Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Ashirin Da Daya

Bookmark

No account yet? Register

<< Previous

Lokaci zuwa lokaci take dan juyawa tana kallon Hamza da yake tukin shi hankali a kwance, ko sau daya bai juyo ya kalleta ba tunda aka tashi daga dinner din da ta kawatu daga wajen shirin kujerun, ko hotunan da aka dinga yi musu sai dai yadan yi murmushi, wani ya rike hannunta, wani ya tsaya a bayanta. Da aka kira su filin ma, hannunta ya rike sukayi tsaye. Tasan daga shi har abokan shi suna da kudi, amman yau sun nuna mata kudin nan da suke dashi basa jin komai wajen likasu. A cikinsu mutum daya ne taga yana lika dari bibbiyu ma. Amman daga dubu sai dari biyar, sosai suka yi ta ruwan kudi, duk da taron awa biyu aka yi, daga takwas zuwa goma na dare.

Kalma ko guda daya bata hadata da Hamza ba, zuciyarta take jin tanayi mata rawa, ta dauka babu wani abu da zai shiga tsakaninta da farin cikinta a rana irin ta yau, ga dinner ta samu irin wadda take mafarki, dan tana da tabbacin zata tsinci hotunan su da Hamza a shafuka daban-daban na Instagram. Amman zuciyarta a jagule take, duk da tabbacin daya bata na cewa babu abinda tayi mishi, kowaye yai mishi wani abu yau bai kyauta mata ba sam, kuma bai mata adalci ba. Duk da fiye da rabin hankalinta akan Hamza yake, tana kula da hanyar da suke komawa bata nan suka biyo ba wajen zuwa. Kanta ta jingina da kujerar motar tana sauke wani irin numfashi mai nauyin gaske.

Idanuwanta na kafe kan titi, amman hankalinta yana can wata duniya da take bakuwa a wajenta, jin Hamza yayi parking yasa ta dago kai tana kallon shi, kafin ta kalli inda yayi parking din, Barcode Lounge, sai take ganin kamar a Barnawa suke, amman batajin ko hanya ta taba biyowa da ita ta wajen. Da matukar mamakin dalilin tsayawar su ta juya ta kalli Hamza da yake tattare babbar rigar jikin shi, kafin ya dan daga yana zarota daga jikin shi ya cireta gabaki daya, duqunquneta yayi yana jefawa bayan motar. Kafin ya fara dube-dube jikin gaban motar yana bude wani waje ya zaro ATM. Ficewa yayi daga motar, bai ce mata komai ba.

Ya kusan mintina sha biyar, dan tanayi tana duba wayarta data karba bayan sun fito daga wajen dinner din, tana jin Dimples nayiwa su Fodio mita.

“Me kuke nufi wai? Yanzun kudin siyan bakin ne ba kwaso ku fitar shine kuke so a rabu tun nan?”

Ta kuma ji AbdulHafiz na fadin.

“Dan kudin siyan baki, ku fadi ko nawane ni in biya. Amman ku taimaka mun, dare nayi.”

Da alama sauri ya keyi tunda da matar shi yazo, yanda take nunawa kuwa a takure take, duk da idanuwanta kawai ake iya gani saboda face mask din daya rufe fiye da rabin fuskarta. Tayi wani irin kyau cikin alkyabbar ta silver. Dan juyawa baya tayi jin Hamza ya bude murfin motar wajen yana saka wani abu da duhun cikin motar bai bari taga ko menene ba, amman kamar lemuka da alama, tunda harda kiret taji alamar kacafniyar kwalabe. Juyawa ta sakeyi tana gyara zamanta, harya gama saka abubuwan da zai saka ya zagayo ya shigo, yana tayar da motar suka bar wajen.

Waje biyu suka kara tsaya, tukunna suka karasa gida, sai lokacin Hindu ta samu ta karema gidan kallo daga waje, yayi mata kyau har saida murmushi ya kwace mata duk da damuwar da take ciki. Da kanta ta bude murfin motar tana fitowa, ganin Hamza nata sauko da kaya, yasa ta mika hannun dan takarbi ledojin da ya tattaro.

“Ki bar shi zan shigo da shi.”

Ya yi maganar da wani irin yanayi a muryar shi.

“Kayan da yawa, ka kawo in tayaka.”

Mika mata ledojin ya yi, saboda baya son doguwar magana, bayama son yin magana gaba ki daya, ji yake kamar zai kurma ihu ko zai samu saukin takurar da yake ji rayuwar shi tayi. Idan har zai samu ya daure zuciyar shi ya kwana a gidan nan yau batare daya fito ya koma gidan Fodio ba, to yana bukatar ya sha wani abu. Yasan bashi da komai a cikin gidan, shisa ya biya ta Barcode ya siyo kalaluwan giyar daya kan sha. A hankali ya dinga dauka yana shiga dasu gidan, baiga inda Hindu tayi ba, Shi dai sama ya haura yana kai kayan part din da nashi ne, dan har furnitures da komai ya zuba. Har kayan sawar shi ya dibo wasu ya kawo nan gidan.

Fridge din bangaren ya shirya komai yana cika shi taf, tunda harda coke ya siyo. Saida ya gama sannan ya balle links din rigar shi yana cire shaddar, daga shi sai singlet a jikin shi yaji kamar ana murda hannun kofar dakin da yake ciki, runtsa idanuwan shi yayi yana bude su a hankali hadi da juyawa, Hindu ya gani data bude kofar tana tsayawa a bakin kofar, rigar da suka dawo da itace a jikinta, amman ta cire mayafin, sai dankwali. Baya son yanda take kallon shi idanuwanta cike da maikon hawaye.

Ita kuma tunda ta shigo, saita wuce dakin da aka fara ajiyeta nan kasa, ledojin ma duk a dakin ta ajiye, wayarta da jakarta ta jefa su akan gado, ta kwance mayafin daga wajen da yake makale a kafadunta tana ajiye shi, ta zame takalman kafafunta, ta karasa ta zauna gefen gadon, wani irin shiru daya gauraye gidan ya saukar mata da kadaici na ban mamaki, ga kuma bakunta da zullumin sabuwar rayuwa duk suka hadar mata. Haka kawai taji idanuwanta sun cika da hawaye, suna zubo mata, musamman da taga Hamza yaki shigowa, sosai hawaye ke zubar mata, wani na ture wani, ba haka ta hango daren farkon ta ba sam.

Wani irin tsoro taji ya tsirga mata da batasan daga inda ya taso ba yana sakata mikewa babu shiri, waje ta fara lekawa ko takalma bata saka ba, sai dai ta hango motar Hamza inda ya ajiyeta, ko ina a rufe kuma, babu kowa, ko maigadi bata iya hangowa daga inda take, sai tarin shuke-shuken da suke a tsare. Dawowa tayi tana fara bin dakunan gidan na nan kasa gabaki daya tana neman Hamza, har kitchen sai da ta shiga. Tana dubawa, hawaye na sake zubo mata, dan batasan koya fita yabarta ita kadai a wannan tanqamemen gidan ba. Da kuwa bai kyauta mata ba.

“Kar kaimun haka, dan Allah Hamza.”

Ta tsinci kanta da furtawa, wasu hawayen na sake zubo mata, tuntuni ta yanke shawarar kiran shi da sunan shi, saboda duk wani suna da tayi tunani, taga tarin yan mata sun kira shi dashi, bataso kuma ta zama kamar su, ko sunan shi a wayarta sai daga baya ta sake zuwa ‘Hilwatee’. Shima din shiya taba kiranta da hakan, ta tambaye shi ma’anar yace mata ‘My sweet’ da yaren Annar shi. Da yake saitama jima ko sunan nashi bata kira ba. Ganin duk ta duba da kunan kasan baya nan, ta yanke hukuncin hawa sama, shima daki biyu ta bude tana lekawa, kafin ta shiga wani dan lungu daya sadata da falon da bai kai na kasan girma ba, a hankali take kawa harta sake yin wani dan lungun tana ganin kofa, murzawa tayi ta tura a hankali.

Ta kuwa sauke idanuwanta kan Hamza da yake tsaye daga shi sai singlet da gajeran wando, saurin sadda kanta kasa tayi, tana kai hannu ta share kwallar da ta taru a gefen idanuwanta, kafin ta sake dagowa ta kalle shi, tana kokarin tsayar da idanuwanta a iya fuskar shi, muryarta na rawa tace,

“Ban ganka ba, inata duba ka.”

Idanuwan shi Hamza yadan murza, yanayin da karara yake nuna mata yanda shigowarta dakin ta takura shi, tana jin wani abu ya bude a cikin kirjinta da ba zata ce ko mene ne ba, amman ciwon shi yasa idanuwanta sake cikowa da hawaye.

“Wanka zanyi Hindu, dan Allah a gajiye nake, kije ki watsa ruwa kema. Zan zo idan na fito.”

Wannan karin batayi kokarin tsayar da hawayen nata ba, barin su tayi suka zubo yaga ni, yana jin kan shi ya kara nauyi da kukan da tayi tsaye tana mishi kamar yai mata wani abu, ko kwana basuyi ba karkashin inuwa daya, amman a wuyan shi yake jinta ta tokare, ko iskar kirki baya iya shaka sam.

“Na tambayeka ko nayi maka wani abu, tun dazun, duk yau kanata bani attitude, idan ma bayau ba, ko wani lokaci a baya nayi maka wani abin daka rike a ranka ka zabi kabari sai yau ka horani, ka dubi girman Allah ka fadamun sai in baka hakuri….amman… Am…”

Hindu ta kasa karasa maganar saboda kukan daya kwace mata, bata baro gidansu tazo nashi dan ya dinga yi mata wannan abin ko kwana batayi ba, amare nawa ne ta karanta, ta kuma ji labarin yanda angwayen ke lallabasu a dare irin na yau, suna lallashin su yayin da suke kukan rabuwa da gida, amman yanzun ita gata a tsaye nata hawayen na zuba akan wani dalili daban, amman ko motsi Hamza bai yi ba, ballantana ya nuna alamar zai karaso inda take ya lallasheta. Kallonta kawai yake yi, inda zai iya shima kukan zai yi saboda abinda yake ji, kawai so ta tafi ya dan jishi shi kadai na wani lokaci.

Amman taqi tafiya, neman dalili take yi bayan ya gaya mata babu, maganar da baya son yi take so ta saka shi dole-dole saboda rashin son zaman lafiya.

“Karya ki ke so inyi miki? Nace miki bake bace ba, dan girman Allah ki kyaleni inji da abinda ya ke damuna mana, haba dan Allah.”

Hamza ya ke fadi yanajin idan ya karasa inda take, turata waje zai yi ya rufe kofar, baya son haka ta faru, baya son yin abinda su duka bazai musu dadi ba, tunda har ranshi yake jin babu abinda tayi mishi, abinda yake ji bashi da alaka da ita, yanzun ne take so ta hada mishi abinda yake ji da ciwon kanta, su zame mishi biyu.

“Me yasa dan Allah Hindu na zaki kyaleni in shaki iska ni kadai ba?”

Hannu ta kai tana share hawayenta da kamar taba wasu hanyar zubowa ne, ta bude bakinta tana shakar iska, dan wadda take zarya ta hancinta da wani irin zafi take jin shigarta, ga kirjinta abinda ya bude dazun takeji yana kara budewa, batasan wanne laifi ta aikata mai girma haka da ta cancanci wannan abin ya faru da ita a darenta na farko ba.

“Wow…”

Ta furta tana sake kai hannu ta goge fuskarta. Kafin ta juya, ko kofar bata rufe mishi ba, tana da tabbacin tsoron da take ji bazai mata komai ba, amman yanayin Hamza da maganganun da yake fada mata na barazana da numfashinta, kafar benen bibbiyu take hadawa wajen sauka, da gudu ta koma dakin da ta fito, tana doko kofar, jikinta ko ina bari yake yi, dankwalin kanta ta fisge tana jefa shi kasa, kafin ta fara kiciniya tana samu ta zuge zif din rigarta, ta zameta tana tsallaketa a wajen, bandaki ta shiga, da sauran kayan da suke jikinta ta bude ma kanta shawa din da ko a film bata taba ganin irin ta ba, ruwan yadan fara zubo mata, tana fita babu shiri jin ruwan zafi ne sosai, anan bandakin ta tsugunna, tana kokawa da numfashinta.

Kuka take yi kamar ranta zai fita, kafin ta samu da kyar ta mike, dubawa tayi sosai tana samu ta dai-daita zafin ruwan ta watsa. Ta cire sauran kayan tabarsu anan bandakin, tana dauro towel ta fito. Tanajin yanda fuskarta ta kumbura har idanuwanta, dakin sake kayan data gani dazun ta shiga, ta kuwa samu kayanta a shirye a cikin wardrobes din, na cikin ta fara sakawa, ta tsaya tunani kafin ta sami wata rigar bacci mai yanayi da kimono ta saka a jikinta tana daure madaurin akan cikinta, duddubawa tayi ta samu wata farar hula, sai da ta saka towel din ta goge kanta, tana jin dadin shawarar Aina’u data dauka, tayi kitso. Sannan ta saka hular, saboda yasa tadan turata baya, dakin ta fito ta karasa kan gadon ta kwanta daga can karshe.

Kanta kamar zai bude saboda ciwon da yake yi, ga cikinta ya daure waje daya saboda rashin abinci. Tunda ba wani abin kirki bane a ciki, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, zuciyarta kanta tayi wata irin natsuwa a cikin kirjinta, su dukansu biyun a gajiye suke da rayuwa gabaki dayanta.

*****

Kwalbar hannun shi ya daga yana sake kafawa a bakin shi, sai da yaji baya iya numfashin kirki tukunna ya sauke kwalbar, a zaune yake dirshen kasa kan kafet, tunda Hindu ta fita daga dakin, yafi mintina goma a tsaye. Yasan wanka ya kamata yayi, amman kanshi ya cunkushe, gabaki daya lissafin shi ya kwance. Ya kasa tsayar da tunanin shi waje daya sam, shisa ya dauko abu daya da yake da tabbacin zai batar mishi da komai, kwalbar ya ajiye yana dafa gado ya mike, ji yayi lum, kan shi yayi wani irin juyawa, wasu taurari na giftawa ta cikin idanuwan shi. Da kyar ya samu ya dai-daita tsayuwar shi, kafin ya fara takawa yana dan tangadi ya fita daga dakin.

Baisan ya bugu ba saida ya fara gwada taka benen yaga yana rabe mishi biyu, kama karfen gefe yayi, amman ya gwada faduwa Allah na tsayar dashi yafi sau biyar, kafin ya samu ya karasa sauke, komai bibbiyu yake ganin shi, saiya runtsa idanuwan shi ya sake budewa yake dan ganin dai-dai. Dakin da Hindu take ya karasa yana tura kofar, ya hangota a kwance, bata koyi motsi ba, ballantana ta dago, da kyar ya karasa cikin dakin sosai, ya kuwa yi tuntube da ledojin da suke ajiye da sam bai kula dasu ba, kafin jiri ya dibe shi yana katantanwa cikin dakin, karar faduwar shi Hindu taji saboda hankalinta sam baya tare da ita.

A firgice da wani irin matsanancin tsoro ta mike gabaki daya, tana sauke idanuwanta kan Hamza cikin tashin hankali, tana kallon yanda yake kokarin tashi, da kyar ya mike zaune, tsaye yake so ya tashi amman saiya kara zamewa ya koma ya zauna. Da wani irin tashin hankali da bata taba sanin akwai shiba a duniya take kallon Hamza, kafin ta sauke daga kan gadon tana jinta kamar a gajimare take yawo, itama jirin taji yana neman kwasarta, saita tsugunna tana rarrafawa ta karasa inda Hamza yake, kafin tayi wani abu harya riko hannunta.

“Baki yi mun komai ba, ina so in zauna ni kadai ne…. Hindu ki taimaka mun, ya zanyi in kwance sarkar da ta daure ni? Ya zanyi? Bana so, ban shiryaa ba, wallahi ban shiryaa ba, ki taimaka mun.”

Idanuwanta cike suke taf da hawaye, hannunta daya ke rike dashi ta dago tare da nashi, tana dumtsawa a cikin nata, ganin a buge yake, kamar baima san me yake ce mata ba.

“Hamza….me ka sha? Me kake sha? Kar kayimun haka, dan Allah ka rufamun asiri, ka rufamun asiri.”

Take fadi, wani irin gunjun kuka na kwance mata, tana saka shi zame hannunshi daga cikin nata, ya kama fuskarta yana fadin.

“Shhhhh…. Ban sha da yawa ba, ban sha da yawa ba, ban sha da yawa ba.”

Yake fadi yana kara maimaitawa, amman ta kasa yin shirun, batasan yanda zata fara yin shiru ba a wannan halin, so take yi idan yau mafarki ne ta farka, dan zuciyarta zata tarwatse, tasan yana neman mata, wannan abu ne da take da yakinin zata iya canza shi a kai, saboda tana da abinda zata bashi, amman wannan, wannan abin da take gani bata san yanda zata fara ba, yarda da abinda ya ke gabanta ma na mata barazana, balle tasan yanda zatayi da shi, ga wani irin wari da batasan meye ba daya cika mata hanci yana kara dagula mata lissafi.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Ta furta tana dora hannayenta kan na Hamza da yake fuskarta, wani sabon kukan na kwace mata, kafin taga ya lumshe idanuwan shi, yana yi mata wani irin nauyin da yake neman rinjayar su biyun, yana sakata sakin hannuwan shi babu shiri, faduwa taga yayi ya kwanta, yana kara mata tashin hankalin da take ciki

“Hamza…”

Ta fadi, tana girgiza shi.

“Hamzaa”

Ta sake fadi, tsoro da firgici bayyane a muryarta, sosai take girgiza shi, amman ko motsi baiyi ba, kuka take har sautin shi baya fita saboda tashin hankali. Hannunta ta dora kan kirjin shi tana jin bugun zuciyar shi daya nutsar da abinda yake mata tunanin ko mutuwa ya yi, kafin ta dora kanta a jikin shi tana kuka kamar ranta zai fita. Tabbas labarin tashin hankali take ji, yaune tasan yanda yake. Ko kadan ba wannan bane abinda ta shirya, a mugun mafarki bata hangoma kanta irin haka ba, yanzun lokaci ne daya kamata ace suna more soyayyar su, ba wannan tashin hankalin ba.

“Babe ji nake kamar in janyo satika biyun nan da suka rage. Bacci ni kadai yana mun wani iri yanzun, saboda ina tunanin yanda zan fara yin shi tare dake.”

Maganganun shi suka fado mata.

“Da zasu mun adalci, sai suce inzo in dauke ki, bama sai sun rakomun ke ba Hindu, in zo in dauki matata mu taho gidanmu.”

Wani irin numfashi take yi, ko shima zai taimaka ya farkar da ita, taga wannan abin da yake faruwa mafarki ne.

“Na kagu lokaci ya yi da zan farka daga bacci in ganki a kusa dani, kece mace ta farko da take gwada hakurina haka.”

Dago da kanta tayi, kan daya sara mata yasa ta mayar da shi a jikin Hamza, zuwa yanzun hawayenta ma sun daina zuba, banda wani yaji-yaji da idanuwanta suke yi mata, kokarin kirjinta take gani, batasan yana da kwari haka ba, sai da taga har yanzun bai tsage dan abinda yake cikin shi ya fado ba. Ciwo dai ya ke mata na ban mamaki. Batasan ya lokaci yake tafiya ba tunda na ganin shi take yi ba, duk da yanzun bata tunanin akwai wani mamaki da rayuwa zata bata, sai da baccin wahala ya dauketa mai nauyin gaske.

Ko motsin Hamza ba za tace taji ba, kawai farkawa tayi cikin wani irin yanayi, kanta kamar dutse saboda nauyin da ya yi mata, kafin komai ya dawo mata, zuciyarta na wata irin dokawa, hanyar bandaki tagani a bude, ta kuwa mike tana shiga, Hamza ta samu yana kwara amai kamar zai fitar da hanjin cikin shi. Shima farkawar ya yi, inda sabo ya kamata ace yanzun ya saba, duk da basai wani ya fada mishi ba, yasan yasha takai mishi karo. Hindu ma da take jikin shi hankadeta yayi, da rarrafe ya fara yana samu ya mike da gudu yana shiga bandakin, da kofar a rufe take zai fara amai a waje, hakan ma ba bakon abu bane a wajen shi.

Saida ya tabbatar ya gama aman tukunna ya dago kan shi, yana tarba hannun shi a jikin fanfo ya kuskure bakin shi, kan shi kamar zai rabe biyu saboda ciwon da yake yi. Hindu na tsaye a bandakin ta zuba mishi idanuwa cikin rashin sanin abinda ya kamata kayi, singlet din shi ya kama ya cire, ya jefar a kasa, kafin ya mike, ganin ya dora hannun shi a kugun shi, yasa ta fita da sauri daga bandakin tana janyo mishi kofar. Sai dai tayi tsaye a bakin kofar, tana jin ya sakarma kan shi ruwa, alamar wanka yake yi. Daga shi sai gajeran wando ya fito yana dafe da kan shi, tana kallon shi ya fice daga dakin, nan ta zame tana zama, hawaye take nema amman sunki fito mata.

Kafin ta ga an turo kofar, Hamzan ne ya dawo, ya saka gajeran wando da riga mai dogon hannu, karasawa yayi inda take ya tsugunna, baisan me yake ji ba, baisan me zaice mata ba, ya tabbata tagan shi a halin da Fodio ne kawai ya taba ganin shi tunda yake a rayuwar shi. Bai kuma san yanda zai dauki hakan ba. Abu daya yasani, bata cancanci wannan abin da yake faruwa da ita ba, kawai baisan yanda zai gyara hakan bane ba, ga kanshi da yake ciwo, hannunta ya kama, yana mikewa ya mikar da ita, janta ya yi har tsakiyar dakin, yana kamata suka sake zama, kafin ya janyota ta matso sosai, yana hadata da kirjin shi ya riketa sosai.

Sai lokacin kukanta da take nema ya fito, bai ce mata komai ba, riketa ya yi sosai, har saida ya ji tayi luf a kirjin shi, alamar ta gama kukan, sannan ya mike da ita, yana jan hannunta suka shiga bandakin, ruwa ya dinga tarba da hannun shi yana zuba mata a nata ta wanke fuskarta da bakinta, sannan suka fito daga bandakin. Zaman suka sake yi, ya mika hannu ya janyo ledojin da suke ajiye, ya siyo kaji, burger da shawarma, yana da tabbacin bata taba ko daya ba, budewa yayi duka.

“Ki ci wani abu.”

Kai take girgiza mi shi, batajin zata iya cin wani abu, har yanzun sama-sama take jinta.

“Kar kisani doguwar magana Hindu, kaina ciwo yake mun. Ki ci…”

Ya fadi muryar shi babu alamar wasa, bata san me ya yi tasiri a kanta ba, burger daya ta dauka tana faraci kamar magani, da kyar taci rabi tana ajiyewa, baice mata komai ba, duk ya tattara yana fita dasu, fridge din kitchen ya bude ya saka. Ya dauko mata ruwa daya gani yana dawowa ya bude ya mika mata, sha tayi tana bashi, ya karba yasha shima sannan ya rufe robar ya ajiye a gefe, kamata ya yi ya dago, suka nufi kan gadon su dukan su, saida yaga ta kwanta, ya kama mayafin da yake kai ya lullubeta. Sannan ya mika hannu ya kashe mata kwan dakin yana takawa ya fice, tana jin rufe kofar shi, ta lumshe idanuwanta, zuciyarta na wani irin ciwo.

Next >>

How much do you like this post?

Average: 4.7 / 5. Rating: 7

As you found this post interesting...

Follow us on social media to see more!

nv-author-image

Lubna Sufyan

Idan har ka taba k'aruwa da littafina ta kowacce siga, ka tayani rokon Allah da ya yafe kuskure na, ya jikan iyaye na. Na gode.View Author posts

Share the story on social media.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.