Skip to content
Part 24 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Wani irin shiru take jin gidan tun fitar Hamza, bata gane akwai wutar lantarki ko babu, kasancewar solar da yake gidan, kullum a cikin wuta suke. Bata taba tunanin zata gaji da kallo ba sai yanzun da take da wadattacen lokacin yin shi. Tun karfe goma ta gama bacci, har sharar rashin dalili ta takalarwa kanta, duk da Hamza yayi maganar cewa za’a kawo mai aiki, a cewar shi Anna tayi mishi maganar, yace kuma ta samo musu.

Riga da wando ne a jikinta, sai ta daura farin dankwali, zaka yi tunanin fita zata yi saboda kwalliyar da take fuskarta. Tun satinta na farko wani ya kwankwasa kofa, ta saka hijab ta leka, yace mata, “Oga yace kibani kayan wanki.”

Mata shine wanda da wahalar gaske ya girmeta, nata dakin ta shiga ta kwaso mishi kayan wankin da ta tara, ta shiga dakin Hamza ma, da kayan suke a cikin wani kwando duk ta hada, washegari suna tare dashi ma aka kawo kayan a wanke tsaf, sun sha guga, har cikin wasu ledoji aka saka su, ta jima tana mamaki, tunda an kawo mata injin wanki, da alama ba wani amfani zai yi mata ba, haka ma ran asabar din shekaranjiya data cika sati biyu cif akazo aka amsa, sai ta saka a ranta cewa duk sati za’a dinga zuwa karbar wankin nasu kenan. Hamza ya tashi da azumi safiyar litinin din, ya fada mata shi baya suhoor, da yaci abinci da dare ya sha ruwa shikenan.

“Daman kana azumin litinin ne?”

Ta bukata daya fada mata zai yi azumi, kafadu yadan daga mata, yana amsawa da

“Wasu lokuttan…”

Da gaske yakan yi azumi duk sanda Allah ya bashi ikon yin hakan, yanzun dai zaiyi azumin ne dan ya daga ma Hindu kafa ta dan huta, a idanuwanta yake ganin yanda ta gaji da shi, in ba hakan ya yi ba gashi can tare da wata tun kafin suyi nisa. Tun daren auren shi rabon shi da wani kafar sada zumunta, ko yanar gizo zai hau da laptop din shi yake amfani, baya son cin karo da duk wani abu da zai tunzura zuciyar shi, yana son yin iya kokarin shi na danne abinda yake ji, Hindun ita kadai ta ishe shi rayuwa, shine abinda yake fadama kan shi, amman yanajin abu mai wahalar gaske ne, sosai zuciyar shi take karyata shi. Yayi ma jikin shi wani irin sabo da canjin yanayi.

Ko abinci kala daya bai cika gamsar dashi ba, ya fiso ko da guda biyu ne ya hada a lokaci daya, balle kuma mace da yake dauka yana ajiyewa a duk lokacin da yaso, rana daya ace hakan ya sauya, abu ne mai wahalar karbuwa a wajen shi, amman zai yi dukkan kokarin shi, ko dan AbdulHafiz da harya daina bude sakonnin shi yanzun, tun bayan auren shi, kullum saiya turo mishi da tunasarwa kan illar shaye-shaye da neman mata, kamar bai sansu ba, kamar yace mishi ya manta da tarin laifin hakan. Yana saka shi jin dauda a jikin shi fiye da wacce yake ji batare da tunatarwar shi ba. Dan AbdulHafiz ne, shi kadai ne yake mishi wannan shiga hanci da qudundunen.

Zama tayi a falon sama, Hamza yace ta dawo nan taki, tunda dai duka ko ina gidanta ne, kuma inda duk taso kwana zata kwana, da ace ma zai dinga daukarta yana sauko da itane, hakan zai mata dadi, amman taga Hamza bashi da wannan tunanin sam-sam, har Korean film tasa suka kalla da hakan ya faru ko zai sanar da shi wani abu, sai ma ca ya yi.

“Dan Allah jibi yanda suke daga matan su, da yake su ba wani kayan nauyi suke ci ba, amman a Najeriya ba yanda zaka juya matarka yanda kake so, nauyin tumbinta kawai yafi na irin yarinyar nan hudu.”

Tashi tayi ma ta shiga bandaki, badan zata yi wani abu ba, sai dan takaicin daya rufeta, ita din ba siririya bace ba, amman kuma bata da wannan jikin da yake magana, tana kuma da tabbacin ba wani nauyi zata yi ba. Kuma Hamzan ai yana motsa jiki, duk girman shi yanzun take kula da mugun lalaci ya yi mishi yawa, shisa har yake tunanin ba zai iya daukar kamarta ba. A yanda yake ganin shi, ta dauka ko yini yayi yana yawo da ita a cikin gidansun nan sam bazai nishi ba. Shisa ta lallaba zuciyarta, tunda Hamza sam ba zai gaji da basu kunya ba. Tun jiya tace mishi yayo musu cefane tayi girki, har da dankali ya siyo musu, shima ta soya ta yi musu sauce da dare.

“Soya dankali da wahala haka daman? Kinga da kin bari mun siyo abinmu.”

Hamza yace, da yake kitchen din ya sameta yayi tsaye, har saida ya gaji sannan ya koma falo ya zauna, ita kuma haka kawai taji tana so ta dafa wani abu taci, ta gaji da abincin waje. Kuma gara ma da tasa yayo cefanen, yanzun sai ta yi mishi kayan buda baki, tun da tazo ta zauna take tunanin abinda ya kamata tayi mishi, tunda ita da safen nan shayi ta hada tasha da cincin dinta na gara da sai yau dinma ta bude shi. Hamza ya kamata ace abokan shi sunzo, ta diddibar musu, amman zata yi mishi magana, su Dimples ma sunki lekota har yanzun, a cewar su saita gama amarcinta.

‘Yan gidansu kuwa batama saka ran ganin su yanzun ba, suna dai waya kusan kullum. Kuma sukan yi chatting, amman tasan ba barinsu zuwa za’ayi yanzun ba. Sai ta kara kwana biyu. Tasan yau aka koma makaranta, ko za’a fara wani abu sai wata litinin din, Hamza ya sani shisa batayi mishi maganar tana son zuwa ba, ca zai yi zata wahalar da kanta. Kawai abu daya ne yake mata dadi har ranta, da safe kafin ya fita yace zai nemo makarantar koyon tuki, a koya mata. Yana so ta koma makaranta da motar ta, duk idan ta juya sai wani nishadi na daban ya lullubeta, ita din, Hindu Al’amin zatayi mota, sosai ya faranta mata rai, shisa itama zata yi kokarin ganin ta faranta mishi rai a yau din nan.

*****

Wanka ta sakeyi tana dauro alwalar sallar Magriba, sunyi waya da Hamza sau daya, shima kawai yaji ya ta wuni ne, sai text da ya yi mata bayan la’asar.

“Nikam na gaji, yunwa na keji.”

Murmushi tayi kawai, dan lokacin harta gama farfesun kaji, tayi miya, ta fere dankali ta zuba mishi ruwa.

“Sannu da aiki, Allah ya dawomun da kai lafiya.”

Bai bata amsa ba, kitchen ta wuce taci gaba da aiki abinta, bata kammala komai ba sai gab da magriba. Yanzun ma kwalliya tayi mai sauki, ta saka riga da skirt na atamfa, ta zauna gefen gado tana jiran a kira sallah tayi saita daura dankwalin ta, wayarta ta dauka, taga Hamza ya kira wajen biyar saura, tana kitchen, sai kuma text daya turo

“Karfa ki wahalar da kanki, ba sai kin dafa mun wani abu ba.”

Murmushi ta yi, tanajin dadi data ajiye gwiya a gefe ta shirya mishi kayan buda baki, tasan zai ji dadi. Ta kula in zasu fita kullum suci abinci a waje ba zai damu ba, idan ya bata kunya ta wani bangaren, sai ya yi wani abu kuma da zai zo dai-dai da mafarkinta. Ana kiran sallah tana mikewa dan ta gabatar da sallarta. Da Hamza manne a ranta lokacin da ta idar, sai take jin kamar motsi a falon kasa, yanke azkar dinta tayi tana mikewa ta daura dankwalinta ta fita, aikam Hamza ne zaune kan kujera, hannun shi ya mika mata, tasa nata a ciki, ya kama ya zagayo da ita tana zama gefen shi, sumbatar gefen fuskarta ya yi.

“Na yi kewar ki.”

Ya furta da wani yanayi a muryar shi da yasa ta fadin, “Buda baki fa zaka yi.”

Murmushi ya yi, sai lokacin ta kula da kwandon da ya ke ajiye a kan kafet. Da mamaki take kallon kwandon, kafin ta kalli Hamza.

“Yunwa nake ji.”

Ya furta, yana fita daga nan da safe gidan Fodio ya wuce, duk acan ya sami su AbdulHafiz. Arafat ne kawai yaje musu Abuja, Fodio nacin indomie, ko Hamza bai tambaya ba yasan AbdulHafiz ma yana azumi, tunda shi kusan duk litinin da alhamis din duniya yana azumi. Sai dai ko in rashin lafiya, kusan ranar duk aiki sukayi, har sai da suka dawo masallaci sallar azahar, yana shigowa Mansy na kiran shi, ya daga ya kara a kunne, maganar farko da ta fara yasa shi yatsina fuska.

“Mansy azumi nake yi ni, bana son iskancin banza.”

Dariya tayi ta dayan bangaren.

“Kai da kake da amaryar da ko sati uku batayi ba, me ya kaika yin azumi?”

Numfashi ya sauke.

“Ya kike?”

Ya bukata cikin son canza maganar, yana da tabbacin in tayi tsayi, Mansy zata saka shi fadin abinda bai kamata ba yana azumi, amsa shi tayi suna dan yin hira

“Yau banajin zuwa aiki, ban fita ba, ko in maka kayan buda baki?”

Kai yake girgizawa tun kafin ta gama Magana.

“Ba zan stressing dinki ba, zamu fita da Madam.”

Ko ma basu fita ba, inya kira Anna yasan za’a kawo musu abinci idan na gida ya ke jin ci, ko daga gidan AbdulHafiz duk yana da wannan alfarmar, Abdallah ma zai iya sakawa a dafa mishi. Duk da yau din ba shi bane ranar farko da Mansy take mishi girki, sosai yana son kalar abincinta, da yawan ranaku idan ya yi azumi tana hada mishi kayan buda baki, ko tazo ta kawo mishi, ko yaje ya karba, duk da baya bari ta shigo har cikin gidan saboda AbdulHafiz, tunda akan abincin ma yana mishi fada.

“Kai baka tsoron a zuba maka wani abu? Gara ka siyi abinci a hotel ko restaurant akan ka dinga karba daga wasu mutanen.”

Murmushi kawai Hamzan ya yi.

“Mansy ce AbdulHafiz, ba zata zuba mun komai ba.”

Ba tun yanzun yasanta ba, inda zata zuba mishi wani abu, tuntuni da tayi, duk iskancin ta bai kai nan bangaren ba, ita ce mace ta farko daya fara nema fiye da sau daya, kuma ta farko da zai kira da kawar shi bayan su Fodio, bafullatana ce, a yanda take fada mishi marainiya ce, ta taso hannun kawunta da tsantsar rayuwar boko ake gudanarwa, babu wanda ya damu da abinda duk takeyi, tana gama makaranta daga service, wajen da take aiki a Kaduna suka riketa, ta kuma kama haya take zaman kanta, yan wanda suka damu a dangi sun mata magana tayi biris dasu, saboda ita ba zata yanke yancin da ta samu saboda surutun mutanen da bayan rasuwar iyayenta babu wanda ya damu da ita ba, su biyu suka haifa daman, yayanta ya rasu tunda karancin shekaru.

“Babu wani stress, dan zan maka girkin shine zai zama wani abu, daman zan dafa nima. In zaka wuce gida saika biyo ka karba.”

Kyaleta ya yi tayi din, suka karasa magana kafin suyi sallama kan cewa zai biya ya karba din. Lokacin da taji labarin aurenshi, ta daga hankalinta ba kadan ba, abinda ko a takalmin Hamza, ya jima da sanin Mansy na son shi, yana jinta har ranshi, amman ba irin wannan soyayyar ba, kuma tayi mishi tsufa, ko ba haka ba, bazai iya auren mace irin Mansy ba, kishin shi ba zai taba bari ba, ko zai bari Anna zata mutu kafin ta yarda da auren. Shisa kai tsaye ya ce.

“Karki mun rigimar rashin dalili Mansy, ke kinsan ba zan taba auren ki ba, ba tun yanzun ba, kuma kinsan dole rana irin ta yau zata zo. Babu macen da zata daga mun hankali banda Anna a rayuwarnan, zabinki ne muci gaba da abokantaka ko kuma akasin haka.”

Kwana biyu basa magana, kafin daga baya kuma ta dawo kamar da, dan shi tsaf zai yakice ta gefe. Kamar yanda ya fadane, har ranshi mace ba zata daga mishi hankali ba, Hindu ma da ta nemi barazana da zaman lafiyar shi, aurenta yayi, gashi nan yanzun komai ya lafa mishi. Shisa ya kira Hindu yace mata karta wahalar da kanta, tunda za’ayi musu abinci. Sai bata daga ba, amman yabar mata text, yasan kuma tagani. Suna gama aikin su da ya dauke su har yamma likis gidan Mansy ya wuce, ko shigar da motar shi bai yi ba, anan kofar gida ya jirata ta miko mishi ya wuce.

A hanya ya tsaya yai sallar magriba, kafin yanzun ya karaso gida.

“Ka biya wajen Anna ne?”

Hindu ta bukata, tana kallon Hamza daya zame jikin shi ya sauko daga kan kujera, yana janyo kwandon, kafin ya girgiza mata kai.

“Gidan AbdulHafiz?”

Ta sake tambaya, saboda tana son jin inda ya je ya shigo da kwando haka, a iya sanin ta dai restaurant ba za su hado shi da kwando ba, kuma ta shirya mishi kayan buda baki, kulolin ya fara fito dasu, sai wasu robobi masu murfi, yana fara bubbudewa, pepper chicken ne, soyayyar doya da kwai, plantain, sai wata irin jalof din taliya da taketa baza kamshin daya cika wajen, ita kanta sai ta raina dan abinda take tunanin ta hada mishi.

“Nima fa na hada maka kayan buda baki.”

Ta fadi da wani yanayi a muryarta da yasa shi kallon ta.

“Na miki text fa, nace kar ki yi.”

Dan rausayar da kai ta yi gefe.

“Ina ka samo duk wannan? Na tambaya ko gidan AbdulHafiz ka yi mun shiru.”

Cikin idanuwa Hamza ya kalleta yana sauke numfashi.

“Ba daga can bane, kibarni ni kam, yunwa nake ji.”

Tasan ya kamata tabarshi din, amman wani abu na azalzalar zuciyarta.

“Ina ka samo abinci?”

Cokullan da suke nade ya warware yana daukar mai yatsu yasa a cikin taliyar yayi Bismillah yana fara ci, ba amsa bane baya son bata, ko ba zai iya bata ba, a gajiye yake jin shi, wani abu kuma na gaya mishi in ya fada mata daga inda abincin ya fito maganar ba zata kare dan yanzun ba. Kwalin Exotic ya dauko ya bude yana kurba, yanajin idanuwan Hindu a kan shi tana kallon shi.

“Me ki ka dafa?”

Ya bukata, duk da baya son yin magana ko kadan idan yana cin abinci.

“Koma me na dafa baka shigo da wani ba?”

Hindu ta amsa shi ranta a bace, ita bawai girki ya dameta bane tun farko, shisa abin yake kara bata mata rai.

“Ina ka samo abinci? Siyowa ka yi?”

Cokalin hannun shi ya ajiye cikin kular taliyar yana kallonta shima na shi ran ya soma baci.

“Ban baki amsa bane saboda ina jin ba lallai kiso amsar ba, ba siyowa nayi ba Hindu, Mansy ta dafamun, daga gidanta na samo abinci.”

Ya karashe maganar yana daukar cokalin shi yaci gaba dacin taliyar a nutse, kallon shi take yi wani irin abu na tasowa ya tattaru ya yi mata tsaya a kirjinta. Mansy, abinci daga gidan Mansy, daga gidan wata tsohuwar banza shisa har yake mata text kar tayi abinci saboda Mansy zata dafa mishi.

“Wow…. Like wow, saboda Mansy zata dafa maka shisa kace ni kar inyi kenan ko?”

Banza ya yi ya kyaleta kamar ba da shi take yi ba, yana cigaba da cin abincin shi, dan harya fara dibar plantain din yana hadawa da doyar.

“Akan me zata dafa maka abinci? Saboda kana tunanin ni ba zan iya dafawa ba ko me?”

Hindu take fadi tanajin kamar ta rufe shi da duka, ga hawaye sun fara cika mata idanuwa

“Me yasa zaka dauko abincin wata banza ka shigomun da shi cikin gida?”

Abincin shi yake ci har lokacin ko dagowa bai yi ba, saboda ita bata isa ta hana shi cin abincin shi ba tunda yunwa yake ji, bata kuma yi shiru ba, surutai ta cigaba dayi, sai da yaji ya koshi, sannan ya rufe kulolin yana mayar dasu mazaunin su, ya mike ya dauki kwandon da nufin kaiwa Kitchen, itama Hindu ta mike

“Ba zaka mayar dani kamar bansan abinda nake yi ba H…”

Yanda yai wata irin juyowa yana hade space din dake tsakanin su yasa maganar koma mata, cikin idanuwa yake kallonta.

“Idan kina so mu zauna lafiya a cikin gidan nan zaki koyi yanda zaki dinga mun magana. Zaku ma ki koyi girmama ra’ayoyina. Dan na miki shiru baya nufin ina gudun rigima dake ne ko wani abu Hindu…”

Numfashi yaja.

“Zan shigo da duk abinda na yi niyya cikin gidan nan saboda gidana ne, zanci kuma abinda nayi niyyar ci, ke baki isa ki hanani ba wallahi, tun kafin in aureki nake cin abincin Mansy, dan na aureki me yasa hakan zai canza? Idan kinga zaki iya ci in nazo dashi kici, idan ba zaki iya ba ko ki fita ki siya, ko ki dafa bai dameni ba, amman ba zaki takurani ba, kina jina? Wallahi baki isa ki takurani ba.”

Ya karasa maganar yana juyawa ya nufi kitchen din, hannu tasa tana share wasu hawaye masu zafi da suka zubo mata, yana fitowa daga kitchen din ta gefenta ya raba ya wuce, tana jinshi ya haura sama, ranta in yayi dubu a bace yake, ashar din da batasan ta iya ba, shi ta dibo tana aikawa Mansy data ja mata wannan bacin ran, kuma sai ta nemota ta zagi ubanta, in bata kyale mata miji ba, tabbas zasu kwashi ‘yan kallo. Ta kai mintina biyar a wajen tana tsiyayar da hawayen bakin ciki, kafin ta shige daki, fuskarta ta wanke, tukunna ta fito tana nufar dining din data shiryama Hamza, yanda baiki cin abinci ba, itama ba zata fasa ba.

Tana cikin ci, ya fito ya sake kaya daga manya zuwa kanana, sai baza kamshi yake yi, ko inda take bai kalla ba, hannu da taga ya kawo cikin plate din dankali da kwan ta, ya sata janyewa.

“Ba akwai ragowar na Mansy ba?”

Ta fadi tana watsa mishi harara, murmushi ya yi, duk yanda take tunanin ta iya rigima bata kai shi ba, da wurin nan ya kamata tasan ita din bata isa tasa shi ko ta hana shi ba, ya tabbatar ma da kan shi auren nan ba zai takura shi ba, shisa ya daina jin kamar an daure shi da sarkoki, ba kuma zata dawo mishi da yanayin nan ba. Zagayawa yayi, ta sake janyewa, hannuwanta ya kama duka biyun ya rikesu da nashi guda daya, yasa karfi ya karbi plate din yana ajiye shi

“Wallahi ka kyalemun abincina, Hamza bana so, kaje kaci na Mansy, karka taba mun.”

Sakinta yayi yana daukar cokali ya caki dankalin yasaka a bakin shi.

“Ke kin isa ki hanani yin abinda na yi niyya?”

Ya furta yana wucewa yabarta a wajen, tunda ba yunwa yake ji ba, fita yayi ta kuma san masallaci zai tafi, hannu takai ta share hawayen da taji ya zubo mata, itama mikewar tayi, ta shiga daki tayi alwala, ta gabatar da sallar isha’i, karatun Qur’ani ta farayi, ta mike tayi nafila raka’a biyu, tana cikin yi taji Hamza ya shigo, ya zauna gefen gado, tana idarwa ta daga hannayenta biyu, kawai sai taji wasu sababbin hawayen sun sake zubo mata.

“Tafdi jan…”

Hamza ya fadi yana karasa maganar cikin yaren da yasa bata fahimci me ya karasa fadi ba, kafin taji ya kama damtsen hannunta yana kokarin mikar da ita

“Tashi wallahi, kuka kike? Kin kalli gabas kin daga hannu kina sharara hawaye zaki hadani da Allah?”

Cike da mamaki take kallon Hamza da yasa karfi ya mikar da ita, kiciniyar cire mata hijabi ya fara ta kama hannuwanshi tana tutturewa amma a banza tunda ya fita karfi saida ya cire mata hijabi, kafin tayi wani motsi ya hade bakin su waje daya. Zuciyar shi sai bugawa take yi, sosai hankalin shi ya tashi, inya barta tayi addu’ar nan da wuri Allah zai iya amsawa, duk da yanajin baiyi mata komai ba, amman dai baya son wani dan Adam daban ya nemi hada shi da Allah. Hindu ikon Allah take kallo kirikiri, mamaki ya hanata yin wani kwakkwaran motsi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mijin Novel 23Mijin Novel 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×