Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Sha Daya

2.5
(2)

<< Previous

“Na hango ki.”

Hamza ya fadi yanda ya sauke kalmar ‘G’ din da take cikin ‘Hango’ din na fito da fulatancin da yake harshen shi, ita kam ta cikin tabaran fuskarta take yawatawa da idanuwa ko zata hango shi

“Ban ganka ba ni kam.”

Cewar Hindu tana danne tambayar da take sonyi mishi ta kowacce irin mota yake ciki. Bataso ya fassara tambayar da ko tana so tajini dan tasan darajar da zata dora motar tashi a kai.

“Zaki ganni nan da mintina biyu, zan yo kwana ne…”

Titi take kallo sosai, zuciyarta na lugude kamar zata fito daga kirjinta.

“Gani nan afuwan…yanzun nan.”

Hamza yake fadi cikin sigar da yasata yin yar siririyar dariya, tana jin wani irin shauqi na lullubeta da batasan daga inda yake tasowa ba. Kafin ta hango wata mota ruwan madara kirar Range Rover da baqin gilasai da akema laqabi da tinted, ta tsaya a gabanta.

“Gani nan na karaso.”

Taji muryar shi a kunnenta ta cikin wayar, kafin ya sauke gilashin motar hadi da sauke wayar daga kunnen shi, yana saka Hindu jan wani numfashi da taji yaki kai mata inda ya kamata. Da alama suspenders ne a jikin Hamzan, dan tana ganin belt din kayan dayake a kafadun shi ya zagaya zuwa bayan shi inda take da tabbacin yana maqale a mazaunin shi jikin wandon shi, rigar shi fara kal mai dogon hannu, ya dora hular hat daya dan tura baya, idanuwan shi kal-kal dasu kamar bai taba cin karo da hayaqi ba, tamkar hawaye basu taba zama a cikin su ba balle su bata asalin hasken da suke dashi.

Yanayin fatar shi yafi komai ba Hindu mamaki, batasan ko idanuwanta bane kawai suke ganin salqin da yakeyi saboda kyawun da yai mata. Bata taba yarda da cewa mutum na maka kyau har kaji numfashinka na tsai-tsayawa ba sai yau, sai yanzun da ta rasa yanda zatayi ta dauke idanuwanta daga kan Hamza.

‘Kice wani abu mana Hindu.’

Wata murya ta fada mata a cikin kanta.

‘Ki daina kallon shi kamar wata sakarai, kice wani abu.’

Muryar ta sake fadi, amman ta kasa ko motsin kirki balle ta iya furta wani abu. Hamza kuwa tun da ta fada mishi kalar Hijab din da take jikinta ya fara hangota, daga farko zai karya idan yace, kalmar ‘Hijab’ din data furta bai mishi wani iri ba, fita yace zasuyi suci abinci, ba wajen wa’azi yace mata zasuje ba. Duk da hotunan da take dorawa da Abaya a jikinta, banda dankwalin kanta wasu lokuttan ba zaice ga kalar kayan da yake kasan Abayarta ba. Amman ‘Hijab’ ta mishi wani iri sosai. Bayason harkar rashin wayewa, tashin farko da suka fara magana batayi mishi kama da local ba.

Sai da ya zagayo ya hangota sosai, sai yanzun kuma daya sauke gilashin mota yake kare mata kallo, bai taba tunanin mace zata saka Hijabi tayi mishi kyau har haka ba, duk da zaiyi komai dan ya daga hijabin yaga abinda take boyewa a kasan shi, amman tayi mishi kyau babu karya. Tabaran da ta sakane ya hana mishi ganin idanuwanta. Murmushi ya tsinci kanshi da yi hadi da fadin,

“Muje?”

Sai lokacin Hindu ta iya daga mishi kai, tana samu ta motsa kafafuwanta dakyar ta zagaya ta bude murfin motar ta shiga. Wani irin kamshi mai sanyi na dukan hancinta. Haka kawai ta tsinci kanta da yin murmushi, zuciyarta take so ko yayane ta tsagaita da dukan da takeyi. Amman kamar da Hamza yaja motar ma zuciyarta kara dokawa tayi.

“Kin san yunwar da nake ji? Banyi breakfast bafa.”

Hamza ya fadi saboda shirun motar yayi mishi yawa. Kuma da gaske bai karya ba, wani irin bacci yayi, sanda ya tashi kuma ana jiran shi a wajen aiki. A gurguje ya shirya ya fita, yanzun ma sai da yazo zai taho yaga AbdulHafiz ya daukar mishi mota yabar mishi wannan da yake ciki, baisan me yasa yake son daukar mishi mota ba, ta AbdulHafiz din har tsada da komai tafi, sai yace ta mishi girma, dan Yayan shine ya bashi kyauta shisa yake dauka, bawai dan yana so ba.

“Me yasa?”

Hindu ta tambaya tana wasa da yatsun hannuwanta, rage gudun motar Hamza yayi yana dan kallonta kafin ya mayar da hankalin shi kan tuqin da yake yi.

“Ba zamuyi haka dake ba, ba zaki fara mun kunya-kunya ba, bana so, ba zamu shirya ba idan kikace zaki fara jin kunyata.”

Wannan karin dago kai tayi tana dan juyar dashi ta kuwa yi sa’a shima ya juyo da nashi kan suka hada idanuwa, nata zata sauke yadan girgiza mata kai.

“Bance kunya ba abu bane me kyau, bana sone kawai. Don’t be local mana Hindatu.”

Dan tari tayi kadan tana hadiye yawu saboda tunda take ba’a taba furta sunanta cikakke da yanayin da Hamza ya furta ba, tsallen da zuciyar ta tayi sai da tajita a makoshinta. Har wani zazzabi takeji yana shirin saukar mata. Kuma shi gaskiya ya fada mata, shisa duk tunanin shi, duk yanda ya hango da wahalar gaske ya iya auran cikakkiyar bahaushiya, bayason gidadanci, idan tace wannan sunkuyar da kan, amsa mishi magana dai-dai zata dingayi, yaune ranar karshe da zata sake ganin shi, zai kokarin hadiye kwadayin shi a kanta dan ba zai iya ba.

Kuma zai karya idan yace bata burgeshi ba, kominta yayi mishi, komai nata yasa shi son daga hijabinta yaga sauran sirrikan da suke tattare da ita. Amman hakan ba zai yiwu inta fara da jin kunyar shi ba. Itama kokari takeyi taga tadan ce wani abu, amman yaune karo na farko da ta taba kebewa haka da wani namiji da ba muharraminta ba, a mota su kadai suna nufar inda bata ma sani ba.

“Ina zamu je?”

Ta bukata, tana saka Hamza sauke numfashi, yadan daga mata kafadun shi.

“Ina kike so muje? Na fada miki yunwa nake ji ko?”

Yar dariya tayi tana daga mishi kai.

“Good… Ina ya kamata muje?”

Dan jim Hindu tayi, ita ba wani wajajen cin abinci ta sani ba

“Duk inda kake so.”

Dan kallonta yayi yana daga girar shi duk biyun.

“Kin tabbata?”

Ta jinjina mishi kai, yanda yake kallonta duk da na wasu dakika ne ya sa gwiwoyinta kamar an bubbuge su da guduma, duk sunyi mata wani irin sanyi. Yanda yake abubuwa kamar baisan komai kara mishi kyau yake ba na kara sakawa ya burgeta matuka. Numfashi ya sake saukewa, yana yanke hukuncin zuwa Byblos Restaurant da yake Abakpa, ta wajen Waziri Ibrahim Crescent. Suna da abinci kala-kala na kasa Najeriya, Lebanese harma da Mediterranean. Indai ba sauri yake ba yakan zo nan, wasu lokuttan kuma yai order tunda suna kaiwa har gida.

“Kin gama assignment din jiya?”

Kai Hindu ta girgiza mishi.

“Na ajiye, Electric nake son karasawa in huta.”

Murmushi Hamza yayi.

“Oye ko?”

Hindu ta daga mishi kai suna dariya su biyun.

“Mutumin nan ya bata mana lokaci ba kadan ba.”

Idanuwanta ta juya.

“Kai ma kenan daka gama, kuma ance zai mana Settlement ne ko meye next semester.”

Sai da Hamza yadan kalleta cike da tausayawa yana girgiza kai sannan yace,

“Hindu”

Wannan karin ita ta dan kalle shi

“Oye zai kashe ku.”

Yanda yayi maganar ya bata dariya sosai, hira suke zaka rantse da Allah sunyi shekaru da sanin juna, ba yau bane haduwar su ta farko. Hamza na cikin mutanen da zasu sa ka sake dasu lokaci daya, bashida wahalar magana, kuma yasan yanda zai jaka da hira ko da bakayi niyya ba. Ba Hindu kadai taga haka ba, abokan shima sunfi so yayi magana da mutane a wajen aiki, musamman idan akace cinikin kudin aikinsu za’ayi. Sai kayi mamakin kudin da Hamza zai caji mutane kuma su biya suna fara’a. Yana da wannan baiwar ta samun abinda duk yake so a wajen mutane, saboda zai nuna maka kana da wani irin muhimmanci da bakasan kana da shi ba.

Yanzun a yan mintina kasa da ashirin daya dauke su zuwa Byblos Restaurant, Hamza yasa Hindu tanajin kamar tana da wani muhimmanci mai girma a wajen shi, a cikin hirarsu ya tabbatar tasan irin aikin daya tsallake ya fito, har saida taji kamar bata kyauta ba, kamar ita dince ta roki ya fito bashi da kanshi ya nemi ganinta ba.

“Da ban sa ka fito ba, ba zaka sami matsala a wajen aiki ba dai ko?”

Hindu ta tsinci kanta da fadi lokacin da Hamza ya sami guri yayi parking din motar, dan gabaki daya yasa taji bata kyauta mishi ba daya fito. Sai da ya murza mukullin motar yana kashewa, ya daga gilasan tukunna ya girgiza mata kai.

“Karki damu, it’s worth it, nagan ki fa, shine abu mai muhimmanci yanzun.”

Murmushin jin dadi Hindu tayi, tana kallo ya bude murfin motar, itama hakan yasa ta bude nata bangaren tana fita. Sosai take jinta sama-sama. Tunda take babu wanda ya taba fada mata magana mai dadin wanda Hamza ya gaya mata yanzun. Ta jira Hamza ya zagayo, tana karema shigar shi da tayi matukar burgeta kyau, duk da takalman da suke kafarta ko kafadun shi kanta bai kai ba, dogone, tsayin shi fiye da wanda take mafarkin samu, hannun shi ya mika mata yana kankance idanuwan shi kamar yana so taga yanda girar shi take a ciki, da mamaki ta dakuna fuskarta, dan batasan me zata bashi ba, sai da taga ya matso dab da ita yana saka zuciyarta wani irin dokawa.

Jakar da take sakale a hannunta yadan kama, tana amfani da dayan hannunta ta zare jakar cikin sauri, dan batason abinda zaija ya tabata, sosai zuciyarta take mata wani irin lugude. Hamza nazarin duk wani motsinta yakeyi, amman baya iya ganin idanuwanta ta cikin tabaran balle ya fahimci kadan cikin abinda take tunani. Da dayan hannun shi ya rike jakar yana jerawa da ita hadi da fadin,

“Muje?”

Kai Hindu ta daga mishi, duk da bugun da zuciyarta yakeyi a cike take taf da wani irin yanayi. A film kadai ta taba ganin namiji ya karbarma mace jaka, ko a tarin burinta bata tsawwala da abinda ake kira ‘Public affection’ ba, wato nuna kulawa ko kauna a bainar jama’a. Saboda abune da bai saba faruwa a Najeriya ba, duk kuwa kalar kaunar da take tsakanin masoya, ta hasaso faruwar abu irin haka idan suna kasar waje lokacin honeymoon dinsu, inda zasu barji soyayyar su batare da fargabar sa idon al’ummar Najeriya ba. Jerewa sukayi har cikin wajen, Hindu najinta kamar wata Sarauniya, musamman yanda Hamza yake janta da hira kadan-kadan suna murmushi.

Sai ta hango hannunta sakale cikin nata, ta hango yara biyu, daya a gefen shi daya a gefenta, a lokaci daya tana hasosu yanda rayuwar auren su zata kasance, kafin taji muryar Dimples na katse ta da.

‘Sannu Hindatu Khan Bachaan’

Kamar yanda takan fada mata idan tana wani zancen soyayyar, ko tana fadar abinda zasuyi ita da mijinta. Dimples kance indiyawa sune karshe dai a soyayya. Kuma Hindu batajin hakan, dan Korea sun shallake indiyawa ta wannan fannin, nesa ba kusa ba, amman gaddama da Dimples babu riba, shisa bata taba kwatantawa ba. Ko da zasu zauna ma, Hamza da kanshi yadan janyo mata kujera bayan ya ajiye jakarta akan tebir din da yake gabansu, yana zama ya kama bayan kujerar yadan tura, sannan yaja tashi ya zauna yana fuskantarta kamar bai lalata mata duk wata fita da zatayi da wani namiji da bashi ba har karshen rayuwarta. Dan sosai zata dinga auna duk wani abu da zai faru da wanda ya faru a tsakanin su.

Hamza take kallo da har lokacin yaki nuna alamun yayi mata wani abu, asalima yanda yake nunawa kamar abinda ya faru ba bako bane a wajen shi, kamar abune da yakeyi yau da kullum, ga restaurant din ya kawatar da ita. Waiters din gurin tsaf-tsaf dasu, daya daga ciki yazo yana kawo musu Menu, amman sam Hindu ta rasa abinda zata ce a kawo mata, dan bama taji yunwa kwata-kwata, hakan yasa ta yanke hukuncin zabar hadin salad. Sai a zabin abin sha ta dauki cocktail. Gira Hamza ya daga mata da yasata dauka hakan sabon shine, dan yayi yafi a kirga daga haduwarsu zuwa yanzun.

“Me kike nufi? Iya abinda zakici kenan?”

Kai Hindu ta jinjina mishi tana dorawa da

“Banajin yunwa”

Yanda ya tsareta da idanuwa yasata dan shagwabe mishi fuska

“Da gaske?”

Kai ya girgiza mata

“Ba zaki kalleni ina cin abinci ba aikam.”

Da kanshi ya kara cewa a hado mata da kaza sai spaghetti. Sannan ya zabi nashi shima, waiter din na tafiya dan ya kawo musu abubuwan da suka zaba din, gyara zama Hamza yayi

“Is not fair kina ganin gabaki daya fuskata ni bana ganin taki.”

Murmushi Hindu tayi a kunyace, kafin tayi wani yunkuri Hamza ya mika hannun shi ya kama tabarau din fuskarta ya zare, yana sauke idanuwan shi cikin nata da suka firfito da alamar tsoro, tana tabbatar mishi da zaton da yakeyi a kanta. Ita din ba kamar sauran matan bace ba, Hindu dabance da duk wasu mata da ya taba cin karo da su, kan tebir din a kusa da ita ya ajiye gilashin yana fadin,

“Hakan yafi.”

Yasa ta sauke idanuwanta daga cikin nashi, wayarta taji tayi vibrating alamar shigowar sako, hakan yasa ta daukar jakarta tana ciro wayar. Bude sakon tayi ta whatsapp tana ganin a class group dinsune wani ya turo zanen da yakeyi dan a duba mishi ko da kuskure. Hamza ita yake kallo, bai saba yana zaune da mace hankalinta na wani waje banda kan shi ba, bama yaso kwata-kwata.

“Baki san ba kyau kina tare da mutum ki dinga danna waya ba?”

Cike da sabon mamakin shi Hindu ta raba idanuwanta da wayar tana kallon shi

“Ko waye ya jira sai bama tare, karya shigar mun lokacina dake, bana so…”

Ya karashe maganar cike da ikon da kyawun da yai mata bai hanata ganin karfin halin shi ba, data dinta ta kashe tana mayar da wayar a jaka.

“Nagode.”

Hamza ya fadi yana sata cewa

“Kana da rigima.”

Dan daga mata kafadu yayi

“Nasani, kawai bai dameni bane tunda rigimar nasani samun abinda nake so.”

Siririyar dariya tayi, ko a littatafai kuwa bata tunanin ta taba ganin kalar shi, tunda yawancin mazan novel basa magana, ita ya kamata ace tanata mishi surutun da tasan ba zata iya ba, amman shi yake ta mata magana bai damu ba, ta dauka tana son namiji shiru-shiru sai yanzun da Hamza yake zaune a gabanta. Abincin su da ya saukane ya ceceta, dan batasan amsar daya kamata taba Hamza ba. Kallon abincin takeyi tana ganin kamar daga Instagram aka ciro shi aka ajiye a gabansu saboda yanda ya kawatu.

Robar ruwa Hindu ta bude tana dan kurba saboda yanda taji makoshinta ya bushe. Tana kallon Hamza ya fara cin abincin shi a nutse kamar bashi da wani abu mai muhimmanci daya wuce cin abincin, itama salad din ta faraci kadan, tana jin yanda yake dira cikinta da wani irin yanayi. Hamza na kallonta ta kasan idanuwan shi, sai dai baya surutu idan yanacin abinci, bama yaso wani yai mishi wata magana, yasan bai isa ya zabi hanyar da zai mutu ba, yana dai kokarin kaucema faruwar hakan ta hanyar shaqewa da abinci. Shi bai ga dalilin da zaisa a dinga magana ba idan anacin abinci.

Ita kuma ta saba tana cin abinci tana danna waya, yanzun sai shirun yai mata wani iri, tana ganin kamar hankalin Hamza na kanta, lokaci zuwa lokaci take dago idanuwa ta kalle shi, amman sai taga abincin shi yakeci a nutse. Dakyar taci rabin salad din da yake gabanta, dan kar yace yasa an kawo mata abinci bataci ba, shisa tadan dibi taliyar tasa a bakinta, ta kuma yi mata dadi, ba zata iyaci bane ba kawai. Kazar ma kadan ta gutsira, ta ajiye cokulan tana ci gaba da kurbar lemon gabanta. Har Hamza ya gama dan kadan ya rage a tarkacen abubuwan a aka kawo mishi, wasu ma bata taba ganin su ba balle tasan sunayen su.

Masu kudi na sha’ani da rayuwar su, ta fadi a ranta

“Karki ce mun kin koshi.”

Hamza ya bukata, kai tadan daga mishi tana murmushi

“Hmm…”

Ya furta yana dorawa da

“Kin kyauta.”

Ya dauki wani dan kati da take tunanin kudinsune a rubuce ya duba, hannu taga yakai aljihun shi yana fito da wallet din shi, sai dai tayi mamakin yan dubu-dubun da taga yana kirgawa yakai na dubu goma sha, ya bude dan katin ya saka a ciki, sannan yadan kalleta.

“Muje?”

Ta bukata, ya jinjina mata kai, a tare suka mike, Hindu na daukar jakarta, da tabarau ta makala a fuskarta,har lokacin tana mamakin yawan kudin da kuma dan abinda sukaci. Suna shiga motar yaga wayar shi na ta haske, dauka yayi ya duba.

“Dammn”

Ya furta yana mayarwa ya ajiye. Yaga Hindu bata wani ci abin kirki ba, yaso su biya ko Havilah ne. Yasan mata bakowa kecin abinci irin haka ba, sunfi jin dadin ci a gida, amman Murjanatu, Autar su tasa yasan mata akwai san kayan zaki, duk da shi baya ta’ammali da kayan zaki, amman tana son desserts sosai.

“Wajen aikine…”

Yai maganar kamar yayi mata wani laifi yana dorawa da

“Nayi alkawari I will make it up to you, In shaa Allah, zamu kara samun time da aikina ba zai shigar mana ba, kina jina?”

Kai Hindu ta daga mishi tana murmushi

“Karka damu, babu komai.”

Wani numfashi ya sauke yana fadin

“Nagode”

Kafin yaja motar, yanzun ma hirar sukeyi, yana bata labarai kananu da suka shafi aikin shi, yana sa tana karajin dadin kasancewa da tayi tana karantar Architecture saboda yanda take fahimtar hirar tashi. Inda ya dauketa suka karasa yasa shi cewa,

“Ina zamu bi?”

Tun kafin ya karasa Hindu take girgiza mishi kai, bugun zuciyar data samu ya tafi ya dawo mata sabo, ta ina Hamza zai fara shiga lungun gidan su da ita, idan wani daga cikin gidan ya fito yaganta ta ina zata fara musu bayanin dalilin da yasa take cikin motar shi

“Karka damu, ka saukeni anan.”

Kallonta yayi da yake fassara ‘kice mun wasa kike.’

Ganin bata da shirin ce mishi wasan takeyi yasa shi fadin

“Saboda me?”

Hadiye yawu tayi tana sauke numfashi, ta rasa abinda zatace mishi

“Kayi hakuri kai dai, kabarni zan karasa, kaga kaima ana jiran ka.”

Badan yaso ba, ba kuma dan da gasken ana jiran shi ba, amman baiji dadin yanda zai ajiyeta a bakin hanya ba.

“Zamuyi waya. Ki kula da kanki.”

Ya karasa maganar yana dan sauka gefen titi dan suyi sallama da kyau, kai Hindu take jinjina mishi.

“Nagode sosai”

Hannun shi ya mika mata, sai dai wannan karin sauka zatayi balle tayi tunanin jakarta zata bashi, ga idanuwan shi daya kafeta dasu, haka kawai yaji idan bai rike ko da hannunta bane komai zai iya faruwa, yanayinta da komai nata yasa wasu kusoshi kwancewa cikin kan shi, ganin kallon da take mishi yasa kama hannunta, yana share yanda take kallon shi kamar shine karo na farko da wani namiji ya taba rike mata hannu, dan matsa yatsunta da yaji cikin nashi yayi. Ko ba nata ba yana son yanda hannuwan mata suke, sirara, yana son jin yatsun mace a cikin na shi, balle nata da haka kawai yake ji kamar an halicci nata yatsun ne don ya rike.

Tunda take a tunaninta tasha hango lahira, amman bata taba hangota wani sashi na jikinta a wuta ba, tana neman tsari daga wuta sau bakwai da safe, bakwai da dare a rana, idan tadan kone ko yayane takan yini tana neman tsari daga azabar wutar da batasan zata iya ba, amman yanzun kam har kaurin konewar da hannunta zaiyi a wuta takeji a hancinta, ta hango shi gashi can an kama an tsoma yana babbakewa, ta kuma rasa abinda ya daskarar da ita ya hanata yin wani yunkuri wajen hana Hamza rikewa, da ya murza yatsunta har ranta taji girman zunubin.

Tana kallon shi ya kama hannun nata yana saka labban shi cikin tsakiyar tafin hannunta ya sumbata, muryar shi can kasan makoshi ya furta

“Sai munyi magana.”

Hadi da sakin hannun nata kamar komai bai faru ba, kamar bai manni zunubai a labban shi ba, dakyar ta iya daga mishi kai tana bude motar ta fice. Hanya ta mike, lungun da zai kaita gida tana ta kokarin ganin hannun da Hamza ya sumbata bai taba ko ina na jikinta ba, karta goga tarin zunubin da taji yasa hannun yayi wani irin nauyi na ban mamaki

“Allah ka yafe mun… Oh Allah na… Me ya faru haka.”

Take fadi ita kadai kamar sabon kamu, a gefe daya na zuciyarta tana jin inda Hamza ya samu sabon waje ya manne.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×