Skip to content
Part 22 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Yafi mintina goma da bude idanuwan shi, amman sam yaki ko da motsawa ne, komai nauyin shi yake ji, da kyar yayi sallar asuba, itama a cikin daki, sabo ne kawai abinda ya tashe shi a yanda yake jin shi kamar marar lafiya. Karatun Qur’ani ma, da kai ya karanta abin da ya sawwaka, yaja jikin shi ya koma kan gado ya kwanta. Baya gane hasken rana ta cikin dakin saboda gabaki daya labulayen a sake suke, kuma ya kashe wutar dakin, akwai dalilin da yasa ya yi zanen taswirar dakin a haka, saboda bayason haske sam idan bacci yake son yi.

Da kyar ya iya juya kwanciyar shi, yana daukar wayar shi ya latsa, sha biyu saura mintina tara. Dan ware idanuwan ya yi ganin rana tayi har haka, sako yagani ta saman wayar, ya cire daga mukulli yana budewa. AbdulHafiz ne.

“Basu dauki yarinyar su sun baka dan sun gaji da ita ba. Kamar yanda wani bai maka dole kaganta kace kana so ba, karka wulakanta musu yarinya Hamza, karka ci amanarta da ka dauka. Allah ba zai barka ba, ka zauna da ita kamar yanda ka ke so mijin Auta ya zauna da ita, ka riketa kamar yanda kaga Appa ya rike Anna, ka kula da ita kamar yanda zaka so a kula da naka yaran wata rana. Allah ya baku zama na aminci, Allah ya kauda fitina a tsakanin ku, Allah baka ikon fin karfin zuciyarka a kowanne yanayi.”

Wani abu Hamza ya hadiye da yazo yai mishi tsaye a makoshi, yanajin jikin shi ya kara nauyi da maganganun AbdulHafiz din, a lokaci daya kuma suna bashi karfin gwiwar mikewa zaune. Dan dafa kan shi ya yi, kafin ya sauke wani numfashi mai nauyin gaske yana mikewa gabaki daya ya nufi bandaki, ruwa ya watsa ya fito, zuwa wani dan lokaci ya shirya kan shi tsaf cikin wani yadi ruwan kasa mai haske, sai kamshi yake bazawa. Idan kagan shi zakace wani waje zaije, dan har hula ya saka a kan shi, ya daura agogo a hannun shi, takalma ya zira da za’a iya kira da silipas, bakake, tukunna ya fito daga dakin, a hankali yake sauka kasa.

Tsaye yayi bakin kofar dakin Hindun yanajin jikin shi a sanyaye, ko kadan baya son tuna abinda ya faru a daren jiya, yasan shi din mai tarin laifuka ne, amman laifukan shi tsakanin shine da Ubangiji, nauyin da yake ji yau na da alaka da rashin kyautama Hindu da bai yi ba, ko kadan baya son hada laifukan shi da hakkin kowanne mutum, musamman ita, musamman matar shi. Numfashi ya sauke da kalmomi biyun karshen “Matar shi.” Shi dinne yau karkashin inuwar aure da wata, shine da mata, da gaskiyar Hausawa da suka ce, “In da ranka ka sha kallo.”

Kwankwasa dakin ya farayi, sannan ya tura a hankali, a tsaye ya hangota, daga inda yake baya iya ganin fuskarta, bata kuma juyo ba, jikinta na sanye da doguwar riga ruwan kwai, bayan a bude, bata kai da zage zip din ba, tanata kokarin daura dankwalin ta, takalman shi ya zare daga nan inda yake tsaye, ya saki kofar yana rufeta, a hankali ya taka har inda Hindun take tsaye, hannun shi yasa yaja mata zip din, kafin ya mika shi yana kama dankwalin da take kokarin daurewa, yana kallo ta sakar mishi, dubawa yake yana tunanin ta inda ya kamata ya fara daurawa dan baisan me take son yi ba, baima san me yasa ya yi kokarin tayata ba.

Tunda ya shigo taji shi, taji shigowar shi, wani irin wahalallen bacci tayi tun bayan asuba, ta kuma tashi da wata irin yunwa, ga alamar zazzabi da takeji, ta dai godewa Allah da kanta baya ciwo, duk da ta kwanta da shi, amman bata tashi da shi ba, da sanyi-sanyi take komai tun tashin nata, sai da ta fara gyara gadon tukunna ta shiga wanka. Ba zatace ga halin da zuciyarta take ciki ba, balle kuma kalar tunanin da take yi, a karo na farko da hatta tunaninta ya kwace mata, bata da karfin kokawa da komai, dan haka bata yi kokarin janyo shi ba.

Shisa tana fitowa wanka ta shafa mai, ta sami riga ta saka a jikinta, Hamza ya kwace mata abubuwa da yawa a daren jiya, ba zata bari ya kwace mata shigar da tayi niyyar yi yau ba, dan bata cikin walwala baya nufin ba zatayi kwalliya ba, ko ba komai shirin zaisa kadan cikin ranar yau tayi mata saurin wucewa. Da taji shigowar shi sai da zuciyarta ta doka, wani sabon tashin hankalin daya daga mata kafa tun tashinta taji ya dawo, jikinta ya fara bari, tana rasa yanda tayi niyyar daura dankwalin kafin shigowar shi. Badan bataso juyawa bane, kafafuwanta taji sun daskare a waje daya, har ya karaso yana kama zip din rigar da take jikinta yayi sama da shi.

Ko ta cikin mudubin ta kasa kallon shi, zuciyarta dokawa take har zazzabinta ya bayanna sosai, dan tanajin zafin da jikinta ya dauka. Tana jin shi ya kama dankwalinta, shisa ta sakar mishi, sai yanzun ta sami karfin gwiwar kallon shi ta cikin mudubi, da yanayin fuskar shi daya nutsar akan dankwalin, zaka rantse bashida abu mai muhimmanci daya kamata yayi, numfashi ta sauke, tana mika hannunta ta dora akan nashi cikin son karbar dankwalin, makale mata kafada yayi yana saka dayan hannun shi ya tutture nata.

“Kibar ni, ina tunanin style ne.”

Yanda ya yi maganar sai ta tsinci kanta dayin dan murmushi, yafi mintina biyar, har saida taji kafafuwanta sun fara gajiya da tsayuwa, sannan ta dan tsugunna tana zame kanta daga cikin dankwalin, ta sake mikewa, ta mika hannu ta fisge dankwalin daga cikin hannuwan Hamza, bude baki ya yi ta riga shi da fadin.

“Ka kyaleni, kafafuwana sun gaji da tsayuwa.”

Ta karasa maganar tana daura dankwalinta mai sauqi ta hanyar lanqwasa shi, ta kuma tura ta baya, daurin da akanyiwa laqabi da ture kaga tsiya. Ya kuma yi mata kyau, ta cikin mudubin suka hada idanuwa, tayi saurin sauke nata, tana sa Hamza zagaya hannuwan shi a qugunta ya rikota jikin shi hadi da lumshe idanuwan shi.

“Idan nace ki yi hakuri ya yi kadan, idan nace ba zai sake faruwa ba zanyi miki karya…na rasa abinda ya kamata ince miki, ki yi hakuri, ban kyauta miki ba, ki yi hakuri Hindu.”

Ya karasa maganar yana bude idanuwan shi cikin nata da take kallon shi ta mudubin, nata idanuwan cike taf da hawaye, bata san ko yanayin muryar shi bane ba, ko hakurin da yake bata, amman koma meye ya yi tasiri a zuciyarta, tunda bata tsammaci hakan daga wajen shi ba, asalima batayi tunanin komai ba, dan a tsorace take.

“Ki yi hakuri…”

Hamza ya fadi da dukkan gaskiyar shi, yana sakinta, hadi da kamata ya juyo da ita ta fuskance shi, yasa hannuwa ya tallabi fuskarta.

“Dan Allah kar kiyi mun kuka.”

Ajiyar zuciya ta sauke, hawayen na zubo mata.

“Ka bata mana daren mu na farko.”

Ta fadi muryarta na rawa, kai yadan daga mata, yasani ba saita fada ba, shisa yasan bai kyauta mata ba.

“Shisa bansan ya zan fara baki hakuri ba, naji dadi da muna da darare da yawa a tare damu, I will make it up to you, na miki wannan alkawarin.”

Wannan karin ita ta daga mishi kai, yasa hannu yana goge mata fuska, kafin ya rankwafa ya sumbaci goshinta cike da ban hakuri, tukunna ya rungumeta tsam a jikinta. Ta zagaya hannuwanta a bayan shi, tasani daman, jiya dai zuciyarta ta fara karyatata, amman yanzun Hamza ya tabbatar mata ita yake bukata a rayuwar shi dan ta canza shi, tasan zata iya canza shi daman. Ba zai zo da sauki ba, saita jajirce, amman tana ji a jikinta ko bajima ko ba dade hakan zai faru. Sun kai mintina biyu a hakan kafin yace.

“Yunwa nake ji sosai…”

Tana lafe a kirjin shi ta amsa shi da,

“Nima haka.”

Dagota ya yi.

“Dauko mayafin ki mu fita.”

Itama sai taji ya kara mata yunwar, gani yake kamar bata sauri saboda hanjin shi da yake kullewa.

“Nikam bari in fito da mota, kafin ki karasa shiryawa.”

Hamza ya fadi yana juyawa ya zira takalman shi ya fice daga dakin, hanyar waje ya nufa, ya kama kofar ya bude, ga mamakin shi, katon kwando mai hannuwa yaci karo da shi a bakin kofar dakin, tunanin farko daya fara zuwa ranshi ko jaririne a ciki, yanda kwandon yake a lullube, sai da kirjin shi ya doka, dan yasha ganin haka na faruwa a fina-finai, amman inda jariri ne zaiyi kuka ai dole. Ganin yar takarda a maqale yasa shi tsugunnawa ya dauko takardar yana dubawa, kafin ma ya karanta yagane rubutun AbdulHafiz ne.

“Eng. AH.”

Kawai aka rubuta a jiki, daukar kwandon yayi yana shigowa dashi cikin gidan, cike da mamaki, tsugunnawa yayi ya fara bude ledar da akayi amfani da ita aka lullube kwandon, yana cin karo da kuloli a shirye tsaf. Fiffito dasu yayi, ya bude na farko, dankaline soyayye da wainar kwai sai kamshi ke tashi, yana kara mishi yunwa, ya sake bude wata, farfesun kayan ciki ne.

“Allah ne kawai zai saka maka AbdulHafiz.”

Hamza ya fadi yana gode ma Allah da kyautar AbdulHafiz a rayuwar shi. Sai yake jin kamar AbdulHafiz bai taba mishi wani abu da yaji dadin shi irin yau ba. Mikewa tsaye yayi yana zaro wayar shi daga aljihun shi, AbdulHafiz ya kira da bugun farko ya daga yin sallama.

“AbdulHafiz…”

Hamza ya kira yana rasa abinda ma zaice, yanajin karamin tsakin da AbdulHafiz din yaja.

“Mene ne?”

Ya bukata, yar dariya Hamza ya yi.

“Na gode, Na gode AbdulHafiz.”

Yanda ya yi maganar yasa AbdulHafiz fadin,

“Kai kam baka da hankali dama.”

Ya kashe wayar daga dayan bangaren,

“Kamshin me nakeji?” Hindu data fito ta fadi yawunta na tsinkewa.

“Abinci AbdulHafiz ya aiko mana.”

Hamza ya bata amsa, abayar da ta saka a jikinta ta cire tana cillawa kan kujerar dake falon, tare suka tattara kulolin suna dawowa falon, suka zauna dirshen, babu wanda yake maganar dauko plate, akwai cokula a ciki, da babu hannuwan su zasu saka, ita kam Hindu batasan ko yunwar da takeji bace ba, amman ta kwana biyu bataci abinda yayi mata dadi ba haka.

“Hindu mun kusan cinyewa.”

Hamza ya fadi da mamaki a muryar shi.

“Kasan yunwar da na ke ji kuwa?”

Hindu ta amsa shi tana saka nama a bakinta.

“Bamuyi Bismillah ba, ko ke kinyi?”

Ya sake tambaya, kai ta girgiza mishi, dariya yake yi yana sakata dariyar itama, cikin nishadi suka karasa cin abincin, suna zaman su a falon dan su dan sami natsuwa, kowa da tunanin da yake yi a ran shi.

*****

Tare sukai sallar azahar, Hamza yayi ja musu sallar. Suna gama azkar dinsu ta gyara zamanta, tanajin wata gajiya na saukar mata, Hamza take kallo da yake karatu a hankali da wayar shi, muryar shi na nutsar da abubuwan da batasan suna tashe ba a zuciyarta, tana kara jinjina ikon Allah da kalar jarabtar Hamzan. Gashi yayi mata wani irin kyau, sai da ya idar tace mi shi.

“Ka yi kyau.”

Kallon kanshi ya danyi, yana kashe mata ido daya.

“Kwalliya na yi miki.”

Murmushi ta danyi, duk da taji dadi har ranta.

“Ko dai zaka fita ba.”

Kai ya girgiza mata.

“Babu inda zanje Allah, sai za’a je wani waje ake kwalliya?”

Ya tambaya, shi zai iya yin wanka ya saka manyan kaya harda hula kuma ya yi zaman shi a daki. Mikewa yayi yana hawa kan gadon ya zauna ya mike kafafuwan shi, itama Hindu mikewa tayi, inda taga jakar system dinta su Anty sun ajiye mata ta nufa ta dauko, akwai socket ta gefen Hamza, ta fara saka cajar, sannan ta hada da system din tana janta zuwa kan gado ta ajiye, ta dayan bangaren ta zagaya ta zauna.

“Me zaki yi?”

Ya bukata cike da son sani, yasan tana da sauran sati biyu kafin ta koma makaranta, zangon karshenta.

“Kallo…”

Da ido yake binta harta kunna system din, tana zama a gefen shi, matsawa yayi kusa da ita sosai, ta kunna korean film din da bata fara kallo ba, Biebee ta tura mata shi.

“Bride of the century”

Hamza ya karanta sunan, yana mamakin inda suke samo sunaye haka, kashi na farko Hindu ta kunna, tana gyara zama, ta kwantar da kanta a kafadar Hamza, tasha mafarkin faruwar hakan, har a ido biyu tana hasasota zaune da mijinta suna kallo haka a system suna taba hira. Yanzun da abin ya faru sai take ganin kamar a mafarki, kamar wani zaizo ya tasheta. Hannun Hamza taji ya kama nata yana hade yatsun su waje daya ya dumtsa, tana jin yanayin har cikin zuciyarta. Kallon suke a nutse suna son fahimtar inda film din ya dosa, har kashi na farko ya kare, Hamza ya mika dayan hannun shi ya shigar musu na biyun, film din ya fara daukar hankalin shi sosai

“Yarinyar nan na da kyau.”

Ya furta a fili, shiru Hindu ta yi mishi bata ce komai ba, sai da akayi wajen mintina sha biyar a tsakani aka sake nuno jarumin film din tukunna tace,

“A haka ba lallai kaga kyawun shi ba, sai ka natsu tukun…”

Bata karasa ba saboda zungurinta da Hamza yayi da gwiwar hannun shi a hakarkarinta

“Wallahi zaki fasa kallon nan, me yasa zaki natsu kina kallon shi?”

Dariya Hindu ta yi, “Oh ashe babu dadi.”

Hararta ya yi kafin ya mayar da idanuwan shi kan laptop din.

“Ni ai ba har zuciyata na fada ba, kinga kinja banga me aka ce ba.”

Ya karasa maganar yana mika hannu yadan mayar da episode din baya. Kallon suka cigaba dayi, ko da sukayi sallar la’asar ma kallon sukaci gaba dayi, suna tattauna abinda yake faruwa a film din, batasan yanda akai Hamza ya koma jikinta ba, ita da take jikin shi a kwance, wajen biyar da rabi ta miqe ta sauka daga kan gadon

“Ina ka kai mana kazar mu ta jiya?”

Saida ya tsayar da film din tukunna ya kwashe da dariya.

“Mene ne abin dariya? Baka jin yunwa kai?”

Kai ya girgiza mata.

“Ina ji wallahi, tun dazun.”

Kallon shi take yi.

“Bana so in fara yin magana ne kawai. Tana cikin fridge a kitchen…”

Ya karasa maganar yana sauka daga kan gadon, tare suka fita kitchen din, komai na mata bakunta, tana mamakin kitchen dinta ne haka. Tukunya ta dauka tana daurayewa ta dora akan gas ta kunna dan ta dunduma musu kazar.

“Kisa a microwave mana…ina da a kitchen din sama.”

Hamza yai maganar, ita ta manta da wani abu microwave, akwai a gidan yayarsu Babba, amman basu da shi a nasu gidan, shisa tunanin tayi amfani da shima bai  zo mata ba, duddubawa take yi a nata kitchen din ko itama an kawo mata. Bata gani ba, tasan wasu kayan sai a hankali zata dinga fiffito dasu. Aikam saman suka hau, lokacin duk da tagama dumama musu ana kiran magriba, anan bangaren Hamza sukayi sallah, suka dauki kazar da sauran shawarmar su da burger suka sake komawa kasa, fita Hindu zata sakeyi yace mata

“Me kuma zaki dauko? Allah zanci gaba da kallo idan kika dade.”

Murmushi ta yi. “Lemo fa zan dauko mana.”

Ta fadi tana ficewa, wani irin sama-sama take jinta saboda nishadin da take ciki, gabaki daya yau din ya wanke mata bakin cikin data kwasa a daren jiya. Shi kan shi Hamzan yau da sauki yake jin shi, kamar zai iya zaman auren, kamar babu wani abu mai wahala a ciki kamar yanda yake tunani. Kallon suka ci gaba dayi har isha’i, da suka idar ne ya sake jansu suka yi nafila raka’a biyu ta godiya ga Allah daya kamata su gabatar tun a jiya, amman hakan bai faru ba. Kallon suka ci gaba dayi har wajen goma na dare, kafin zancen ya fara sauyawa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.2 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mijin Novel 21Mijin Novel 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×