ka cire Khadija da Sa’ad wadanda ba wani sani na sosai suka yi mishi ba adalilin karatun da ya tafi a jami’ar A.B.U Zaria. Ya kammala kuma cikin nasara ya haɗa takardunsa ya dawo gida.

Sadda ya ke karatun yakan leƙo amma ba sosai ba. Sama-sama suka san shi amma babu zancen shaƙuwa da shi, Khadija takan ji Umman na kiransa da surukinta, sai dai ko a ka ba ta taɓa kawo komai ba a ranta.

“Kin yi shiru Amaryata.”

Ta bishi da hararar wasa suka dara. Ta jinjina kai tana murmushi.

“Farin ciki nake sunan da na laƙabawa Mahmuda zai tabbata. Surukin nawa ne dagaske ashe, wannan abin farin ciki ne ai Abban yara, ba daga gareni kadai ba, har ita kanta Hajiya Maryama. Allah Ya tabbatarmana da alherinSa.”

Abban yara wanda tun soma zancenta ya ke zubamata murmushi ya amsa da amin.

“Ina da yaƙinin bani da matsala da Hadizatu, na kula ko sauraron samari ba ta yi.”

Umma ta yi ƴar dariya.

“Khadija ba ruwanta kam. Bana jin a tarbiyyar da ka yiwa yaranka, za ka kawo wata buƙata su ƙi yi maka.”

Ya jinjina kai yana mai farin cikin hakan.

*****
Rayuwa tana tafiya, soyayya da shaƙuwa na ƙara wanzuwa a zuƙatan masoyan biyu, basu da wata damuwa, farin cikinsu yana ninkuwa sosai ganin suna dab da cika burikansu. Khadija sai shirin zana jarrabawa ake yi yayinda Mansur kai ya dauki zafi ana ta shirin soma jarrabawar karshe a jami’ar Bayero.

A lokacin kuma Fatima ta ƙara haihuwa, ɗanta namiji. Yaranta biyu yanzu. Gidan Fatima sai ya kasance wurin zuwan jama’a ƴan barka hakan ya kara dakile haduwarsu. Sai da aka yi suna kafin su samu su hadu. Ta lura tun zuwanta gidan, Fatima jikinta yake a sanyaye. Ta yi tambayar duniya  amsar daya ce, babu komai.

Khadija itama sai ta tsinci yanayinta da sauyawa, sai dai zuwan Mansur ya mantar da ita komai, ya lallaɓata da nunamata zai iya yiwuwa sauyin yanayi ne.

Bayan komawarta gida, ta kula da yanayin fara’ar Ummansu, na ranar ya fi na kowace rana. Itama sai ta tsinci kanta cike da farin cikin, har ta manta da yanayin da ta baro yar uwarta.

“Ki shirya, gobe muna da manyan baƙi. Hajiya Maryama zasu zo da iyalinta.”

Ta san irin aminci da shaƙuwar da ke tsakanin iyayennasu mata, zumuncin ya fara sanadin mazan, amma tsananin zumuncin ya fi karfi a gurin matan kai kace dama su ne suka haɗa mazajennasu. Ba wai a dalilinsu ne suka san juna ba. Duk da cewa Hajiya Maryama ita ce mata ta biyu, sun fi shaƙuwa fiye da uwargidan Hajiya Zahra’u. Ita sam ba ta da sabo, ga rashin yarda. Ita din Babarbariya ce, daga can nijar ya auro ta, tun arzikinsa bai kai haka ba. Yana sana’ar kiwo da kuma siyar da dabbobi, suke tare. Anan ne ma ya samu lakabin Mai Shanu.

Ta yi dariya sosai, ganin yanda Umman ke murna kamar ba kwanakin da suka wuce ba ne aminan suka hadu a gidan Fatima ba.

“Allah Ya nunamana.”

Shi ne kawai abinda Khadija ta ce.

Washegari kuwa ta ga irin hidimar girkin da aka tashi da shi, Abban yara har da siyo kaji da kayan haɗin lemo. Daga jin yanda Umma ke faman nanata kalmar surukinta, Khadija ta sha jinin jikinta. Ta sani eh, sunan Mahmuda kenan a wurin Umma, amma yau sai ta tsinci jikinta da yin wani irin la’asar. Ko kusa ba ta son jin Umma na kiran sunan, duk ta bi ta tsani sunan. Amma ina! Ummanta yau dai ko sunan Aminiyarta ba ta ambato kamar na Surukinta.

Bayan kammala girkin, Umma ta sanya Khadija gyara jikinta da sanya hijabi, nan fa kan Khadija ya kara daurewa. Sai dai babu musu ta bi umarninta. Sai wurin sha biyun rana suka zo har Alh Labaran. Falon Abban Yara na suka sauka. Aka shiga gaisawa, Khadija ta shigo dauke da sallama a bakinta, ruwa ta kawomusu ta ajiye. Kafin ta gaishesu, suka amsa da fara’a.

Yaran Alh Labaran da Maryama su shida ne cif. AbdulHamidu shi ne na farko, babu shi a taron, ya yi aure yana zaune da iyalinsa a Kaduna inda yake aiki. Sai mabiyinsa Ridwan, shima yana zaune ne a unguwar Dakata tare da iyalinsa. Na ukunsu Mahmuda, sai Naja’atu, Safiyya da karaminsu wanda ke firamare aji hudu, Muniru.

“Kin gaida kowa amma  ban ji kin gaishe da yayannaki ba.”

Fadin Abban yara kenan, Khadija ta dubi Mahmuda lokacin da duka ake mata dariya shima murmushi lallausa ya yi mata har gefen kumatunsa na loɓawa sai kuma ya sunkuyar da kansa hakan ya tona asirin kwantacciyar sumarsa baƙi suɗik. Kyakkyawan bafulatani, wanda ya dauko tsawo da rashin girman jiki  irin na Bafulatanin mahaifinsa Alh Labaran.

“Ina wuni.”  Ta gaishe shi bayan ta sunkuyar da nata kan itama. Kirjinta na dukan tara-tara, ta kara tsorata da  abinda zai  fito daga bakin iyayennasu. Shi kuwa ya amsa cikin nutsuwa.

Sai da aka yi hira aka ci abinci kafin dakin ya yi shiru, daga iyayenta sai na Mahmuda sai kuwa Mahmudan da ita da aka dakatar da su aka kori sauran waje.

Hankalinta ya tashi da jin abinda ya fito daga bakin Mahaifinta, inda ya yi musu zancen auren da zasu haɗa su da zarar ta kammala jarrabawarta.

Innalillahi…har zuwa ƙarahenta, shi kadai Khadija ke karantowa ga wani uban gumi da ta hada. Kirjinta banda zafi ba abinda yake yi. Mansur fa? Me za ta ce masa? Ina za ta fara ajiye sonta? Ko wannan shi ne dalilin sauyawar Fatima? Tana da labarin wannan hadin?

Ita dai eh ko aa bai fito daga bakinta ba, sai ji ta yi iyaye su na hamdala gami da sanyamusu albarka. Ta mike a da sauri ta fita daga dakin. Amma munafukan kunnenta da suka bijirewa gangar jiki da zuciyarta wurin yin biyayya, sai da suka jiyomata dariyar iyayen har muryar Abban Yara na fadin “Amincewar mace kenan daman ai.”

Kamar ta juya ta koma ta ce Abba ba haka bane, tunaninka ya sha bamban da ra’ayina, sai dai ba za ta iyaba. Har abada ba za ta iya ba.

Wannan rashin iyawar shi ya cutar da rayuwarta, ya cutar da rayuwar Mahmuda, ya kuma cutar da rayuwar abinda suka haifa!

*****
Mansur kuka wiwi da roƙon Khadija, Fatima har mijin Fatima akan kar a yi masa haka, su shigemasa gaba. Khadijar ma kanta yana bisa cinyar Fatima. Basu kara tabbatar da soyayyar ta kai girman haka ba sai a ranar.

Mijin Fatima, Zahraddeen ya ba da shawarar Mansur ya tunkari Abban yara.

“Khadija ta sani, kamar yanda na sani, Abban yara ba zai saurare su ba. Banda faɗa da ɓacin ran da zai nuna akan ɓoyon da suka yi mishi, abin har ni da kai zai shafa.”

Fatima ta tari numfashin Zahraddeen.  Wannan magana sam ba ta yiwa masoyan dadi ba sai ma ƙara shiga damuwa. Rarrashin duniya, amma sun ƙi saurarensu, Zahraddeen ya ja hannun matarsa suka bar su a falon su biyu.

“Kin amince da wannan haɗin? Za ki bi saɓin Abbanki ki auri mutumin da bakya so?”

Khadija ta dubi Mansur tana ji kamar ƙirjinta zai tsage zuciyarta ta fito. Hawaye na zirarowa yana shiga har baka. Ta haɗiyi miyau mai ɗaci sai kuma ta ƙara sautin kukanta har sa rakiyar majina.

“Ka yafemin, ba zan iya saɓawa Abbana ba, ka yafemin don Allah.”

Mansur ya jinjina kai bai ce uffan ba, jijiyoyin kansa duk sun fito, idanunsa kamar an watsa barkono. Ya shafi tarin sumar kansa don a lokacin yana ɗaya daga cikin gayun matasa.

“Ina yi maki fatan alheri. Allah Ya ba ku zaman lafiya.”

Yana kai wa nan ya mike da sauri ya fice daga falon. Khadija ta ƙara ƙarfin kukanta, sai da ta yi mai isarta kafin ta share fuskarta.

Wannan shi ne sallamar ƙarshe tsakanin Mansur da Khadija, sallamar da ba su ƙara sanya junansu a ido ba har auren Khadija da Mahmuda ya tabbata.

*****

Alƙawari ɗaya ta ɗaukarwa kanta, alƙawarin da ta ke ganin har numfashinta ya yanke, muddin tana ƙarƙashin inuwar auren Mahmuda, ba za ta fasa cika shi ba. Wato, Mahmuda ba zai ga haƙoranta ba. Ta ji ta yarda za ta bi shi, sai dai hanya daya da ta zaɓi gallaza masa, shi ne rashin sakarmasa fuska har abada.

Haka suke zaune a gidan Mahmuda dake kusa da gidan iyayensa har ma da gidan gandunsu na kakanni.

Tun Mahmuda na ganin kamar watarana Khadija za ta sauko ta hakura ta kaunace shi, har ya fidda rai. 

“Waye shi? Wa kike so?”

Watarana ya tambaye ta bayan ya risƙeta zaune tana kuka, kuka mai taɓa zuciya sakamakon sun je asibiti dalilin ciwukan da take yi, likita ya auna ya ba su tabbacin tana dauke da juna biyu. Ta dago ta dubi Mahmuda, idanunsa sun kaɗa jazir, kallon da ya ƙara tabbatarmasa da zarginsa, ya jima yana ji a jikinsa Khadija akwai wanda take so, ya sha jin ta tana bacci tana mafarki har da na kuka tana wasu kalamai mai nuni da cewar akwai wanda take so.

A ɓangaren Khadija kuwa, kukanta ya tsaya cak, ta kauda fuskarta daga kallonsa, wannan tsanar da ɓacin ran da take ji a kansa ya ƙaru. Ta riga ta kai ƙarshe, labarin shigar cikinta, ya fi  kowane labari muni da kunnuwanta su ka ji. Ba ta taɓa zaton sakacin da ta yi na amsa gayyatar Mahmuda sau biyu kacal a cikin watanni uku da aurensu zai ba da wannan sakamakon da gaggawa ba. Sam ba ta kawo haka ba.

“Ina ruwanka da abinda ke zuciyata? Ba damuwarka ba ce! Har abada ba za ka taɓa kai darajarsa a idanuna ba. Na tsaneka, na yi maka tsanar da ban san adadinsa ba.”

Mahmuda ya runtse idanunsa yana jin saukar kalamanta a kunuwansa da  kirjinsa kamar ruwan zafi. Ya haɗiyi miyau, a hankali kuma ya bude idon ya sauke a cikin nata, ƙyar take kallonsa, kallon wanda ya ga maƙiyinsa. A hankali ya mike daga zaman da ya yi a gefenta a saman gado, ficewa ya yi ya bar mata dakin gaba daya. Gujewa yanke hukunci cikin fushi.

Ran Khadija ya ɗan yi sanyi, ko babu komai ta furzar da abinda ya jima yana cinta a rai, ta tabbatar ba lallai ya juri zama da ita ba kuma, watakila ma a yammacin da suke ciki, ya kawomata takardar sakinta.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

13 thoughts on “Mijin Mahaifiyata | Babi Na Daya”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×