Skip to content
Part 16 of 33 in the Series Mijin Novel by Lubna Sufyan

Tunda ya shiga gida, kayan jikin shi kawai ya sake yana saka wando iya gwiwa sai wata riga mai dogon hannu hadi da hula ruwan madara. Yaja hular yana dorata saman kan shi, tukunna ya dauki wayar shi, earpiece ya duba ya hada a jikin wayar, ya makala ma kunnuwan shi batare daya kunna komai ba, magana ce bayaso yayi da kowa, kuma akwai aikin da bayaso ya kwanar mishi, da ba zai fita falon ba. Yana karasawa ya dauki system din shi daga kan tebirin da take yana jan cajar da take hade da system din ya koma kama cikin falon in da su Fodio suke zaune suna hira.

System din ya kunna yana jira ta gama budewa gabaki daya, saiya tsinci kan shi da lulawa duniyar tunani, har lokacin yana kasa yarda da abinda ya faru.

“Appa aure zanyi, sunce in tura manya na.”

Shine maganar farko daya fara furtawa bayan sun gaisa da Appa din, sosai kuma yake karantar mamakin da yake shimfide a fuskar Appa.

“Aure?”

Appa ya jinjina maganar yana dorawa da,

“Ma shaa Allah, Allah yasa albarka, sun fadi ranar da zamuje ayi maganar?”

Kai ya tsinci kan shi da girgizawa Appa.

“Su saka mana ranar da zamuje sai ka fadamun.”

Kan ya sake jinjinawa, yana kasa furta wani abun.

“Hamza.”

Appa ya kira, duk da yana dadewa bai kira sunan shi kai tsaye haka ba, ba kunya bace ta dan fari, kawai Appa bai cika kiran sunayen mutane ba.

“Auren nan fa ba abu bane da zaka wayi gari kawai kace zakayi saboda kana da halin yi, ba kudin bane shiri, wannan yana daya daga cikin abubuwan da ake bukata, idan har a zuciyarka baka shirya ba, karka dauko yarinyar mutane, yau da gobe tafi karfin tunaninka, duk yanda za’a gaya maka aure idan bayi kayi ba sam ba zaka fahimta ba.”

Cewar Appa yana dorawa da,

“Hakurin da kakeji anayi, shi kan shi akan wayi gari a neme shi a rasa, abubuwan da suke rike da aure sunfi karfin kudi, karka sakani zuwa karbo maka amanar da ba zaka iya rikewa ba.”

Idan akwai abinda yake bata ma Appa rai bai wuce yanda ake ma aure rikon sakainar kashi ba a yanzun, kwata-kwata daga Samarin har ‘yan mata basu san mene ne auren ba sukeyin shi. Kusan ya zama gasa, wane yayi, bai kaini samun kudi ba, wane na bashi shekara biyu gashi yayi aure harda yaro, amman ni ina nan zaune. Sam suna mantawa da yanda tsarin rayuwa yake tafiya akan cikar lokaci. Sai ayi auren a kasa hakuri da yanda rashin dadi da jarabtar da take cikin shi lokutta da dama kan rinjayi jin dadin ciki. Shisa bai taba yiwa Hamza maganar yai aure ba, ko kuma ya tambaye shi yaushe zaiyi aure.

Saboda yasan ba a samun kudin abin yake ba, idan har bai shirya a zuciyar shi ba, auren zai zo mishi a baibai. Yanzun ma sai yake karantar shakku a idanuwan Hamzan, shisa yayi mishi magana, yafi so ya zamana dari bisa dari ya tabbatar da ya shirya ma auren.

“Idan har akwai wani bangare na zuciyarka da bai natsu da maganar nan ba, ka hakura Hamza. Karkai gaggawa, aure ne, lokaci yake da shi kamar mutuwa, indai an rubuta maka yin shi, zai zo ya sameka, ba saika neme shi ba.”

Numfashi Hamza ya sauke, zai kuma yi karya idan yace maganganun Appa basu taba zuciyar shi ba, zai kuma yi karya idan yace ya shirya yin aure har a zuciyar shi, abu daya kawai ya shiryama a halin yanzun, bin duk wata hanya da take karkashin ikon shi dan ganin ba’a raba shi da Hindu ba, yana son ta, tunanin rabuwa da ita na wanzar da wani irin tsoro hadi da firgici a cikin zuciyar shi, balle kuma ya hasaso ta da wani da bashi ba, kan shi har sarawa yake saboda tashin hankali.

“Na shirya Appa.”

Ya furta da muryar shi can kasan makoshi, kai Appa ya jinjina mishi.

“Allah yasa hakan ne mafi alkhairi.”

Mikewar da Appa yaga Hamza yayine yasa shi sake fadin,

“Ka gayawa Annarka ne?”

Kai Hamza ya girgiza mishi, yasan ya kamata yaje yayi ma Anna maganar, amman kuma a yanayin da yakeji, sam ba zai iya amsa duk wasu tambayoyi da yake da tabbacin Anna zata jero mishi ba.

“Akwai aikin da zan karasa Appa, gobe In shaa Allah sai in dawo in fada mata, kasan Anna.”

Murmushi Appa yayi cike da fahimta, yana sakeyi mishi addu’a, kafin ya wuce, dan yaji dadin samun Appa shi kadai a falon, shisa ya jashi bangaren shi, ta baya ya fice daga gidan. Ko gaisawa da Anna baije yayi ba, yasan Appa ba zai ce mata komai ba.

“Sai magana nake maka, Banza kawai”

Arafat ya fadi yana dukan kafadar Hamzan daya sa hannu ya zare earpiece daya daga kunnen shi.

“Shine zaka cire mun kafada? Dan ubanka baka ga earpiece bane a kunne na?”

Hamza ya karasa maganar yana kara hade fuska.

“Ina flash dina?”

Arafat ya bukata.

“Ka duba cikin jakar system dina.”

Hamza ya amsa shi yana shirin mayar da earpiece din shi.

“Jakar ka na ba flash ko kai? Ka tashi ka dauko mun.”

Kai Hamza ya jinjina, yana mayar da earpiece din shi hadi da fadin

“Ka zauna ka jirani in dauko maka.”

Kafin ya cire wayar shi daga key yana cigaba da dannawa, yanajin zagin da Arafat din yayi mishi kafin ya mike, bai damu bane ba. Lambar Hindu yake ta kira tunda ya baro wajen Appa, amman tunda tayi ringing din farko ba’a daga ba, yana sake kira a kashe yaji ta, har yanzun kuma a kashe take, yabar mata sako yakai goma, yanzun ma sakon ya sake tura mata.

“Me yasa zaki kashe wayarki? Idan caji ne ya kusan karewa me yasa baki fadamun ba? Ki kirani muyi Magana.”

Baisan me yasa ya sake binta whatsapp yana tura mata.

“Kina ina wai?”

Tunda yaji wayar a kashe, tick daya dayaga sakon yayi alamar baije mata ba yasa shi jan karamin tsakin da yayi shi babu a dadi a cikin yan dakikan daya kirata zuwa tura sakonnin. Earpiece din ya zare yana ajiye su tare da wayar akan system din shi, kafin ya dafe fuskar shi da hannuwa yana fitar da wani numfashi mai nauyi, sannan ya sauke hannuwan, bayan shi ya jingina da kujerar falon, da wani nisantaccen yanayi a muryarshi yace.

“Aure zanyi.”

Coke din da Fodio yake zuka da straw yaji ta bi mishi ta wata kafar daban, kafin ya soma tarin da yasa shi sake zukar wata coke din ko zai samu kafofin iskar shi da suka toshe su bude, Arafat kuwa fasa makala flash din da yake shirin yi a jikin system yayi yana dago idanuwa ya kafe a kan Hamza, bakin shi yaki rufuwa cikin tsananin mamaki. AbdulHafiz da yake zaune kan kujera bayan Hamza sai da ya gyara zaman shi ya miko hannu yana taba fuskar Hamzan daya doke hannun AbdulHafiz din.

“Lafiyar shi kalau?”

Fodio ya tambaya yana cigaba da tari, kai Arafat yake girgiza.

“Haba Fodio, ya maka kama da mai lafiya? Bakaji me yace ba? Ko ni kadai naji? Dan Allah kuma kuce mun kunji.”

Kai AbdulHafiz yake jinjina ma Arafat.

“Bakai kadai ba, nima naji.”

Numfashi Hamza ya sauke, ya tsammaci fiye da abinda sukeyi yanzun, shi kanshi bai gama mamaki ba, ballantana kuma su.

“Ina zaune fa.”

Ya furta ganin yanda su Fodio suke maganar shi kamar baya wajen.

“Da gaske aure zanyi.”

Ya fadi yana kallon Fodio daya sake zukar coke din shi yana hadiyewa.

“Dan Allah ka daina wannan wasan mana.”

Kai Hamza ya girgiza mishi.

“Wallahi ba wasa nake ba.”

Wannan karin AbdulHafiz ne yace.

“Wai da gaske kakeyi?”

Yasan sunyi maganar Hindu da shi.

“Ka manta abinda kace mun?”

Hamzan ya tambayi AbdulHafiz cikin yaren fulatanci, yana saka Fodio daukar filon kujerar da yake gefen shi ya jefa mishi.

“Uban me kace mishi?”

Ya tsani Hamzan yayi ma AbdulHafiz fulatanci, dan ma da yawan lokutta AbdulHafiz baya mayar mishi, sai dai ya bashi amsa da Hausa, kuma Hamzan mantawa yakeyi tunda AbdulHafiz yana ji, shikuma inba da su ba, sai kuma mutane, amman indai yana cikin gida yare suke.

“Shine yake nufin me? Zakayi aure?”

AbdulHafiz ya bukata cikin harshen Hausa, Hamza bai juya ba, amman yanajin idanuwan AbdulHafiz din na yawo a bayan kan shi, kamar suna neman hanya su leka ciki suga duk wani abu da yake boyewa.

“Ku daina yi kamar kunsa ran bazan taba yin aure a duniya ba…”

Hamza ya fadi yana mikewa, so yake ya fada musu daman ko zaiji maganar ta daina tokare mishi makoshi. Amman yanda sukeyi na kara mishi shakku, yasan bai shirya ba, suna kara nuna mishi yanda bai shirya din ba da gaske, system din shi da waya ya dauka yana wucewa daki yabar su anan. AbdulHafiz na bin shi da kallon da yake cike da alkawarin cewar basu gama maganar ba, tunda bai bashi amsar tambayar da yayi mishi ba. Dan yace karya taba Hindu, baya nufin yace mishi ya aureta dan kawai ya tabata.

Wani irin shiru ne ya biyo bayan tashin Hamzan, kafin Arafat ya kore shi da maganar kwallon kafar Laliga ta shekarar, kafin suci gaba da hirar suna aikin su. AbdulHafiz ya fara tattara kayan shi wajen sha biyun dare yana wucewa daki. Idanuwan shi yake jin yana dagawa da kyar saboda baccin da yake cikin su. Yana kai wayoyin shi da system ya ajiye a daki, ya zauna gefen gado, wayar Hamza ya kira daya daga a bugun farko.

“Ka shigo muyi Magana.”

Ya furta yana kashe wayar, yana kokarin ganin bai shiga dakin Hamzan ba, dan karya ga abinda zai bata mishi rai. Ko mintina biyar ba’a yi ba, Hamzan ya shigo dakin yana tsayawa bakin kofa.

“Karka tambayeni me yasa zan aureta, karka cemun ban shirya ba AbdulHafiz na sani, ita kanta ban shirya zan so taba, ka kalleni yanzun.”

Kallon nashi AbdulHafiz yakeyi.

“Kayi istikhara, karka kara wani abu akan maganar nan baka nemi zabin Allah ba.”

Kai Hamzan ya jinjina mishi, alwala ya dauro daman, zai saka dogon wando ne AbdulHafiz din ya kira. Sallah yake so yayi ko raka’a hudu ce, tunda har lokacin yana kiran wayar Hindu amman a kashe yake jinta. Batare da yace komai ba ya kama hannun kofar ya murda yana janta ya bude.

“Kar sha’awa ta zama jigon yin auren ka Hamza.”

Cewar AbdulHafiz din, ficewa daga dakin Hamza ya yi yana ja mishi kofa. Koma mene ne jigon yin auren bashi da wani muhimmanci tunda ba zai hana ba.

*

Da zazzabi ta tashi da safe, da kyar ta iya shan ruwan shayi, tukunna ta hadiyi panadol. Anty ma sai da tace ta hakura da zuwa makaranta, tace mata test zatayi, tana gamawa zata dawo gida, ba wani abu bane ya ke damunta, bacci ne. Kuma tasan kukan da tayi ne yasa mata zazzabi, sunyi waya da Dimples, ta kira zata tambayeta wani film taji tana kuka, duk da ta fada mata Hamza ne, bata dai gaya mata ga dalili ba kawai.

“Tun baki aure shi ba harya fara sakaki kuka? Hindu anya wannan mijin aure ne kuwa? Bai sameki bama bai san ya lallabaki ba, me zai faru idan ya sameki?”

Bata samu amsar da ta bata ba, tadai tsinci kanta da kin dagawa daya kirata, gabaki daya wayar ma a kashe take tun jiyan. Ta dai sakata a caji ta cika, ta zare ta jefa a jakarta. Tayi kwalliya sosai dan ta boye yanayin da yake kan fuskarta. Tun jiya bata ko gwada yima kanta karya ba, ba zata iya rabuwa da Hamza ba in dai hakan ya zama zabinta. Abu daya ne zai faru, ya gama tabata bai aureta ba, dole ya jira, ko kuma batasan me zai iya faruwa ba idan yaki, hango rabuwa dashi bata cikin tsarin abubuwan da suke zuciyarta.

Iya jiya ta tabbatar da Hamza ya zama bangare na rayuwarta, kuma tasha ganin jarumai na canza halayen wanda suke soyayya dasu, daga film har a littafi, ko a korean films, cikin Secret garden ma yar talakawa ce fitik, dan da gani ma yake yafi karfin ya yi soyayya da ita, sai gashi zance yasha banban, rabuwa yayi da mahaifiyar shi akan yarinyar, sukai auren su harda yara uku, a cikin The Heirs ma sai da soyayyar yarinyar tasa azzalumin film din yayi laushi tubus, tana da yakinin idan ta dage tsaf zata sakewa Hamza hali, balle taga soyayyarta a cikin idanuwan shi.

Da wannan tunanin ta tashi, har addu’a tayi a sujjada Allah ya bata karfin gwiwar yin wannan jahadin, dan rabashi da neman mata idan tayi nasara ba karamin jihadi bane ba.

“Zan canzaka Hamza, soyayyata zata canza ka.”

Take fadi tana kara maimaitawa a cikin kanta harta fito daga gida, tana mike hanyar da zatayi kwana ta nufi makaranta. Tana shan kwanar kuwa tana ganin motar Hamza daya taka wani irin burki yana sauka gefen hanya ta dayan bangaren, zuciyarta takeji tana wani irin tsalle, da alama ko motar bai kashe ba ya fito yana zagayowa ya tsallako inda take, tun kafin yayo gab da ita take ganin tsantsar rikicin da yake shimfide a fuskar shi da tayi mata wani irin kyau, sportswear ne a jikin shi, riga da wando bakake

“Me yasa zaki kashe wayar ki?”

Ya tambaya yana dorawa da,

“Kinsan aikin da na ajiye na taho? Saboda kin kashe wayar ki?”

Cikin idanuwa take kallon shi

“Ai bance ka ajiye ba, ban kuma ce ka zo ba.”

Numfashi ya sauke, yanajin wani abu na tsirga mishi daga tafin kafar shi zuwa tsakiyar kan shi, kallonta yake yi, komai nata yayi mishi, kamar yanda ita da kanta din tayi mishi.

“Kinyi kyau.”

Ya tsinci kan shi da furtawa, yanajin yanda duk wata masifa daya kwaso ta bace mishi, tun da asuba yake kiran wayarta a kashe. Har sun fita wajen aiki tun karfe bakwai, ya kasa zama ya taho ya dubata.

“Ni makaranta zanje.”

Cewar Hindu da takejin ganin shi ya taso mata da tukukin kishin duk wasu yan mata da ya kasance da su.

“Hindu.”

Ya kira cike da kashedi, yana runtsa idanuwan shi ya bude su a kanta.

“Karki batamun rai fiye da yanda yake a bace, ki kunna wayarki. Kizo in sauke ki sai in koma wajen aiki.”

Kai ta girgiza mishi.

“Kaje abinka zan karasa.”

Kafin ta sake magana ya kama hannunta yayi mata rikon da batayi tunanin kwacewa ba, ya jata suka tsallaka dayan bangaren.

“Ka sakar mun hannu, wallahi ka sakeni.”

Take fadi cike da masifar da Hamza baibi ta kai ba, ya bude murfin motar.

“Zaki shiga da kanki ko in dauke ki in saka?”

Ya tambaya yana tsareta da idanuwa, dariya tayi me sautin da bashi da alaka da nishadi.

“Karki gwadani Hindu, zaki sha mamaki wallahi.”

Ganin da gaske babu alamar wasa a fuskar shi yasa ta fisge hannunta tana shiga motar ta zauna, dan tsilli-tsillin mutane na wucewa.

“Na gode.”

Hamza ya fadi yana rufe murfin motar, ya zagaya ya shiga shima, yaja motar yana samu yayi kwana dan ya fita titi.

“Ya kika tashi?”

Ya bukata.

“Lafiya.”

Ta amsa a takaice, kai ya jinjina hadi da sauke numfashi.

“Ba zaki tambayi ya na tashi ba?”

Shiru tayi ta kyale shi.

“Nai ta kiranki jiya, nayi magana da Appa azo a tambayar mun auren ki.”

Zuciyarta taji tayi wani irin tsalle kamar zata bar kirjinta, da sauri ta kalli Hamza, wani murmushi da bata sani ba ya kwace mata, tun ba’aje ko ina ba, ta dauka akwai aiki shimfide a gabanta kafin ta canza shi, kafin suzo wajen nan, amman kashe wayarta tayi na rana daya gashi ya rikice har yana maganar aurenta, ina ma zata ga wanda suke karyata faruwar rayuwar cikin litattafai, tayi musu misali da kanta.

“Shine yace daga gidan ku za’a fadi ranar da za’a zo.”

Dan gyaran murya tayi, tana kokarin boye tsantsar farin cikin da take ciki.

“Ni nace ina so in aure ka bayan jiya?”

Dariya Hamza ya danyi

“Ni ina so in aure ki, ya ishe mu.”

Harar shi tayi, tana saka shi karayin dariya, yanda take da karfin bata mishi rai ta kuma batar da shi cikin kankanin lokaci na bashi mamaki. Hira yake janta da ita har suka karasa makaranta, duk da tana ta kokarin share shi kamar tana fushi har lokacin, bayan ya gama wanke mata duk wani bacin rai da ya yi sanadi.

“In dawo muje muci abinci da rana?”

Ya bukata, kai ta girgiza mi shi.

“Ina yin test din nan gida zan koma inyi bacci, sai dai gobe.”

Shagwabe mata fuska Hamza ya yi.

“Dan Allah, bansan ko zan samu in ganki anjima ba…”

Numfashi ta sauke.

“Karki ce mun a’a.”

Kai ta tsinci kanta da jinjina mishi, yako yi mata kyauta da wani rantsatsen murmushi da taji har kasan zuciyarta, kafin suyi sallama tana wucewa aji. Da wani irin nishadi take duk wata hidima ta ranar, tana jin yanda data koma zatayi wa Anty maganar dan ta fadama Baba a saka masu Hamza ranar da zasu zo. Da zata samu ma a saka lokacin bikin daya dana Khadee, tunda ita gidan mijin sunzo sun roki alfarmar a kara musu wata biyu, bai karasa ginin da yakeyi ba, saura fenti, tayal da kuma wayarin din wuta. Baba bai yi musu ba, ya yi gini, ya kuma san wahala da kashe kudin da yake cikin hakan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 7

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mijin Novel 15Mijin Novel 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×