Skip to content

Mijin Novel | Babi Na Sha Hudu

4
(4)

<< Previous

Da ya koma gida kwanciya ya sake yi, saboda yanda yakejin jikin shi, har wani zazzabin wahala ya rufe shi. Ya dauka inya sami wata zai rage abinda yakeji, amman fuskar Hindu ya dinga dorawa a ta yarinyar. In za’a yanka shi har ya baro hotel din ba zaice ga kalarta fuskarta ba, ballantana yanayinta, gangar jikin shi ce kawai ta kasance da ita, tunanin shi da ganin shi duk Hindu ce tayi kane-kane. Sosai abin yake tsorata shi, da ace baije gidansu ba, zai dauka ko aljana ce ya hadu da ita shisa ta dabai-baye rayuwar shi haka. Yanzun ma duk abinda ya durama cikin shi, bai daina ganinta tana gilmawa ta cikin idanuwan shi ba, bai kuma daina jin duminta a jikin shi ba.

Giyar yau taqi tasiri ballantana ta disar mishi hasaso lokacin daya rike Hindu a kirjin shi, daya rufe idanuwan shi sai yaji kamar har lokacin tana rike a kirjin shi. Ya rasa kalar jarabar data same shi haka. Da kyar ya iya zuwa sallar isha’i. Yaga text dinta ya share bau amsa ba, kamar yanda yaki daga kiran daya biyo bayan text din, muryarta wahala kawai zata kara mishi. Har tunanin yaje gidan su yaganta yayi, amman bayajin idan yaje zai iya controlling kan shi da abinda yakeji, kuma yana da yaqinin basuyi nisan da zai nuna Hindu asalin maitar shi ba. A hankali yake so ya jata, lokacin da zai ajiyeta ba zata san me ya faru ba, ko ya akayi ya faru.

Yanzun ma a kwancen yake a falo, kan doguwar kujera, dakin yana nan yanda su Fodio suka fita da safe suka barshi, sai robar coke da yasha rabi, yaje ya bude daya daga cikin giyar shi yana karasa cika robar da shi ya dawo falo ya ajiye. Arafat ke siyan abin zuqar lemo ya ajiye a gidan, ya dauka ya saka cikin robar coke din, bayajin dadin jikin shi, tun abincin rana rabon shi da wani abu, sai giyar da yaketa kwankwada. TV nata aiki, amman hankalin shi baya kai, tunanin shi na tare da Hindu, da abinda takeyi, sai robar coke din da yake dan dagowa yana zuqa daga kwancen a hankali, a hankali.

A haka su Fodio sukayi sallamar daya amsa can kasan makoshi, AbdulHafiz na dorawa da

“Ka gyara kwanciyar ka Malan.”

Dan ya tsani yaga daya a cikinsu yayi ruf da ciki, sai yaita ganin kamar mutuwa zata iya dirar musu cikin wannan kwanciyar da batada kyau a addinance. Numfashi Hamza yaja yana saukewa da fadin.

“Arafat baku gaji bane?”

Da kuna mishi fuska Arafat da yake cire jacket din jikin shi yayi, ya jefa kan kujera, yana kwance agogo kafin ya amsa Hamzan

“Asalin gajiya ma, kaji kasusuwan jikina kuwa”

Numfashi Hamza ya sake ja

“AbdulHafiz naga yana da sauran karfin takura mun”

Dariya Fodio yayi, AbdulHafiz ya dauki jacket din da Arafat ya cire yana jefa mishi a fuska

“Wai me yasa zaku dinga baza kaya ko ina?”

Cire rigar Arafat yayi daga fuskar shi yana rikewa a hannun shi.

“Dan Allah karka fara dani, wai mu ba Maza bane ba? Me yasa ba zamu dinga baza kaya inda muke so ba. Fodio….”

Arafat ya karasa maganar yana mayar da hankalin shi kan Fodio daya sunkuya zai dauki robar lemon da Hamza ya janye

“Ba lemo bane kawai”

Ya fadi dai-dai kunnen Fodio din, daya jinjina mishi kai, sannan ya sakar mishi robar

“Fodio kana jina fa”

Zuqar lemon yayi sosai, ya mayar ma Hamza, tukunna ya kalli Fodio da yake harar shi

“Nan gidanka ne, kai ya kamata ka fadama AbdulHafiz ya dinga kyalemu muna barbaza kaya yanda muke so”

Dagowa AbdulHafiz yayi, dan kofuna yake tattarawa, a gajiye yake, koma bayajin gajiya ba zai bata bakin shi akan Hamza ba, yasan ko dan ya saka shi magana zai iya kin dauke kwanonin. Da sauri Fodio ya daga mishi hannuwa alamar bada kai, wato ‘surrender’. Yanayin da ya saka Arafat zagin Fodio din yana dorawa da

“Matsoracin banza kawai”

Dariya Fodio yayi yana wucewa dakin shi dan ya watsa ruwa. Arafat dinma wucewa yayi, AbdulHafiz kuwa sai da ya tattara duka kwanonin da suke cikin dakin yakai kitchen, tukunna ya dawo yana wuce Hamza batare da yace komai ba, kara gyara kwanciya Hamza yayi yana zuqar lemon shi har lokacin. Wayar shi da yaji kararta alamar shigowar sako, yasa shi miqa hannu ya lalubota daga gefen shi, yana dubawa. Hindu ce

‘Ina ka shiga haka? Kana lafiya dai ko?’

Birkitawa yayi, yana kwanciya kan bayan shi

“Bana lafiya wallahi, ke nake bukata a kusa dani”

Ya furta a fili, yana tura mata.

‘Inata hidima, kuma banama jin dadi dai’

Wayar ya saka a silent, yana sakata a key ya ajiye a gefen shi, text din da sukai musaya kawai na neman sake birkita shi. Sauran lemon ya karasa shanyewa, yanajin kan shi yayi nauyi sosai. Idan ya kara zai iya buguwa fiye da yanda yake so. Ba zai iya hada abu biyu a lokaci daya ba, tunanin Hindu kawai ya ishe shi, ba saiya hada da fadan AbdulHafiz da bazai kare ba, idan ya gan shi a buge. Da zai sha har sai ya daina gane abinda yakeyi. Ba zaice ga iya lokacin daya dauka ba, yanajin shige da ficen su Fodio duk da idanuwan shi a lumshe suke. Sai da yaji Fodio na kiran

“Kai ba zaka ci wani abu ba?”

Idanuwan shi ya bude da yakejin sunyi mishi nauyi sosai

“Bana jin yunwa nikam.”

Ya furta yana kara gyara kwanciya, Fodio na shi ya dauka yana fadin

“Sai da safen ku.”

Arafat daman a fridge yaje ya saka, shi yaci samosa da lemo a hanya. Bacci kawai yake son yi, AbdulHafiz suka bari da yake zaune akan kafet yana cin abincin suna hira da Nabila da take mishi rikicin aiki yasa basuyi magana da yawa ba, ganin lallashi ba zai aiki ba, yasa shi nuna mata jan ido yasa ta sauka ta kwanta, tunda tace mishi tana da makaranta da sassafe.

“Kai me kaci?”

AbdulHafiz din ya bukata, dan ya san ba bacci Hamza yakeyi ba

“Ka kyaleni dan Allah”

Hamza ya fadi cikin bacin rai, bayason wata takura koya take a yanda yake jin shi, amman AbdulHafiz ne, in baiyi niyya ba, babu wanda ya isa ya saka shi barin abu, ko ranshi kake son ganin ya baci, sai yayi niyya ne zai nuna maka

“Me yake damun ka?”

Hamzan yasan inba maganar sukayi ba, AbdulHafiz zai share duk wani abu da zai fada yaci gaba da maimaita tambayar har saiya amsa

“Bana jin dadi”

Ya amsa a taqaice yana mikewa zaune, ya runtsa idanuwan shi saboda dakin dayaga ya wulwula mishi

“Ok”

AbdulHafiz ya furta yana dan ture robar take away din da take gaban shi, dan ya koshi. Yana karantar damuwa a fuskar Hamzan, ya kuma kula da yanda yake komai a hankali, kamar yanda yakanyi duk idan yasha wani abu, bayaso AbdulHafiz din ya gane. Yana kyale shine, saboda addu’a ce kawai zata fi saurin tasiri akan shi, tunda yana kokarin boyewa, hakan na nufin akwai sauran imani a tare da shi, akwai kuma yiwuwar shiriya zata same shi a kowanne lokaci.

Kai Hamzan ya girgiza

“Ka daina mun haka”

Fuska AbdulHafiz ya da kuna mishi cike da alamar tambaya, yana saka shi nuna shi da dan yatsa

“Gashi nan, abinda kakeyi ne bana so, ka daina yi kamar ni nake so in fada maka matsalata, bayan kaine ka tambayeni”

Mikewa AbdulHafiz yayi, ya dauki robar take away din

“Sai da safe, idan kana son shawarata, kasan zaka iya kwankwasa mun kofa”

Ya karasa maganar yana wucewa abin shi, numfashi Hamza yaja, yana komawa kan kujerar ya kwanta, bayajin karfin tashi ballantana ya wuce yaje ya kwanta, kuma shi bashi da matsala da kwana akan kujera, balle Fodio ya zuba kujeru masu fadi, yana jin dadin kwanciya a kai sosai. Ya lumshe idanuwan shi, yana addu’ar samun bacci, ko zai daina tunanin Hindu da son kasancewa tare da ita.

*****

Kwata-kwata batajin dadin jikinta, duk motsin da zatayi sai taji kamar wani bangare na Hamza na liqe da ita. Sai take ganin kamar ta makara wajen tuban da tayi, kamar Allah ba zai amshi tuban nata ba, shisa takeji tamkar an tsaga fatar jikinta an tura mata zunuban da takejin nauyin su har lokacin

‘Allah Kabani karfin gwiwar ko da ture shine idan ya sake kwanta irin hakan. Allah Kaa yafe mun Ka karemun imanina’

Shine abinda take maimaitawa duk juyin da zatayi, zanen ma ganin layukan na hade mata yasa ta hakura, ga rashin maganar da basuyi ba da Hamzan ya kara sakata shiga yanayi. Lokaci zuwa lokaci take tsintar kanta da duba wayarta ko ya mata magana, itace bataji karar wayar ba. Har kallo ta fara data kwanta, ko zai dauke mata hankali, amman ta kasa, tunani ne kala-kala a ranta, musamman yanda zatayi ma Hamza magana karya sake tabata, ya hakura suyi aure tukunna, kafin ta fara tunanin ai har yanzun baima ce yana sonta ba ballantana magana irin wannan ta shiga tsakanin su.

Ganin tunani zai dameta ya sata shiga Instagram, tana ta kallon kwalliya tunda tana da wadattaciyar data, Hamza na tura mata kati har ta rasa abinda zatayi da shi. Sai dai ta siyi data ta shiga YouTube ko taje Instagram taita kallon shagalin bukukuwan da ake sakawa a shafin 9ja weddings. Abin yana kayatar da ita, wasu bukukuwan kan sata hasaso yanda nata zai kasance. Yanzun din ma abinda takeyi kenan, tana hango dinkin da za’ayi mata, sai taga notification na cewa an mata sako, da sauri ta duba ko Hamza ne, dan sha biyun dare, sai taga Ahmad ne yayi mata sallama, duk sai taji haushi ya kamata, dan har ranta ta saka ran Hamza ne.

Kamar ta share shi, saita bude ta amsa sallamar

‘Wai kinga abinda ya sami Mike?’

Da sauri ta fara bashi amsa

‘Wallahi Ahmad karka bani labari, karka batamun kallona, ka kyaleni’

Kawunan dariya ya turo mata, kafin suci gaba da hira, yana dan debe mata kewar Hamzan da takeyi. Batasan lokaci na ja bama, dan in suka fara hirar films ita da Ahmad din, ko waya sukeyi hakan ne yake kasancewa, kan abu daya daya faru a film din zasu iya kwanaki suna gardama a kai, kamar yanzun da ta dake babu abinda Mike zai nuna ma Harvey sai kwakwalwar shi, amman Ahmad din yaki yarda. Wajen daya saura, taji idanuwanta sun fara mata yaji, ta fita daga chat din su da Ahmad din taga Hamza yayi mata magana a Instagram din, kuma baifi mintina biyu da sauka ba. Amsa Hello din shi tayi, sakon na shiga tana ganin ya turo mata alamar tambaya a whatsapp.

Sai ta koma can din, kafin ta amsa shi ya sake turo

‘Bakiyi bacci ba? Me kike yi? Zane?’

Ya jero mata tambayoyin yana sakata yin murmushi

‘Aa, ina kwance ne ma, yanzun dai zanyi baccin, kai ma bakayi ba, ko aikin ne?’

Tana kallon yana rubutu

‘To me kikeyi? Bakiyi bacci ba har yanzun’

Ya turo yana share tambayar ita da tayi mishi, tasan halin rikicin shi

‘Naje Instagram ina kalle-kalle, sai kuma na tsaya muna hirar film ni da Ahmad’

Tana ganin ya dauki lokaci yana typing

‘Ahmad? Waye shi din? Har tsakiyar dare kina hira da shi? Me yasa zaki dinga magana da shi da daren nan? Akan me? Shi me yasa zaiyi hira dake da daren nan?’

Yau kam ji tayi tagaji da kishin da yake nunawa a kanta ba soyayya suke ba, baice yana son ta ba, amman ya dinga tsareta da tambayoyi, yanzun bata isa ta amsa wani a comment section ba sai sunyi rigima, ko hoto ta saka nata sai yace ta cire.

‘Kai ga shi ina hira da kai, menene dan nayi da shi? Abokina ne’

Gani tayi yana typing, ya kai mintina biyu, amman sako bai shigo mata ba, har tayi tunanin ko network dinta ne, kafin taga kiran shi na shigowa, sai da taji gabanta ya fadi, da sauri ta danna gefen malatsin wayar tana sakata a silent, tashi tayi ta sakko daga kan gadon tana zuwa ta duba kofar dakin, taga Asma bata rufe ba, ita ta murda mukullin, sanda ta koma kiran harya yanke, saiga sakon shi ya shigo

‘Ki daga wayar nan Hindatu’

Kafin ta amsa ya sake kira, dagawa tayi muryarta can kasa tana fadin

“Hello”

Ta dan runtsa idanuwanta jin yanda muryar shi ta daki kunnenta a fadace

“Ni da shi daya ne? Me yasa zaki hada mu kamar muhimmancin mu a wajen ki iri daya ne? Akan me zaki ce dan kina magana dani ko da yaushe shima zakiyi magana da shi haka?”

Tashi zaune tayi dan taga alamar rigimar Hamza yake so suyi, abinda bai sani ba shine ita kanta ta iya rigimar, kawai dai bata nuna mishi ne, tana lallaba shi, idanuwan shi kawai idan ya kafa mata sai taji duk jikinta yayi sanyi, amman yanzun bata ganin shi, zata iya tattaro kwarin gwiwarta ta fada mishi duk abinda take son fada

“Kasan ko bashi ba dole zan kula wasu ai…”

Tana jin hucin da yake har ta cikin wayar

“Saboda me?”

Numfashi ta sauke

“Saboda ni macece, budurwa kuma, ko ba abokai ba, zanyi samari”

Tana jin shirun daya biyo bayan maganarta, dan saida ta ciro wayar daga kunnenta dan taga bai kashe ba, tana ta reading, kawai shiru yayi da yasa zuciyarta cigaba da dokawa kamar zata fito daga kirjinta

“Bana so”

Ya fadi can kasan makoshi, yana sa ta sauke muryarta

“Haka zakayi hakuri… Dole zanyi samari Hamza, kaima abokina ne”

Tayi maganar da wani irin ciwo da taji ya fito daga zuciyarta, tasan karya takeyi, tana kuma addu’ar baiji yanda muryarta take rawa ba, yanda ya wuce matsayin aboki a wajenta, tana son shi, tana son shi fiye da yanda take tunanin soyayya take, tana son shi har mamaki abin yake bata.

“Kibari, bana so, karki sake hadani layi daya da abokan ki”

Cike da gajiyar da takeji har a kasusuwanta, da kuma kukan da take son tarbewa tace

“Ina kake so in ajiyeka? Ka fadamun inda kake so in ajiyeka”

Shirun ya sake biyo baya, fiye da na dazun, kafin kamar wanda aka shaqe yace

“Ki ajiyeni a saurayin ki, karki hadani da kowa, bana so, karki hadani da kowanne namiji. Wallahi zamu sami babbar matsala”

Murmushinta da wasu hawaye masu zafi ya bayyana, tasa ka hannu tana share su, tana jin yanda zuciyarta take tsalle-tsalle

“Ahmad da wa kike hira cikin daren nan?”

Kai ta girgiza tana danyin gyaran murya kafin tace

“Shi kadai ne”

Da sauri ya amsata da

“Ban yarda ba”

Kafin ta amsa ya sake cewa

“In gani”

Yana kashe wayar, Hindu ta sauketa daga kunnenta tana binta da kallo, kafin sakon shi ya shigo mata ta whatsapp

“Menene Password dinki?”

Tsintar kanta tayi da tura mishi

‘HAlamin’

Tana cigaba da kallon wayar, baifi mintina biyar tsakani ba, ta sake ganin ya mata magana

“Jibi tarin mazan da kike magana da su, Hindu kina so ki kasheni ko?”

Murmushi tayi, bata san abinda zatace mishi ba, can ta sake ganin yayi magana

“Kina Twitter daman? Me yasa wannan banzan yake tambayar handle dinki?”

Batama san waye yake magana akai ba, ikon Allah kawai take kallo, kafin taga notification din twitter alamar anyi following dinta, tana dubawa taga Hamza dinne, shisa ta neme shi bata gan shi ba a Twitter, HAbuAbbas ya saka a handle din. Bin shu tayi itama, tana fara duba tweets din shi, duk yawancin hirarrikin shi da abokan shine, sai wata Mansy_ da taga suna magana, ta bude profile dinta tana duba hoton ta, sai da taji gabanta yayi mummunar faduwa ganin hoton jikin Avi din Mansy din ita da Hamza ne, da alama ita ta dauka, dan Hamzan yana bayanta ya daga girar shi duka biyun da murmushi a fuskar shi.

Da sauri ta koma tana sake duba hirarrikin nasu da bata fahimta, dan yawanci da yaren fulatanci duk maganganun da sukayi yake. Handle din Mansy din ta sake komawa tana shiga gabaki daya hotunan ta da sun kai dari takwas, tana kuma matuqar mamakin ganin wajen kala talatin duk tare da Hamza ne, sai wasu da yawa kuma nashi ne shi kadai. Zuciyarta ta so gaya mata kanwar shi ce, amman kuma yanayinta ya nuna zata iya zuwa shekaru daya da Hamzan, dan ba yarinya bace ba, kuma kanwar shi ba zata saka hoton su da caption din ‘Me and Mine’ ba. Ta kira shi nata a yawancin duk hotunan da ta saka nasu, kuma bata ga inda ya gyara mata ba.

Kanta taji ya fara sarawa saboda tashin hankali, tsintar kanta tayi da dawowa Whatsapp inda Hamzan yabar mata tarin saqonni yana mata tambayoyi akan mazan da suke DM dinta na Instagram din

‘Wacece Mansy?’

Ta tambaya, bai ko numfasa ba ya dawo mata da amsa

‘Qawata ce’

Yana dorawa da

‘Mariya24’

Kafin ya sake cewa

‘Shine password dina na Twitter, ki duba kigani, banda abinda zan boye miki’

Numfashi Hindu ta sauke da batasan tana rike da shi ba, duk da ta sami waje a layin mutanen da ta tsana ta saka Mansy a saman dukkan su, zata hau twitter din tagani kamar yanda yayi ikirarin bashi da abinda zai boye mata. Gara ta tabbatar dai, amman ba a daren nan zatayi haka ba. Sai da safe, zuciyarta gara ta nutsu waje daya. Kar ta buga da irin tsallen da taketa faman yi, yau zata kwanta da nasara guda daya, zata iya nuna ma kowa Hamza ta kuma kira shi da saurayinta, wannan kadai ya isheta, shine kuma abinda zatayi tunani, Mansy da komai zasu iya jira sai da safe. Hakan kuwa tayi tana lumshe idanuwanta, ko sallama batai ma Hamza ba, bacci yayi gaba da ita cike da mafarkin shi.

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.