Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Goma

5
(2)

<< Previous

Gabaki daya satin wani irin sama-sama take jinta, kamar wadda take yawo a saman gajimare, ko tafiya takeyi sai ta dinga jinta kamar reshen bishiya saboda nishadin da take ciki. Babu rana daya a cikin satin da ta wuce batare da tayi magana da Hamza ba, yana kiranta, duk da baya mata wata magana da ta shafi wani abu banda Architecture, jiyane kawai ya bukaci sanin inda take karatu. Ta kuma fada mishi, muryar shi wani irin sanyi take mata, duk yanda take a bude. Hausar shi tafi komai burgeta, bawai bai iya bane, akwai yanda yakan fitar da wasu haruffan da zasu tabbatar maka da cewa ba Hausa bace yaren da harshen shi ya fara lanqwasawa.

Har yan gidan su zuwa yanzun sun fahimci nishadin da take ciki, hatta Zaid da ba shiga harkar kowa yake yiba sai da yace mata

“Wai ke uban me yake damun ki kwana biyun nan?”

Dan tabe baki tayi tana girgiza mishi kai

“Babu komai, me kagani?”

Bai sake kallonta ba, ballantana ma tayi tunanin zai furta wata maganar. Duk yanda take son ko Khadee ce ta ba labarin Hamza wannan karin taja bakinta tayi shiru, ba zatayi jinxing din abin ba. Kuma Khadee din ma bata dameta da tambaya ba, dan hidimar bikinta da yake gabatowa, bakomai take mayar da hankali a kai ba. Garama Asma kan bita da kallon tuhuma duk idan tana waya da Hamzan, saboda yanda murmushi sam baya barin fuskarta, haka idan suna chatting dashi. Sosai take son sanin wani abu a tare dashi da ba a kafar sada zumunta ya saka ba.

Bataso tayi mishi tambayar da zata saka ya daina mata magana, dan taga har yanzun baya kula duk wani comment da zatayi a kasan posting din shi na Instagram. Ta dauka tunda suna magana ko dan liking ne zaiyi, amman bai ma nuna mata yagani ba, ta dai ga alamun yana WhatsApp ne saboda taga ya saka status kwana uku bayan ya kirata, sai tayi commenting, suka koma magana a can, maimakon Instagram. Yau kam tunda ta dawo gida wajen sha biyu da rabi, sallah ce kawai take rabata da tebirin zanenta, so take ta gama duk wani assignment da take dashi zuwa safiyar gobe asabar, dan ta samu ta fara karatun test din da take dashi ranar litinin.

Sai bayan isha’i tukunna ta samu taci abinci, ta koma kan gado ta zauna, tana dora system dinta akan cinya, taji dadin wutar da suka kawo, tana addu’ar su barta har zuwa safe. Wani American film ne take kallo, series, mai suna SUITS. Tana kuma jin dadin shi fiye da yanda tayi tunani, akwai abokinta a Instagram, Ahmad. Shi yace mata ta kalla, har makaranta yazo ya kawo mata daga farko zuwa inda aka tsaya dan ana kanyine, jininsu ya hadu da Ahmad din, yana level 3 a KASU. Shima mayen kallon fina-finai ne, shine ma abinda ya fara asassa abokantakar tasu.

Tunda tayi system ta daina damuwa da zaman falo, duk abinda take son kallo zata saka a cikin system din ta, ko kadan film baya yanke mata. Kallon taci gaba daga inda ta tsaya, da earpiece manne a kunnuwanta. Taji zir alamar shigowar sako a wayarta, batare da ta tsayar da film din ba ta dago wayar tana budewa. Hamza ne yai mata magana ta whatsapp

‘Hey’

Ya fadi, amman sai da taji wani abu na yawo a kasan cikinta kafin ya gauraye zuwa ko ina na jikinta yana karasawa cikin kirjinta yai zaune. Saboda yaune karo na farko da ya fara mata magana batare da ita ta fara mishi ba, shiga WhatsApp din tayi tana amsa shi da

‘Hey’

Tana fara rubuta gaisuwar da kafin ta tura yace mata

‘Me kikeyi?’

Goge gaisuwar tayi

‘Kallo’

Emoji din alamar tambaya ya saka mata, tayi murmushi

‘American film, Suits’

Ta dora da

‘Kai me kakeyi?’

Ya dan dauki lokaci kafin ya amsa cikin yaren turanci

‘Ba wani abu mai yawa ba.’

Kallon amsar takeyi tana rasa abinda ya kamata tace, ba hirar da bata shafi Architecture suka cikayi ba, tunanin abinda zata tambayeshi takeyi

‘Baka fadamun dan wanne gari bane kai.’

Cewar Hindu din

‘Kaduna’

Kai ta girgiza tana murmushi

‘Bakayi kama da ‘yan Kaduna ba.’

Wannan karin shiya turo mata da Emoji din murmushi, bai amsata ba, sai ga kiran shi ya shigo. Film din ta saka a pause tana amsawa da

“Hello”

Muryar shi na dukan dodon kunnenta

“Da ‘yan ina nayi kama?”

Siririyar dariya tayi

“Bansani ba, shisa nake tambayarka ai, har Hausar ka batayi kama da ta ‘yan Kaduna ba.”

Tana jin numfashin daya sauke ta cikin wayar

“Ann shuwace, Appa bafullatani, amman ni dan Kaduna ne tunda anan aka haifeni”

Wannan karin ita ta sauke numfashin, batayi mamaki ba sam, dan batama yi tunanin baban nashi zai kasance dan kasa ba saboda kamannin shi, duk da ba haske ya cika can ba.

“Kace kana jin yarika da yawa.”

Zata rantse taji girgiza kan da yayi duk da bata ganin shi

“Guda hudu ne kawai, babu wani yawa.”

Dariya tayi cikin yanayin da yake nuna alamar ya burgeta sosai. Kafin ta amsa yace

“Zan danyi abu, muyi magana anjima.”

Ya kashe wayar, yana sakata sauketa daga kunnenta tana dakuna fuska, haka yake mata wannan kashe wayar, ko ba zaiyi wani abu ba, da shi ya gama maganar da yake sonyi da ita yake kashewa batare daya jira amsarta ba. Amman kuma kalar ajin shi yayi mata, saboda yayi dai-dai da kyawun shi, tana hango musu abinda batason furtawa ita da shi, addu’a kawai ta karayi, dan yanzun bata asarar gabaki daya darenta a wajen zane, tunda Hamza ya amsata, ko yayane sai tayi sallah dan tana da tarin bukatu.

Alamar shigowar sako taji, ta duba taga text ne wannan karin Hamza yayi mata, bata WhatsApp ba

‘Zamu iya haduwa mu gaisa?’

Batasan ta saki wani ihun murna ba sai da taji sautin cikin kunnuwanta, zufa takeji ta wajajen da bata taba zaton suna fitar da ita ba. Yau ita Hamza Abu Abbas yake tambaya ko zai iya haduwa da ita su gaisa, ba tun yanzun tasan Allah ya amshi addu’arta ba, kawai lokacine baiyi ba sai yanzun, daman Allah yana tare da mai hakuri. Yau kuma taga ribar hakurin takaicin duk tarkacen samarin da ta dinga kwasa a baya.

‘Babu wata damuwa’

Ta amsa shi, kafin ya sake tunani, kafin ya tuna cewar shine Hamza Abu Abbas, gayen da matan Instagram suke tururuwa a kanshi

‘Lunch?’

Gabanta taji yayi mummunar faduwa, kafin ya gama luguden ya kara mishi gudu ta hanyar fadin

‘Ki saka time ki turomun address in zo in daukeki.’

Wannan karin fankar dakin bata hana gumi jiketa sharkaf ba, tabbas wannan shi Hausawa ke kira ga koshi ga kwanan yunwa. Hamza na tambayar su fita abinda turawa ke kira da ‘Date’ ne, yanayin shi bai nuna mata yayi kama da wanda zaizo kofar gidansu ta saka musu kujerun roba su zauna ba, batasan me yasa tayi tunanin hakan zai faru ba tun daga farko. Tasan ko mutuwa tayi ta dawo, Anty ba zata taba barinta fita da Hamza wani waje ba, kullum cikin maganar lalacewar da ta sami al’ada irin ta Malam Bahaushe take, tunda taga wani video na yawo a whatsapp na wata matashiyar budurwa da saurayinta ya hadama patin cikar shekara ashirin da uku, ya kuma tsugunna ya mika mata zobe yana tambayar ko zata aure shi kamar a kasar waje.

Anty bataga komai ba, saka mata zoben kawai yayi, sai abokanan shi da nata da suke tafa musu, matan na fitar da wasu sautika da Anty ta kira da kukan mage, cikin nuna alamar yanda abin ya kayatar dasu, amman kwana tayi tana fada kamar zata ari baki, ita Hindu taga cikakken video din, har rungume juna sukayi, suka kuma sumbaci junansu, sosai ita kanta abin yayi mata wani iri, duk da bangaren da aka bada zoben da yanda wajen ya kawatu ya matukar burgeta.

Balle kuma yanzun ita Hindu ta dauki kafafuwanta ta fadama Anty cewa Saurayi zaizo ya dauketa su fita cin abinci. Tasan magana ce da ko shaye-shaye tayi ba zata taba fara kwatantawa ba, ballantana kuma cikin hankalin ta, amman kuma ba zata bari wannan damar da ta samu ta wuce ta ba. Batare da sanin ya zatayi ba ta turama Hamza address dinta tana dorawa da

‘Bayan azahar yayi?’

Emoji da yake nuna ‘ok’ ya turo mata. Ta saka hannu tana goge zufar da take tsatssafo mata, kafin ta lalubo Dimples, dan tasan Biebee tsaf zata sami Anty ta gaya mata ga abinda yake faruwa idan ta hanata bataji ba, inma fada zasuyi suyi, sun shirya daga baya. Amman zatace da wani abu ya sameta gara sun daina magana.

‘Dee saurayi nayi haka. Ya hadu da komai dai, so yanzun yana tambayata zamu fita cin abinci, kinsan Anty ba zata taba bari ba, bansan karyar da zan ba wallahi’

Tana ganin kawunan hararar da Dimples din ta turo mata

‘Babu shinkafa a gidanku ne halan?’

Yar dariya Hindu tayi duk da batajin nishadi

‘Kefa banza ce matsalar, me zance mishi?’

Harar dai ta sake turowa

‘Ki fada mishi gaskiya, yazo kofar gidan ubanki ya sameki, kuna da shinkafa a gidanku, idan ita yake marmari ki zuba mai a plate ki fitar mishi da ita. Amman karki fara bin saurayi yawon cin abinci, ba kowacce wayewa bace abin kwaikwayo.’

Sauka Hindu tayi daga whatsapp din, Dimples ba zata taba ganewa ba, Hauwa ta kira tana fada mata abinda ta fada ma Dimples din

“Babe… Yazo gida zaifi fa.”

Kai Hindu take jinjinawa

“Nasani wallahi, amman banason blowing wannan chance din, Hauwa yamun, irin yamun ba kadan ba. Dan Allah ki taimaka mun.”

Tana jin Hauwa ta sauke numfashi, kafin su tsayar da magana akan dabarar da zasuyi Hindu din ta fita ko da na awa dayane. Ta sauke wayar da murmushin nutsuwa a fuskarta, tana tsintar kanta da kashe system din gabaki daya, bata da wata natsuwar da zata cigaba da kallo, gara suyi hira da Hauwa ta tayata zaben abinda ya kamata ta saka, tsikar jikinta sai mikewa take saboda excitement, ta kasa yarda da cewar itace zata ga Hamza Abu Abbas gobe.

*****

“Wai murmushin me kakeyi?”

Fodio ya tambaya da mamaki bayyane a fuskar shi, sai da Hamza ya gyara zaman shi akan doguwar kujerar da yake zaune ya mike kafafuwan shi, hannun shi da kofin da ya zuba giyar da turawa kema laqabi da beer. Saboda bayaso ya rike kwalbar, a samu akasi AbdulHafiz ya shigo. Tun randa yasha wiwi a cikin gidan yana nan, har yanzun baya sakar mishi fuska. Wata magana mai tsayi ma bata hadasu ba, gara jiya da suka hadu wajen aiki sunyi magana kan project din da suke kanyi na zanen Estate a jahar Kano da ya samo musu daga gwamnatin tarayya.

“Ba zaka gane ba.”

Cewar Hamza yana cigaba da danna wayar shi, hira yake da Hindu, abinda a sati daya ya fara zame mishi jiki, duk yau sau daya sukayi magana tace mishi tana makaranta, yanda yaita duba wayar shine yasa ya yanke hukunci fara yi mata magana. Dariya yayi yanzun kam mai sauti, bakomai yakan saka shi dariya haka ba.

“Allah mai iko.”

Fodio ya fadi yana kallon Hamza daya daga waya ya kara a kunne da alamun kira yakeyi, tashi wayar Fodio ya sauke daga kunnen shi yana sauraren hirar da Hamzan yakeyi da shigowar kiran Anna yasa shi yima Hindu sallama yana kashewa, ya kira Ann din yaji ko lafiya.

“Mai gyara ya kawo mun mota ta yanzun.”

Ta sanar dashi, ya jinjina kai, dan sunyi waya, ya rigada ya bashi kudin gyaran tun kafin ma ya gama.

“Yawwa to, ki hau kiji, in batai miki yanda kike so ba saiki fadamun”

Hamza ya fadi kafin Anna ta kashe wayarta. Ya siyo motoci har biyu da kannen shi zasu dinga yawon su a ciki, amman baisan me yasa suke son daukar mata mota ba. Duk da bayason musu fada, amman wannan karin ya sauke musu sosai, idan suka gama aikin da sukeyi aka basu kudinsu, zai sai mata sabuwar mota, sai su karata da wannan din da suke naci.

“Zaka fara magana ko sai na nemo wanda zai mun hacking wayarka?”

Kallon ‘Baka da hankali’ Hamza yaima Fodio daya daga mishi girar shi duk biyun

“Kayi budurwa ban sani ba.”

Kai Hamza yake girgizawa

“No… Nope…. Ba budurwata bace ba, kawai muna magana ne”

Dariya Fodio yayi mai sauti

“Kai? Hamza, kai? Kake magana da mace, kiranta kayi fa. Banda Mansura ka fadamun macen da kake magana da ita?”

Dan dakuna mishi fuska Hamza yayi

“Ina magana da wasu mata mana.”

Ganin Fodio na mishi kallon ‘Nine fa, karka raina mun hankali’.  Shisa ya dora da

“Ok, naji, ina magana da ita saboda tamun kyau, ba budurwata bace, ina so in tasting ne kawai.”

Sosai Fodio yake dariya irin ta gogaggun yan duniya

“Yanzun ka fito mun a mutum, me yasa ka tsaya kana wani boye-boye to, ka taya kawai.”

Kai Hamza ya girgiza mishi

“Ina ganin ta ba kamar sauran ba, ina so mu hadu ma bansan ta inda zan fara ba, ni ban saba neman su ba kasani, su suke nemana.”

Kai Fodio yake girgizawa yana mika ma Hamza hannu, da bai musa ba ya mika ma Fodio wayar yana furta.

“Hindu”

Fodio ya jinjina mishi kai, ko mintina biyar baiyi ba ya mikama Hamza tare da fadin

“Ga address dinta nan, zaku fita cin abinci gobe.”

Dan ware mishi idanuwa Hamza yayi yana amsar wayar ya duba hirar

“Woo Maza…”

Tashi wayar Fodio ya dauka yana dafa kujera ya mike, dan zaune yake kan kafet

“Kai ni yunwa nakeji, in zaka taso muje.”

Kai Hamza ya girgiza mishi

“Kamun take away. Zan danyi abu.”

Wucewa Fodio yayi batare daya amsa ba, Hamza kuwa murmushi yayi, da gaske yake da yace ma Fodio yana son dandano ne kawai a tare da Hindu, saboda yanda ta manne mishi a kai, yana son fitar da ita, bashida lokacin wannan a yanzun. Akwai matakin da yake son kaiwa tukunna, ginin da yakeyi ma bai karasa ba, saiya kammala tsaf, yaji wasu miliyoyi a account din shi, saiya nemo wata ‘yar ustaziya ya kawo ya ajiye dan Anna ta kwantar da hankalinta da maganar aure da ta fara yi mishi.

*****

Wasu kayoyi takeji sun mata tsaye a cikinta tun da ta tashi, gashi ko baccin kirki bata samu tayi ba, saboda tunanin yanda yau din zata kasance, dakyar ta samu bacci da safe, shima zuwa goma da rabi harta tashi, ta fita kitchen ta samu Asma har tayi wanke-wanke ta wuce Islamiyya abinta. Ko da suna gida, ko da Hindu bata da wani abin da zatayi, Asma bata jiranta, sam basa raba aiki, ita Asma bata da son jiki, ko Anty na fada. Hindu kam in zata iya gujema aiki tsaf zata guje mishi.

Shayi ta dan sha da biredi kadan, dan sam batajin yunwa, ta koma falo tana zama, daga Anty sai Khadee suna kallon Hanyar Kano da aka saka a tashar Arewa. Itama zama tayi suna yin kallon tare, lokaci-lokaci take kallon wayarta da tabar ma Hauwa sakon ta kirata tana zaune kusa da Anty. Zuwa can kuwa Hauwar ta kirata, daga wayar tayi tana sakawa a speaker

“Yan mata, ya ake ciki?”

Hindu ta fadi

“Lafiya kalau, ya su Anty da kowa?”

Hauwa ta amsa ta dayan bangaren

“Suna lafiya, tana ma jinki.”

Ta karasa tana mikama Anty wayar suka gaisa da Hauwar, tukunna ta sake miko ma Hindu

“Ke kinji Aboje wai yau zaiyi lecture din shi ko? Karfe daya ne ko biyu, banma duba ba sosai.”

Dakuna fuska Hindu tayi tana cire wayar daga speaker ta kara a kunne

“Kice mun wasa kike, dan ban niyyar zuwa makaranta ba yau, ni zan rage zane ne ma fa da in danyi karatun test.”

Cewar Hindu tana jin yanda Anty take binta da idanuwa kamar ta gane shirine duk maganganun nasu, amman da gaske ne akan saka musu lecture ranaku irin haka. Ko idan suna presentation, yakan kai daga Alhamis har zuwa Asabar, ba bakon abu bane ba daman. Wata rana ma in sun kai Magriba wani a gidan kanzo ya dauketa su dawo. Bata taba karyar tana da aji ba sai yau, shisa ta tsargu, tana sauke wayar ta zabga uban tsakin da yasa Khadee yin dariya.

“Yarinya sai a tashi a fara shiri.”

Hararta Hindun tayi.

“To Hajiya, ai sai da azahar akace ba wai yanzun bane, bari in tashi in rage wani abin kawai.”

Hindu ta karasa tana mikewa kamar ranta ya baci da maganar fitar da zata yi

“Karatu sai da hakuri daman ai, wata rana sai kiga kamar ba’ayi ba.”

Anty ta fadi, dan wani lokacin har tausayin Hindun takeji, duk idan taga alamar haske a dakin su idan ta fito, ko ta shiga dubasu taganta tsakiyar dare tanata faman zane da takardu a gabanta, karatunsu ba mai sauki bane ba.

“Allah dai ya nuna mana mu gama din mu huta.”

Hindu tai maganar tanajin wani bargon rashin gaskiya daya lullubeta da karyar da tayiwa Antyn. Kafin Anty da Khadee su amsa da

“Amin…”

Hindu na wucewa daki tabarsu anan, tana shiga ta tura kofa ta tsugunna tana mayar da numfashi, zuciyarta na harbawa kamar zata fado daga kirjinta saboda tsoron da take ciki.

“Wooo… Allah nagode maka.”

Ta furta tana mikewa, sun gama magana da Hauwa, tace mata ta saka wandon pallazo, sai ta saka dogon hijab da takalma masu tsini, ta dauki jaka da zata tafi da shigar, ta dora tabaranta, karta cika wata kwalliya mai yawa, jambaki ma zaiyi, dan zai iya dauka cewa tayi kwalliyar ne kawai dan zasu hadu. Shisa take bala’in jin dadin kawancen su da Hauwa. Ba magana ta cika ba, asalima randa yan miskilancin nata suke kanta, tana iya wuni da fuskar nan tata a murtuke, kawai tasan kayane, ta kuma yarda da shigar alfarma, wanda basu santa ba zasuce ko tana karyane, kuma ba haka bane, da dukkan gaskiyarta take gayu, saboda bata son harkar zubar da girma.

Bata da hijabi, amma Asma nada su kala-kala, dan ita duk shigarta da Hijab takeyi, kuma doguwa ce sosai, tama danfi Hindun tsayi. Harma ta zabi hijabin da take so din ta dauko ta ajiye, sauran kayan ta fito dasu tana hadawa waje daya. Ganin lokaci yaki mata saurine yasa ta yanke hukuncin yin zane, dan yafi komai sa taga saurin lokaci. Aikam kafin kace wani abu har karfe daya ta saura kwata. Ta mike tana kara watsa ruwa ta dauro alwala, lokacin data dan murza mai da hoda a fuskarta har an kira sallah. Gabatar da azahar tayi tana yin azkar din bayan sallah tayi addu’a tana dorawa da

‘Allah Ka san duk abinda yake a zuciyata, Ka san Hamza ne kalar mijin daya dace dani, Allah Ka tabbatar mun da mafarkina. Allah kasa wannan karin shine karshen wahalata, Allah Ka haskani a zuciyar shi, idan yana da wata ma ta fice fit daga ran shi, Allah kasa gabas, yamma, kudu da arewa idan Hamza ya juya kar yaga kowa, kar yaga komai Saini.’

Sabonta ne, shisa ta maimaita sau uku tana rufewa da Salati dan ya tunkuda mata addu’ar tayi saurin karasawa da sauri. Sannan ta mike tana sake kaya. Batasan ko ita kadai bace, ko dan ba zata ga muninta ba, amman tayi ma kanta kyau a mudubin data kalla, alamar shigowar text taji ta karasa ta dauki wayar.

‘Zan karaso nan da mintina sha biyar ko sama sa haka kadan.’

Murmushi tayi tanajin wani abu ya kulle a cikinta duk da farin cikin da take ciki.

‘Ok’

Ta amsa shi, dan batasan meya kamata tace ba, mintina goma ta bashi, tukunna ta saka hijab din da ruwan kasa ce mai haske, yadin mai yashi, sai roba da aka saka a jikin hannun, sosai taga tayi kyau, ba kadan ba Asma take mata kyau a cikin shigar hijabanta, kawai dai ita tafi jin dadin saka abaya ne. Tunda duka biyun sun rufe jiki yanda ya kamata. Tabaranta ta dauka na gayu ruwan kasa mai cizawa tana sakawa, sai taga ta fito a yar gayu sak yau, fiye da kullum, sannan ta saka takalminta baqi tana daukar bakar jaka ta sakala a jikin tsintsiyar hannunta, turare mai kamshin sauki ta fesa, ta cire tabaran tana rikewa a hannu, daman duk ta saka abinda take bukata a jakar harda wayarta, sannan ta fito.

Taji dadi sosai da taga Anty na sallah, dan haka ta furta.

“Na wuce Anty, saina dawo.” Tana jan kofar ta fice daga gidan tana sauri, dan gani takeyi kamar Anty zata idar da sallah ta fito tace mata ta dawo tasan karya takeyi, sai da tabar gidan tana karya kwana sannan ta saka tabarau din a fuskarta tana takawa zuwa bakin hanya, sannan ta ciro wayarta daga jaka dan ta kira Hamza tace mishi ya tsaya a bakin hanya karya shigo kwanar gashash street din, ta fito.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×