Skip to content

Mijin Mahaifiyata | Babi Na Uku

2.9
(7)

<< Previous

Murɗar da ya yiwa hannunta sai da ta fita a hayyacinta na ƴan daƙiƙa, wannan fuskar tasa mai cikar kamala ta komawa Khadija tamkar na wani ingarman zakin da ya hango nama. Ta runtse idanun hawayen na ci gaba da kwaranya, kirjinta ya ci gaba da bugu da sauri-sauri, ya kara kusanto ta yana ƙara murje ƙwayoyin magungunan da ita kanta Khadijar idan za’a tsire ta ba ta san illar hada su wuri guda a sha ba bisa cewar likita ba. Ya sani, burinta kawai shi ta fi kaunar cikarsa.

“Na juri abubuwa da yawa tun farkon fari, na kuma zauna da ke da halinki, amma ki sani, duk radda kika ƙara ƙoƙarin maimaita wannan kuskuren, ni Mahmuda zan ba ki mamaki. Ki haifa ki ajiyemin ni ina son abina, zan kuma raine su!”

Daga nan ya saki hannunta ya fice abinsa yana mai jin wani ɗaci a kan harshe da maƙogwaronsa tamkar wanda ya haɗiyi ganye shuwaka.

Tun daga ranar ya kashe tsiwarta, ba ta kuma kara yunƙurin zubar da cikin ba sai dai hatta ƴan uwanta da nashi sun fahimci akwai matsaloli a zamantakewarsu domin Khadija ta bar ɓoye ƙiyayyar Mahmuda a gaban kowa hakazalika wani sauyin da ta dauko shi ne cin zarafin yan uwansa idan sun zo gidan don kawai ta musguna mishi. Labari yana kai wa kunnen mahaifin Mahmuda ya tara dukkan yan uwan Mahmudan ya taka musu burki daga zuwa gidan, ya kuma ce duk su yi mata uzurin juna biyu tunda yakan sa yanayin mace ya sauya. Su dai sun ji kuma sun bi ba su kara kallon gidan Mahmudan ba. Wannan ya kara haifar wa da Mahmuda cuta a zuciya, a hankali ciwon da yake ɓoyo ya soma neman fin karfinsa. Sai dai bai bari wani ya gane ba, ramarsa ta tashi hankalin iyayensa, ya nunamusu ba komai.

*****

“Nayi mamaki da kalaman nan suka fito daga bakinki, kodayake ba abin mamaki bane, daman na jima ina zargin har yanzu kina son Mansur kuma hankalinki ba ya kan mijinki. Tirr da wannan so mai janyo makanta. Kin makance Khadija kin kuma kurumce da har kika kasa fahimtar waye masoyinki na gaske tsakanin su biyu. Amma ba komai, ki je duk abinda kike yiwa Abban Bahijja watarana za ki yi kuka da nadama, ranar da ba zai amfaneki da komai ba.”

Fatima ce, ta yi maganar cikin bacin rai. Ta kuma ji bakin cikin sabbin halayen da Khadija ta ɓullo da su, koda dai dama ta jima tana zarginta amma ba ta da hujja. Da kuka a idanunta ta bar gidan ta kuma ci alwashin ba za ta ƙara tako ƙafarta gidan ba, kunyar Mahmuda sosai ta ke ji, wato ya jima yana shaƙar baƙin cikin yar uwarsu amma bai taba gwada musu ba.

Bayan Shekaru Biyar

Kareema Mahmuda Labaran, yarinya mai shekaru biyar a duniya, ta tashi cikin gata da soyayya musamman na UWA. Khadija na son Kareema, wacce ta ke kiranta Ummi. Ba don komai ba sai don darajar sunan a wurinta, sunan mahaifiyar Mansur ne. Ta kuma yarda suna linzami, hakanan kawai Mahmuda ya sanya sunan, ba tare da sanin ainahin me sunan ba a duniyar Khadija. Fatima da ta san komai, ranta ya kara baci, ta tabbatar nan gaba wannan wariyar launin fatan da Khadija ke yi tsakanin Bahijja da Kareema zai zame mata babbar matsalar da za ta yi kuka da hawayenta. A lokacin ne kuma za ta bambance tsakanin aya da tsakuwa, za ta gane shayi ruwa ne.

Bahijja yarinya mai shekaru takwas, ita ta biyo mahaifinta tamkar anntsaga kara an karya yayinda Kareema komai nata na uwarta ne. Tana son kanwarta sai dai kuma ganin fifikon da mahaifiyarta ke nunawa karara ya haddasa mata tsanarta a zuciya. Ga wani raini da Kareema ke da shi tun tana karama da kuma wani irin sangarta da da Khadija ta yi mata. Babu abinda yarinyar ke nema ta rasa, Mahmuda dai shiru bai cewa uffan, yarinyar ma ba ta damu da shi ba yanda ta damu da uwar.

Kwatsam a wannan yanayin rayuwar, Allah ya dauki ran mahaifin Khadija. Tsakaninsu da marigayi Alh Labaran mahaifin Mahmuda shekara daya kacal. Bayan sadakar bakwai Khadija ta tada wa Mahmuda bori akan sai ya saketa.

“Ka dauka ina zaune da kai ne har yanzu don ina sonka? Idan ma akwai wannan tunanin a zuciyarka ka cire shi, ina zaman aure da kai domin iyayena, yau kuma babu ko ɗaya a cikinsu, don haka Mahmuda a yau sai ka sakeni, na rantse maka da Allah ba na sonka, na kara faɗi don ka ji kuma ka kara tabbatarwa. Idan har ka cika ɗa na halak haihuwar Labara…”

Marin da ya ɗauke ta da shi ne ya yi silar daukewar numfashinta na ƴan daƙika, ya kuma yi daidai da karasowar Innarsa cikin gidan, ta shigo domin ƙara tausar Khadija da ba ta maki akan rasuwar mahaifinta musamman ganin irin yanayin da ta shiga har da suma.

Zafin marin ya ratsa ta amma ko a jikinta sai ma kara damƙe kwalar rigarsa da ta yi. Ta fiddo idanunta sosai wadanda suka rine.

“Oho dai Mahmuda, ko me zaa yi sai ka sake ni! Ko ana dole? Sai ka ce maye?!!!”

“Aa ba maye ba ne, ban kuma haifi maye ba, kiyi hakuri a yau kuma a yanzu Mahmuda zai sauwake maki idan har na isa da shi.”

Suka juya gaba daya suka kalli kofar shigowa falon, Inna ce. Hawaye ke gangaro mata, ba ta fiye shiga shirgin yaranta ba amma yau ta ji ba za ta iya juriya ba. Ta karaso ciki, Bahijja da ke laɓe a bayan labule ta karaso a guje ta rungumeta tana kuka da ajiyar zuciya.

“Inna ki koreta, bana sonta. Ba ta son Abbana, tana saka shi kuka.”

Maganar yarinyar ya bugi zuciyar Inna, Mahmuda ya sunkuyar da kai yana dafe da saitin zuciyarsa da ta motsa. Ita kuma Khadija ta sakar masa wuya ta matsa baya amma fa ba ta jin za ya hakura ta ci gaba da zaman hakuri.

A nan dai take, saki ya shiga tsakanin Mahmuda da Khadija, kuma a daren ta tafi ta bar sa, dama Kareema tana gidansu wurin Fatima, ta kuma ci alwashin rike ta, har abada ba za ta bar wa Mahmuda ita ba.

Wannan shi ne mafarin komai. Yanzu aka fara labarin.

*****

Ruwa, walƙiya mai tsananin haske, tsawa dake biyo bayan walƙiya har ma da iskar da ake yi har tana motsa kalandar musulunci dake kafe a dakin mai dauke da katifa sai sif mai murfi biyu na kaya, gefe kuwa karamar dirowa ce a samanta an jera litattafai sun yi gwanin sha’awa. Sai kuwa madubi ƙarami na katako da ke jikin bango a manne shima yana barazanar faɗowa sakamakon iskar da ke rinjayarsa, duka waɗannan ba su zamo dalilan da matashiyar budurwar matsawa daga jikin tagar ɗakin ba balle ta yi tunanin rufewa gudun yin asarar da zai ƙara mata wani baƙin cikin. Kamar yanda feshin ruwan ke jiƙa doguwar rigar baccinta marar nauyi, haka idanunta ke zubar hawaye. A kowane bugu na zuciyarta, kamar yanda jini ke fita yana zaga ilahirin jikinta, haka tunanin baya kan dawo ya yi mata lahani ya kassarata har takan kasa saita kanta idan irin hakan ta faru, sassaucinta ɗaya ne, shi ne ta yi kuka son ranta. Yanayi na damina, abin so da ƙauna ne ga mafi yawancin al’umma, sai dai a gareta, lokaci na ruwa kan motsa mata damuwar da ta shafe shekaru masu yawa cikinsa.

Shigowar dattijuwa Hajja cikin ɗakin, da tsayuwarta a gefenta, bai sa ta ankara ba, wanda ya yi nisa ba ya jin kira. Hajja ta karasa ta rufe tagar ɗakin, ƙarar rufewar ne ya maido ta hayyacinta, ta dube ta da sauri kafin ta juyamata baya tana share fuska ba tare da ta ce uffan ba. Hajjar ma ba ta ce ba illa ta jawo zanin wanka saman sif ta miƙa mata, ta riga da ta fahimci yaren, don haka ta sa hannu ta karɓa ta ɗaura, da taimakon tocila dake hannun Hajja ta fiddo wata rigar doguwa da ta fi waccan kauri ta sanya. Hajja tuni ta jingine katifa don ruwa ya taɓa ta, ta dauki bargo ta shimfida mata. Kallon Hajjar kawai ta ke yi, dattijuwa mai ran ƙarfe. Ga ta da shekaru sai dai Allah Ya mata baiwar jiki mai kyau tamkar tarwaɗa, kai ka rantse iyayensu har shida cif ba daga jikinta suka fito ba. Koda dai, yanayin jikin nata irin na fulani.

“Ba zan ce da ke komai yanzu ba, sai dai ina shawartarki da yawaita addu’a da kirari ga Allah a irin wannan yanayin, babu abinda mamaci ya fi buƙata sama da addu’a. Hawayenmu sai dai mu zubar domin kewa da kuma son zuciyarmu, ba zai amfani na kabari da komai ba. Ki dinga kokari addu’arki ya fi hawayenki yawa. Yarda da kaddara da kuma imani da ita, ciko ne na addini. Ki kwanta sai da safe.”

Daga haka Hajja ta miƙe da niyyar fita, caraf ta sa hannu ta riƙe na Hajja gam! Suka dubi juna, kauna da soyayyar jikarta ta ya kara mamayarta, babban dalilinta na son barin ɗakin bai wuce kar ya kasance an yi ba’a yi ba, itama hawayen ke son zubomata.

“Ki yimin alfarma Hajja, ki kwana tare da ni. Mai ɗebemin kewar ba ta nan.”

Tana nufin abokiyar kwananta a ɗakin, Yusra. Hajja ta gyada kai. Haka suka kwana kowannensu zuciya a cunkushe, Hajja dai ba ta samu bacci ba sai da ta ji saukar numfashin jikarta ta shaidar cewa bacci ya yi awon gaba da ita kafin ta kara tofesu da addu’a, lokacin ruwa ya ɗan tsagaita, cikin ikon Allah kuma itama ta samu runtsawar. Hajja ta dube ta kafin ta kawar da kai tana share kwallar da ta cika mata idanu, shekaru goma sha daya da rasuwar Mahmuda, amma yana nan daram a zuƙatansu. Bahijja ita kadai ce ƴa ɗaya tilo da ta zama tamkar fitila mai haskaka mata rayuwar gidan, ba ita kadai ba, hatta abokiyar zamanta Hajiya Zahra’u da ake kira Mama, duk rashin kaunarta da Hajja tana yi da Bahijja domin yarinya ce da ta mayar da kowa nata. Idan tana wasu lamuran sai ka rantse ba ta da damuwar komai, amma idan damuwar ta motsa, takan jima ba ta fita a ciki ba.

*****

An wayi garin cike da ni’ima, ya yi luf gwanin sha’awa, gefe guda wani irin sanyi mai dadi ya lulluɓe shi. Ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar leshinta ja, ta yafa bakin mayafi. Fuskar babu ko hoda sai kwalli da ta rambaɗa a idanun, sai ka yi zaton ma har hodar ta shafa. Ta fito falon Hajja sai tashin ƙamshin humra take. Turare yana daga cikin abin da Bahijja ta fi kauna a rayuwarta shiyasa ba ta rabo da ƙamshi, hakan ya ja yan uwanta maza da mata na kafatanin gidan suka koma kiranta da Antin Ƙamshi. Tun tana jin haushin sunan har dai ta haƙura ganin ba za su fasa tsokanar ba. Musamman ma da ta riga da ta sani cewa mutan gidan su na da tsokana muddin ka nuna ba ka son abu, wannan ya na daga cikin dalilan da ya sa ta shanye dukkan ɓacin ranta.

Ta yi turus cike da takaici ganin Hajja da Talatu mai taya ta hidima har ma da wasu ƴan mata uku jikokin gidan sun yi shiru an sa rediyon Hajja a gaba ana sauraron labarin Akan So na Lubna Sufyan a shirin Zaman Duniya wanda Garzali Yakub ke gabatarwa a gidan rediyon nan mai farin jini wato Haske.

A duniyarta ba abinda ta tsana kamar wannan shirin, ba domin ba ta da ra’ayin karance-karance kawai ba, a a sam, har ma da yadda mai gabatar da shirin ke taƙarƙarewa yana kwantar da murya wurin kwaikwayon duk inda furucin mace ya zo a labarin. Amma koda ta lura ta fahimci cewa ko ma me yake karantawa a yau, labarin ya taɓa zuƙatan mutanen nata, Hajja idanun sun cicciko da kwalla yayinda Talatu ta taƙarƙare tana kuka har da shan majina, su kuwa su Fa’iza, Rufaida da Hafsat, ba a maganarsu ma domin kuwa kuka su ke risga sosai abinsu. Sai mamaki ya kashe ta daga tsaye da takaici. Ba ta kai ga katse su ba sai ga Fadil ya faɗo da sallama yana faɗin Hajjos! Wato da Hajja kamar yadda ya saba kiran ta. Shima turus ya yi yana kallon wannan iko na Allah. Ya dubi Bahijja wacce ke tsaye kamar an kafe ta a ƙofar ɗaki, kafin ya maida kai ya dube su, lokaci guda kuma ya kwashe da dariya. Dariyar da ta sanya su dubansa, amma ba su iya cewa komai ba don ba su kaunar ko da kalma ɗaya na labarin ya wuce su.

Bahijja ta shige kicin ta bar su da Fadil wanda ya rarumi rediyon da zummar ya kashe, ita kuwa Hajja ta rarumi maficinta ta na shirin kai mishi. Ta ƙara fitowa hannunta dauke da kofi, sauri ba ya daga cikin ɗabi’unta, don haka ba ka fahimtar saurin Bahijja sai ta hanyar duba agogo. Hankalinta sam ba ya kan Fadil da ya ke jan musu da su Hajja akan shirin da suke sauraro, rabin hankalinta yana kan agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, tana kuma shan ruwan shayin. Karshe ma haka ta hakura ta mayar da kofin ta koma ɗaka, jakarta ta ɗauko sai waya. Nan ta iske missedcalls din aminiyarta Meenat. Madadin ta kira sai kawai ta jefa a jaka.

“Hajjaju.”

Sai lokacin hankalinsu ya dawo kanta. Ta ƙara gaida Hajjar, suka gaisa da Talatu, su Fa’iza ma suka gaisheta.

“Kin fito kenan? Wannan taƙadarin yaron ya sanya ni a gaba. Bari na sallameki.”

Murmushi Bahijja ta yi.

“Ki bar shi kawai Hajja, da sauran chanji a jikina. Na tafi sai na dawo, lokaci na ƙuremin.”

“Toh ai shikenan, Allah ya ba da sa’a.”

Tayi gaba tana amsawa da amin.

Koda ta isa makarantar sai da gabanta ya fadi da ta hango ajin da suke ɗaukar lakcar a cike taf, ta tabbatar Wancan masifaffen ya riga da ya shige. Ta tabbata dakyar idan zai amince ta shiga amma dai ta ga ya fi ta gwada sa’arta. Ta yi shahada ta shiga ajin, ya juya mata baya. Dogo kuma ƙaƙƙarfa ne, kamar koyaushe, yau din ma shigar farin yadi ya yi, kusan kowa ya san shi ma’abocin sanya fararen tufafi ne, ba kasafai ya fiye sanya wasu kalolin ba, sai ya share kwanaki goma sha yana halartar aji da fararen kaya, wannan yasa Bahijja ta laƙaba mata suna Tattabara. Hakanan dalibai kowanne da kalar sunan da suka sanya mishi.

Hankalin aji kaf ya koma ga Bahijja wacce ta shigo ta yi fuska tana shirin neman mazauni. Ya ɗaga dara-daran idanunsa da gashin gira suka yiwa luf saboda tsawo, ya dubi ɗaliban, tabbatarwar da ya yi hankalinsu ba ya gareshi ne yasa shi juyowa don ganin abinda ya ɗauke hankalinsu. Ransa ya ɓaci ainun.

“Ke.”

Ta tsaya cak ba tare da ta juya ba, sai kuma ta yi shahada ta juyo. Bai ƙara komai akai ba banda yatsa da ya nuna mata. Ta kauda fuskarta, kallon waɗannan idanun nasa ba duk mace ba, kaifinsu wane harsashi, wani irin kwarjini Allah ya ba shi wanda zai wahala kai tsaye ya samu ɗalibin da zai raina shi. Koda mutum ya yi gigin gwadawa, to fa akwai matsala. Kamar yadda wata mai ji da kanta wai Billy Slow ta taɓa karambani yi mishi rashin kunya duk don ta burge shi, amma ina! Gaban jama’a ya yi mata disgin da har gobe aka tayar da zancen sai ta ji ta tsani kanta. Har fashin zuwa makarantar ta yi na satittika kafin ta haƙura ta dawo.

Bahijja kam ba ta tsaya wani ja in ja ba ta fice, tana kai wa ƙofa ta ja tsakin da ake kira banza domin kuwa wanda aka yi don shi, bai ji ba. Can gaba ta yi ta nufi ƙasan bishiyar mangwaro ta zauna saman kujera. Waya ta fiddo ta shiga shafin Instagram, hotuna ta ke kallo iri-iri na ƴan gayu, masu kuɗi da ma masu ƙaryar kuɗin. Idanunta ya sauka kan hotonta, ta tsaya cak tana ƙarewa budurwar dake jikin hoton kallo. An ɗauki hoton ne tana zaune saman mota ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Riga da siket ƴan kanti ne a jikinta, kan babu ko ɗankwali. Baƙa ce, irin baƙin da hutu da jin dadin rayuwa ya ratsa. Murmushi mai kyau da har wushiryarta ta bayyana muraran shi ne a saman fuskarta. Beauty Queen, kamar yadda sunan shafinta yake a rubuce madadin ainahin sunanta. Bahijja ta ƙuramata idanu, sai kuma ta ja tsaki ta yi saurin fita daga shafin. Wayar ta mayar cikin jaka fuskarta sam babu walwala har sadda ta ga fitowarsa akan idanunta ya nufi hanyar ofishinsa. Ta bi takunsa da kallo, ta yarda koda ba ta daga cikin matan da yake burgesu, ta yarda dagasken shi din abin burgewar ne. Komai nashi a nutse yake, ga haɗe rai gudun a kawo mishi wargi. Ƴan mata har kan matan aure, rububin cika aji ake yi matukar shi ne zai shiga aji, hatta da wadanda ba ya ɗaukar su, kawai don su ji daddaɗan muryarsa da kalle surarsa. Wannan na ɗaya daga cikin abinda ya sa ya ƙara ficewa Bahijja a rai. Ta sani ba laifinsa ba ne, ba kuma shi ya ba kansa abinda ake rububinsa don shi ba, amma ita kam ta rantse ba za ta iya auren namijin da hatta da jahilan matan aure su na burin kasancewa da shi ba. Ta yi nisa a kallonsa har ya ɓace mata, hakanan kuma a tunaninsa, ba ta ji tahowar Meenat ba sai dai jin saukar hannu saman kafaɗarta. Wannan ya sa ta ɗan firgita, Meenat ta zauna tana sakin baki.

“Ah, kodai idanuna ne ba su ganemin daidai ba, ke da kanki ke bin Tattabaran da kallo?”

Bahijja ta ja guntun tsaki.

“Sau da dama mutum kan yanke hukunci ne bisa zargi, ke kika ga ina kallonsa, toh eh, kallonsa nake, amma ba da kowacce manufa ba. So nake na ga abinda ya fi sauran maza da shi da har matan auren da ke ƙasan ikon wasu mazan, ke kallon haram.”

Meenat ta yi dariya.

“Kin gano ko mene?”

Cikin basarwa Bahijja ta ce.

“Ni ba wannan ne a gabana ba, ya muka kwana batun maganar da nace zamu yi? Kin shirya mata?”

Meenat ta hangame baki tana mai sakin hamma.

“Na shirya, amma kinsan Allah kuwa yunwa nake ji, babu abinda zan fahimta.”

Sauke ajiyar zuciya ta yi, ko ba komai ta hango alamar nasara don kuwa babu wannan fargabar da tsoron da fuskar Meenat ta nuna a farko da ta zo mata da batun yin wani gagarumin aiki. Tana ji a jikinta za ta goyamata baya. Komai zai tafi daidai yadda ya kamata.

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×